Showing 234001 words to 237000 words out of 257722 words

Chapter 79 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

ya kalleta ya amsa sannan ya kalli Nenne yace "Kun zo lafiya Baaba" Nenne tace "Wallahi lafiya lau ranka shi dade, na ce ni dai yau a kawo ni in gaishe ka in sa maka albarka don kai din mutumin kirki ne kowa ya shaida, Allah Ubangiji yayi maka albarka ya kare gaban ka da bayan ka, ya rufa maka asiri duniya da lahira, Allah ya albarkaci zuri'ar ka, ya ja da ranka, ya kara maka lafiya da kwanciyar hankali, Allah ya taya ka riko..." Ya gyada kai with calmness yace "Ameen Baaba, Ameen, dama albarkan irin ku abun so ne gare mu, muna godiya kwarai, Allah ya kara girma, madallah" Nenne tace "Ni dai nayi farin ciki da ganin ka, nace duk yanda za ayi yau dai a kawo ni wajen sarki mu gaisa, shi ne na saka Parida kanwar surkata ta rakoni muka taho tare" Mai martaba yace "Madallah, ai ba a jima ba aka kirani ake sanar min wakilan da na tura sun isa can gidan Alhaji Aliyu, kuma anyi komai lafiya har an tsaida lokaci ban san ko sun sanar maki daga Kanon ba" Nenne da ta bude ido sosai tana sauraron abinda Sarki ke cewa tayi kasa da murya tace "Wallahi ba a sanar min ba, kilan Aliyun zai ce a jira in dawo kafin a sanar min, amma nayi farin ciki da wannan abun arziki haka, ai hada zuri'a da kai Mai martaba abun alfahari ne abun farin ciki ne, nayi murna sosai, Allah Ubangiji ya sanya alkhairi..." Maganar da Umma ta kira Aunty Farida zata yi mata kenan kafin shigowar Mai martaba da Nenne ke tayi mata bala'i, Aunty Farida ta dade bata ji farin ciki irin na wannan lokaci ba, she is finding it hard to believe it, yanxu har an aika neman auren Khaleesah kenan amma ko da wasa daga Jay har Ajay babu wanda yace masu komai all this while, kuma kullum sai sun je can gidan Aunty Murja, Nenne ta nuna masa Aunty Farida tace "Kanwar uwar yarinyar kenan uwar su daya uban su daya, ita kanta bata sani ba banda yanxu da muke ji tare..." Sarki ya jinjina kai yana kallon Aunty Farida yace "To Madallah, ke ya sunan ki..." Nenne ta gyara zama tace "Parida, sunanta Parida Isuhu, tun tana er shekara goma Aliyu ya daukota daga gaban iyayenta a Nijar ya kawota gaban yayarta wato uwar wannan jikar tawa da aka je neman aurenta yau, to Ali ne yayi mata auren fari aka zo zaman babu dadi kuma gashi abokinsa ne mutumin saboda ya yarda da shi ya basa ita ga manema kaca kaca ya hanasu, to daga karshe dai da kansa ya amso mata takardarta ya raba auren ganin tana cutuwa gashi ita ba me baki bane sai dai kuka, to tun sannan har yau tana gaban Ali, duk wanda ya zo neman aurenta sai taki basa hadin kai yau shekara bakwai kenan, duk bayan wasu shekaru za su shirya su je gaida iyayensu ita da yayarta a Nijar, iyayen nasu buzaye ne mutanen kirki wallahi, aure me hada mutanen arziki ga shi ya hada zumunci tsakanin Nijar da Najeriya" Mai martaba yace "Wannan gaskiya ne Baaba" Nenne tace "To tun da har mun samu ganin ka har mun gaisa, to ina ga mu za mu zo mu koma Ranka shi dade kar mu shiga lokacin ka" Mai martaba yace "A'a, ku bari a karasa da ku bangaren fulani ku samu ku ci wani abun kafin ku tafi