Showing 114001 words to 117000 words out of 178785 words
damuba ta nufi kitchen ɗakko musu ruwa dan ba yau ta saba da halinsu ba tunda sanda tana can gidan su Fadwa ɗin ma suna zuwa babu kalar wulaƙancin da basa gani su masu aiki a wajensu su a dole ƙanen masu gida (Karku manta suma ƙanen uba suke ga Fadwa, kuma ƙanen uwa ga Shareff).
“Baki da lafiya ne?”.
Aunty Sakina ta faɗa idonta fas akan Fadwa. Kanta ta girgiza mata kawai. Baki aunty Sakinar ta taɓe. Hajiya Luba ta karɓe da faɗin, “Ciwo ya wuce baƙin cikin miji da kishiya mai kama da karuwai, k yanzu nan Fadwa har waccan ƴar tsefatar yarinyar ce zata razanaki ki koma haka firingau-firingau ido luhu-luhu. Kuka kenan kika zauna kinayi kamar wata sakara?”.
Hawayen da taketa riƙewa ne suka silalo mata. Aunty Sakina da Hajiya Luba suka ɗauki sallallami da tafi kamar waɗanda sukai gamo. Ita dai Fadwa kanta a ƙasa tana hawayenta.
“A to wlhy aiki ya ganki kuwa, yima kishiya kuka. Kishiyarma wadda bata wuci a sati ki kaɗa shegiya ba tabar gidan saboda ke ɗin shashashar ce kika zauna kinamata kuka. To bara kiji, idan zaki dawo cikin hankalinki ki dawo, a duk zuri'armu babu sakarai. Balle ke da mijin nan naki tako ina jininki ne, da ubansa da uwarki uwarsu ɗaya ubansu ɗaya, da ubanki da uwarsa iyayensu uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Gaba da baya aka tsaga jikinku jini iri ɗaya za'a gani, itako fa miye haɗinsa da ita banda ɗiyar ɗan uban ubansa, dalla malama sharemin waɗan nan banzayen hawayen ki tashi ki rakamu sashen shegiyar”.
Hawayen Fadwa ta share, sai dai kuma tuna yana gidan yasa ta kasa tashi. “Aunty yana nan fa a gida”.
“Shi wa ɗin?”.
Cewar Hajiya Luba.
“Shareff! Yau bai fita aiki ba wai hutu ya ɗauka harna sati ɗaya”. Ta ƙare faɗa da rushewa da kuka tabbacin abinda ke cin zuciyarta kenan tun ɗazun.
Cikin riƙe baki Aunty Sakina tace, “Iyee wato sati guda, amma uwarsa nacan ko sau ɗaya baije ya gaisheta ba. Shiko dai Al-Mustapha yayi asara. Aini namaji daɗin samun nasa a gidan zanfi jin daɗin cin uban shegiyar yarinyar a gaban nasa sallamamme kawai. Tashi muje ki kaimu, kuma karna sake ganin waɗan nan hawayen banzar kema shashasha”.
Anaam na kwance cikin kujera tana buga game suka faɗo mata ko sallama babu. Da farko tayi kamar ta share dan Fadwa ce ta fara shigowa, sai dai ganin su Aunty Sakina ya sa ta tashi zaune tana danne sosuwar da zuciyarta tayi akan shigo mata kai tsaye da sukai. Ta san aunty Sakina dan sun taɓa zuwa gidanta ita da Aysha. Daga Hajiya Luba har aunty Sakina bin falon suke da kallo baki a taɓe, sai dai acan ƙasan ransu razani ne na gaske, dan ko makaho ya shigo ya laluba yasan annunama duniya yariyar ƴar gata ce.....
Cigaba da game ɗinta tai domin basu dama su gama kalle-kallen, saiko da sukai iya iyawa sannan suka juyo gareta.
“Oh lallai, ga ƴan iska sun shigo ko?”.
Aunty Sakina ta faɗa murya a sama. A karan farko Anaam ta saki murmushi, ta ɗago idanunta dake cikin gilashi tana kallonsu, cikin hausarta dabai gama nuna ba ta gaishesu kamarma bata fahimci harzuƙowar aunty Sakinar ba..
“Uhm lallai kam Shareff ka amshi ruwan dafa kanka. Wato k a dole ƴar bariki”.
Sarai ta fahimci abinda Hajiya Luban ta faɗa, dan kuwa zuwa yanzu Alhmdllhi hausa ta fara zauna mata a brain da harshe da ƙyau saɓanin farkon zuwanta. Amma sai tai kamar bata fahimci komai ba, fuskarta da murmushi ta miƙe tana faɗin, “Aunty ku zauna Please bara na kawo muku ruwa”. Bata jira cewarsu ba ta nufi kitchen.
