Showing 249001 words to 252000 words out of 257722 words
Chapter 84 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar
gama magana ba Halysaah" Tace "Sai mu yi ta WhatsApp, ban gaya maka ba gobe da safe zamu tafi Kano da Aunty Murja da yarinyar kishiyarta sai Maman kishiyarta" Jay ya dinga kallonta, can yace "Amma shi ne baki gaya min ba all this while, gobe fa Friday" Ta ɗan yi murmushi tace "Na sani" Shiru yayi for almost 30 seconds kafin a hankali yace "In sha Allah zan zo da wuri sai in kai ku Kanon" Khaleesat ta ɗan bude ido tace "Tasha fa za mu je mu hau mota" Jay yace "Na ce zan kai ku, ku shirya da wuri..." A hankali tace "Toh Allah ya kai mu" Yace "Ameen" Hannu ta ɗaga masa alamar Bye bye sannan ta bar wajen, Jay dai ya kasa ce mata komai ya bi ta da kallo har ta shiga cikin gida, jiki a sanyaye ya zaga ya shiga front seat yana kallon Ajay with disappointment written all over his face yace "Nasan kasan cewar Mami taje gidansu Halysaah a Kano Amma ka boye min baka gaya min ba Junaid" Ajay ya ɗan kallesa yace "To meye amfanin gaya maka, me zaka yi? She is ur mother babu yanda ka iya, Mai martaba did the needful, so babu amfanin gaya maka ayi ta jan magana....." Jay ya dinga kallonsa kawai, Ajay ya daga kafada yayi igniting motarsa ya fara reverse, har suka isa gida babu wanda yace komai cikinsu, har sannan jikin Jay a sanyaye yake ya rasa dalilin da yasa yaji ya fara loosing hope kuma yanxu, yaji ya shiga damuwa fiye da wanda yake ciki a baya, bai taɓa expecting haka daga Maminsa ba, Ajay na parking Jay ya bude motar slowly ya sauka, Ajay ya bi sa da kallo har yayi nisa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya kashe motarsa ya sauka shi ma, har ransa yake jin tausayinsa kuma shi dai yasan duk rashin kirkin Mami bata kai haka ba kawai Aunty ce ke instigating dinta tana exaggerating mata lamarin shi yasa take ta wannan abubuwan da take yi. Ajay ya kalli agogon wrist dinsa ganin there is still time ya nufi bangaren Abbansa don ya kirasa daxu suna unguwan su Aunty Murja, zai bude kofar parlorn aka riga sa budewa sai ga Mami ta fito daga parlon fuskarta a daure ko kallon Ajay bata yi ba tayi wucewarta, Ajay ya bi ta da kallo sannan ya shiga babban parlon, Zaune ya tarar da Mai martaba a parlon, Aunty dake zaune parlon ita ma tayi kasa da kai cikin kwantar da murya tana cewa "Allah ya huci zuciyarka ranka shi dade idan maganganunta sun maka zafi, Allah ya baka hakuri Me martaba, a gaskiya Fulani bata kyautawa sam, ban san me take son a mata ba, amma babu komai ita kanta tasan albarkacin wa take ci, kuma zata ci gaba da cin albarkacin nasa, Allah ya sanyaya ranka Mai martaba, Allah ya huci zuciyar ka, Allah ya baka hakuri" Ajay ya dinga yi ma Aunty wani kallo, sannan ya zauna kasan lallausan Carpet din parlon yayi kasa da kai yana gaida Mai martaba, Mai martaba ya ɗaga kai ya kallesa yace "Ka dawo Yarima" Ajay bai dago kansa ba yace "Mun dawo Ur highness" Sarki yace "To maa sha Allah, na ma ga takardun da na kira nake tambayarka daxu" Ajay yace "To in ba damuwa zan iya tafiya ur highness?" Duk da akwai maganganun da Sarki ke son yi da shi