Baaba, bazai yiwu ku tafi baku sha ko ruwa ba a masarautar nan..." Nenne zata yi declining offer din nasa sai ga kanwar Aunty ta shigo parlon da sallama tana rike da bowl din fresh fruits, tare da Auntyn suke amma ita tana can baya tana tafe tana waya don wani lkcn in har Aunty zata kawo ma Mai martaba abun ci ko sha kanwarta ke rike mata har zuwa parlonsa in ta ajiye sai ta fita, Sarki na kallon Zuwaira yace "Ki shiga da baƙin nan cikin gida Zuwaira, ayi masu duk abinda ya kamata" Zuwaira ta kalli Nenne sai kuma ta kalli Aunty Farida dake kallon direction daban hakan yasa bata ga fuskarta da kyau ba kawai dai tasan fara ce kamar za a latsa ta jini ya fito, kallon Mai martaba tayi da ladabi tace "To ranka shi dade" Ta kalli Nenne ta gaisheta a takaice sannan tace "Mu je" Nenne ta mike bayan ta amsa gaisuwanta, Aunty Farida ta sauke Nikab dinta sannan ta tashi ita ma, hada ido suka yi da Mai martaba, tayi masa sallama ta bi bayan Nenne dake biye da Zuwaira, sun fita daga parlon kenan sai ga Aunty cikin shiga ta alfarma ta sha gwala-gwalai tana taƙu dai dai, daga sama har kasa take kallon Nenne da Aunty Farida dake sanye da Nikab, Aunty ta kalli Zuwaira tana yatsine fuska tace "Su waye wannan kuma Zuwaira?" Zuwaira ta taɓe baki tace "Oho, Mai martaba ne yace in shiga da su cikin gida, a parlonsa na same su" Nenne ta kwantar da murya tace "Ina wuni Pulani, baƙi ne daga Gombe...." Ko amsa gaisuwan Nenne Aunty bata yi ba ta shiga parlon Mai martaba, Zuwaira tana kallonsu a walakance tace "Mu je don Allah ina da abinda zan yi ni kam...." Bata jira cewarsu ba ta ci gaba da tafiyarta, Nenne ta kalli Aunty Farida, sai da taga Zuwaira tayi nisa sannan tayi kasa da murya tace "Parida kira mana Ahamad kice mun gana da Sarki ya fito ya maida mu gida" Ko Nenne bata ce haka ba dama Aunty Farida bata yi niyyar bin Zuwaira ba, haka nan suka canza hanyar da zai sada su da Compound Aunty Farida na kokarin kiran Ajay ta wayarta... Aunty na shiga parlon Mai martaba tana kallonsa tace "Ranka shi dade, wasu baƙi ne wannan aka kawo su har cikin parlon ka? Kuma ni ban taɓa ganinsu ba alamar babu abinda aka hada da su, ita dayar Nikab ma ta saka balle in ga fuskarta, su waye ne su da za su shigo har wannan parlon bayan ga can inda ake sauke baƙi?" Calmly Mai martaba yace "Ina ce kin gaisa da su ai?" Aunty ta ɗan hade rai tace "Eh, wai daga Gombe suke in ji tsohuwar" Mai martaba yace "To haka ne" Mikewa yayi yace "An sanar min ina da baƙi a fada yanxu, zan je in same su Fulani"


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
07087865788


Bear with me pls, I am not well

HALYSAAH 94

Calmly Ajay ke driving bayan sun baro masarautar, yana ta sauraron Nenne da tun fitowar su take fadin irin kirkin Mai martaba tana sa masa albarka, shi dai ba abinda yace don kawai gani yake ba a tare su da kyau ba, yasan dai Abbansa zai sake masu kamar yanda ya saba yi ma kowa amma mutanen cikin masarautar will never do so, ita dai Aunty Farida hankalinta na kan wayarta, Sai duk yaji bai ji dadi ba don ya fahimci ko ruwa basu sha ba balle har a basu wani abinci, ko da gangan Aunty zata iya hanasu