Showing 180001 words to 183000 words out of 257722 words

Chapter 61 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

Khaleesat ta wani kalleta, Shi dai Jay Murmushi kawai yayi, Safiyyah tace "Ka ɗan matsa kusa da ita kadan Yaya Housemate so that the space won't make the picture look somehow" Slowly ya matsa kusa da Khaleesat yana kallonta yana murmushi, Khaleesat ta ganta er karama a kusa da shi ga daddaden kamshin turarensa da ya cika ta, tuni Safiyyah ta koma baya da gudu ta ci gaba da daukan hoton da take tana washe baki, farin ciki kamar ya kasheta, haka ta dinga controlling dinsu wajen daukan hotunan, tace su koma can, tace su dawo nan, ta tabbatar tayi masu hotuna masu bala'in kyau, har dai daga karshe Jay yace mata ya isa ita ma ta shigo su yi hoton, zai ba wata er Africa dake wajen wayarsa ta masu hoton har Safiyyah amma Safiyyah taki shiga tace "A'a kar in bata maku hoto ina baƙa da ni" Dariya Housemate yayi haka dai ya lallabata ta shigo aka yi masu hoton su uku, Safiyyah na murmushi tace "Amma fa tunda nake daukan hoto ban taɓa daukan wanda ya dauku kamar hotunan nan da na maku ba wallahi" Jay na murmushi yace "Dollar nawa za a baki to?" Dariya tayi ta tattara lemonade dinta da tacos da ya siya mata tace "Wannan ma da aka siya min Allah ya amfana" Daga haka ta kara gaba ta bar masu wajen, Jay was amaze at how Safiyyah snapped the pictures so well, ya kasa daina kallon Khaleesat a hoton, the pictures where so beautiful, Khaleesat tun da ta kalli hoto daya ta kasa ci gaba da kallon sauran ta koma ta zauna kawai, after a while ta daga ido ta ɗan kalli Jay taga kallonta yake, da sauri ta maida kanta kasa, a hankali yace "Halysaah" Bata dago kanta ba still tace "Uhm" Yace "Me yasa baki sakin jiki da ni yanxu? You weren't like this before, ko don nace zan aure ki?" Sunkuyar da kanta tayi alamar kunya, yace "To meye amfanin zuwa nan tunda baza ki saki jikin ki ba, i want us to have a quality time together amma kiyi ta sunkuyar da kai...." Tana murmushi a hankali tace "To ai kunya nake ji" Yace "To kalleni zaki dena jin kunyan" Taki dagowa tayi shiru, yace "Halysaah" Tace "Ni bazan iya ba" Bai sake ce mata komai ba, ganin haka ta daga idanuwanta ta kallesa taga kallonta yake, murmushi yayi mata murya can kasa yace "You are specially made Halysaah" Rufe idonta tayi tana murmushi a hankali tace "Thank you" Yace "Kin dai ji me kawarki ta ce ko?" Khaleesat ta daga ido ta kallesa tace "Me ta ce?" Yayi kasa da murya yace "We will make beautiful Babies together...." Khaleesat ji tayi wani azababben kunya ya rufeta, yana murmushi yana kallonta yace "Ni ko guda daya kika bani me kama dake i will appreciate..." Kamar zata yi kuka tace "Ni dai mu tafi gida" Yace "A'a sai kin ban labari, kina ban labari ko daya ne sai mu tafi" Shiru tayi, sai kuma tana wasa da straw din drink din gabanta tace "Wani irin labari?" Yace "Ko ma wani iri ne, ko kuma ki bani labarin yanda ku ka hadu da Funny frnd dinki Safiyyah" Khaleesat tayi murmushi ta dago kai tace "Ohk...." Babu bata lokaci ta fara basa labarin farkon haduwarta da Safiyyah a school, shi dai kallonta kawai yake ko kiftawan kirki baya yi, everything about Khaleesat is just beautiful and breathtaking, tsakaninta da Allah take ta basa labarin Sophie ashe ko sanin abinda take cewa bai yi ba ya kafeta da ido with many imagination running his mind, daga bada labarin Safiyyah kawai ta saki jiki a wajen, dama kuma haka yake so... kamar yanda ya so hakan ne ya faru don they had a wonderful time together, labari sai wanda ta manta ne bata basa ba a kan experience dinta a America tun daga shekaran da ta zo har zuwa yanxu, wani yayi dariya, wani yaji tausayinta wani ya ga wautan ta, babu abinda ya kara burgesa da ita tana basa labarin sai turancin ta, she was so vocal, duk da timidness dinta she was very outspoken kamar ba a unguwan nan da gidansu yake ta tashi ba, he never knows she speak so well sai yau, yayi kasa