Showing 231001 words to 234000 words out of 257722 words

Chapter 78 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

alhamis, sai dai Jawwad" Jay ya juya ya kallesa, Nenne tace "Ai kuwa yau alhamis nima ina yi saboda ba a garina nake ba shi yasa ban yi ba" Matsar da farantin kwan tayi gaban Jay da katon bredin da kopin shayi duk ta maida gabansa, Khaleesat bata san sanda dariya ya kusa taho mata ba duk da yanda take fama da kanta ganin how shock Jay was looking at Nenne, shi kansa Ajay kawai dakewa yayi, yayi keeping serious face a gefen Jay kar yayi dariya, Nenne tace "In kuma baka ci ba Allah ya sani bazan ji dadi ba, kuma jikina zai yi sanyi" Daga haka ta nemi waje ta zauna tana jiran ya fara shan shayin, Jay ya ciro handkerchief dinsa yana goge fuskarsa, Aunty Murja ta nemi waje ta zauna ta kara gaisawa da su da fara'a sannan tace "Wani unguwa ku ke a Bauchi?" Nenne tace "Nima dai na tambaya ranan amma bai gaya min..." Jay ya ɗan kalli Ajay, shi dai Ajay babu abinda yace, Jay ya sauke idonsa ya sanar masu daga inda suka fito a garin Bauchi, Nenne ta saki baki tana kallonsu can tace "Kun hada wata dangantaka da sarki ne?" Jay yace "Mahaifinmu ne" Wani salati Nenne ta saki saboda shock tana kallonsu tace "Sarkin ne mahaifinku?" Jay bai sake cewa komai ba, Nenne ta kira full sunan Mai martaba tace "Kuna nufin shi ya haife ku??" Aunty Murja tace "Haka fa kika ji suka ce Nenne, ni dama ina ta kallon wannan na kusa da shi naga yana kama da yaran gidan sosai, tunda zaki ga ana nuno mana su ta waya yanxu, su dai wa ennan ban taɓa ganinsu a waya ba" Tsabar yanda Nenne ta girgiza ta kasa cewa komai sai kallonsu Jay take kamar ranan ta fara ganinsu, can ta ambato sunan Baban Jay me rasuwa sai kuma ta fashe da kuka tace "A sannan ina garin nan Allah yayi masa rasuwa, duk muka gigice, garin nan ya dawo shiru kamar ba kowa tsabar tashin hankali, Sarki adali me jin tausayin al'uma, mun yi babban rashi wallahi, kaninsa dake kan kujeran yanxu ne ban wani san sa ba, amma yanxu ace zan samu hanya wallahi zan je har fadarsa mu gaisa in saka masa albarka in masa addu'a" Jay na murmushi yace "Sai mu kai ki Kaka, ai yana nan" Nenne tace "Da kuwa nayi farin ciki wallahi, sai Parida ta rakani mu je, ita wannan rubabbiyar me ciwo ta zauna a gida ba sai mun je da ita ba, ita kuma Murja tana da yarinya me shafar aljanu bata zuwa ko nan da can saboda yarinyar...." Ko rufe baki Nenne bata yi ba sai ga yarinyar Aunty Murja na kokarin shigowa dakin, Nenne tayi wani ihuu ta dau mafici ta fara korar ta daga inda take zaune tana cewa "Fitaa, tafi kofar gida, Murja ba nace ki saka kwado a dakin ba wannan wani irin fitina ne saboda yarinyar nan nake fargaban zuwa gidan nan wallahi" Ajay ya mike yana kallon yarinyar yace "Ta fita kuma Kaka?" Nenne tace "Ta fita mana ɗan nan, er ruwa ce fa" Jay was totally speechless yana kallon Nenne, Aunty Murja ta mike zata dau yarinyar ta bar wajen Ajay yace "A'a ki kyaleta" Sai ya karasa ya shigo da ita dakin ya zaunar da ita kusa da shi, ga shi Fes uwar ta shiryata har da su packing gashinta me uban yawa, Nenne