Showing 237001 words to 240000 words out of 257722 words

Chapter 80 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

Aunty Farida yace "Aunty ko dai kawai ta dauko kayanta ku tafi" Aunty Farida tace "Ai babu inda zata je sai tayi kwanakin da aka ce tayi a gidan nan tunda gidan kanwar Babanta ce" kiris ya rage Ajay bai yi dariya ba a front seat yana kallon Khaleesat, bakin ciki kamar ya kashe Nenne don Khaleesah ta gama kunyatasu gaban surkai, Jay ya bude driver seat ya sauka ya nufeta, tana ganinsa ta bar wajen da sauri alamar bata ma son jin abinda zai ce mata kuma bata fasa rusa kukan da take ba, Nenne ta kalli Ajay cikin sanyin murya tace "Kaga mu yarinyar nan zata kunyata ta tona mana asiri a unguwan mutane ko? Gudun wancan yaron Awdul ya sa fa nace ta zauna nan ko na sati biyu ne shi ne take mana wannan tijara haka kamar mun ajiyeta wajen yankan kai" Ajay dai yayi murmushi kawai ya bude motar ya sauka ya koma driver seat ya zauna, da su Nenne basa wajen tsaf babu abinda zai hanasa korata da dorinar gaban motar, ya danna ma Jay horn alamar ya shigo su wuce, Nenne tace "Madallah, gwara ya kyaleta da halinta ya shigo mu wuce don ba sauraronsa zata yi ba" Da kyar Aunty Murja ta shiga cikin gida da Khaleesat, Jay ya dawo ya bude front seat ya shiga, Nenne tace "Mu bamu san har yanxu bata dena wannan shagwabar ba wallahi, ko kanninta basa mana wannan iskancin mu dai" Duk bayan sati hudu zuwa shidda ake shirya meeting a fadan dake bangaren sarki, wanda kusan kowa na family din ke halartan wannan meeting din barin wa enda ke gari har ma wasu da ba gari suke ba kuma suna da sararin zuwa, tun daga jikoki, 'ya ya, kanni, yayyi, cousins da dai sauransu, akwai kuma meeting da ake yi bayan wata uku amma ba na kowa da kowa ba, duk meeting din da za ayi Mami bata taɓa halartan ko daya, don ko tana gari bata zaman meeting din, rabonta da zama ayi meeting da ita zai fi shekara goma, sai dai daga baya a gaya mata me aka yi wajen meeting din, duk aka yi mamakin ganinta a wajen ranan, shi kansa Jay was surprise seeing her at the meeting, sai da ta jira aka gama meeting lafiya sannan daga karshe tace tana da magana, Sarki na kallonta ya bata daman magana, Aunty ta gyara zama don duk tare suka shirya komai, Kai tsaye Mami ta fara magana tace "Ranka shi dade, duk da ni dai nasan bani da matsayin da za a sanar min abinda aka zartar kan Jawwad, amma dai na samu labarin har an kai kudin aurensa Kano, to ni duk wannan ba matsalata bace don yawanci duk abinda ya shafesa dama sai an zartar nake sani, to babban abun tambaya a nan shi ne haka aka je neman auren babu bincike kenan ranka shi dade?" Wata cousin sister din Mai martaba wanda duk ta girme ma matan dake zaune gun meeting din cikin fushi tace "Ki kula Fulani da sarki fa kike magana, ya kamata ki tausasa kalamanki ki kuma san abinda ke fitowa bakin ki" Mami ta wani kalleta daga sama har kasa, shi dai Mai martaba kallon Mami kawai yake, Ajay ya kalli Jay dake kallon Maminsa shi ma with shock, Mami ta ci gaba da maganarta babu yabo babu fallasa tace "To idan kuwa haka aka je neman auren yarinyar nan babu bincike ya kamata a koma ayi bincike kasan wacece kake kokarin hada ɗan ɗan uwanka aure da, ni da ya zame min dole tunda ɗa na ne shi nayi iya binciken da zan yi ban ga ta inda aure zai kullu tsakanin Jawwad da yarinyar nan ba, don kuwa shi din ba sa'an aurenta bane ta ko ina...." Bayan kusan minti daya Mai martaba yace "Fulani, no one is in the rightful place to question my decision in this palace, duk abinda na zartar hakan zai kasance in sha Allah, babu me canza hakan har ke da kike mahaifiyar Ahmad...." Mami tace "Kana nufin ka zartar da hukuncin Jawwad ya auri bazawara mara cikakken asali sannan er kananan mutane?" Tsawa Hajiya Shafa'atu da ta fara yi ma Mami magana tun farko a parlon ta sake yi mata tace "Kina cikin hayyacin ki kuwa Fulani? Shi Mai martaban kike furta ma wa