Showing 75001 words to 78000 words out of 257722 words
Chapter 26 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar
sai a sannan taji hawaye masu zafi for the first time a idonta, ta kai hannu a hankali tana sharewa ta juya tana kallon Abdul dake baccinsa hankali kwance, dai dai nan alarm din wayarsa ya kada, ta juya da sauri tayi backing dinsa tana goge hawayen da ya fara zubo mata sosai, after some seconds taji alamar ya tashi yana karanto addu'an tashi bacci, ita dai hawaye kawai take, sai da taji yayi sallah ya fita daga dakin sannan ta mike zaune tana kuka a hankali. Nenne ta bude hannu tana kallon su Aunty Farida cikin nutsuwa tace "To kun ga ai baza mu shiga hurumin Allah ba, ko akwai me tsaurin idon da zai shiga a cikin ku? Allah Ubangiji ne kadai yasan daliliin da ya maidata hannun mijinta cikin ruwan sanyi babu tashin hankali, to don me za mu shiga hurumin da ba namu ba? A'a gaskiya banda ni tunda ni dai nasan wanene Allah, kuma shi kadai yasan hikimarsa ta yin hakan, da yasan Khaleesah zata cutu hannun Awdul da bazai fara basa sa'ar sungumeta ba don bamu fi sa sani ba, ko ba komai ɗa na zai samu kwanciyar hankali ya ci gaba da sabgogin rayuwarsa kamar ko wani ɗan adam, mu mun yarda da kaddara mummuna ko kyakkyawa tunda mu musulmai ne, kuma duk abinda Allah yayi mu din banza za mu ce don me, domin haka nake cewa Allah ya bata zaman lafiya da mijinta, ɗan halayyarsa da yake yi mara kyau Allah ya gyara sa ya dena, ai babu wanda bai da taɓon wani mugun abu a rayuwar nan, in sun dawo kano mu kuma sai mu je ganin daki mu sa albarka, duk sanda ya bar ta ta zo ta gaida mu a Mariri sai ta zo bakinta alekum, shi kuma Ali Allah ya sa karshen wahalarsa kenan a duniya" Wani irin kallo Aunty Farida ke ma Nenne zuciyarta na tafarfasa, Umma dai kanta na sunkuye bata ce komai ba amma ita kadai tasan abinda take ji a zuciyarta, Mama Zubaida tace "Amma dai Nenne ai ya kamata a bibiyi halin da take ciki, an taɓa tarewa haka kawai a zo a sungumi yarinya a mota da asuba ba a san ko shi din ne ba ko ba shi ba amma duk a rasa me bibiyar hakan, wannan ai abun dubawa ne, tun da mu dai har yanzu bai ce mana shi ya dauketa ba" Nenne tace "To er bakin ciki, shi din ne ya sungumeta ba kowa ba aniyarki ta bi ki, kuma ai halaliyarsa ya sunguma ba wata ba, duk wanda ya sake cewa zai bada shawara a wannan lamari idan ban sa Ali ya sallamesa ba shegiya uwata da ubana suka haifeni, kwata kwata bakwa neman ma ɗa na sauki a rayuwar nan, burin ku kawai tashin hankali ya kashe Ali ku huta ni kuma in shiga uku, ita uwar da ta tsugunna ta haifi yarinyar bata da bakin magana sai ke me baki kamar ta dorinar ruwa?" Mikewa Mama Zubaida tayi ta shige dakinta, Mama Shatu ta kyabe baki tace "To Allah ya kyauta, in ya dawo mana da gawar ta ai sai mu zauna mu yi zaman makoki ba shikenan ba" Nenne tace "Sai dai ki ga gawar er ki Labeebah amma ba Khaleesah ba, kuma bakin cikin da ku ka kasa boyewa ne zai kashe ku ke da Zubaida" Mikewa Umma tayi hawaye cike idonta ta shiga dakinta, Nenne ta kyabe baki ta mike tana kallon Aunty Farida tace "In Ali ya dawo ki ce masa nace ya zo ya amshi tuwo da miyar taushe zan ajiye masa, wallahi wata guda zan yi ina masa girki ya marmaro" Daga haka ta fice daga gidan, Aunty Farida tayi tagumi hawaye cike idonta.