amma ganin Aunty a parlon kawai yace "Sure, Allah ya tashe mu lafiya" Mikewa Ajay yayi ya ɗan kalli Aunty yayi mata sai da safe sannan ya juya ya nufi kofa ya fita, direct bangaren Jay ya nufa yaji ya kulle kofar shiga part din nasa, hakan yasa ya juya ya koma bangarensa.... Ana idar da sallan asuba bayan Jay ya dawo masallaci ya tafi part din Ajay, bai samesa a bangaren nasa ba, ya zauna nan parlor ya jira har ya dawo, Jay ya ɗaga kai a hankali ya kallesa yace "Yau Halysaah da Aunt dinta za su koma Kano, na ce mata zan je da safe in kai su Kanon, but i don't think I am okay Ajay, bazan iya driving din ba..." Ajay ya katse sa ya zauna yana kallonsa yace "What's wrong with you?" Jay yace "I just need rest, zan kwanta ko zan ɗan yi bacci, shi ne nake son tunda bazan iya kai su Kanon ba ka taimaka kayi dropping dinsu motor Park su hau public transport, ban san nawa bane kudin motan but you can sort that out" Ajay dai kallonsa kawai yake, can yace "To me yasa baza a tura masu kudin motar ba kawai, har sai an je uwa duniyar unguwan nan nasu an dauke su an kai su Motor park" Jay ya mike yace "You just have to help pls, they are leaving very early this morning" Daga haka ya nufi kofa Ajay ya bi sa da kallo har ya fita, kawai yayi shiru ya kyalesa ne ganin da gasken he is not looking okay. Duk tunanin Khaleesat idan ta fito zata ga Ajay da Jay duk da Ajay ne ya kira wayarta, amma sai ta ga Ajay kadai, gaishesa tayi yace "I have where I am going, do not keep me waiting...." Juyawa tayi ta koma cikin gidan, sai da suka ɓata kusan 15 mins sannan suka fito, ya bude motar ya sauka yana gaida dattijuwar cikinsu sannan ya gaida Aunty Murja ya bude masu booth suka saka akwatinsu, ya bude masu back seat ya koma cikin motar ya zauna, sai da Khaleesat ta jira Inna da Aunty Murja suka shiga motar Zainab ma ta shiga sannan ta koma front seat ta shiga tana rike da handbag dinta, yan gidan gaba daya suka fito har da makota ana masu Allah ya kiyaye hanya har Ajay ya bar unguwan, at first tasha yayi niyyar dropping dinsu amma sai ya kasa hakan, still dai yana driving yana estimating lokacin da zai kai su Kano ga daurin aure yau, what if Mai martaba yayi realizing baya garin idan yana bukatarsa, daga karshe yayi deciding in ya samu available flight kawai sai ya bi ya dawo tunda bayan an sauko juma'a ne daurin auren and this is just few minutes to 7am, yana daukar hanya da raɓar AC ya bugi su Aunty Murja duk suka ɓige da bacci a bayan motar, tafiyar kusan 2 hours suka yi Khaleesat ta juya tana kallonsa a hankali tace "Don Allah zaka iya tsayawa, it seems I want to throw up" Ya daure fuska ya kalleta, tana ganin haka ta fara yunkurin amai tana rufe bakinta, gangarawa yayi gefen hanya yayi parking ta bude motar ta sauka, su Aunty Murja dai sai bacci suke basu san me ke faruwa ba, bayan kusan minti uku ya dau bottle water ya bude motar ya sauka ya nufeta, Mikewa tayi tana kallonsa a hankali tace "Ai ban yi ba" Yace "Kika sake tsayar da ni zan sauke ki inyi tafiyata Malama, you can't come and be stressing me here" Amsan ruwan hannunsa tayi ta bude ta wanke fuskarta, sannan ta mika masa