ennan kalaman? Menene wannan ya same ki?" Rai bace Mami tace "In dai akan Jawwad ne baza a taɓa samuna cikin hayyacina ba, yau in uban Jawwad na da rai zai yarje ma Jawwad auren bazawara mara asali? Bazawara fa? Anya an duba ma uban Jawwad da ƙasa ta rufe ma ido kuwa? Yau don babu shi a duniya sai ayi ma ɗan sa haka?" Kowa dake zaune a fadan was speechless and shock at Mami's action banda Aunty, Mami ta ci gaba kanta tsaye babu ko shakka tace "In lamarin gaskiya ne a aura ma Junaid da ko macen auren bashi da ita har yanxu mana, sai Jawwad da kowa yasan da maganarsa da Hadiyah?" Mai martaba ya ɗan yi murmushi, abubuwa da yawa suka sa yake raga ma Mami kuma zai ci gaba da raga mata saboda abubuwan nan, bazai taɓa daukan mataki akan ta ba, with calmness yace "Ai Junaid bai kawo min ita yace yana so ba Fulani, don haka shi Jawwad din da ya ganta yace yana so shi din dai zai aureta ko ki amince ko kar ki amince, idan kuma da inda aka haramta auren bazawara a addininmu Enlighten us" Yana kai wa nan ya mike, Hajiya Shafa'atu ta fara basa hakuri cikin girmamawa tana jero masa kirari, Jay couldn't believe all what his Mami was saying, he was just shock and weak, Mai martaba na barin fadan Ajay ya mike shi ma zai fita, cikin fushi Aunty da Mami suka hada baki wajen cewa "Munafiki, me mugun nufi, duk kai ka hada wannan tuggun...." Shi dai ko kallon inda suke bai yi ba har ya fita, Mami ta ci gaba tana huci tace "Sai dai in bayan raina ne za a aura ma Jawwad bazawara wallahi, ai in an san wata ba a san wata ba" Tana kai wa nan ita da Aunty suka fice daga fadan, kuma duk wannan abun da Mami tayi bata yarda ko da wasa ta hada ido da Jay ba ko kuma ta kalli inda yake, yi ma tayi kamar bata san yana padan ba.



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
07087865788

HALYSAAH 95


Ajay ya bude kofar dakin Jay a hankali yana kallonsa, zaune ya samesa kan kujera yana danna wayarsa, karasawa cikin dakin yayi ya zauna still looking at him, shi dai Jay bai kallesa ba he was just pressing his phone, wani lokacin har mamakin karfin hali irin nasa Ajay yake yi ga dakiya da basar da duk wani situation that is a threat to him in anyway, bayan kusan minti daya Ajay yace "I think this shouldn't be something to be worried about Bruh, I guess you weren't expecting less duba da cewar baka sanar masu wacece yarinyar da kake son aure ba, sannan baka gaya masu matsayinta ba so their reaction is nothing to be surprised or worry about, even our dad was a bit disappointed at first after finding out truth, so sauran ma duk za su yi give up su hakura daga karshe, just that you have to turn deaf ear since the king is fully in support of you" Shi dai Jay bai ce komai ba kuma bai ɗago kansa ba, mikewa Ajay yayi yace "Abba yace kaje yana jiran ka..." Daga haka ya juya zai fita daga dakin sai kuma ya karasa gaban mirror dake dakin ya dau turarensa biyu da Jay ya ajiye wajen, ta madubi yaga Jay na kallonsa, Ajay ya bude turarurrukan yana perceiving kamshinsu yace "Why will you hijack my birthday gift..." Shi dai Jay bai ce masa komai ba, Ajay ya dau wanda kamshinsa yayi masa ya bar masa dayan sannan ya fita daga dakin. Jay na zaune gaban Mai martaba idonsa a kasa yana sauraronsa, Mai martaba yace "Don haka ka kwantar da hankalin ka Ahmad, babu me hanaka auren yarinyar nan as far as I am concern don baza a maida ni karamin mutum ba, Fulani kuma ka kyaleni da ita ni nasan yanda zan yi da ita, kaje ka ci gaba da shirye shiryen ka tunda kaga ba lokaci me tsawo aka tsayar ba don nasan ire iren issue din nan dole zai yi arising daga ɓangaren iyayenka mata dama, daxu mun yi magana da Shafa'atu akan kayan da ake hadawa na aure, so ita zata hada na ita wancan yarinyar, su kuma nan su hada na Hadiyah ina ga zai fi" A hankali Jay yace "Nagode Abba, Allah ya kara girma" Mai martaba yace "Za ka iya tafiya Ahmad" Mikewa yayi Mai martaba ya bi sa da kallo har ya