da murya yace "You know what Halysaah?" Ta girgiza masa kai tana kallonsa, a hankali yace "I love you so much" Rufe fuskarta tayi da sauri tana murmushi... Sai wajen karfe bakwai suka bar park din, sai da suka fara dropping Safiyyah a gida before heading home, Jay na parking Khaleesat ta kalli motar Ajay dake parking Space, can ta kalli Jay tace "Is he waiting for you?" Jay yace "I don't think so, kinsan yana da aboki a Neighborhood din nan shi ma PhD yake, the frnd is at the far end of this street, External defense dinsu is around the corner...." Khaleesat tace "Ohk har da kai?" Jay yace "Yea in sha Allah, period din exam din ku ne Defense dinmu" A hankali tace "To Allah ya baku nasara" Yana murmushi yace "Ameen" Tace "To a ina zaka yi parking since he is occupying the space?" Yace "Zan je gida in dawo anjima" A hankali tace "To ni kadai a apartment din?" Yace "Ga motar Ajay kina gani, ai yana ciki kenan" Shiru tayi tana kallonsa, ya mata murmushi yace "Mu je in raka ki ciki to" A tare suka sauka daga motar ya rakata har cikin apartment din, yana kallonta calmly yace "Can i go now?" Jingina tayi da bango a kusa da shi ta langwabar da kanta kawai ta marairaice tana kallonsa, ya sauke idonsa daga kallonta trying to calm his self down, a hankali yace "I need to go Halysaah, ki kulle kofar" Daga haka ya juya ya fita daga parlon without looking at her, ta bi sa da kallo kafin ta kulle kofarta....


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke


HALYSAAH 78


Bayan Khaleesat tayi karatun da zata yi ta kashe laptop dinta ta ajiye sannan ta saka hijab ta fito daga dakin don tun da ta dawo bata ci abinci ba gashi har karfe goma ya wuce, downstairs take leke ko zata ga Housemate dinta, Ajay ta gani yana danna wayarsa, hannunsa rike da Can din soft drink, tana ta tsaye a corridor din don da ba don yunwan da take ji ba komawa dakinta kawai zata yi ta hakura da abincin, after a while ta fara saukowa staircase din trying not to make any sound, tun daga nesa take kallon screen din wayarsa ganin kamar hoton da suka yi da Jay daxu a park, tsaye tayi tana ta kallon wayarsa da mamaki, after some seconds taga ya fita daga hoton kasa gane inda ya samu hoton tayi, tasan dai Jay bazai tura masa pictures din ba, to kaddai a status Housemate dinta ya dora hoton, ta shiga uku, sosai taji gabanta ya fadi, lokaci daya Ajay ya juya bayan yayi sensing kamar mutum na tsaye bayansa, ta ɗan koma baya kamar munafuka tana kame kame tace "Kitchen zan je dama" Ajiye wayarsa yayi ya juya da kyau yana kallonta da mamaki, ta langwabe kai sai kuma ta nufi kitchen din da sauri tana ɗan waigen sa, ko da ta fito bata gansa a parlon ba, bayan ta koma daki ta ajiye shayin hannunta ta dau wayarta da sauri ta bude WhatsApp dinta, status din Housemate dinta ta bude taga hoton amma ya rufe fuskarta with the caption "Halysaah" da yayi ma hoton, to amma wanda ta gani a wayar Ajay fuskarta a bude yake, ta dinga kallon hoton duk da fuskarta a rufe yake, bata san sanda murmushi yayi escaping lips dinta ba don sun yi kyau sosai, har ta ajiye wayar sai kuma ta dauka tayi masa reply din picture din tace "What if gal frnd dinka ta gani" ajiye wayar tayi ta dau cup din shayin da ta ajiye tana juyawa a hankali, taji wayarta yayi vibrate alamar shigowar message, daukan wayar tayi taga ya mata reply yace "Ke ba Gal frnd dita bace? Ai ke zabina ce, ita kuma zabin iyayena" Hmm kawai ta mayar masa sannan ta kashe data dinta ta ajiye wayar, lokaci daya duk jikinta yayi sanyi tana maimata zabin iyayensa da yace a ranta, duk yunwan da take ji haka nan ta neme sa ta rasa shayin ma bata wani sha sosai ba, bayan ta gama shirin kwanciya ta dauro alwala ta fito sannan ta kashe wutan dakin ta kwanta, wayarta taji na vibrate ta jawo wayar a hankali tana dubawa taga Housemate dinta ne ke kiranta, sai da ya kusa katsewa tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, yace "Why did you go offline Halysaah?" Ta