Showing 117001 words to 120000 words out of 257722 words

Chapter 40 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

'yan Adam, don zaka ba mutum kudi sai aka ce ka walakantasa? Ka ki darajasa?" Aunty Farida taki tanka Nenne, Umma na kallon Khaleesat tace "Tashi ki je Jiddah, Allah ya tsare ya kai ku lafiya" A hankali Khaleesat tace "Ameen Umma" Daga haka ta mike ta dau handbag dinta don duk an fitar da akwatunan ta kofar gida, Nenne na kallon Umma tace "In ji dai duk an saka mata doya da dankalin da na kawo mata a akwatin nata?" Da sauri Aunty Farida tace "An saka komai" Nenne tace "Wake da su albasa da garin masara da na alkama fa?" Aunty Farida tace "Har su an sa" Nenne tace "To mu je" Khaleesat ta bi bayan Nenne suka fita daga dakin, Aunty Farida ta kara tura doya da dankalin da Nenne ta kawo da su garin alkama da Masara a bayan kyaure ta boye yanda Nenne bazata gani ba ko ta dawo dakin, daga nan ta bi bayan su, kasa daurewa Umma tayi ta mike ita ma ta fita, su Mama Zubaida da Mama Shatu na tsaye tsakar gida duk suka bi Khaleesat da kallo, Kana ganin fuskokinsu kasan babu farin cikin komawa Amurka da Khaleesat zata yi, Yaron Mama Zubaida ya nufo Khaleesat da gudu yana mika mata kudin hannunsa yace "Wai gashi inji Ummanmu da Mama Shatu ki sha ruwa a hanya" Nenne ta karbe kudin a hannun yaron ta kirga taga dubu biyu ne, sokesa tayi jikin haɓar zaninta tace "Ta gode" Daga haka ta kalli Khaleesat tace "Mu je" Khaleesat tayi ma kishiyoyin ummanta sallama sannan ta bi bayan Nenne suka fita daga gidan Aunty Farida na biye da su, a kofar gidan Khaleesat ta kara sallama da Babanta don bai fita kasuwa ba ranan yana jiran tafiyarta, kasa hada ido tayi da shi yana mata addu'a da fatan alkhairi, Nenne ta bude mata bayan motar tace "Ni dai shiga don Allah, tun jiya basu san da addu'an su ba sai yau da kike sauri salon jirgi ya tafi ya bar ki" Khaleesat ta shiga motar Nenne ta kulle, haka kawai Khaleesat taji hawaye ya cika idonta, ta daga masu hannu kawai sannan drivern ya ja motar suka bar kofar gidan. Ko da Khaleesat ta isa airport ta tarar Safiyyah na ta jiranta don tun daxu ta iso airport din, Khaleesat ta amshi boarding pass dinta suka nufi Departure Lounge, bayan minti ashirin jirginsu ya tashi zuwa garin Abuja, inda a nan za su hau jirgin da zai kai su kasar America.



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*



We sell all kind of children school shoes, school bag, Lunch box, Readymade for children.... Atamfa, Lagos laces, veils, Handbags, shoes, lafaya, jewelries, kitchen items e.t.c.....
All at affordable prices

Akwai adashin kayan kitchen, kayan yara and atamfa with laces if interested....



Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM

HALYSAAH 57

Tun da suka sauka Amurka wajen karfe hudu na asuba gaba daya walwalar Khaleesat ya bace, ta dawo so silent kamar mara lafiya, cikin rashin kuzari ta dinga yin komai har suka gama da custom da Immigration, Safiyyah na kallonta tace "Wai duk sanyin ne yasa kika dawo haka? Naga mood din ki ya canza all of a sudden, are you okay?" Khaleesat tayi murmushin karfin hali ta girgiza mata kai kawai tana gyara Jacket din jikinta don tun a kasar da suka yi transit duk suka saka Jacket din su saboda sanyi, Safiyyah na kallon wayar hannunta ganin kiran Mustapha for the 4th time tace "Shi kuma wannan daga sauka ko kashe jirgin ba ayi ba ya fara doka min kira kamar jira yake, kilan kewan fadan da muke yi da matarsa kullum yake yi, bai san i came fully ready for her ba, don this time around bazan sake tolerating nonsense dinta ba wallahi" Khaleesat dai murmushi kawai tayi bata ce mata komai ba har suka fita daga Arrivals, Safiyyah tace "I don't want us to stress ur Housemate, naga message dinsa tun muna Abuja yana tambayar karfe nawa za mu taso kuma a ina za mu yi transit, kilan da na gaya masa zai iya estimating time din da za mu iso ya zo yayi picking din mu daga airport cikin azababben sanyin nan da ake, shi yasa kawai ban masa reply ba kar muyi inconveniencing dinsa" Khaleesat ce ta fara hango Ya Mustapha tsaye jikin motarsa kafin Safiyyah ma ta gansa tayi kasa da murya tace "Sai kin ga yanda ya addabi Dad din mu wai an koma makaranta naki dawowa, sai kace zaman jin dadi nake yi a gidansa da shegiyar matar nan tasa" Khaleesat ce ta fara gaida Mustapha bayan ya iso inda suke tsaye, ya amsa da fara'a yace "Ya hanya Khaleesah?" Khaleesat tace "Alhamdulillah" Safiyyah ma ta gaishesa ya amsa sannan suka nufi motar sa gaba daya, ya amshi trolley dinsu ya saka a booth din motar yace "Kun ji sanyin America ko, don ma yau babu snow" Khaleesat dai tayi murmushi, Safiyyah ta bude mata back seat tana kallonta, Khaleesat ta shiga sannan Safiyyah ta zaga ta bude gaban motar ta shiga ita ma, Mustapha ya tada motar bayan sun bar Airport din ya kalli Safiyyah yace "Amma dai Khaleesat won't be going to her apartment now, zai fi kyau mu je can gidana idan ta huta sai ta koma Apartment dinta anytime she is ready" Safiyyah tace "Dama gidan ka zaka kai mu gaba daya mana, cikin sanyin nan ta ina zata je ta fara gyaran apartment dinta ga gajiyar hanya" Ko da wasa Safiyyah bata ba Mustapha labarin abinda ya faru da Khaleesat ba, ita dai Khaleesat tayi shiru a bayan motar tana tunanin another new life that she is going to begin in America with her burden on people's shoulder, shikenan ita kuma daga wannan ya dau responsibility dinta sai wannan ya dauka, sosai tunanin nan ke kara kashe mata jiki, gashi rayuwar America ba dai tsada ba, kawai tasan takura Housemate dinta zata yi da burden dinta, a haka suka isa gidan Mustapha da tunani iri iri a ranta, bin unguwan ta dinga yi da kallo don bata san unguwan ba, sati biyu da fara exams dinsu Last semester Safiyyah ke gaya mata Mustapha ya amshi wani apartment da ya fi wanda suke ciki girma za su tashi a gidan da suke, ita dai har suka bar America bata san gidan da suka koma ba, bayan Mustapha yayi parking suka sauka a motar Safiyyah ta bar sa da shigo masu da kayansu ta kama hannun Khaleesat zuwa cikin gidan, ita dai Khaleesat