fita. Jay na fita parlon Mai martaba babu dadewa sai ga Aunty ta shigo parlon, ta ajiye masa fruit din da ta kawo masa ta zauna tayi masa sannu da hutawa sai kuma tayi shiru, bayan wani ɗan lokaci cikin kwantar da murya tace "Ranka shi dade dama wata er shawara ko ince suggestion nake son badawa idan ka bani dama" Sarki na kallonta calmly yace "Ina jin ki Fulani" Ta gyara zama cikin nutsuwa ta fara magana tace "Ranka shi dade akan zaman Meeting din daxu ne da aka karesa babu dadi a zukatan mu gaba daya, sam ban ji dadin irin maganganun da Fulani Asiya tayi maka akan ɗan ta ba a gaban kowa da kowa, kuma ba yau ta saba maka irin wannan ba, amma na yau yayi min ciwo matuka, tun safe har yanzu bani da sukuni, ni kuma bana son biyeta mu yi batattciya a gidan nan, shi ne ni a nawa tunanin nake ganin for peace to reign da an hakura da batun auren ita bazawaran nan tunda har Asiya ta nuna bata so, yanxu zancen da nake maka maganar nan duk ya zagaye masarautar nan kan kace me kuma har cikin gari sai maganar nan ta fita, kaga nan jama'a za su dinga ganin don ba ɗan cikin ka bane shi yasa ka amince da bukatarsa na auren Bazawara, don guje ma wannan zargi ina ga zai fi kyau a ajiye batun auren yarinyar kawai mu yi facing na Hadiyah ranka shi dade, ba wannan karon bane na farko da mutane ke ganin kamar kana nuna bambanci tsakanin Jawwad da Junaid, ita dama Asiya kullum tunaninta a haka yake tana ganin baka yi ma ɗan ta adalci don kawai ƙasa ya rufe ma ubansa ido, to ina amfanin wannan ranka shi dade ana ɓata maka suna a gari? Tun asali bai kamata ka biye Jawwad da maganar nan ba duba da irin zaman da uwarsa ke yi da mu da wasu abubuwa marasa amfani da ta dauka ta saka a ranta taki a zauna lafiya, don haka ni a nawa karamin tunanin ya kamata kayi watsi da maganar bazawaran nan don a samu zaman lafiya a gidan nan ka kuma guje ma kanka zargin da jama'a za su fara yi maka, tunda ga ɗan cikin ka Junaid har yanxu ko buduwar auren ma bai da ita kuma baka ce lallai sai yayi ba, yanxu fa kamar ace Walid ya kawo maka bazawara mara asali yace zai aura ne, zaka fara sauraronsa? Amma fa ni a karamin tunanina nake magana ranka shi dade tunda ban fi ka hangen nesa ba, kuma ina fatan ban ɓata maka rai ba Ur Highness" Mai Martaba dake ta sauraronta ya ɗan yi murmushi yace "Kina zaune da ni shekara da shekaru kin taɓa ganin maganganun mutane ya girgiza ni ko ya hanani abinda nayi niyya Fulani?" Aunty tayi shiru, yace "Don haka in this case i don't think there is anything that will move me, as far as Ahmad is okay with marrying the lady, I am also okay with that, kawai dai Hadiyah ce zata zama matarsa ta farko kafin ita yarinyar wanda na riga na sanar da hakan tun farko, Walid kuma da kika ce in yau ya kawo min bazawa yace yana so zan basa shawara ya hada da budurwa duk a aura masa, hakan ma gata ne ai" Aunty ta sauke wani ajiyar zuciya ganin babu nasara a plan din nan ma, shiru tayi bata sake cewa komai ba. Har washegari Jay bai yarda ya hadu da Maminsa ba cause deep down he was really disappointed, tun jiya har yau bai dawo dai dai daga shock din da ya shiga ba, it was something he never saw coming, ko da ya dawo masallaci ko zuwa gaisheta kamar yanda ya saba bai yi ba ya koma bangarensa ya kulle, bai san ita ma ana idar da asuba ta bar masarautan ba da traveling luggage dinta.... Wajen karfe shidda na yamma Malam Ali na tsakar gida bakin pampo yana alwala, Nenne na zaune kan farin kujeran roba tana kara jaddada masa abubuwan da za ayi ma Khaleesat na fita kunya tunda ba karamin gida za a kai ta ba, Tace "Wallahi Ali sai kaga setin kayan gadon aka ce mana miliyan uku babu ragin ko biyar, setin kujeru kuma Miliyan biyu cif cif, in ba 'ya yan sarakunan ba ma ni bana jin akwai er da za ayi ma wannan setin kayan dakin, ko iya su muka kai mata babu me renamu wallahi, akan dai ace mu cakalkala kudi mu siya mata tarkacen banza masu arha da baza a ga