“Babbar b*r* uba kai. Wai wannan yarinyar tana nufin bama tajin mi muke faɗa ko mi?”.
Fadwa da batace komaiba tun shigowarsu tana kuma daga tsaye dan bata zauna ba tace, “Hummm! Tana jin komai sarai iskanci ne kawai fa Aunty. Ni dama kun barta dan ALLAH kawai....”
Harara Hajiya Luba ta zuba mata. Shigowar Shareff a bazata ta saka Fadwa haɗiye abinda zata faɗa babu shiri da risinar da kanta ƙasa, wani yawu mai kauri ya wuce muƙut a maƙoshinta ƙirjinta na bugawa.
Idanunsa ya janye a kanta da ƙarasowa cikin falon hannayensa duk biyu a cikin aljihun wandonsa.
“Oh dama kana gidan?”.
Aunty Sakina ta faɗa tana hararsa.
Duk da sarai ya jita sai bai amsa ba, sai da yakai zaune cikin kujera da ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya sannan ya dubesu. “Barkanku da safiya aunty kune a gidan namu?”.
Sosai ransu ya sosu da salon rainin wayonsa su duka. Sai dai kafin wani yace wani abu a cikinsu Anaam ta fito ɗauke da tray shaƙe da kayan ciye-ciye da ruwa da lemo. Itama dai ta ɗanji wani iri na ganin nasa, amma saita fiske abinta ta ajiye tray ɗin a gabansu tana murmushi. “Aunty ga ruwa to....”
A matuƙar harziƙe Hajiya Luba ta tura tray ɗin da ƙafarta tana ballama Anaam harara. “Tunda shine ya kawomu ba, k ki kama kanki wadda ta haifeki ma a tafin hanunmu take balle ke kanki...”
“Juwairiyya bani lap-top dana bari a ɗakinki”. Shareff ya katse hargowar Hajiya Luba tamkar bai ji mima take faɗa ba. Tsamm Anaam ta miƙe batare da tace uffan ba, ba kuma ta kalli sashen da Shareff ɗin yake ba balle Fadwa ta ɗauka wayarta ta wuce bedroom.
“Oh ke ko ga mahaukata suna magana dole ka sata aika. K! Fadwa shaƙomin ƴar iskar yarinyar can na nuna mata wacece ni dan ubanta”.
Muƙutt Fadwa ta haɗiyi yawu da ƙyar a karo na biyu domin jin umarnin Aunty Sakina tamkar saukar aradu bisa kai. Ta ɗan saci kallon inda Shareff ke zaune a harɗe har yanzu kai kace baima san wainar da ake toyawa a falon ba. Kanta ta girgiza a hankali, so take tayi magana amma ta kasa motsa lips ɗinta sai kawai ta juya da sauri ta bar falon ma gaba ɗaya. (Tabbas Fadwa nada kurari da hayaƙi, amma kuma tanada tsoro bata cika iya jure hatsaniyar faɗa ba. Idan mai karatu bai manta ba kokuma ya lura da ƙyau zai fahimci Anaam ta fita tsiwa, saboda a lokuta da dama takan takaleta faɗa amma a ƙarshe Anaam ɗin ke tsigeta itako sai tai laƙwas. Tabbas a cikin raunanan halayanta wannan yana ciki rashin juriyar hatsaniya, a wani fannin kuma zamu iya kiransa haƙuri😜).
Daga aunty Sakina har Hajiya Luba baki suka saki uwa sakatar sakarai dan al'ajabin Fadwa. “Oh ni Sakina ato lallai Fadwa kema kin cika asararriyar yarinya, to kodai ba Al-Mustapha ɗin kawai aka shanye ba harda ke ɗin kema?”.
Maimakon samun amsa daga Fadwa data fice sai Hajiya Luba ce ta amsawa Aunty Sakinar. “A to ga halama kin gani kuwa Sakina. Ƙanƙanuwar yarinya ke juya gida miji da kishiya duka a tafin hanunta.”
