Showing 27001 words to 30000 words out of 257722 words
Chapter 10 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar
da yake kawo min ban taɓa amfani da ko daya ba duk na tara masa kayansa waje daya, ga atamfofinsa nan da turarurruka da tarkace, ba ruwana ban yi amfani da su ba, ke ma Zahra'u inda abunsa da kika san ya taɓa baki ki tattaro su waje daya, shi Ali ina ma yayi amfani da nasa shi ya sani, sai ya shiga kasuwa da wuri wuri" Ita dai Umma tayi shiru bata ce komai ba, Khaleesat kuwa kuka take a hankali, Cikin sanyin murya Umma tace "Kin mance abinda ke kasa ne Nenne, ai yanzu ba maganar wai abinda ya bamu bane damuwar" Nenne tace "Yo ina ruwana da abinda ke ƙasa, ko ina ruwan yarinya da abinda ke kasa? Sai a ma jikata auren dole kike nufi kenan? Ni fa tun asali katon mutumin nan bai min ba sam, ayi mutum ba fara'a ya shigo maka sandan sandan ya fita gansan gansan? A duba fa wannan lamari, da kyar kaga murmushinsa kamar rikakken ɗan ta'adda da aka kusa yi ma preedom, yo wannan uban kudi na ubansa wa ma yasan ko ta'addancin suke da garkuwa da jama'a, hatta ruwan gidana gansamemen mutumin nan bai taɓa sha ba, yanda na ajiye masa haka yake barin min tsiyata bai san yarana mata ruwan gora suke siya min ba ya zata durawa nake, haka zai zauna maka kamar sarki yayi ta danna waya ga gidan er banza ya shigo, to ban isa da Ali ba kannensa mata ma basu isa da shi ba, shi kawai ta kansa yake a rayuwar nan baya duba makomar er da ya haifa a cikinsa, ko dan yaga yaran rakacaa an haifa masa ne ba kwantrol oho, gashi ba jin maganar yayyin uban nasa zai yi ba balle ince ku je ku samesu, in kuma muka ce mu tafi mu kai rahotu gidan yan sanda daga karshe mu za a kulle, to ni Ramatu ya zan yi? Amma dai ba komai zan aika a kira min Alin anjima, hatta batun daurin auren sai jiya da za a daura muke samun labari" A hankali Umma tace "Shi ma Malam din shekaranjiya da yamma suka kirasa suka sanar masa ga abinda suke so za ayi" Nenne tace "Tirrr, duk sun rainamu sun mayar da mu yan iska kawai, na tabbata shi kansa Alin bai taɓa rokon Awdul din naira biyar ba balle uban Awdul" Umma ta girgiza kai tace "Bai taɓa ba kam, jarabawa ce kawai Allah ya dora mana babu yanda mu ka iya" Nenne tace "A'a har da dai iskanci, ku baku da baki? ke da er taki baza ku iya kwatar en cin ku ba, ita kadai ce mace a gidan? Tun asali dama kin maida kanki gantalalliya a gidan" Umma dai tayi shiru, Nenne tace "Ko kuma kawai ku tafi gida zan daidaici lkcn da zai koma gida da magariba in taho gidan" Umma tace "Toh shikenan Nenne" a haka Khaleesat da Ummanta suka bar gidan bayan Nenne ta dama mata fura da nono ta tilastata ta sha. Khaleesat na kwance dakin Ummanta wajen karfe shidda na yamma, har zuwa sannan ta kasa cin komai tun bayan furan da ta sha gidan Nenne, tun da suka dawo gida take karatun qur'ani don ta rasa me ke mata dadi a duniyar kawai bata son tayi ta daga ma Ummanta hankali yasa ta hakura da kuka sai na zuci kawai da take yi, gaba daya taji duniyar yayi mata zafi, da ta tuna wai fa ita matar aure ce yanzu kuma matar Abdul, sai taji dama kawai Allah ya dau ranta ta huta, bayan taji she is exhausted