bin ta kawai take, upon yanda ta tsani duk abinda zai hadata da gidan Mustapha saboda matarsa sai gashi yau saboda rashin option da choice ya sa ta amince da zuwa gidansa babu ko musu, zaune suka tarar da matarsa a parlor ta sha uban rigan sanyi ga daurin dankwalin ture kaga tsiya da tayi da zaninta, sosai jikin Khaleesat yayi sanyi ta rakube jikin kujera tana kallonta ta gaisheta, amma matar nan ta dinga kallon TV tana cin popcorn kamar bata ji Khaleesat ba, Safiyyah dama ko kallonta bata yi ba ta nufi hanyar dakinta ta murda taji a kulle kuma babu makulli a jikin kofar, tsaye tayi fuskarta babu yabo babu fallasa tana jiran Mustapha ya shigo gidan, bayan yan sakwanni sai gashi ya shigo parlon da akwatuna biyu, Safiyyah tace "Yaya ina makullin dakina?" Ya karasa ya murda kofar yaji a kulle, ya dawo parlor yana kallon Surayya yace "Surayya ina makullin dakin can yake?" Sai a sannan Surayya ta juya ta wani kallesa tana ci gaba da cin popcorn din hannunta tace "Makullin daki? Ban gane Makullin daki ba, Ajiyar makulli aka bani da za a tambayeni?" Safiyyah dake ta kallon Ya Mustapha tana huci tace "Kai dama yaya da ka wani ishi Daddy da kira cewar mun koma makaranta in dawo a saman roofing din gidan nan kake da niyyar ajiyeni tunda gashi an dauke makullin dakin an boye? Wannan ai iskanci ne da walakanci, mutum yayi dogon tafiya haka ya dawo kuma yaga an dauke masa makullin daki?" Mustapha ya karasa kusa da Surayya da sauri yace "Ke Surayya ko dai Aslam yana wasa ya cire Makullin dakin ne a jikin kofar?" Surayya taki ko kallonsa, Safiyyah ta wani tsuke fuska tace "Aslam ne tsayinsa zai kai har ya cire makulli a kofar daki? Ai sai dai Uwar Aslam, kuma Allah ya so ban bar komai da za a sace min a dakin ba sai takardu, tunda an saba min satan dama" Mikewa Surayya tayi tana mata wani tsinannen kallo tace "Keeee, in kina cin kasa ki kiyayi ta shuri, wallahi ki iya bakin ki don ni ba sa'ar ki bace ki kiyaye ni, in kika yi wasa za ki sha mamakina yanxun nan" Safiyyah tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Osheyy ancient of days, ashe dai ke ba sa'a ta bace, ai sai yau kike gaya min nake ji, kuma in kin fasa bani mamaki sunanki ba Surayya ba, shege ka fasa tsakanin ni da ke" Fada Mustapha ya fara yi yana cewa "Meye haka? Ko kuna hauka ne? Wannan wani irin iskanci ne? A gaban nawa ku ke wannan rashin hankalin?" Magana yake yi at the same time yana kai kawo yana dube duben makullin dakin Safiyyah a parlon, Ita dai Khaleesat na rakube jikin kujera taji kanta har ya fara mata wani azababben ciwo, banda rashin option me zai kawota gidan nan ita kam, tunanin hakan yasa ta ji hawaye ya cika idonta, Safiyyah sai girgiza kafa take tana hararan Surayyah da ta koma ta zauna tana cin Popcorn dinta tana gyara daurin ture kaga tsiyan dake kanta tana kara cokarosa gaba, Mustapha ya karasa inda Aslam ke kwance yana bacci a parlon ya fara tashinsa yana tambayarsa makullin dakin Safiyyah, yaron da ko shekara biyu bai karasa ba, a fusace Surayya tace "Wallahi kar ka tada min yarona Mustapha, shi yasan maka wani makulli da zaka tashesa yana bacci" Mustapha ya juya ya kalleta yace "Surayya in ke kika dauke makullin nan ki fito da shi bana son rainin hankali" Surayya ta wani hararesa tace "Kar ka bata min rai this early morning, in dau makulli inyi uwar me da shi? Plss do not provoke me Mustapha" Tana kai wa nan ta mike ta