dai sai zazzare ido take tana kallonsu don ita abun kunya ta dauka ai, Ajay ya kalli Aunty Murja yace "Ya sunanta" Aunty Murja tayi murmushi, Nenne tayi karaf tace "Sunansu daya da Khaleesah, ita ma Hauwa ce, dama kuma sunan uwar Murjan Khaleesah ta ci, kunsan uwarta kishiya ta ce kuma mun yi zaman mutunci, Murja na da shekara biyar uwar ta mutu rikonta ya dawo hannuna har na aurar da ita, Ali na ji da Murja kamar ni na haifeta, yanda na sha wahala Ali yayi karatu ita ma haka don sai da tayi poly kafin tayi aure, da iliminta haka da ku ke ganinta har turanci tana ji, bayan na mata aure haihuwar farko ɗan ya rasu bayan shekara hudu Allah ya bata wannan yarinya er ruwa" Calmly Jay yace "Kaka ba haka bane, ki dena kiranta da er ruwa, ita din mutum ce kamar kowa, a ƙasashen da aka ci gaba masu irin wannan lalura kulawa ta musamman ake basu, babu tsangwama babu kyara sai soyayya da ake nuna masu ana jan su jiki, wannan lalura tasu a likitance ita ake kira da Cerebral Palsy ba wai yan ruwa ba kamar yanda yawancin Hausawa ke kiransu wasu ma su ce ai aljani ne ya taɓa su, to duk ba haka bane, kusan lalura ce ta ƙwaƙwalwa wanda jariri ke samu tun yana cikin mahaifiyarsa ko kuma bayan an haifesa, kyara da tsangwamar masu irin wannan lalura da ake yi yana jefa iyayensu cikin damuwa, duk da yanxu kai ya waye hakan ya ragu ba kamar da ba, don haka Kaka don Allah wannan yarinya soyayya take bukata da kulawa ba tsangwama ba, haka Allah ya so ya ganta, mutanen dake kewaye da ita sai su ja ta jiki su nuna mata so da kulawa" Nenne ta sauke ajiyar zuciya tace "Ai shikenan, mu ce mana ake yan ruwa ne zamanin mu, amma tun da ba haka bane ko ta shigo na dena korarta sai dai Allah ya kiyaye mu kar ta mana barna mu shiga uku" Ajay yayi murmushi kawai ya kalli Aunty Murja da kanta ke kasa yace "In sha Allah za a duba mata Wheelchair that will improve her mobility, da abubuwa da suka kamata" Mami ce zaune tare da Mai martaba a parlonsa, bayan sun gaisa tace "Dama Allah ya taimake ka akan maganar Jawwad nace bari in sameka, bayan sun dawo ya kawo min maganar wata yarinya da yake so da aure, duk da nasan kun yi magana da shi kafin yayi da ni, to nayi masa fatan alkhairi, shi ne yanxu na same ka inji what is ur take on the matter" Mai martaba yace "Ai mun gama wannan maganar, har nayi ma wakilai na maganan tafiya wajen iyayen yarinyar, akan haka ake yanxu" Mami tayi shiru tana kallonsu, can ta gyara zama tace "Amma Ranka shi dade ban tari hanzarin ka ba, daga magana sai tura wakilai na zata ai sai anyi bincike me zurfi kafin tura wakilai" Mai martaba kallonta kawai yake don dama ta saba fada masa duk maganar da ya zo bakinta, can ya sauke ajiyar zuciya bayan kusan minti daya yace "Kina ganin zan tura zuwa gun iyayen yarinyar babu bincike Fulani?" Mami tace "To naga abun yayi gaggawa ne ranka ya dade...." Mai martaba yace "To haka muka shirya Fulani" Tace "To yanxu har an tsaida ranan zuwa Kanon kenan?" Mai martaba yace "Kwarai kuwa... Nayi wasu baƙi zan je in same su yanxu Fulani" Yana kai wa nan ya mike ta bi sa da kallo har ya fita daga parlon.