sauran, daga sama har kasa ya kalleta ya juya ya koma cikin mota ta bi bayansa..... Har kofar gida Ajay yayi dropping dinsu bayan sun sauke kayansu an shiga da su ciki su Aunty Murja suka masa godiya suka shiga cikin gidan, Khaleesat ta zaga ta driver seat tana kallonsa tace "Mun gode Allah ya saka da alkhairi, amma baza kayi breakfast ba?" Sai bayan da ta fada hakan ne ta tuna waye shi, ta langwabar da kai tace "Shikenan, are you going back to Bauchi?" Tada motarsa yayi yace "Kina da sako ne..." Murmushi tayi ta girgiza masa kai, sannan tace "Allah ya kiyaye hanya, Allah ya kai ka lafiya" Daga haka ta juya ta nufi gate zata shiga gida, sai da ta shiga gidan sannan yayi reverse ya bar unguwan. Karfe uku saura Khaleesat na zaune parlor bayan Aunty Farida ta gama yi mata gyaran gashi, tun da suka shigo gidan da safe ta samu labarin har yanxu da batun daurin aurenta yau hankalinta ya kasa kwanciya duk tunaninta till further notice duba da abubuwan da suka faru a kwanakin nan, ba ita ba har su Nenne da Ummanta da Aunty Farida kawai sun zuba ma sarautar Allah ido ne gani suke auren fa ba mai yiwuwa bane kawai dai baza a ja da Mai martaba ba, Umma kuwa ko baccin kirki bata yi ba daren jiya haka ta kwana sallah tana rokon Allah Ubangiji ya kawo sanadin fasuwar wannan aure don kwata kwata bata son auren kuma, bata fatan er ta ta koma gidan jiya, gwara ta dauwama a gabanta har Allah ya fito mata da miji wanda ba shi kadai ba hatta yan uwansa da iyayensa za su so ta kamar yanda yake son ta, har zuwa yanxu da Umma ke zaune bata fasa wannan addu'a a ranta ba don tana cikin tashin hankali da rashin nutsuwa a zuciyarta, Ahmad mutumin kirki ne wanda ko wace uwa zata yi ma er ta fatan samu amma tun da uwarsa ta zo har gida ta nuna masu bata son auren Khaleesat da ɗanta tayi masu rashin mutunci Umma taji aurensa da Khaleesat ya fice mata a rai, amma kuma ga Mai martaba a tsakani shi yasa suka rasa say din kansu akan lamarin duk suka zuba ma sarautar Allah ido, Nenne ce ta shigo parlon a gigice da almajirinta da wasu matasa yan Mariri duk sun sha fararen yadi tana kallon su Aunty Farida da Mama Shatu sai Aunty Murja dake parlor tace "Kun ji fa wai an daura auren da Ahamad din, yanxu almajirina ya shigo yake ce min daga wajen daurin auren su ke yanxu haka, mutane ba masaka tsinke a wajen har da sarakuna da manyan mutanen kasar nan, sai jiniya ake ta ko ina...." Sosai Umma taji gabanta ya fadi tana kallon Nenne babu ko kiftawa, Khaleesat sai da taji kamar amai zai taho mata tsabar yanda maganar Nenne ya kidimar da ita ya rikitata, har sai da ta kasa daurewa ta mike da sauri ta nufi bandakin dake parlon tana yunkurin amai, Nenne ta kalli wani matashi me suna Sagir don duk yafi sauran nutsuwa cikin samarin tace "Kai Sagir sai kaji ance an daura auren wa da wa?" Sagir yace "Ni iya na Khaleesat kawai na rike don daurin auren biyu aka yi Nenne" Nenne ta sharce zufar da ya keto mata tace "To ya aka ce na Khaleesah din?" Sagir yace "An daura aurenta da Ahmad Yusuf...." Mikewa Umma tayi ta bar parlon ta wuce daki hawaye na zuba idonta, Aunty Farida da duk jikinta yayi sanyi ita ma ta