da karatun qur'anin da take tayi shine ta kwanta gefen katifar Ummanta, tayi nisa tunanin da take jin hawaye na taruwa idonta ta mike zaune tana kallon Ummanta dake gyara kayan su Islam a dakin tace "Umma ina wayarki?" Umma ta kalleta tace "Ko sati ba ayi ba na nemeta na rasa an dauke a gidan nan" Khaleesat tayi shiru tana kallon Ummanta, sai kuma ta jawo handbag dinta a hankali ta bude ta ciro wayar da Jay ya bata duk da babu SIM card a ciki, she just want to do something that will keep distracting her from her worries, har zata shiga game sai kuma ta fasa ta shiga gallery din wayar, ta ɗan yi jim na few seconds kafin ta bude hotunan, a hankali take flipping tana kallon each and every image of him and AJ, sai a sannan ta lura da kaman da suke yi even though it's not obvious, wani hotansu tare ta tsura ma ido ganinsu cikin shiga ta alfarma irin ta sarauta, ita dai tana ta kallon hoton babu ko kiftawa, sai kuma tayi flipping zuwa next image, haka ta dinga ganin ire iren hotunan, wani taga Jay shi kadai wani taga Ajay shi kadai, ko kuma ta gansu tare, with horses and so many things related to gidan sarauta, kashe wayar tayi a hankali ta mayar cikin jakarta ta ajiye jin muryan Babanta ya shigo gidan, ya ɗaga labulen dakin Ummanta yana kallonta yace "Ki fita ga Abdul can ya zo yanxu" Sosai gaban Khaleesat ya fadi ta dinga kallon Babanta bata ko kiftawa, Umma ta juya ta kallesa tace "Ta fita kuma Malam? Dama ana haka? Ai ina ga ba sai ya zo ba sai ya jira har zuwa sanda zata tare ko" Malam Ali da ya bude baki yana kallonta yace "Wato dai duk wani salon dauko min magana kun iya shi Zahra'u, in ya zo ta fita sai aka yi yaya? Addini ne ya haramta hakan ko kuwa shirmen ku? Kuma da kike batun tariya ko gobe yace yana bukatar ta tare mu muna da ja ne dama?" Umma tace "Ai ko muna da ja Malam, tunda baza mu dau yarinya haka kawai mu kai ta dakin miji ba, duka duka ma yaushe ta dawo kasar" Khaleesat ta fashe da matsanancin kuka tana jin kamar zuciyarta zai fashe ta huta, Babanta da ya bude baki yana kallonta yace "Ni kike neman tona ma asiri ko ko ya kike so inyi? Sabon magana za ku ja min ke da uwarki kenan? In ma ba yanzu za a tare ba tunda ya zo ai sai ki fita ku gaisa tunda ba haramun bane, in kun gaisa sai ki dawo cikin gida" Khaleesat taki cewa komai sai kuka take, Ya daka mata tsawa yace "Kar ki ga ina lallabaki don uwarki, zaki tashi ki fita ko sai na rarrade ki da icce" Khaleesat na kuka ta sauka daga kan gadon, Umma da hawaye ya cika idonta ta kauda kanta, Khaleesat ta dau Hijab dinta ta saka ta fita daga dakin tana kuka sosai, Kishiyoyin ummanta dake zaune tsakar gida duk suna sauraron abinda ke faruwa sai tabe baki suke, ganin Malam Ali ya bi bayan Khaleesat, Mama Shatu tace "To rakata wajen nasa zaka yi ne Malam?" Sai kuma ya juyo da sauri yace "Au to" Ya nufi ɗan karamin dakinsa dake tsakar gidan, Mama Zubaida ta tabe baki tace "Ma ji ma gani dai" Khaleesat na fita kofar gida hawaye na sauka idonta taga motarsa wanda ke dauke da tinted glass yayi parking dai dai inda su AJ suka tsaya jiya, ko saukowa bai yi daga cikin motar ba, hawaye na bin fuskarta ta tafi ta tsaya