figi yaronta dake bacci ta nufi dakin ta da shi, Mustapha ya kasa cewa komai ya bi ta da kallo yana rike da waist dinsa, can ya juya ya kalli Safiyyah dake masa wani mugun harara kamar zata kwadesa, karasawa yayi kusa da ita yace "Look Safiyyah...." Katse sa tayi a fusace tace "Babu abinda zaka gaya min Yaya, Don't tell me anything, dama don matarka ta min wannan walakancin ya sa ka dage sai na dawo an koma makaranta, wallahi ni dai Daddy zan kira a samar min wani gidan da zan zauna in karasa final year dina kawai in peace, don bazan iya zama da wannan devil wife dinka a gida daya ba" Kamar zata yi kuka ta kare maganar, Mustapha bai iya yace mata komai ba, can dai ya nufi hanyar dakinsa don daki uku ne a gidan, yana shiga dakin ya dau duk abinda zai bukata ya fito da shi parlor ya ajiye yana kallon Safiyyah yace "Ga bedroom dina can ku shiga" Safiyyah na jin haka ta figi hannun Khaleesat zuwa dakin nasa, da sauri Surayya ta fito daga dakinta don bata kulle kofar dakin ba saboda ta dinga jin abinda za ace a parlon, tana kallonsa da wani irin mamaki tace "Ban gane ga Bedroom dinka can su shiga ba Mustapha, turakar namu za su shiga kake nufi ko me?" Safiyyah ta kwashe da wani dariya har da kyakyatawa ta ja Khaleesat suka shiga dakin sannan tayi banging kofar ta kulle, Surayyah zata yi magana Mustapha ya ɗaga mata hannu fuska a murtuke alamar baya son jin komai sannan ya fice daga parlon zai shigo da sauran akwatunan su Safiyyah, Khaleesat da duk jikinta yayi sanyi ta dinga kallon Safiyyah tace "Haba Sophie, this isn't proper mana, why not mu zauna a parlor har san da za a ga makullin dakin naki, dakinsu ne wannan fa" Safiyyah ta mata wani kallo tace "Ai ba kowa ne ɗan iska mara zuciya kamar ki ba Khaleesat, kuma wallahi ina dakin nan babu inda zan je har sai ranan da ta fito min da makullin dakina...." Khaleesat ta kasa cewa komai don da gaske she is shock, sai ga Mustapha yayi knocking kofar dakin sannan ya ajiye masu hand luggage dinsu yace "Me za ku ci yanxu?" Safiyyah na zaune gefen gadonsa fuskarta babu walwala irin ita an bata mata din nan tace "Kawai shayi da cookies kafin gari ya waye" Yace "Ohk" Juyawa yayi ya fita daga dakin ya kullo masu kofa, har sannan Surayyah na tsaye inda take a parlor ta kasa motsin kirki, ta bi sa da kallo har ya shiga kitchen zai hado masu shayin, bata san sanda ta fashe da kuka ba tana rufe bakinta ta nufi dakinta da sauri, Mustapha ya dawo dakin nasa da Cup din shayi biyu da cookies ya ajiye masu ya fita.... Khaleesat na idar da sallan Asuba ta kwanta kasan carpet din dakin Mustapha don dakin da dumi saboda room heater dake kunne, amma hakan bai hanata dinga jin sanyi ba saboda wankan da tayi, babu yanda Safiyyah bata yi da ita ta kwanta saman gado ba amma Khaleesat taki tace kasan carpet din ya isheta, wayar Safiyyah ya fara ring, ta mike ta dauko handbag dinta ta ciro wayar, kallon Khaleesat tayi tace "Housemate dinki ne ke kira" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba, Safiyyah ta zauna gefen gado sannan tayi picking call din tayi masa sallama tare da gaishesa, daga daya bangaren yace "How are you, naga baki yi replying message da na maki ba tun jiya" Safiyyah tace "Kawai bana son inyi stressing dinka ne probably kace zaka zo picking din mu a airport" Yace "Kuna ina yanxu?" Safiyyah tace "Muna gidan yayana, ga Housemate din ka nan, let me give her