Meemah ta shigo parlon Momy ta zauna tana ɗan murmushi, ta jira har Momy ta gama wayar da take yi da aminiyarta godiya sannan tace "Momy na samesa a waya" Da sauri Momy tace "Ya daga kuma?" Meemah tace "Eh ya daga bayan yaga text din da na tura masa kenan" Momy na gyara zama tace "Toh Alhamdulillahi nagode ma Allah, sai yace maki me?" Meemah tace "Kema kinsan dole zai taho ai, amma tsorona daya kada ya kira Daddy kuma ya daga waya yace masa ba haka ba" Momy tayi wani murmushi tace "Bazai daga ba, tunda na riga na gaya masa abinda ke faruwa ai" Meemah ta sauke ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah, in ya samu flight yau za mu iya ganinsu a gidan nan" Momy tace "Me zai hana ya samu jirgi, ai da sauran lokaci dole zai samu" Mai aikin Momy ce tayi sallama tana makale jikin kofar parlon duk da a bude yake amma bata shiga ba, hannunta rike da tray me dauke da plate din gasasshen kaza da lemon kwali biyu, Meemah ce ta amsa sallaman tana mata wani kallo tace "Tun da kika ga kofa a bude ba sai ki shigo ba, kin wani raɓe jikin kofa kamar munafuka, don Allah ki dena wannan kauyancin yana damun mu a gidan nan" Momy ta hade rai tana kallonta har ta karaso ta ajiye plate din, cikin ladabi tace "Ga kazar ta kammala Hajiya" Momy tace "Kalan Hijabin nan naki na daga min hankali a gidan nan, kar ki sake saka min shi, in yar wa zaki yi to ki yar bana son shi kwata kwata yayi kalar talauci" Mai aikin ta dukar da kai tace "Toh Hajiya in sha Allah bazan sake sa shi ba, kiyi hakuri" Fita tayi daga parlon da sauri, Momy ta dau plate din tulin kazar da aka ajiye mata ta fara ci tana cewa "Ai dama tunda aka ce min zai taho da ita hankali na ya kwanta, don dama taho da ita shi ne me wuyan...." Meemah tayi murmushi ita ma ta dau yankan kaza daya tana ci tace "I trust you Momy" Khaleesat ta saka Hijab dinta har kasa tana harhada wasu daga kananun kayan dake cikin closet din dakin kamar yanda Abdul ya umarceta tayi, absentmindedly take aikin don tayi nisa a tunanin da take, bude kofar dakin yayi ya shigo, ita dai bata juya ba tana ci gaba da abinda ya sakata, ya karasa har bayanta ya tsaya, taki juyowa gabanta na faduwa, juyo da ita yayi yana kallonta ta sunkuyar da kanta, yace "Me ya sa baki son ki saki ranki har yanxu? Always looking worried" A hankali ta daga kanta ta kallesa amma bata ce komai ba, yace "Kin gama hada kayan ne?" Girgiza masa kai tayi, yace "To gama" ta juya ta ci gaba da abinda take, shi dai yana tsaye yana kallonta, pad ta dauko a karshe zata saka cikin karamin trolley din yace "What are you using that for? Ba yau zaki gama ba?" Taki kallonsa zuciyarta na bugawa tace "Amma ban gama ba ai" Bata jira me zai ce ba ta saka a akwatin sannan ta kulle ta mike tsaye, kamo hannunta biyu yayi yana kallon cikin idonta, speaking slowly yace "Promise me you won't act silly har mu isa kano Khaleesat" Ta rasa dalilin da hawaye ya cika idonta, shi dai kallonta kawai yake, after some seconds yace "If you try anything silly, zaki yi matukar mamakin abinda zan yi, i promise you" Da kyar tace "Toh, amma plss ina son inyi waya da Safiyyah, i am missing her" Yace "Baza ki yi waya da Safiyyah ba, amma idan muka isa kano zan fara kai ki gidanku ki gaishesu sannan mu tafi gidanmu" Ita dai bata ce komai ba hawaye na zuba idonta, a haka suka bar gidan zuwa airport tunda yana da hoton National ID dinta a wayarsa. Da yamma suka sauka garin kano, driver din gidansu har ya iso airport din yana jiransa, Drivern ya bude ma Khaleesat back seat bayan ya gaisheta, kanta a kasa ta shiga motar, kana ganinta kasan tana cikin damuwa sosai gashi ta kara zagbewa gaba daya, Abdul ya shiga ta daya side din, sannan drivern ya shiga motar ya tada suka bar airport din, sai bayan da suka fita daga cikin airport Abdul ya gaya ma drivern inda zai fara kai su, sun yi nisa sosai da tafiyar Abdul ya juya ya kalli Khaleesat da tayi nisa cikin tunanin da take, hannunta ya saka cikin nasa wanda hakan ya dawo da ita reality, ta ɗan kallesa, yayi kasa da murya yace "Are you