kusa da motar taki budewa kuma tasan yana kallonta, after almost 5 mins taga ya sauke glass din motar yace "Ni zan sauko in same ki?" Ita dai taki kallonsa, kuma taki cewa komai, after few seconds ta bude gaban motar a hankali ta shiga amma ta ki kulle motar, yace "Sauron unguwan ku zaki cika min a motata, are you in ur right senses?" A hankali ta ja motar har sannan taki yarda ta kallesa ta kulle, gabanta sai faduwa yake don jin muryarsa take kamar ana tsira mata allura a kunne, Lokaci daya ta juya da sauri tana zaro ido ganin ya zuge glass din ya tada motar ya kara volume din sautin da yake ji sannan ya ja motar, a rikice ta fara kokarin budewa motar taji a kulle gam, ta kwala wani azababben kara tace "Na shiga uku na lalace, don girman Allah kayi hakuri ka rufa min asiri ina zaka kai ni? Ka bude min in sauka...." Ko kallonta bai yi ba fuskarsa babu yabo babu fallasa yake driving dinsa idonsa na kan hanyar dake gabansa, ta rikosa da hannu biyu cikin gigicewa tana masa magiyan ya bude mata motar, bai yi wata wata ba ya sauke mata wani lafiyayyen back hand slap a fuska, sai da taji dumm na few seconds, lkci daya jin ta da ganinta ya dauke na ɗan lokaci, duk da haka bata sake sa daga rikon da tayi masa ba tana kururuwan ya bude mata motar, ya fincikota ya jefar kan kujeran motar cikin kaushin murya yace "Kika sake taɓa ni sai na wanka maki wani marin" Lokaci daya duk jikin Khaleesat ya mutu saboda shock, ta dinga sauke numfashi da kyar idonta na ganin dishi dishi daga marin da yayi mata tana kallonsa, shi dai driving dinsa kawai yake fuskarsa babu yabo babu fallasa......
*
HALYSAAH 29
Sai da Khaleesat taga sun bar unguwansu gaba daya sannan reality yayi hitting dinta ta kara fahimtar me Abdul ke da niyyar yi, she felt so helpless at this point, ta jinginar da kanta jikin kujeran motar hawaye masu zafi na sauka idonta ta kasa cewa komai, shi dai driving dinsa kawai yake bai ko kalleta ba, ganin tafiya kawai yake ta juya tana son ko hakuri ne ta bude baki ta basa amma tsoron kar ya sake marinta yasa ta kasa don babu alamar rahama a fuskarsa, ta rufe fuskarta da hijab din jikinta hawaye wasu na bin wani a idonta, tsabar tashin hankali da firgicin da ta shiga a wannan moment din kilan da za a duba jininta za a ga ya hau, bayan tafiyar kusan minti talatin taji ya tsaya cak, da sauri ta sauke Hijab dinta zuciyarta na bugawa tana kalle kallen inda suke, taga dai dai wani eatry ya tsaya, ita dai kallonsa take har sannan hawaye bai daina sauka idonta ba, ya sauka daga motar without looking at her ya kulle, ta bi sa da kallo har taga ya shiga gidan cin abincin, ta fashe da matsanancin kuka tana waige waigen wajen cikin tashin hankali, babban wajen cin abinci ne sosai, ga mutane suna ta kai kawo a gurin, glass din motar ta fara bubbugawa da hannunta amma taga nobody is noticing her, ta fara kalle kallen cikin motar taga bunch of keys da ya ajiye ta dauka da sauri ta fara bubbuga glass din motar da shi da karfi, hakan ya ja attention din wani mutumi da ya fito daga cikin eatry din zai shiga motarsa dake kusa da inda Abdul yayi parking, ita dai bata fasa bubbuga glass din ba tana