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
Ur evidence via 07087865788

HALYSAAH
PAGE 93

Jay na zaune parlon Maminsa ta dalilin kiransa da tayi, ko minti talatin basu yi da dawowa gidan tare da Ajay ba don yau ma sun je duba Khaleesat, Mami ta kallesa tace "Ina kuma yake jan ka kuke tafiya duk kwana biyun nan daga safe zuwa dare" Jay ya daga kai ya kalleta, sai kuma yace "Yake ja na kuma sai kace wani yaro Mami?" Mami tace "To ai hakan kake a wajensa, ba kai ne Drivern sa duk inda za shi a garin nan ba" Jay bai sake ce mata komai ba don tunda suka fara zuwa unguwan da Halysaah suka sauka Ajay ne ke driving din, Mami tace "Daxu Me martaba ke gaya min yanda ku ka yi da shi, dama da ban je na samesa ba kawai sai dai inji magana a sama, kai menene dalilinka na ƙin gaya min yanda ku ka yi da shi? Kun je kun yanke shawara har za a zartar amma ni ba a fita hakkina an sanar min ba and you are okay with that" Jay dai yayi shiru don he was only following Ajay's advice, Mami tace "To ai shikenan, Allah Ubangiji yayi mana me kyau" Jay yace "Ameen" Mami tace "To a tudun yolan wace unguwa suke?" Jay ya daga kai ya kalleta yayi shiru, tace "Ko ba Tudun yola ka ce ba?" Yace "Eh can suke, amma ban rike address din gidan ba ai, any problem Mami?" Mami tace "A'a wai in ji, amma tunda baka sani ba ai shikenan" Wayarsa ne ya fara ringing yana dubawa yaga Mai martaba ke kiransa, ya daga kai ya kalleta yace "Mai martaba na kirana" Mami tace "Ohk" Mikewa yayi ya fita daga parlon, after a while ta tashi zata fita sai ga Aunty ta shigo, dama kuma wajen nata zata je don gaba daya akanta tayi relying all this while tunda tace ta bar mata komai, Mami ta koma ta zauna tace "Kuma gun ki zan tafi yanxu" Zaunawa Aunty tayi tana murmushi tace "Toh albishirin ki, yanxu haka na samo Address din gidansu yarinyar a wajen Mai martaba, ashe daga Kano zai wakilta aje gidan nasu, iyaka mutane biyu ne za su tafi daga nan" Mami tace "Da gaske kin samo Address din?" Aunty tace "Kwarai kuwa, ce masa nayi mijin er uwata dake Tudun yola yace min a basa address din gidansu yarinyar in dai Tudun Yola suke kilan bazai rasa sanin Ubanta ba tunda duk sun san kansu a unguwan, tun da safe muka yi hakan da shi shine ya kira Jawwad din ta waya a gabana ya tambayesa Address din, nan take kuwa ya gaya masa, sannan Mai martaba ya sake nanata min address din, ina komawa parlona na rubuce address din a waya don kar in mance, to na fita ne, sai yanxu na dawo shi yasa ban shigo na sanar maki ba" Mami tayi shiru tana kallon Aunty, can tace "Amma kinsan yanxun nan Yaron nan ya fita a parlon nan ina tambayarsa Address din yace bai sani ba???" Aunty ta taɓe baki tace "Ai ko ya gaya ma Mai martaba daxu da safe" Mami tayi wani murmushi tace "Ki bar ni da shi, in yasan wata ai bai san wata ba" Aunty tace "Ba nace ki fito masa a mutum ba kin ki kina gudun bacin ransa, tun yaushe za ki ce masa bai isa ba kuma hakan ya zauna" Jay na zaune gaban Mai martaba a parlonsa, Mai martaba was quiet for a minute kafin yace "Jawwad..." Jay ya daga kai ya kallesa don sai da gabansa ya fadi cause Mai martaba da serious tone