Ƙololuwar ɓacin rai kam Aunty Sakina takai, musamman biris da su da Shareff yayi. Tsabar wulaƙanci ma sai latsa wayarsa yake yana ɗan girgiza ƙafarsa da yay crossing. Anaam dake danne dariyarta da jinjina tsaurin idon mutumin nan ta ƙaraso ɗauke da lap-top ɗin a hannu. Gabansa gab ta matsa, ta miƙa masa harda takardun data haɗo da su. Idanunsa dake akan wayar ya ɗago yana kallonta, ta ɗan tura baki gaba tana son dangwarar da kayan bisa cinyarsa ya riƙo hanunta. Fuska ta ɗan narke da ƙyaƙyƙyafta idanu tai ƙoƙarin janye hanunta.........✍
_ZAFAFA BIYAR_
*_INAYAH_*
_MamuhGee_
*_GURBIN IDO_*
_Safiya Huguma_
*_SANADIN LABARINA_*
_Hafsat Rano_
*_FARHATAL QALB_*
_(Miss Xoxo)_
*_BABU SO_*
_Billyn Abdul_
_*Littafi daya 300*_
*_Littafi biyu 400_*
*_Littafi uku 500_*
*_Littafi hudu 700_*
*_Littafi biyar 1k_*
YADDA ZAKU BIYA KUDIN BOOKS👇🏾👇🏾👇🏾
ZENITH BANK
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
SEKU TURA SHEDAR BIYA TA:
07040727902
IDAN KUMA KATI NE SEKU TURAWA👇
09134848107
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻_*
[11/23, 10:16 PM] My Zafafa: *_Typing📲_*
*_❤🔥BABU SO....!!❤🔥_*
_(Miya kawo kishi?)_
*_Bilyn Abdull ce🤙🏻_*
*_BABU SO👉🏻AREWABOOKS_*
https://arewabooks.com/book?id=63447a616580db4ec203d718
*_54_*
.........Ƙara riƙo hanun yay da ƙyau idanunsa masu kaifi na saukar mata da kasalar data mantar da ita wanzuwar su aunty Sakina a falon. Dama haka yake buƙata, ta manta da wanzuwar tasu ya samu damar isar da gargaɗinsa garesu batare daya samu wani tangarda daga gareta ba.
“Dama haka ake bama miji abu?”.
Ya faɗi maganar a salon daya nema ɗauke numfashin Anaam na wucin gadi, dan muryar da yay mata magana da ita muryace da zata iya rantsuwa bata taɓa ji daga garesa ba. Da ƙyar ta iya ƙwato kanta, tai ƙoƙarin ajiye masa kayan a hanun kujerar da janye nata idanun daya sargafe a nasa dan ta gama yanke shawarar barin wajen kafin a samu matsala yaga rauninta. Tana daga kafa ya riƙo hanunta tare da jawota sai gata ɗaram a cinyarsa tamkar walƙiya. Kafin tunanin wani abu ya risketa har ya yimata zobe da hanunsa ta hanyar ɗorawa a saman cikinta ya manne bayanta da ƙirjinsa kansa bisa wuyanta yana shinshina da fara magana cikin kunenta da wani salon daya saka tsigar jikinta tashi.. “A haka ake bama miji abu ba'a tsaye ba”.
Saukar wata mulmulalliyar ashariya cikin kunnuwansu ta tilastata ƙanƙamesa babu shiri dan da gaske ta tsorata dama gata a tsakkiyar wani firgicin. Harga ALLAH ta manta da su a falon, saɓanin shi da duk abinda yakeyi domin su ɗinne dama. A firgice ta ɗaga ido zata kallesu ya hana hakan, dan kuwa hanunsa ya tura cikin rigarta sai dai akan cikinta ya tsaya.. Ɗan matsawar da yay ta sata saki ƙarar ruɗewa dan a bazata abin yazo mata kuma taji zafi......
Rige-rigen fita aka farayi tsakanin Hajiya Luba da Aunty Sakina, saboda ƙarar Anaam ɗin fassara daban suka bata. Aunty Sakina ma harda gwara kai a jikin garu lokacin da suke turereniyar ficewa.
Hanunsa da taketa faman kaima mintsini ya janye, ta mike zumbur daga cinyar tasa idanunta taf kunya. Riƙota ya sake yi fuskarsa ɗauke da murmushin ƙeta. “Malama nace na gama n....”
Hararar data wulla masa ce ta hanashi ƙarasa faɗa ya saki dariyar data ƙara ƙular da ita tana jin zafinsa har cikin maƙoshinta. Sake fisgota yay ta dawo saman cinyar tasa. Ya haɗe hannayenta duk biyu dake son turesa ya danne akan cikinta. “Idan idanunki suka cigaba da harararta daga yau sai na miki haɗiyar ɗan sululu a gidan nan fitsararriya”. Mutsu-mutsunta ta cigaba dayi na son ƙwacewa yaƙi bata dama. Saima lanƙwansota yay ta kwano jikinsa ya kai goshinsa kan nata ya haɗe. Yawu ta fara kokawar haɗiyewa da sauri-sauri ganin yana daidaita lips ɗinsu.