ɗan yi murmushin karfin hali tace "Na je nayi alwala ne zan kwanta" Yace "Ohk, kina da class gobe ne?" Ta ɗan yi shiru, duk da bata da shi tace "Eh ina da...." Jay yace "Yaushe?" Tace "Da safe" Yace "Ohk, na tsaya wani aiki ne a system dina shi yasa ban dawo ba, may be we will meet in school tomorrow in sha Allah" Tace "Allah ya kai mu" Yace "Ameen, Good night Halysaah, naga kamar kin fara jin bacci ko?" Cikin sanyin murya tace "Uhm, sai da safe" Yace "Allah ya kai mu lafiya" Daga haka ya katse wayar sa, Khaleesat ta ajiye wayar hannunta ta juya ta lumshe ido. Da safe Khaleesat na saukowa downstairs taga parlon soo tidy, kamshi sai tashi yake ta ko ina via diffuser da ta gani a parlon, makalewa tayi jikin staircase tana ta kallon parlon, ai kuma ta shiga uku da gori, after a while ta nufi kitchen, ta window din kitchen din take kallonsa don karamin garden ne a waje, entrance din garden din yana ta wajen Garage, tunda ta zo apartment din bai fi sau biyu ta shiga wajen ba, press up yake yi a wajen, juyawa tayi ta kalli Yoghurt da diff kind of berries da granola da nuts sai kiwi and apple dake ajiye kitchen din, nan ta gane parfait zai hada, har zata hada masa wata zuciyar tace ta kama kanta tayi abinda zata yi ta fita, noodles ta dauko zata dafa, tana cikin dafa noodles din ta daga kai taga ya fita daga garden din, bayan ta gama girkin ta fita daga kitchen din zuwa dakinta, after almost 20 mins ta sake saukowa downstairs ta shiga kitchen din, har sannan fruits din suna wajen, ta ɗau karamin bowl ta fara tsinkar different berries din wajen ta yanda bazai gane ta taɓa masa ba, tana wankesu a sink ta fara sha, da sauri ta juya tana kallon kofar kitchen din tayi ido hudu da shi, ita kanta bata san dalilin da yasa ta fara dariya ba, ta ciro berry din da ta kai baki tace "Wanke maka su zan yi fa, so that i can help you dice them" Tana fadin haka ta ajiye bowl din hannunta ta dau wuka zata fara fere Kiwi fruit dake wajen, taji yace "Zo ki fita ki ban waje" Ta ɗan kallesa tace "I want to help you wash them...." Tana ganin kallon da yayi mata, ta ajiye wukan ta wanke hannunta a sink sannan ta ajiye masa bowl din Berries din da ta diba a kofar sauran fruits din, kofa ta nufa ta bi gefensa ta fita daga kitchen din ya bi ta da kallo yace "Ke da baki iya gyaran gidan da kike ciki ce zaki wanke ma mutum abinda zai ci" Khaleesat ta juya ta kallesa dama tasan sai yayi maganar nan, tace "Tun da kai ka gyara ba shikenan ba, ai don ina zuwa school ne...." Yace "You are dirty dai Malama, do not use school to cover ur untidiness" Yana fadin haka ya karasa cikin kitchen din, ta tsaya bakin kofar tana kallonsa taga ko da Liquid wash zai wanke fruits din karewar tsafta, sai da ya fara tura bowl din Berries din da ta diba zuwa can far end of the kitchen yanda bazai dinga ganinsa a kusa da shi ba sannan ya fara wanke fruits din a sink, bayan gishiri har da Venegar yayi using wajen wanke fruits din, a ranta tace to ai wannan ba sabon abu bane kowa na yi, ita tsakaninta da Allah take jiran taga ya zuba liquid wash wajen wanke fruits din, amma taga bai yi hakan ba, tana ta tsaye jikin kofar kitchen din har ya gama hada lafiyayyen parfait dinsa, ta shiga kitchen din ta dau bowl din Berries dinta da ya gantalar gefe daya ta ajiye kusa da shi ta kallesa, ko kallonta bai yi ba, can ta ga ya jawo sauran Yoghurt da ya rage ya tsiyaya mata a bowl din ya ci gaba da abinda yake yi, dariya ya bata amma ta dake bata yi ba, tana ta kallon rich parfait dinsa da yaji fruits da Granola da Nuts, tana kallo ya dau zuma ya tsiyaya a kai, dai dai nan aka bude kofar parlor, ya ajiye zuman hannunsa ya karasa kofar kitchen din don ganin wanda ya shigo, da sauri Khaleesat ta kai hannu ta lakaci honey din da yoghurt, akan idonsa don har ya juyo ya dawo cikin kitchen din, komawa baya tayi da sauri, bai ko kalleta ba ya dau spoon yayi scoping dai dai inda ta saka hannu sannan ya ajiye spoon din a sink, ita