barin ace ta samu labarin shi ya kawo su gidan, Nenne tace "Toh wai Ina Ahamad din, ko a masarautar ma fa bamu gansa ba" Sai a sannan Ajay yace "Ya je ajiye Baabarsa unguwa" Nenne tace "Allah sarki, iya sarki kawai mu ka samu muka gaisa da, kai ma kaga ko Baabar ka bamu gani ba" Ya ɗan yi shiru, sai kuma yace "Ni Mahaifiyata ta rasu" Nenne tace "Allahu Akbar, Allah sarki, Allah ya ji ƙan ta, ya gafarta mata, to ko dai kishiyar baabar taka muka gani za mu fito parlon Mai martaba, wata tana nan ita ba fara ba, sannan tana ɗan da narkeken jiki ba can can ba, tana da matsakaicin tsayi" Ajay yace "Eh..." Nenne tace "Amma dai bata da kirki kwata kwata, saura kadan ta walakanta mu in gaya maka" Ajay ya kalli Nenne ta madubi yace "Ta maku magana ne?" Nenne tace "Ina fa, ina gaisheta ko amsawa bata yi ba ta sha gwala-gwalai, ni na zata ma uwarka ce shi yasa na ja bakina nayi shiru ban gaya maka ba" Ajay yayi shiru, kuma bai yi mamaki ba kwata kwata, after a while yace "Ku yi hakuri, yawanci bata son baƙi dama" Nenne tace "To er sarkin wani gari ce take wannan uban girman kan haka da rashin son talakawa?" Ajay ya ɗan yi murmushi bai dai ce komai ba, sun yi tafiyar kusan minti talatin kiran Mai martaba ya shigo wayarsa, dagawa yayi ya kai kunne tare da sallama, after some seconds yace "Eh muna hanya ne yanxu zan maida su, na zata kun yi sallama ranka shi dade...." After few more seconds ya ajiye wayar ya kalli Nenne yace "Dama baku yi sallama da Sarki ba?" Nenne tace "Cewa yayi a shiga damu a bamu abun sha, da naga ba arziki yasa muka ki bin yarinyar tana nan wata kitiɓir kitiɓir da ita, dama Parida da nasani ba zuwa zata yi ba don bata son rainin wayo" Ajay yace "Ohk, yanxu yake gaya min ai baku yi sallama ba" Nenne tace "Tun da mun gansa ai an wuce wajen kawai, wataran za a sake haduwa in sha Allah" Suna kusa gidan Aunty Murja after 40 Mins ride Ajay ya ajiye wayarsa da yake driving yana dannawa, bayan sun shigo unguwan ya kalli Aunty Farida yace "Mai martaba ya bada sako a baku, na tura a account din Jiddah" Aunty Farida ta ɗan yi shiru, sai kuma tace "To mun gode Allah ya saka da alkhairi" Nenne tace "Wallahi mu ba don ya bamu komai muka je gaishesa ba, banda shi din babba ne ai da nace kawai a maida masa, amma dai babu laifi, don Allah kayi masa godiya in ka koma gida tunda bamu da wata hanyar yi masa godiya" Ajay yace "In sha Allah" Suna shan kwanan gidansu Aunty Murja, Nenne ta fara hango Khaleesat karkashin bishiyar mangwaro dake gaba da gidan Aunty Murja da dogon sanda a hannunta ita da yaran gidansu Aunty Murja tana tsalle tana plucking Mangwaro, tsohon zanin Aunty Murja ta daura sai er karamar Hijab da slippers a kafarta, Nenne taji kunya ya lullubeta ta rike haɓa tace "Kwance fa muka baro ta sheme sheme daxu ba lafiya, yanxu meye wannan take yi cikin 'ya yan cikinta fisabilillahi?" Khaleesat bata hangosu da wuri ba don da suna shan kwana taga motar zata gudu ta shige gida tun basu karaso ba, sai kawai yara taji suna Nenne Oyoyo bayan sun ga motar, ta juya suka hada ido da Ajay dake kallonta a gaban motar, sai yanxu ya kara tabbatar da ashe yarinya ce er karama