Showing 90001 words to 93000 words out of 257722 words

Chapter 31 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

uku ma ya muka kare a baya balle kin shigo cikinmu Farida? Ko dai a cinyar su zasu dora ki?" Shi dai Abdul murmushi kawai yayi, Khaleesat tace "Toh ni sai in zauna a bayan" A fusace Nenne tace "To ke dole sai kin bi mu ne kamar en matan amare? Kawai don na zo gidanki sai in koma gida da ciwon jiki? ni wallahi in da matsi a mota ma bana shiga, da mun sani da bamu taho da Zubaida ba don duk ita ta cika waje..." Abdul ya kalli Khaleesat yace "Don't worry, ki koma ciki kawai" Hawaye ne ya cika idonta tana kallonsa, Aunty Farida ta yi ma Nenne wani kallo ta shige gaban motar, Nenne ta kyabe baki ta shiga bayan motar tana hararansu Zubaida da su ma duk suka shiga motar kuma babu warce tayi gigin gogan jikin Nenne a cikin motar, Nenne tace "To duk ku sauka Khaleesah ta fara shigowa ta dawo kusa da ni tunda ba wani auki gareta ba, ku ne abun tsoron dama" Babu musu duk suka sake sauka daga motar suka koma gefe, Nenne na kallon Khaleesat tace "Ba sai kin yi kuka ba, shigo ki matso kusa da ni mu ga adadin wajen da zai rage, in ya kama wata sai ta hau adaidaita sahu" Khaleesat ta goge idonta ta karasa ta shiga cikin motar ta matsa kusa da Nenne, space din da ya rage a motar tsaf zai dauke su Mama Zubaida, Nenne ta tabe baki tayi kasa da murya tace "Duk fa wari suke, in Farida ta shigo nan ai jikina za su rakube in ta shakan wari su cuce ni, in de ba kusa dani Faridan zata dawo ba, kuma Zubaida duk ta fi warin, banda akwai turare da AC a motarsa ai da mun ji kunya" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba su Mama Zubaida suka shigo motar Nenne na yatsine yatsine, a haka suka bar gidan. Sai kusan karfe biyar suka isa Mariri, bayan Abdul yayi parking dai dai kofar gidansu Khaleesat Nenne ta bude motar ta sauka tare da Khaleesat, su Mama Zubaida ma duk suka sauka da Aunty Farida suna ma Abdul godiya sannan suka shiga cikin gida, Nenne na gyara gyalenta tace "To Allah yayi maka albarka Awdul mun gode, amma dai zan yi maza in karasa gida akwai sakon Khaleesat da zan dauko in bata tunda Allah ya kawo ku ta tafi da kayanta kawai" Yana zaune driver seat ba tare da ya juya ba yace "Toh Kaka" Tana kallon Khaleesat tace "Mu je ki taho da sakon" Khaleesat bata ce komai ba ta fara bin Nenne zuwa gidanta, bayan sun yi nisa Nenne tace "Ai kinga shegen bai ce bari ya karasa gidan nawa da mu a motar ba, gaba daya baya ganin mutuncin gidana dama" Ita dai Khaleesat tayi kamar bata ji me tace ba, har suka isa gidan Nenne Khaleesat na gaisawa da mutanen anguwan, Nenne tace "Munafukai, sun yi mamakin ganin ki haka ai, kinsan duk ca aka yi kin shiga duniya kin gudu, sai daga baya kuma aka ji kina gidan mijin ki" Murmushi kawai Khaleesat tayi, bayan sun shiga gidan Nenne ta dauko turaren wutan ta saka su a katon leda da kasko biyu sannan suka fito, suna isa kofar gidansu Khaleesat Nenne ta saka ledan a bayan motar Abdul tana cewa "Kaga har mun dawo Awdul, dama turaren wutan ne ba wani abu ba, don haka ku yi maza ku tafi kar Magariba ya tarar da ku a hanya" Yace "To Kaka" Khaleesat na kallonsa tace "Zan shiga in gaida Ummata" Bata jira cewarsa ba ta shiga cikin gidansu ya bi ta da kallo, ko minti uku bata yi da shiga dakin Ummanta ba sai ga Nenne, tana tsaye bakin kofar dakin bayan ta dage labule tace "Abun kuma ba hauka bane ai, taso ki fita yana jiran ki..." Khaleesat ta daga kai tana kallon Nenne, Nenne tace "Ae sai yayi mana kallon mutanen banza marasu hankali, taso nace ki fita kar ki ja mana reni" Umma na kallon Khaleesat tace "Ku je Khaleesat, kin ga yamma tayi" Fuska a daure Khaleesat ta mike ta fita daga dakin, Nenne ta rakata har bakin motar Abdul, tana shiga gaban motar yayi ma Nenne sallama ya ja motarsa ya bar wajen, har suka isa gida ana kiraye kirayen magrib bai ce mata ba, ita ma bata ce masa komai ba, bayan yayi parking ya sauka motar ita ma ta sauka, tana tafiya a hankali ta bi bayansa suka shiga gidan, Kitchen ya shiga direct, har zata wuce dakinta ta tuna sakon da Aunty Farida tace ta bar mata kan kujera, ta karasa inda Aunty Farida ta zauna ta dauke throw pillow din wajen ta dinga kallon Dollars din dake ajiye da wayoyi biyu, daukan 1000 dollars din tayi wanda Jay ne ya bata da zata dawo Nigeria, ta dau wayoyin biyu, daya na Ajay daya na Jay, lkci daya jikinta yayi sanyi hawaye suka cika idonta, muryar Abdul taji a kanta yace "What's that?" Da sauri ta boye hannunta a baya tana kallonsa tsabar yanda ta gigice.