the phone...." Calmly yace "Ohk..." Safiyyah ta mike ta tafi inda Khaleesat ke kwance ta durkusa tana mika mata wayar, Khaleesat ta kasa amsan wayar, har sai da Safiyyah ta kai mata wayar kunne, daga daya bangaren Khaleesat taji yace "Halysaah...." Kasa ce masa komai tayi, lokaci daya taji hawaye masu zafi sun fara sauka idonta, a hankali yace "Can you hear me?" Muryarta na rawa da kyar tace "Uhm" Shiru yayi, after some seconds yace "I will come over later in sha Allah" Ta gyada masa kai kamar yana ganinta, kashe wayarsa yayi, ta ajiye wayar wasu hawayen na sauko mata, ita dai Safiyyah bata ce mata komai ba. Karfe takwas na safe Safiyyah ta fito daga dakin Yaya Mustapha zata je kitchen ta duba menene available da zata girka masu ita da Khaleesat, ga mamakinta sai taga an ajiye makullin dakinta kan Centre table din parlon, dariya ma abun ya bata, ta karasa ta dauki makullin sannan ta koma dakin ya Mustapha da sauri ta kulle kofar, dariya ta dinga babbakawa Khaleesat na kallonta, tana nuna ma Khaleesat makullin hannunta tace "Kin ga er iskar ta ajiye min makullin kan Centre table saboda taga na tare dakin mijinta, ashe karamar er iska ce ita ban sani ba? ai wallahi boyewa zan yi inyi kamar ban gani ba don ni kam naga dakin zama..." Safiyyah na fadin haka ta bude zip din akwatin ta ta cusa makullin ciki, Khaleesat dake ta kallonta ta girgiza kai tace "Don Allah tunda har ta ajiye maki makullin kiyi hakuri mu koma dakin ki Sophie" Safiyyah tace "Wallahi bazan koma ba for now, next time in ance ta boye min makulli bazata boye ba, ba tace ita er iska bace ni kuma zan nuna mata er daba ce ni, ina nan dakin sai naga abinda ya ture ma buzu nadi" Murmushi kawai Khaleesat tayi bata ce komai ba, Safiyyah ta kyalkyale da dariya tace "To ni ba na manta ke buzuwa bace" Khaleesat tace "A'a ni bafillatana ce, babana bafillatani ne" Safiyyah tace "To Umma fa?" Murmushi kawai Khaleesat tayi bata ce mata komai ba, Safiyyah ta nemi waje ta zauna tace "Ke kiji rashin kunya kiri kiri ta ajiye min makulli kan Centre table da taga ba sarki sai Allah, to da menene nufinta da ta boye makullin in koma garage da zama ko me?" Knocking kofar dakin aka yi Safiyyah ta mike ta bude taga Mustapha tsaye ya shirya alamar zai fita aiki yace "Zaki fito ki yi maku breakfast ne?" Safiyyah tace "Har yanxu duk jikina ciwo yake min wallahi Yaya" Yace "Toh bari ayi maku order" Ta gefen ido Safiyyah ke kallon Surayya da ta fito parlon daga dakinta idonta akan Centre table wato tana duba makullin da ta ajiye, Surayyah ta kalli Mustapha tayi mitsi mitsi da ido tace "Mustapha bayan Aslam ya tashi bacci na tambayesa makullin shi ne ya dauko min wani toy dinsa ashe ciki ya zura, na samu da kyar na ciro makullin sannan na fito na ajiye mata kan Centre table 30 minutes ago, to kaga dai yanxu babu makullin kan Centre table din sannan bata fito daga dakin ka ba, me hakan ke nufi??" Mustapha ya kalli kan Centre table din, can ya kalli Safiyyah da ta hade rai tana rike da waist dinta yace "Safiyyah kin dau makullin ne?" Safiyyah ta wani kallesa tace "Ban gane na dau makullin ba Yaya" Cikin daga murya Surayyah tace "Wallahi in baki fito min daga dakin miji ke da shegiyar kawarki ba duk abinda na maku ku kuka ja ma kan ku a gidan nan" Safiyyah tayi wani dariya tana tafe hannu tace "Toh ni kuma dakin yayana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login