sae rashin kunya idan ta samu waje, Tuni Nenne ta sauka daga motar tana kara yi ma Ajay godiya, Khaleesat ta bi bayan Nenne da sauri zata shige cikin gida, Nenne ta hade rai tace "Baki da kai ne, baza ki je ki gaishesa ba tunda kin riga kin kunyata mu, meye hadin ki da bishiyar mangwaro kamar mayya, yanxu da tare muke da Ahamad din shi ma haka zae ganki kamar almajira" Khaleesat ta wani turo baki tace "To haka zan je, ai ba sai na gaishesa ba" Nenne tace "Ina ruwan sa dake idan kin je a hakan? Wannan ai ba sa'an yin ki bane, kina ganin mutum kamili ga nutsuwa wanda magana ma sai ya ga dama, ai ke Ahamad din shi ne dai dai ke shi zai dau ko wani kalar shirmenki da wauta tunda shi faram faram yake, yanxu banda shirme godai godai dake ki shige cikin yara kina tsalle zaki tsinko Mangwaro da kodadden zanin Murja" Khaleesat tace "Wallahi bazan je ba, ai ba wajena ya zo ba" Nenne tace "Ni zaki kunyata? Mutumi ya gan ki kice baza kije ki gaishesa ba dubi yanda yayi ta sintirin zuwa unguwan nan da Ahamad suna zuwa duba ki, sannan ya zo yau ya dauke mu ya kai mu har gaban ubansa yau, ni dai ki rufan asiri ki je ki gaishesa, ai babu dadi haka Khaleesah, dama bai ganki bane wannan daban" Khaleesat ta kalli Aunty Farida dake tsaye jikin motar suna magana da Ajay, can ta fara tafiya zuwa wajen, tana isowa Aunty Farida ta wani kalleta sai kuma tayi ma Ajay sallama ta bi bayan Nenne zuwa cikin gida, Khaleesat ta jingina jikin motar tana kallon wani direction daban, dama tun shekaranjiya take jin haushinsa baya ce mata ya jiki duk ciwon da take ta yi, sai dai kawai ya zo yayi ta kallonta, tada motarsa yayi ita dai bata matsa jiki ba kuma bata kallesa ba, taji yace "Baza ki bar nan ba??" Sai a sannan ta juya ta kallesa, yana kallonta da kyau yace "In kika samu waje ba karamar kazama bace ke, i am telling you this for free...." Ita kanta bata san me yasa ta fara dariya ba kamar warce ake yi ma cakulkuli, reverse ya fara yi ta zaro ido ta koma baya tana kallonsa tace "Buge ni kake son yi?" ko kallonta bai yi ba a haka ya juya ya bar unguwan, kallon kanta tayi daga sama har kasa, sai kuma ta taɓe baki tayi wucewarta cikin gida yara na biye da ita da Mango din da suka tsinko... Da daddare Ajay na zaune parlon Abbansa yana saurarensa kansa a kasa, Mai martaba yace "To amma ku menene dalilin ku na boye min gaskiyar lamarin gaba daya? Ko kai ka basa shawaran kar ya gaya min gaskiya? Sannan duk saboda yana son ya aureta ne duk yayi mata wannan hidima?" Ajay yayi kasa da murya yace "Ko daya Abba, need din fadin gaskiyar ne bai yi arising ba sai yanxu ranka shi dade, taimako kuma kai muka yi kwaikwayo don da haka muka san ka, nasan Jawwad duk abinda yayi mata ba yayi mata bane saboda yana sonta da aure at first, he did all what he did for God sake ba don ya aureta ba, tausayinta ne yayi leading har yaji zai aureta, kuma idan ba auren tayi ba tsohon mijinta will keep on hunting her" Mai martaba yace "Kuma duk zuwa biyun da nayi Amurka tare nake ganin ka da yarinyar a maimakon Jawwad din ae" Ajay ya kallesa, sai kuma ya sauke kansa yace "I helped him with some responsibilities too" Mai