“Please Yaya dan ALLAH kar kayi bana so”.
Gira ya ɗaga mata da kashe ido ɗaya, “Fitinanniyar yarinya minace zanyi to?”.
Bakinta da take faman karewa da hannu tatura gaba da ƙoƙarin kauda fuskarta ya tare da hannunsa, tare da janye nata hanun ya manne lips ɗinsu. So take ta turesa, amma tasirin abinda yake matan a cikin jini yana barazanar hanata kowanne irin yunƙuri, daɗin daɗawa ya riƙe hanunta ta yanda bazata iya ko motsashi ba. A karon farko ta fara maida masa murtani a yau dan tasirin salon nasa jinin jikinta ya fara amsarsa da ƙarfin gwiwa da wani sirrin ɓoye dake can ƙasan zuciyarta da ita kanta har yanzu bata san da zamansa ba tattare da ita. Hakan tamkar ƙara zugane a garesa da dukkan haƙurinsa, dan kai tsaye zuciyarsa ta fara ingizasa ga kaiwa inda bai gama shirya kai kansa ba. Ring na wayarsa ne ya dawo dasu duniyar da suka jima da yin nisan barin cikinta da lissafi irin na masu hankali. Sakinta yay, zaram ta miƙe kamar wadda take a tsinin allura. Da sassarfa ta bar falon ko waiwayensa taƙi tayi. Da kallo ya bita yana sakin kakkauran numfashi da murmushi, a hankali yakai bayansa jikin makarin kujera ya kwantar yana mai lumshe idanunsa da sake sakin ajiyar zuciya a jajjere yana kai hanunsa ya shapo lips ɗinsa....
Tun fitowarsu take faman kaikawo a harabar gidan, dan ko sashen Fadwar sun gagara komawa tsabar mamaki da jinjina ƙwarewar iskancin Shareff ɗin a yau. Yaron da ko ido bai cika ɗagawa ya kalla mutane ba shine yay musu wannan baƙin iskancin. Ina bazata iya haƙuri har sai sunje gida ba, dole ne ta kira Mommy kam ai. Takai wayar kunenta tana faman kaɗa ƙafafu da jijjiga jiki na tsantsar bala'i. Cikin sa'a aka ɗaga mata gab da zata tsinke.
“Sakina har kun isa gidanne?”.
Mommy ta faɗa tunkan aunty Sakinar tace wani abu. Aiko cikin matuƙar ɗacin murya ta tare numfashin Mommy din da faɗin, “A dole Mustapha kam yafi karfinki wlhy Yaya Nafi! Dan tabbas babu makawa an wanke an basa ya sha.”
Ƙirjin Mommy ya buga da ƙarfi, sai dai kafin tace wani abu Aunty Sakina ta cigaba da bata labarin abinda ya faru yanzu-yanzun nan. Ta ƙare da faɗin, “Zama dai kam bai gammu ba dan wannan yarinyar tafi uwarta hatsabibanci. Nan gaba babu makawa zaima iya cewa kwanciyar aure zaiyi da ita a gabanki saboda ya tabbatarma duniya shi ɗin tantirine na gask......” Ƙitt!! Wayar ta yanke. Tai saurin cirota a kunenta tana kallo a tunaninta ko kuɗine suka ƙare. Ƙoƙarin siya tai ta banki ta ƙara kiran Mommy ɗin. Sai dai kuma number busy ake nuna mata alamar waya take ko kiran wani.....
Ring ɗin wayarsa ne ya sake sashi buɗe idanunsa da har yanzu ke'a rufe. Ya kafe fuskar wayar da kallo tamkar mai tsoron ɗauka ganin sunan First Luv ruƙu-ruƙu na yawo. Rabon da suyi koda waya ne harya manta, ya kuma tabbatar gargaɗin da yayma su Aunty Sakina ya risketa ne matsayin saƙo. Bazai iya ƙin ɗaga kiranta ba koda yana jin tsoron dukkan wani furuci daga bakinta, kimarta da girmanta sun wuce a musalta a cikin idanunsa da zuciyarsa. Hannu ya kai ya ɗaga tana gab da tsinkewa, yakai kunen nasa cikin ƙarfafa kai....
“First luv barka da safiya”.
“First ubanka ba first luv ba. Al-Mustapha wlhy ina gab da jamaka kalmar ALLAH ya i.....”
“Please First luv, abeg kar kice haka dan girman ALLAH.”