ya kirasa, a nutse Mai martaba yace "Me yasa baka gaya min yarinyar da kake nema ta taɓa aure ba?" Jay ya dinga kallonsa babu ko kiftawa zuciyarsa na bugawa, Calmly Mai martaba yace "Ko ba haka bane?" Sauke kansa ƙasa yayi ya kasa cewa komai at first, shi gaba daya mance Khaleesat ta taɓa wani aure yake yi, lokaci daya yaji jikinsa yayi sanyi sosai, ya dafe kansa da yayi masa nauyi a take, Cikin kwantar da murya Mai martaba yace "Ba hakan zai sa in hanaka aurenta don ta taɓa aure Jawwad, my concern is why did you hide this important thing away from me? Idan da ban sa an min bincike kafin in tura zuwa ga mahaifin yarinyar ba da sai in wakilai na sun je mahaifinta zai sanar masu matsayin yarinyar kenan? Or probably kun ma riga kun hada plan ace budurwa ce duk ban sani ba... kuma duk hakan zai iya yiwuwa tunda har ka iya boye min, Kai ba aure ka taɓa ba Jawwad, this is ur first marriage idan Allah ya tabbatar, ka kuma san yanda al'adar gidan nan yake, tun asali da ka sanar min cewar ta taɓa aure ai sai an fara auren ka da Hadiyah idan ya so ko bayan wasu watanni ne sai ka auri ita wannan din, nobody will question you Jawwad, an sanar min abubuwa da yawa a binciken nan da na sa aka min wanda ina ga babu amfanin in zauna ina zayyano su a nan, har ma unguwan da suka baro kafin su dawo tudun yola na sani, just that I was taken aback knowing so many things.... kawai dai nasan ni bazan hanaka aurenta ba tunda kace kana sonta Ahmad, although bayan binciken nan da aka min akwai abubuwa da yawa wanda na kasa fahimta har yanxu, ban san ko da wani abu da ku ke boye min kai da Junaid ba, ko kuma akwai wani abu da ku ka juya kai da shi akan lamarin nan, anyway... ba hakan zai sa a fasa zuwa gun mahaifinta gobe asabar kamar yanda na tsara ba, sai dai za a fara zuwa gun dangin uban Hadiyah tukunna, so dalilin kiran ka kenan Ahmad, Allah ya maka albarka...." Jay dai ya kasa ɗago kansa don gaba daya jikinsa yayi sanyi qlau, kenan an sanar ma Mai martaba karatun da take a Amurka ma Saurayi ne ke sponsoring dinta tun bai aureta ba, bayan nan ya gano shi da Junaid suka ci gaba da dawainiya da ita a Amurka kenan bayan mutuwar aurenta? Yanxu har labarin prison din da aka kai babanta da dalili duk yaji, ta yaya ma har aka gano tsohon unguwan da suka baro?? Babu abinda ya kara sanyaya masa jiki sai batun gidan da ya siya masu don ya ma san har shi za a gaya ma Mai martaba kawai bazai dai ce masa komai bane, tun da gashi yace yaji abubuwa da yawa, Mai martaba ya katse masa tunaninsa yace "Ko da wata maganar da zaka yi ne Ahmad?" Da kyar ya ɗago kai, cikin sanyin murya yace "Kayi hakuri Abba, nayi kuskure boye maka duk abubuwan nan da nayi tun farko, a gafarce ni Abba" Mai martaba ya ɗan yi murmushi yace "It's fine Ahmad, i only called to correct you, in sha Allah bikin ma baza a saka lokaci me tsayi ba, kawai asalin mahaifin yarinyar ne ake contemplating har yanxu, ance Kano kuma aka dawo aka ce Bauchi... How true is that? Although ba mu ji daga mahaifin nata ba har yanxu ai, mahaifiyarta kuma aka ce buzuwa ce er Nijar ko?" Da kyar Jay yace "Haka ne, Mahaifinta a Kano aka haifesa