mike da kyar ta bi bayan Umma, Mama Shatu tace "To mu ai wannan abun farin ciki ne a gare mu, tun da aka daura auren dama Allah ya ƙaddara mijinta ne babu yanda uwarsa zata yi sai dai ta bi su da fatan alkhairi" Nenne tace "Atoh dai, ni dai wallahi nayi farin ciki matuka nayi murna, yanxu tashi za ku yi ku baza turaren wuta a gidan nan da kyar in jiga jigan masarautan baza su yo nan a gaida uwar yarinya da kakarta ba, maza tashi murja kar mu ji kunya" Amai sosai Khaleesat tayi a bandakin, nan da nan taji kamar zazzaɓi zai rufeta ta fito ta wuce dakinta da kyar, sai a sannan hawaye masu zafi suka fara sauka idonta, she is just confuse, ta rasa wani irin tunani zata yi, bata taɓa tunanin za a daura aurenta kwana kusa ba with the way things were going, ko dai almajiran basu ji da kyau bane ba ita ake nufi ba, tayi karfin halin jawo wayarta tana kallon screen din, da kyar tayi dialing number Jay, amma kamar daxu da ta kirasa bai shiga ba yanxun ma bai shiga ba, hakan yasa tayi dialing number Ajay, har ya katse bai daga ba, ta ɗan jira ko zai biyota kamar yanda ya saba, amma har bayan minti biyar bai biyo ba, sake kira tayi still har ya gama ringing bai ɗaga ba, bata taɓa kiransa a take bai yi picking ba ko ya biyo kiran, ajiye wayar tayi ta kwanta gefen gado hawaye masu zafi na zubowa idonta, a haka Aunty Farida ta shigo ta sameta tana kallonta cikin sanyin murya tace "Kun yi waya da Jawwad din ne?" Khaleesat ta girgiza kai hawaye na sauka idonta tace "Wayarsa a kashe" Aunty Farida ta zauna kusa da ita amma ta rasa ma me zata ce, su kansu fargaban auren nan suke balle ita, can Aunty Farida tace "To ki kira Junaid sai ya hadaki da Ahmad din" Khaleesat ta mike zaune tace "Na kirasa bai daga ba" Tana fadin haka ta sake dialing numbersa sai taji a kashe, ta daga kai ta kalli Aunty Farida, Aunty Farida ma tayi dialing number tasa a nata wayar, ita ma taji switch off.
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
Ur evidence via 07087865788
Halysaah Page 99 By Khaleesat Haydar
Sai kusan Magrib Malam Ali ya dawo gida tare da wasu abokansa daga Mariri, bayan anyi magariba Nenne ta sa Aunty Farida ta kai masu abinci compound, Aunty Farida na komawa cikin gidan ta tafi dakin Umma, tana kallon coolern abincin dake dakin da damuwa tace “Wai har yanzu baki ci abincin ba dama Umma? Don Allah me yasa zaki sa ma kanki damuwa haka ne Umma?” Muryar Nenne suka ji tace “Don Allah ki rabu da ita Parida, ta dade bata sa ma ranta damuwa ba, wannan ai sai in iya cewa bakin ciki take ma er cikinta, tun da muka ga har aka daura auren nan to fa dama Allah ya kaddara sai an daura ba wani tsimi balle dubara, to meye bazata bi yarinya da fatan alkhairi ba da kyakkyawan addu’a, tunda dai mijinta da sarki suna son ta ba shikenan ba uwarsa taje can ta karata da mugun halinta, in taga ta haifo mata jikoki masu shiga rai sai a ga ta sakko ta so ta ko don jikokin, nima farko nan ba haka nayi ta fargaban Zahra’u zata raba ni da da na ba da na samu labarin buzuwa ce, har ya aurota ni dai bana sonta don ina tsoron asirin kabilar su haka kawai wataran ta janye min yaro ita da iyayenta, amma tana