dai bata san ya aka yi ba kawai ganin bowl din parfait din tayi ya kife a kasan kitchen, ya koma baya yana kallon parfait babu ko kiftawa, tun tana daurewa har ta kasa ta dafe base cabinet din kitchen din ta tuntsire da dariya kamar an aikota, Ajay dai kallon Parfait din kawai yake a kasan kitchen din, after some seconds ya shafa kansa trying not to laugh too, don dariyarta kadai ya isa ya saka mutum yayi dariya bai yi niyya ba, irin dariyar muguntar nan kawai take yi, ita kuwa ba abinda ya bata dariya ganin bai tsam mata ba gashi duk sun tuntsire a kasan kitchen, kuma shi ya kifar da kayansa da alama, kawai ya juya ya fice daga kitchen din ta bi sa da kallo tana kyalkyala wani sabon dariya, sai kuma ya sake dawowa yana kallonta yayi kasa da murya yace "Kin ga idan ina abu a kitchen kika sake shigo min i will fling you out of this window, ai ni ban san ke mayya bace" Yana fadin haka ya sake ficewa daga kitchen din, Khaleesat dai bata fasa dariyan da take ba, da ta kalli bowl din da ya ɗan tsiyaya mata zallan yoghurt sai ta kalli rich parfait dinsa dake kasan kitchen a kwance, sai ta kara kwashewa da dariya, ta dade abu bai bata dariya kamar haka ba, tayi dariyarta ma'ishi sannan ta fara gyara kitchen din, sai kuma ta fara jin tausayinsa don duk effort dinsa bai sha ko spoon daya ba, gwara ita ta ɗan lasa zuma da yoghurt, the incident was so funny to her, haka duk ta kwashe fruits din da granula dake kasa tayi disposing a shara, bayan ta gama goge kitchen din ya dawo fess ta fito parlor taga Housemate dinta zaune a parlon yana danna wayarsa, tana murmushi ta karasa cikin parlon ta zauna sannan ta gaishesa, ya daga kai ya kalleta ya amsa, bata sake cewa komai ba, shi ma haka, after a while yace "Ba kince zaki school da safe ba?" ta langwabar da kai tace "Kawai fasawa nayi" Juyawa tayi ta kalli Ajay dake saukowa downstairs fuskarsa babu yabo babu fallasa yana rike da makullin motarsa, ta bi sa da kallo trying not to start another laugh har ya fice daga parlon, sai kuma ta kalli Jay ta fara basa labarin abinda ya faru a kitchen, she couldn't hold her self anymore ta dinga kyalkyala dariya har da saukowa daga saman kujera, shi dai Jay kallonta kawai yake, sai kuma ta dena dariyar da take tace "Isn't it funny?" Jay yayi murmushi wanda iyakarsa lips yace "It is, sai yace maki me?" Tace "He was very shock too, nasan da ya san abinda zai faru kenan da ya debar min, Allah ne ya kamasa, ga shi yayi stressing kansa ya gyara gidan nan gaba daya yau" Tana dariya ta kare maganar, Jay yace "Gaskiya ne, amma baza ki je school ba me yasa kika ce min za ki je?" Shiru tayi, sai kuma tace "Kawai da gari ya waye na canza mind" Jay yace "Ohk" Wayarsa ne ya fara vibrate ya mike yace "Zan fita sai anjima" Khaleesat na kallonsa tace "Kayi breakfast ne?" Yace "Nayi" Tace "Ohk, byee" Juyawa yayi ya nufi kofa ta bi sa da kallo har ya fita.... Khaleesat na kitchen da yamma bayan ta dawo school taji an bude kofar apartment dinta, sosai taji gabanta ya fadi don dama tunda ta dawo taga ba kowa apartment din take a tsorace, sai da taji muryar Ajay a parlon sannan hankalinta ya kwanta, jingina tayi jikin cabinet din kitchen din tana kirga kwanakin da taga Jay last, after a while ta kashe wutan girkin don ta gama, ta dan leka parlon taga Ajay da wani abokinsa ne bayerabe yana gwada masa abu a Laptop dinsa da alama shima Phd yake yi, fitowa tayi daga kitchen din ta gaida abokin ya amsa yana kallonta, sai kuma ya kalli Ajay yace "Is she ur sister" a takaice Ajay yace "Yeah" Yana ci gaba da nuna masa abinda yake nuna masa, da broken English abokin yace bazai basa ita ya aura ba, Ajay ya daga kai ya kalli Khaleesat yace "Ke dalla malama wuce ki ba mutane waje" Khaleesat ta kallesa da mamaki don ita dai ba tsayuwa tayi a parlon ba, sama ma zata wuce, Femi na kallon Ajay yace "I am very serious Prince, i will marry her as far as una go

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login