amma asalin babansa ɗan Bauchi ne, zama ya maida shi Kano, daxu kakarta ke sanar mana don tana garin nan, har ma tace tana son a kawota ta gaishe ka" Mai martaba ya ɗan yi murmushi yace "A nan garin kakarta take kenan?" Jay yace "A'a zuwa tayi, dama kuma tana zuwa" Mai martaba yace "Shikenan, babu matsala sai ka kawo ta din, zaka iya tafiya..." Jay yayi masa sallama ba tare da ya yarda sun hada ido ba ya mike ya bar parlon, bangaren Ajay ya nufa, ya samesa zaune parlor yana dube dube a laptop, Bayan ya zauna Ajay ya kallesa, Jay ya jinginar da kansa jikin kujera a hankali yace "Kasan Mai martaba ya sa anyi bincike a Kano? And he found out everything, when I say everything I mean Everything Ajay" Ajay ya ɗan bude ido ya ajiye laptop dinsa yace "Really?" Jay ya sauke ajiyar zuciya yace "Dama ai zancen duniya baya buya, but banyi expecting za a gano komai easily haka ba, yau na kara jin tsoron mutum, mutum abun tsoro ne Ajay, nasan har gidan da na siya Abba ya sani yanxu, he was angry but calm at the same time, I wish I told him all this before he find out himself..." Ajay was quiet for some time don shi ma ya girgiza, can yace "To yanxu me yace maka at the end?" A hankali Jay yace "He said it's fine, I told him about her Grandma da tace zata zo, gobe kenan...." Ajay yace "Ba nace ka kyale wannan tsohuwar ba, sai ta zo ta karasa fada masa abinda ba a fada ba a Kanon hankalin ka zai kwanta, she talks too much shi yasa nace kayi ignoring kawota da tace kayi gidan nan, but you still went ahead and told Abba" Jay ya sauke wani ajiyar zuciyan yace "Bazata yi abinda kake tunani ba, i will bring her tomorrow in sha Allah, don Abba na contemplating asalin Baban Halysaah, an ce masa Kano aka dawo kuma aka ce Bauchi" Sosai Nenne ta nutsu tayi zaman ladabi da biyayya tun da aka shigo da ita babban parlon Mai martaba, don a iya saninta ba kowa ne ke da access din parlon sarki ba, ita a ganinta ba karamin karramata da mutunta ta aka yi ba haka, dama ta baza tsadadden turaren Khaleesat da suka barota a gida, sai zuba uban kamshi take abun ta ga sabon gyale da atamfa a jikinta kai baza ka bata shekarunta ba, zuwa sannan sun kusa minti goma kenan a parlon a zaune, Ajay ne yayi leading dinsu zuwa parlon sannan ya fita, Nenne ta saci kallon Aunty Farida da tayi picking call din da ya shigo wayarta ta hade rai tace "Ke Parida ba nace ki ajiye wayar nan ba, ba fa parlon gidanmu bane nan, ba fa kowa ake ma iso zuwa wannan parlon ba sai wanda ya isa, wannan wani irin kunyata ni kike son yi bayan na yarda dake na jajibo ki, Haba parida..." Ko rufe baki Nenne bata yi ba sai ga Mai martaba ya shigo parlon walking like the king he is, Nenne ta sinne kai irin babban mutum ya shigo, Sau daya Aunty Farida ta daga kai bayan ta gansa ta ajiye wayar hannunta, ya karaso har cikin parlon ya zauna a spot din da ya saba zama yana kallonsu, tuni dama Nenne ta fara jero masa gaisuwa tun bai kai ga zama ba, shi ma ya gaisheta cikin girmamawa, Aunty Farida ma ta ɗaga karamin Nikab din da ta dora kan Abayan jikinta ta gaishesa kanta a kasa,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login