hungry?" Girgiza masa kai tayi, ya jawota zuwa jikinsa yana kallonta, ita dai bata ce masa komai ba zuciyarta na bugawa, a haka suka isa Mariri wajen karfe biyar da rabi na yamma, Drivern na parking daga opposite din gidansu Khaleesat Abdul ya bude motar ya sauka, jiki a sanyaye Khaleesat ta sauka daga motar, ta ma rasa ko farin ciki zata yi ko akasin haka ganinta a kofar gidansu, Abdul ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gidan sai a sannan hawaye suka cicciko mata ido, Noor ce ta fara hangota tana hura gawayi ta taso da gudu ta rungumeta, sai a sannan sauran en gidan duk suka juya suna kallon Khaleesat, Umma dake zaune bakin kofar dakinta ita ma ta dinga kallonta, Mama Zubaida da Mama Shatu suka taɓe baki suna kallon juna, Aunty Farida dake gyara dakin Umma ta fito da sauri jin sunan wanda Noor ta kira, Khaleesat ta tafi ta rungumeta ta fashe da matsanancin kuka, Farin ciki wajen Aunty Farida ba a cewa komai don duk tunanin su Ajay ne suka dawo da ita gida, sallaman Abdul yasa duk suka juya suna kallon hanyar shigowa gidan da mamaki, nan da nan fara'ar Aunty Farida ya bace, su Mama Shatu ne kawai suka amsa masa sallaman, ya karaso cikin compound din, Aunty Farida ta saki Khaleesat ta tafi ta zauna kusa da Umma fuskarta babu yabo babu fallasa, Mama Zubaida ta mike da sauri ta shimfida masa tabarma ita da Mama Shatu na masa sannu da zuwa, ya zauna kan tabarman yana kallon Umma ya gaisheta, Umma ta amsa tace "Sannu da zuwa" Aunty Farida ta mike ta shige dakin Umma, Abdul ya gaida su Mama Zubaida dake ta washe baki, duk suka amsa da fara'a, Ita dai Khaleesat na durkushe kusa da Ummanta kanta a kasa, Abdul ya kalli Umma yace "Baba baya nan ne" Umma tayi karfin halin cewa "Eh bai dawo ba" Ko rufe baki bata yi ba sai ga Malam Ali ya shigo gidan da rabin buhun dankalin Hausa a hannunsa, ajiyewa yayi ganin Abdul da Khaleesat, yace "A'aa, ikon Allah, baki mu ka yi yau a gidan" Abdul ya tashi ya tafi har inda Malam Ali ke tsaye ya gaishesa, Malam Ali ya amsa yana kame kame, ya tafi da sauri ya dauko tabarma ya kara shimfida ma Abdul yace "Yi zaman ka a nan, bari in zubo mana ruwa a buta lokacin Magariba yayi" Da sauri ya tafi ya dauko butoci biyu ya tafi zai debo ruwan, Umma ta mike ta shige dakinta, Khaleesat ta bi bayanta, Nenne ce ta shigo gidan da sallama tace "Allah me hikima, sannunku da zuwa Awdul" Abdul ya gaisheta, ta jawo kujera ta zauna tana facing dinsa tace "Lafiya lau wallahi, ya iyayen naka, ina kokarin daura sanwa kenan sai ga wani almajiri da gudu ya zo ya sanar min ai kun zo, kasan ɗan albarka ne almajirin nan duk wani abu da ke faruwa a gidan Ali kamar kiftawan ido yake rugowa ya sanar min, ni kuma in ina da er dabino kwara uku in basa la'ada, nayi farin cikin ganin ka wallahi, ina matar taka, in ji tare ku ke?" Yace "Tare mu ke" Sai ga Malam Ali da ruwa a butoci yace "Ai ina jin tana dakin uwarta" Nenne tace "Kai kuma lafiya? ina zaka da butocin ruwa ko karfe shidda bai yi ba?" Malam Ali yace "Au? To to bari a ajiye, na zata magariba ta yi" Da sauri ya koma ya ajiye butocin ya dawo, Nenne tayi kasa da murya tana kallon Abdul tace "To Awdallah, ka dubi girman Allah ka rike amanar da muka baka, yanxu kai ne uwarta kai ne ubanta, duk ta kuskure maka ka kawota wajena ni zan san yanda zan yi da ita, kuma albarkacin auren da ya shiga tsakaninka da jikata ka kara ba Mahaifinka hakuri ya yafe ma Malam Ali komai ya wuce a wajensa don girman Allah, don yanxu kam duk mun zama daya tunda ga aure har ya shiga tsakani, Allah Ubangijin ya baku zaman lafiya ya kauda duk wata fitina ya kawo zuri'a dayyaba" Abdul yace "In sha Allah Kaka" Nenne na murmushi tace "To madallah, gashi ko tuwon dare ban yi ba balle in zubo maka" Yace "Ba komai, can gidanmu za mu wuce yanxu yamma tayi" Nenne tace "Gaskiya kam, bari in fito maka da ita ku tafi, go slown hanyar nan bata da kyau" Tashi Nenne tayi ta nufi dakin Umma, kuka kawai Khaleesat take Umma tayi tagumi tana kallonta ta ma rasa abun cewa amma daurewa kawai take ita ma hawayen