haifo Khaleesah na saduda saboda yanda yarinyar ta shiga raina da yan unguwa, to ita ma uwargabanta har abinci naga ta ci daxu, sai kece sarauniyar damuwa da kuncin yan Najeriya, to wallahi ki cire auren jikata a ranki, kada Allah ya dubi zuciyarki abinda kike tsoro ya je ya faru mu shiga uku, ai fata na gari lamiri” Nenne na kai wa nan ta fice daga dakin, Dakin Khaleesat Aunty Farida ta shiga ta sameta zaune saman darduma ta idar da sallah, Aunty Farida ta zauna gefen gado tace “kin same su a wayar?” Khaleesat ta girgiza mata kai kawai, Aunty Farida tace “Waya kuma a kashe tun safe, ai Junaid shi naga da wuya a ki samun sa….” Ita dai Khaleesat bata ce komai ba. Karfe takwas da rabi Malam Ali na zaune parlonsa sai su Umma da Aunty Farida da Nenne wanda duk shi yayi kiransu, Nenne na gyara zama tace “Wallahi har ka fara dawowa Alin ka na da, ga hasken ka sai dawowa yake” Malam Ali dai bai ce mata komai ba, babu bata lokaci ya fara sanar masu dalilin da yasa yayi kiransu gaba daya, tun da ya fara magana Nenne ta bude baki tana kallonsa, Umma da Aunty Farida ma sai kallonsa suke kamar ranan suka fara ganinsa, Nenne ta tsuke dankwalinta da kyau, cikin rashin fahimta tana zaro ido tace “Ban gane ba Ali, ba a daura auren ba kenan kake nufi ko me?” Malam Ali ya kwantar da murya yace “Shi ne nake kai ku ai Baaba, ban gama bayanina ba” Nenne ta zauna da kyau cikin kaguwa tace “Gama Ali, Innalillahi wa Inna ilaihi raji’una, muna jin ka Ali, ga jama’a duk mun gayyato mun ce gobe biki ya za mu yi da su ni Dije, amma Allah ya tsine ma wannan yaro Sagir da yace mana an daura aure” Malam Ali ya ci gaba da bayaninsa Nenne bata kara interrupting dinsa ba tana gwale ido har ya kai karshe, Umma ta juya ta kalli Aunty Farida da tsabar mamaki ita ma baki ta bude kamar Nenne tana kallon Malam Ali, Nenne fa bata fasa zare ido ba tana kallon Malam Ali duk da ya gama bayaninsa, can ta kwance dankwalin da ta tsuke tace “Kana nufin kace da wannan dan uwan nasa mara walwala wanda shi ne ainahin dan Sarkin aka daura auren?” Malam Ali yace “Haka maganar take, shi ma ai sunansa kenan Ahmad….” Nenne ta saki wani salati tana tafe hannu sai kuma ta dafe kanta, can tace “Ikon Allah yafi gaban haka Ali, dama shi bama shi da uwa a gidan ta mutu balle mu ji fargaban zata zo ta walakanta mu, yanxu dai kana nufin Yarima ne mijin Khaleesah, shi ainahin dan sarkin?” Umma ta rasa me yasa taji wani nutsuwa ya zo mata bayan bayanin mai gidanta, Aunty Farida tsabar yanda lamarin ya girgizata ta ma kasa cewa komai don ganin abun ta dinga yi kamar al’mara, Junaid kuma, Nenne ta sauke ajiyar zuciya tace “Lallai sarki ya cika mutum, wato da uwar Ahamad ta nuna masa ba shi ya haifi Ahamad din ba sai ya nuna mata me yayi zafi shima ai ya haifa, ikon Allah, to amma yanxu wannan kwamacalar ta ina za a fara Ali, shi dai wannan kamilin yaro da ko magana sai ya ga dama yake yi ma mutane bai ce fa yana son Khaleesah ba ita ma haka, to ta ina za a fara wannan lamari, sannan shi Ahamad wani hali ake son ya shiga yanda yake bala’in son yarinyar nan ace kuma yaga dan uwansa da ita a matsayin matar aure, anya Sarki bai