“Idan ka sake kirana da sunannan ALLAH sai naci ubanka. Kuma kazo ina nemanka idan ba hakaba ka bari na tako ƙafata gidanka da kaina yarinyar nan na a ciki wlhy wlhy wlhy kadaiji na rantse ko! Sai na jamaka ALLAH ya isa da manyan baƙi no-no na daka sha dan bakai kaɗai na haifa ba balle ka ɗauramin hawan jini”.
Harshensa har sarƙewa yake wajen faɗin, “Shi... Shike nan naji zanyi, zan zo, amma kimun alfarma Mommy dan ALLAH sai gob.......”
“Alfarma ubanka, Al-Mustapha ni kake son tozartawa a idon maƙiyana dai ko? Kana nunama duniya mace ta fini daraja da kima a idonka?”. Ta faɗa tana fashe masa da kuka. Idanunsa ya rumtse da ƙarfi, ya girgiza kai tamkar yana a gabanta. “Mommy wlhy babu wata mace da darajarta zata ko kama ƙafarki a wajena. Dan ALLAH ki fahimceni Mommy ina a tsaka mai wuya......”
A fusace ta yunƙuro zatai magana Gwaggo ta fisge wayar. “Nafisa wai kin rasa hankalinki ne halan?! A tunaninki wannan butsutsun naki akan Mustapha shine mafita ta ƙarshe da zakibi wajen raba auren?!!......”
Wata wawuyar ajiyar zuciya ya sauke da lumshe idanunsa ya saki wayar a jikinsa batare daya ƙarasa jin abinda Gwaggon ke faɗa ba. Dan kuwa tabbas a wannan gaɓar ta taimakesa taimako irin wanda bakinsa bazai iya maimaita faɗa ba, sosai al'amarin Mommy ke daɗa tayar masa da hankali, ya rasa ta inda zai kama domin shawo kanta akan wannan aure. Har yanzu yarasa gane minene takamaimai laifin su Abie a gareta da take musu irin wannan ƙiyayyar (Niko nace Shareff a haka ta tashi, tun tana ƙaramarta an riga an cusa mata ƙinsu. Haka ɗan adam yake, a duk lokacin daka koyar da shi wani abu ƙyaƙyƙyawa ko mummuna yakanzo ya fika iyawa. Iyaye tabbas muna kuskure, kuskuren da shike saka ƴan ubanci a zukatan ƴaƴanmu tsakaninsu da ƴan uwansu. A kullum baki da aiki saina aibanta kishiyarki gaban ƴaƴanki, baki da aiki sai na zaginta da nuna cutarki take zaluntarki take bata sonki, bata ƙaunarki, maƙiyarki ce kuma a gaban ƴaƴanki. Tayaya kike tunanin bazasu tsaneta su tsani ƴaƴanta fiye da yanda kike tsanarta ba, saboda ke ra'ayin ƙinta ya shigekine da girmanki da hankalinki, idan kin so zaki iya yaƙarsa, suko kin raini zukatansu ne akan wannan ƙiyayyar, dolene su dawwama da ƙinta da ƙin duk wani abinda ya shafeta koda bata aikata musu komai ba na ƙi ɗin. ALLAH ka gafarta mana ka gana damu gaskiya koda bazata mana daɗi ko zuwa dai-dai da son zukatanmu ba).
Anan falon yabar lap-top ɗin da takardun ya fice, koda ya fito su Aunty Samira sun wuce dan baiga motarsu ba. Motar ya shiga shima ya fita a gidan, dan yana buƙatar yin nesa da su har zuciyarsa ta huce. Haka yake baya son yanke hukunci cikin fushi, ya gwammaci yin nesa da abu a duk lokacin da zuciyarsa ta harzuƙa. Asibiti ya nufa wajen Dr Jamal, sai da ya shigo cikin asibitin sannan ya kira wayarsa..
Daga can Dr Jamal yace, “Ka shigo mana, ni kaɗaine ma a office”.
Ƴar ƙaramar ajiyar zuciya ya ɗan sauke da yanke wayar, bai cika san buɗe cikinsa ga kowa ba. Amma dai mutane biyunnan sun wuce abokai kawai a garesa aminaine na gaskiya. Daga Dr Jamal har Fharhan abokansa ne tunna ƙuruciya, koda yabar ƙasar kuma basu yarda juna ba. Basu da abokin shawara sama da shi, duk da shi yakan jima basuji nasa cikin ba saboda yanada zurfin ciki matuƙa. Na ukunsu kuwa shine Khaleel, duk da kasancewarsa ƙani a garesa hankalin yaron da nutsuwarsa kansa ya kallesa tamkar aboki, sannan shima Khaleel ɗin bashi