kuka sosai tana cewa don girman Allah ya taimaketa, da alama baya ganin cikin motar saboda tinted glass din, ya zaga ta gaban motar yana duba ciki, ta dinga kuka tana cewa don Allah ya taimaketa, ba ta damu ko yana jin abinda take cewa ba ko baya ji ita dai kawai ya taimaketa, mutumin ya tafi ya taho da wani security dake wajen, dai dai nan wani soja da ya fito eatry din zai shiga motarsa shi ma ya karasa gun motar kan kace me attention din jama'an dake gurin gaba daya ya dawo kan motar Abdul, Khaleesat bata fasa kukan da take ba duk da ta samu relieve ganin mutanen da suka zagaye motar wasu na kokarin mata magana suna haska cikin motar da fitila, mutane duk suka tsaya aka yi cirko cirko a kusa da motar, ita dai kuka me sauti kawai take kamar ranta zai fita, babu wanda bazai ce sato ta aka yi a lkcn ba, bayan wasu mintuna Abdul ya fito daga Eatry din rike da abinda ya siyo, yana zuwa inda yayi parking yaga jama'a jikin motar ya tsaya yana kallon ikon Allah, Security din dake tsaye wajen don yaga sanda Abdul yayi parking ya shiga eatry din, ya kalli sojan dake tsaye yace "Ga me motar nan ya fito" Da wani expression Abdul yace "What happened?" Sojan yace "Bude motar ta sauko Malam" Abdul yace "Ban gane in bude mota ta sauko ba, matata ce a ciki" Sojan yace "Ai bamu mu sa ka ba, mota kawai zaka bude ta sauko, ba wani abun tashin hankali bane ai" Nan jama'an wajen suka dinga cewa ya bude motar suna hayaniya, Abdul ya bude motarsa da Key din hannunsa daga inda yake tsaye, Khaleesat na jin alamar yayi unlocking din motar ta bude ta sauko da sauri tana kuka, Sojan ne ya fara mata magana yana nuna mata Abdul yace "Waye wannan?" Ta fashe da matsanancin kuka muryarta na rawa tace "Ni ban san shi ba" Kallonta Abdul ya dinga yi da mamaki babu ko kiftawa, hayaniya sosai mutanen wajen suka hau yi sojan na kokarin calming dinsu, Sai kuma ya sake kallon Khaleesat yace "Baki san shi ba? To garin yaya kika shiga motarsa?" Tana shessheka tace "Kawai dauko ni yayi a unguwanmu wallahi, ni ban san shi ba" Tuni matasa yan zaman kashe wandon dake wajen suka fusata suka zagaye Abdul suna dure duren ashar suna kokarin fara mazgarsa, gaban Eatry din ya cika da jama'a an zo kallo wasu har sun fara video, with the intervention of the soldier and the security men da wasu responsible mutanen dake wajen aka saka Abdul cikin motar Sojan don tsaf sun kula matasan za su yi aika aika ne a wajen, wannan opportunity din Khaleesat tayi using cikin dubara ta sulale cikin jama'ar wajen without letting anyone to notice her don gaba daya hankalin mutane ya koma kan Abdul a wajen, a haka ta samu ta tsallaka titi ko waigawa bata yi ta afka wani layi, nan ma tayi ta tafiya da sauri da sauri gabanta na faduwa, duk inda taga alamar hanya ce haka ta dinga bi ba tare da tasan inda zata ba, tafiyar kusan minti arba'in tayi a kafa hawaye na zuba idonta, ko sanin unguwan da take bata yi ba, daga karshe tsabar yanda ciwon kai ya matsa mata ga jiri dake ta kwasarta ya sa ta samu gaban wani gida ta zauna ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kuka, tana ta zaune for almost 10 mins wani mutumi dake ɗan nesa da