martaba yace "Then why were you trying to cover that up? Kace komai shi yayi" Ajay yace "I am not hiding it sir, we were all protecting her from her Ex differently, shi yasa har kake zuwa kake samunta a gidan..." Mai martaba yace "Duk yanda zaka kare kanka you are very good at that Junaid, shi kuma Jawwad always take the Consequences no matter how deep it is for you" Ajay yayi shiru trying to understand what his dad meant, after some seconds Mai martaba yace "Shikenan.... Kai ya batun naka maganar auren?" Ajay yayi shiru bai ce komai ba don shi kansa ya gaji da tsara new excuse kullum, Mai martaba ya ɗan yi murmushi yace "Karyar taka ta kare kenan?" Ajay dai bai ce komai ba. Ranan laraba Nenne ta gama hada kayanta a er jakar da Aunty Farida ta ara mata don a buhu ta so saka kayan nata tun daga Kano, Nenne na kallon Aunty Farida tace "Kar fa su zo su yi ta jiranmu Parida kiyi da jiki" Ita dai Khaleesat na zaune ta jingina da bango a dakin Aunty Murja idonta yayi jajir saboda kuka, Nenne tace "Ke da naga har kin saba da yaran unguwar, baki bishiyar mangwaro baki bishiyar Amburela ke da yara kuna tsinkar 'ya yan itatuwa, to me zai dameki don ance ki zauna kiyi sati biyu ayi maki magani ayi maki gyara yanda ya kamata, kin zata gidan sarauta gidan banza ne da za mu bari ki shiga kamar gantalalliya kai tsaye, miliyan biyu sarki ya bada a bamu da Parida amma haka nan na kashe kusan dubu ɗari biyu akan ki ina nema maki taimako saboda Allah, sannan ga gyaran jiki da za ayi maki tunda ba wani lokaci me tsayi aka saka na auren ba, Ina laifina a nan daga abun arziki?? So kike mu kwashe ki mu koma Kano Awdul din ya ji dadin sungume ki mu shiga uku, babu abincin da yaron nan Ahamad bai ajiye maki ba a gidan nan na jin dadin rayuwa, gashi shi da ɗan uwansa suna zuwa ganin ki, har wata panka me tsada ya siya maki saboda zafi da daddare yarinyar nan ke kadai kike saita pankan dai dai inda kike kwanciya mu kuma zafi ya kashe mu, to me kike so da ya wuce haka? Ai gwara tun yanxu ki fara sabawa da zaman Bauchi tunda nan aure zai kawo ki, Kano da zan koma cikin gaggawa duk domin ki ne inje asan shirye shiryen da za ayi na biki tunda ga damin kudi har dubu dari takwas a lalita ta, ki fa ji tsoron Allah Khaleesah" Aunty Farida dai ko kallon Khaleesat bata yi ba don dama a ranta tace bazata sake lallabata ba tunda kamar tunzurata ake kara yi in ana lallabata, ita ai duk tunaninta tun bayan da Abdul ya koya mata rayuwa ta ajiye wani shagwaba da iskanci a gefe ta canza hali, ashe ba haka bane waje ne bata samu ba kukan banzan na nan har yanxu, a haka su Jay suka iso za su kai Nenne da Aunty Farida park, Ba Ajay kadai ba hatta Jay sai da yayi shock da Khaleesat a kofar gidan don tara masu jama'ar anguwan tayi da kuka da ruri a kofar shiga gidansu Aunty Murja ita baza a tafi a bar ta ba, Aunty Murja na aikin lallashinta, Nenne ta dinga kauda kai tana daura gyale a kai tana rufe fuska tsabar kunya, Aunty Farida dama tuni ta shiga mota don bata da lokacinta, Jay dai ya kasa cewa komai don bai san lamarinta ya kai haka ba, can ya kalli

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login