bai zubo mata ba, don bakin ciki Aunty Farida na jingine jikin bangon dakin ita ma ta kasa cewa komai, a haka Nenne ta shigo dakin ta same su, taɓe baki tayi tace "Ta so ki fita mijinki na waje na jiranki" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba tana kuka kamar ranta zai fita, Nenne tayi kasa da murya tace "Wato a yanda kanwar uwarki ke zube ba mashinshini shekara da shekaru haka kema kike son ki zauna mana tunda kyau kawai gare ku amma babu farin jini, banda samun waje ki samu miji zankadede kamar Awdul amma son zuci irin taki da na uwarki da kanwarta bazai sa ku yi farin ciki da hakan ba, in a baya Awdul ɗan iska ne dama Allah ya taɓa halittar da bai shiryar ba in yayi niyya? Daga yanda Awdul ke magana a kintse na gane ya shiryu wallahi, to ko kawota da yayi ta gaishemu kadai ya isa mu shaida shiriyarsa, wallahi ku dinga jin tsoron Allahn da ya halicce ku, duk wanda burinsa ya raba aure to tsinuwar Allah ne zai tabbata a garesa, kuma in sha Allahu Khaleesat tayi aure kenan mutuwa kadai ne zai rabata da mijinta tunda duk mun san yana sonta, tashi ki fita gun mijinki ku tafi munafuka kawai, duk da can baki san baki son shi ba sai da ya aika ki kasar turawa idonki ya bude a can" Cikin kuka Khaleesat tace "Ni wallahi bana son sa, bana son sa, bazan iya zama da shi ba" Nenne tace "Aikin banza, to uban me ya rage kuma bayan ya kwana da ke? Ai duk rashin son da kike masa dole ki zauna da shi tunda ya kwana dake yau kusan satin ki daya a gidansa ba kuma ajiye ki zai yi yana kallo kamar hoto ba tunda shi ba ɗan iska bane, kuma gidan Ali ba Obalande bane da za a tara masa fararen zawara har biyu a gida, Farida ma kadai ta ishemu, tashi ki fita ki bani waje ko in tafi in kira maki Ali yanxun nan ya fitar min da ke, tun da uwata ta haifeni ban taɓa ganin er da bata son kwanciyar hankalin ubanta ba sai ke" Umma ta share hawayen dake zuba idonta tana kallon Khaleesat tace "Ta shi ki je Khaleesah, Allah ya maki albarka, Allah kuma ya baku zaman lafiya" Mikewa Khaleesat tayi tana kuka sosai ta fita daga dakin Ummanta, Nenne tace "Atoh dai, iya addu'ar da za mu yi mata kenan a matsayin mu na rikakkun musulmai, tun da muka ga haka to Allah ne kadai ya san hikimarsa nayin hakan, kuma dama an gaya min aurenta da Awdul aure ne me kyan gaske in har zata kwantar da hankalinta, gashi mun shaida yana son ta, kuma ta dalilinta arzikin ubanta duk zai dawo har ma ya fi na da, wallahi haka aka ce min, kawai dai babba ba a son yayi ta surutu ne shi sa nake jan bakina nayi shiru" Har suka bar gidan da Abdul hawaye ne kawai ke zuba idon Khaleesat, dubu talatin ya ba kishiyoyin ummanta ko wacce 15k, ya ba Islam 50k, Nenne ya bata 20k, Malam Ali kuwa bai amsa kudinsa ba sai ajiye masa Abdul yayi kan tabarman dake bakin kofar dakinsa, babban tashin hankalin Khaleesat yanxu period dinta da ya dauke, don kafin su taho kano a dari dari tayi sallahn Azahar kar ya shigo ya ganta, tasan yau dai ƙaryar ta ya kare kawai, a haka suka iso gidansu Abdul bayan sallan magrib, Driver na shiga babban compound din da mota Khaleesat taji gabanta ya tsananta faduwa, bayan yayi parking a space din parking Abdul ya sauko daga motar yana kallonta, da kyar ta iya saukowa daga motar zuciyarta na bugawa sosai wanda ita kanta bata san dalilin hakan ba all of a sudden, ya fara tafiya tana bin sa har suka isa entrance din shiga parlorn gidan....
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
_Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albishir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da kayan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you that duk wani product dinmu is tested and trusted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via +234 803 810 3096_
45
Khaleesat na tafiya a hankali ta shiga parlon tana karanto addu'o'i a ranta don irin faduwar da gabanta yake yi isn't normal, ga tsikar jikinta sai tashi yake, she was so uncomfortable and restless at the same time, Abdul ya kulle kofar parlon ya kalli mahaifiyarsa dake zaune