*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*


We sell all kind of children school shoes, school bag, Lunch box, Readymade for children.... Atamfa, Lagos laces, veils, Handbags, shoes, lafaya, jewelries, kitchen items e.t.c.....
All at affordable prices

Akwai adashin kayan kitchen, kayan yara and atamfa with laces if interested....



Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM

HALYSAAH 49

Abdul ya zagayowa ya tsaya gabanta yana kallonta ya mika mata hannu yace "Give me what you are hiding" Sosai gabanta ya fadi tana kallonsa ta kasa cewa komai, tsawan da ya gigitata ya daka mata yana mata wani kallo, lkci daya hawaye ya cika idonta ta mika masa wayoyin da kudin hannunta, amsan su yayi yana kallon su, ta sunkuyar da kanta zuciyarta na bugawa, Calmly yace "Who gave you this?" Kasa dago kanta tayi hawaye na zuba idonta tana jiran jin saukan mari at anytime, juyawa yayi ya bar wajen ya nufi dakinsa yana rike da wayar da dollars din, Khaleesat ta bi sa da kallo har ya shiga dakin, taji kafafuwanta sun kasa daukanta tsabar yanda ta tsorata, da kyar ta karasa ta zauna gefen kujera tana jin bugun zuciyarta na karuwa, tana goge hawayen dake sauka idonta.... Abdul na shiga dakinsa ya zauna gefen gado ya ajiye dollars din yana jujjuya wayoyin hannunsa ganin iri daya ne with different colors, kuma duk a mace suke babu caji, Exactly irin second phone din da yake using ne, ya mike ya tafi yayi plugging din wayar Jay da chargern sa, sannan ya koma ya dau kudaden ya kiraga yaga 1k dollar ne, ya ajiye su saman gadon yana kallonsu, jin za a tada sallah a masallaci ya shiga bathroom dinsa, bayan ya fito zai tafi masallaci ya kulle Bedroom din nasa da makulli, har sannan Khaleesat na zaune parlor ta kasa motsi a inda take zaune, tana ganinsa ta mike tsaye a tsorace tana kallonsa, ko kallonta bai yi ba ya nufi kofa ya fita daga parlon, a sanyaye ta tafi dakinta hawaye na sauka idonta zata je tayi alwala ita ma. Abdul na dawowa masallaci bayan ya bude dakinsa ya shiga ya dau wayar Jay ganin har yayi caji ya kunna kansa, ya cire wayar jikin chargern ya dauko wayar Ajay ya jona, sannan ya koma gefen gado yana duba wayar tunda babu lock jiki, gani yayi ba Sim card a wayar, ya dai ci gaba da dube dubensa, babu inda bai shiga ba a cikin wayar yana bincike but bai ga komai ba don babu any form of Media a wayar, messages ma ko daya bai gani ba, bayan ya shiga Email yaga Business class flight ticket da Jay ya siya mata da zata dawo Nigeria, ya dinga kallon Ticket din for almost 30 seconds, sosai fa yayi mamaki ba kadan ba, fita yayi daga Email din ya shiga Gallery din wayar hoping zai samu hoto a ciki, a nan ne ya ga Hotunan Jay, wanda duk yawanci tare zaka gansu da Ajay, Zooming pic din Jay yayi yana kallonsa with full concentration, sai kuma ya koma kan Ajay shi ma ya dinga kallonsa baya ko kiftawa, at once ya gane da shi ne suka samu Encounter a Amurka, but sai ya ga Ajay looks familiar, where did he know him from? mikewa yayi da sauri ya dauko wayarsa ya shiga Instagram dinsa yayi Searching sunan da yake tunanin ya san sa da shi a Instagram, amma sai yaga account dinsa is locked, komawa yayi ya zauna ya kasa dena kallon hoton Ajay babu ko kiftawa, can ya kara duba hoton Jay yayi Zooming dinsa yana kallo, kawai bai san me yasa yaji yafi jin tsanar Jay ma akan Ajay, mikewa yayi ya dauko wayar Ajay don har ya ɗan yi caji, babu lock a wayar hakan ya sa ya shiga, nan yaga Ticket da aka siya mata from Kano to Lagos, iya shi kadai ya gani a wayar babu hotuna, babu WhatsApp, babu komai, hatta sim card babu a wayar, fita yayi daga dakinsa ya tafi dakin Khaleesat ya sameta tana sallah, tun da taga yanda