darajarsu ba, don haka ni dai ga dubu dari biyar ina da shi a ajiye, Parida zata kawo Miliyan daya tace, ita Zahra'u dama babu ita a lissafi in ba dogon hancinta zata kai kasuwa ta siyar ba, don haka nake baka shawara wannan gidan nan naka na Mariri da nawa ka siyar kawai mu fita kunya, ko miliyan hudu aka samu aka siyar da gidajen kaga ai sai mu fitar da er mu kunyar gidan sarauta Ali, wallahi hankalina a tashe yake ga lokaci da aka sa ba mai tsawo ba, kan kace me zaka ga kamar gobe ne" Malam Ali dake ta sauraronta ya idar da alwalan da yake sannan yace "Allah ya rufa asiri ya nuna yanda za ayi amma siyar da gida kam bai taso ba Nenne, shikenan fa gare mu...." A fusace Nenne tace "Baza ka raba kanka da kalman nan na shikenan gare ka ba, shi kuma wannan da muke ciki na gwamnati ne?" Malam Ali dai bai ce mata komai ba, don su ne suke ma gidan nan kallon gidan zamansu amma banda shi, har cikin ransa ya riga ya sa cewar gida ne aka basa ya zauna na ɗan wani lokaci ya tashi, Tsayuwar mota suka ji a kusa da gate, Nenne ta kalli gate din, can tace "Kaddai tsinannun iyayen Awdul din ne suka sake biyo ka..." Mikewa tayi ta nufi gate din fuskarta babu rahama, wasu manyan mata ta gani har su hudu cikin shiga ta alfarma, suna kallonta suka ce sannu, Nenne ta koma gefe tace "Yauwa sannun ku, ko batan hanya ku ka yi ne" Daya daga matan tace "Ba nan ne gidan su Halysaah ba?" Nenne tace "Eh nan ne, Khaleesat ba, Malaman makarantar su ne halan?" Matar tace "To mu dai shiga daga ciki ko?" Nenne ta juya ta koma ciki da sauri tana cewa "Bisimillan ku, sannun ku da zuwa, ai Khaleesar ma ta ɗan yi tafiya bata nan, amma ku shigo ciki" Suna biye da ita har zuwa parlon gidan, shi dai Malam Ali bai ce masu komai ba kamar yanda babu wanda ya ce masa komai balle su gaishesa, Nenne na shiga parlor ta kora yaran Mama Shatu dake zaune suna kallo, duk suka fita daga parlon, ko wacce a cikin matan ta samu kujera ta zauna a parlon, Nenne na murmushi tace "Halan kun samu labarin an sa mata rana ne, bari in kira maku uwarta tana ciki" Da sauri Nenne ta tafi dakin Umma ta sanar mata Khaleesat tayi baki kamar Malaman makarantar su a Amurka don ko wacce shiga tayi ta alfarma ga gwala-gwalai, a tare Umma da Aunty Farida suka fito parlor, haka kawai Umma taji gabanta ya fadi, ta dai karaso parlon ta zauna ta gaishesu duk suka amsa, Aunty Farida ma ta gaishesu tana kallonsu, ledan pure wata guda Nenne ta kinkimo ta kawo masu tsakar parlon ta ajiye tana cewa "Wallahi yaran duk sun shanye wanda ke prij me sanyi" Matar dake tanka Nenne tun daxu tace "Mun san duk baku san mu ba, baku kuma san daga inda muke ba" Nenne ta daga kai ta kalleta, sai kuma tace "Ba Malaman makarantar su Khaleesah bane a Amurka?" Matar tace "Ko daya, ni sunana Hajiya Fatima, kuma ni din kanwata ce ga Mai martaba Sarkin Bauchi..." Ƙabbara Nenne ta saki ta mike tsaye tana tafe hannu tace "Lale lale, lale marhaba, sannun ku da zuwa, ashe manyan baƙi muka yi bamu sani ba, wallahi ba a sanar mana kuna hanya ba" Hajiya Fatima tace "Yana da kyau dai ki fara sauraronmu ki ji me ke tafe da mu tsohuwa" Nenne ta zauna kan Carpet tana kara masu sannu da zuwa baki har kunne, Hajiya Fatima ta nuna warce ke zaune gefenta tace "Fulani Asiya kenan, matar yayanmu Marigayi sarki Ahmadu Yusuf, mahaifiya ga Ahmad Jawwad...." Nenne tayi shiru tana kallon Mami da idanuwanta kamar za su fito, haka ma Umma da Aunty Farida da duk jikinsu yayi sanyi tun Hajiya Fatima bata fara introduction ba, suna ganinsu sun san babu alkhairi a tattare da zuwan su dama, Hajiya Fatima ta ci gaba da magana cike da isa da gadara tana nuna warce ke zaune 2 seater tace "Wancan Hajiya A'isha kenan kanwar Fulani Asiya, ta kusa da ita kuma Hajiya Nafisah kanwar matan Mai martaba Sarkin yanxu...." Nenne tayi karfin halin cewa "To Allah Ubangiji dai yasa lafiya, don ni ban gane kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login