ita yana zaune kofar gidansu ya mike ya nufota, don tun da ta shigo layin ta zauna ya ganta, sallama yayi mata ta dago kanta a tsorace, yace "Baiwar Allah lafiya dai ko?" Ta girgiza masa kai da kyar tana goge idonta tace "Bana jin dadi ne, kuma gida zan je" Yace "Ikon Allah, to ina ne gidan naku?" Without second thought tace "Hotoro" Yace "Hotoro? To bari in samo maki adaidaita sahu sai ya kai ki" Ta gyada masa kai cikin rawan murya tace "Nagode" Ya juya ya bar wajen, bayan wani minti goman sai gashi ya dawo cikin adaidaita sahu bayan yaje har bakin titi ya samo mata adaidaita sahun, ya sauko daga ciki yana kallonta yace "Toh ga adaidaita sahun na samo maki Hajiya" Tace "Nagode" Ta mike da kyar ta dafa adaidata sahun sannan ta shiga ciki, mutumin ya ciro wayarsa ya mika mata yana kallonta yace "Ki saka min lambarki sai inji ko kin isa gida lafiya" Ta girgiza masa kai a hankali tace "Matar aure ce" Mutumin yace "Ohh, na gane to, Allah ya tsare Hajiya, Allah ya baki lafiya, na biya sa kudinsa ba sai kin basa ba" Ta gyada masa kai tace "Nagode, Allah ya saka da alkhairi" yace "Ameen ya Allah" a haka mai adaidaita sahun ya bar layin. Har suka isa hotoro Khaleesat bata san sun iso ba, sai da me adaidaita sahu ya ankarar da ita, dai dai kofar gidan Gaje ta sa ya tsaya, ta sauka tayi masa godiya ta shige cikin gidan, nan gaban Gaje dake zaune tsakar gida ta zuba tana kuka kamar zata shide, Gaje tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'una, Khaleesah? Me ya faru? daga ina kike haka?" Da kyar Gaje ta lallashi Khaleesat tayi shiru bayan lokaci me tsayi, sannan ta fara gaya mata abinda ya faru, Gaje ta saki salati a rikice tace "Mun shiga uku mun lalace, yanzu gidan yan sanda suka tafi da Awdul din kenan?" Cikin kuka Khaleesat tace "Ban sani ba nima" Gaje tace "To kuwa zaman gidan nan bai kama ki ba Khaleesah, yasan bayan gidanku baki da inda zaki taho a kano da ya wuce gidana ko gidan Nenne, wannan fa ba karamin kess bane, Awdul na zuwa nan ya ganki sai ya zata da hadin bakina kika yi abinda kika yi, ya sa yan sanda su kulleni in shiga uku" Cikin kuka Khaleesat tace "Toh ya zanyi yanzu Baaba Gaje?" Gaje ta mike ta figi gyalenta a igiya tace "Ta shi mu je" Jikin Khaleesat na rawa ta mike ta bi Gaje suka fita daga gidan, da kafa suka tafi gidan kawar Aunty Farida da ake ce ma Maman Fu'ad, bayan sun shiga gidan Gaje tayi mata bayanin duk abinda ke faruwa, Maman Fu'ad tunda ta rike haɓa har gaje ta gama bada labari bata iya tace komai ba, Gaje tace "Don haka ki rufa mana asiri Sadiyah ta kwana gidanki zuwa gobe a ga abinda hali zai yi" Maman Fu'ad ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Khaleesat, gwalo ido tayi ganin jinin da ya kwanta idonta tace "Me ya samu idonki?" A hankali Khaleesat tace "Marina yayi" Maman Fu'ad ta saki salati tace "Mari?? Har sai da jini ya kwanta maki a ido? ga lebenki ma a fashe? A'a gaskiya tsinanne ne wannan mutumi" Gaje ta rike haɓa tana kallon idon Khaleesat sai kuma ta fashe da kuka tace "Yanzu wannan har mijin aure ne in ba don Ali ya cuceki ba, dubi fa tafin hannunsa a fuskarta?" Maman Fu'ad tace "Da kyar ma in baya shaye