ya tsaya mata a bakin kofa taki idar da sallan da take yi da wuri kamar me Tuhajjud, muryarsa taji cikin tsawa yace "Idan baki sallame sallan nan da kike yi continuously ba zaki ga abinda zai faru yanxu" Sosai jikinta yayi sanyi, haka nan ta daure ta sallame sallan tana ji kamar bango ya tsage ta fice daga dakin tsabar tsoronsa, duk da yanda gabanta ke faduwa haka ta hade rai taki kallon direction dinsa barin da ta ga both wayar Jay da Ajay a hannunsa, ya karaso cikin dakin yana mata wani kallo cikin daga murya yace "Wayoyin su wanene wannan??" Still taki kallonsa, wani tsawa yayi mata yace "Are you stupid? Are you Mad? Ina maki magana kina kallon wani direction din daban?" Sai a sannan ta kallesa, har sannan fuskarta a daure yak, amma Allah ya gani daurewa kawai take, yace "I am asking you whose phones are this?" A takaice tace "My Housemate and his Brother....." Ya dinga kallonta babu ko kiftawa, she just realized she said her Housemate to him, ta kallesa a sanyaye, ganin kallonta yake yi baya ko kiftawa, ta sauke idonta a hankali tace "I mean...." Ya girgiza kai yace "No, you mean ur Housemate, dama Housemate dinki ne ranan da na je kika min karya? Dama gida daya ku ke tare da wannan katon banzan da na gani?" Gani tayi shiru fa ba nata bane, don shirun nata duka kawai zai ja mata, in ma maganar tayi ba hakan zai hana ya doketa ba in yayi niyya, ta wani hade rai duk da mugun faduwan da gabanta ke yi, a takaice tace "Eh, he is my Housemate, Nancy moved out of the apartment shi ne shi ya shigo, and i have no choice but to live with him, tunda bana son in dinga bothering dinka da Expenses, kuma naga in just few months za mu yi hutu, dama nufina idan mun yi hutu sai in ce maka ka canza min wani apartment din since a sannan ne zaka yi renewing house rent dina" Kallonta kawai Abdul yake yi babu ko kiftawa, ita dai ta kasa kallonsa gabanta na faduwa tana expecting ta ji saukan mari at anytime a cheek dinta, Calmly yace "So, shi ne kike zaune gida daya da shi ku ke rayuwa, ku yi sharing same kitchen, same parlor and same corridor, if coincidentally kin fito daki shi ma ya fito sai ku kusa karo da juna ko? Ki fito babu hijab ya gan ki haka, ki fesa turare ki zo ki wucesa yana jin kamshi, in ma ya kama ki zauna ku yi hira da shi, in kinyi girki ya diba ya ci" Sai a sannan Khaleesat ta kallesa tace "I don't mind if you believe me or not... But shi baya kwana gidan, karatu kawai yake zuwa yi ya tafi don suna da gidansu a Amurka" Abdul ya dinga kallonta, sai a sannan ya tuna abubuwa masu tsadan da ya dinga gani a kitchen sanda yaje, tun daga kan bottle water, cikin nutsuwa yace "Shi ne dalilin da ya sa kika fara min wasu stupid attitude kenan? Kin samu wanda yake siya maki duk abinda kike so a gidan har ma ya ɗebe maki kewa, To bari ki ji, ko duk jikina kunnuwa ne bazan taɓa yarda babu wani intimacy da ya hada ki da shi, ke kika san me kike basa da yasa yake siya maki abubuwa masu tsada yake ajiye maki a kitchen, sannan har ya cire kusan 5000 dollars ya siya maki Business class ticket kawai don ki dawo Nigeria...." Nan da nan hawaye ya cika idon Khaleesat, ta mike tsaye tana kallonsa tace "Ko me zaka fada bazan ce maka ba haka bane, amma put this at the back of ur mind, ba kowa ke da halin son taɓa warce ba muharramarsa ba kamar ka, kuma shi bai dau kudin Business class ticket wata tsiya ba shi yasa ya siya min, akwai difference sosai between you and him" Kallonta Abdul ya dinga yi da mugun mamaki, bata ankara ba sai jin saukan tagwayen mari tayi a fuskarta, ta fashe da kuka tace "Iya mari kawai?? ka kasheni mana ka huta kawai Abdul...." Ya fizgota da karfi yana huci yana kallonta da idanuwansa da suka yi jajir yace "Ni kike comparing da wani ɗan iska matsiyaci can??" Cikin kuka tace "May be if i do that you will change ur terrible ways, he made me realize i am dating a monster because of his kind attitude toward me, babu komai tsakanina da shi amma shi din mutum ne me kirki da sanin darajan ɗan Adam da sanin ya kamata, he always make sure i am fine, baya barina da damuwa komin kankantar sa, kuma ko da kuskure bai taɓa saɓa min ba a duk zaman mu da shi a America, kyawawan halayyarsa da irin yanda yake interacting yasa naji i am fed up with ur attitude, all this made me realize you are enslaving me ba sona kake ba, why not treat me the way he is treating me idan har sona kake da gaske? Bani da daraja da mutunci a idon ka, kullum cikin duka da cin mutunci nake a wajenka tun sanda baka aureni ba, iyayena ma basu da mutunci a wajen ka, to menene yasa baza kayi releasing dina zuwa inda za a ga mutuncina da na iyayena ba kuma a san darajata? Is it my father's fault da kaddarar sa ta zo a yanda take? Ku kan ku kun san bai ci kudin mahaifinka ba, bai salwantar masa da kayansa don son rai ba, ba ku tunanin ko ba ta sanadin mahaifina ba sai kun yi asaran kudaden nan tunda ku ma a kaddarar ku hakan take? Kuma meye zaka daga min hankali a kan su bayan kace baza ka sakeni ba kuma kowa yasan igiyar auren nan a hannun ka yake? Duk cikin rashin lissafin naka ne yasa kake kishi da su bayan ka ri ga ka aureni??" Turata yayi har sai da ta bugu sosai da bango sannan ya juya ya fice daga dakin kamar zai tashi sama. Wajen karfe dayan dare Khaleesat dake kwance taji an bude kofar dakinta, da kyar ta bude idonta da yayi mata nauyi tsabar kuka da ciwon kai, tana ta kwance a yanda take bata juya ba duk da bata ga ya kunna wutan dakin ba, duvet din jikinta ya sauke kasa ya jawota kusa da shi yayi kasa da murya yace "Kinsan da igiyata a kanki kike da effrontery din kawo min maganar wani katon banza can har kike comparing dinsa da ni? What wrong have i commit to you da kike ganin shi yana da halayya masu kyau wanda ni bani da shi" Khaleesat taji zuciyarta na mata wani zafi jin useless question din da yake tambayarta, tayi kamar bacci take taki motsawa, yayi kasa da murya yace "Khaleesat..." Still tayi kamar bata jin sa, duk da idonta a rufe yake she could feel the tears accumulating in her eyes, kiranta ya sake yi a hankali jin bata amsa masa ba ya juyota zuwa jikinsa yana kallonta cikin duhun, ya dora goshinsa kan nata yayi kasa da murya yace "But you know i love you so much Khaleesat, da bana son ki bazan yi wasting shekaru kusan biyar a kanki ba, i gave you the best of everything i can kema kin sani" Bata san sanda ta turasa ba tsabar wani tsanarsa da take ji a rai jin abinda yake cewa, ta mike zaune muryarta na rawa tace "Duk saboda kana sona kake dukana kake marina kamar jaka? Shi ma duk cikin so ne? Plss ka koma ka fahimci menene kalmar so...." Sauka ta fara kokarin yi daga kan gadon tana shesshekan kuka, ya rikota da sauri yaki barinta ta sauka, ta fashe da matsanancin kuka sosai tana jin zuciyarta na mata zafi saboda bakin ciki, ya rungumeta gam a jikinsa, a hankali yace "Kiyi hakuri, amma Allah ya sani ina son ki, in ma baki yarda ba i owe you no explanation tunda Allah shi ya sani, kuma today should be ur first and last warning Khaleesat.... I mean in ur life do not ever ever dare compare me with any stupid guy born of a woman, kar ki sake kawo min zancen wani ɗan iska ko shi wanene a kunne na, sannan bazan yi taking zaman da ku ka yi tare da shi and whosoever da kuma alakar ku personal ba because you are my wife now, duk wannan ya zama pass and shi ne looser,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login