Showing 96001 words to 99000 words out of 257722 words

Chapter 33 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

min transfer ba lallai sai can kasar ba..." Hawaye na sauka idonta ta kare maganar tana kallonsa, ya mike yace "You think i am stupid da zan bari ki kara komawa America ki ci gaba da karatu? to ai kai ki can ma da nayi tun farko i deeply regret doing so, nayi da na sanin kai ki karatu America da har ya bude maki ido, kuma tunda ba kudin ki ko kudin wani naki aka kashe ba all this past years ina ruwanki da asaran da za ayi? How is the lost going to affect you da kike nagging akan expenses din? Ina ce kudina ne sai ko kudin mahaifina? So babu ruwanki, na gwammace inyi asaran duk abinda na kashe maki da dai ki koma kasar nan, kuma kika kuskura kika sake kawo min maganar karatu sai nayi mummunan saɓa maki wallahi, kuma bari kiji, common University din kasar nan ma baza ki yi ba balle na wata kasar don babu inda aka ce lallai lallai sai kinyi karatu, at first nayi tunanin kina da kamun kai da nutsuwa ne shi yasa confidently na kai ki America, amma sai kika tafi kina rayuwa da wani ƙaton ɗan iska a gida daya without my knowledge, ya kai ya kawo ko kudi na tura maki sai kiyi kamar baki gani ba for days tunda kin samu ɗan iskan dake siya maki abubuwa, not even one guy, kattin maza har biyu kika je kina mu'amala da su a can, ko wanne kuma ke kika san abinda kike basa da yake kashe maki kudi, so ko da kuskure kika sake kawo min maganar karatu wallahi sai na maki abinda har ki koma ga Allah baza ki manta ba" Yana kai wa nan ya dau wayarsa ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Khaleesat ta bi sa da kallo hawaye masu zafi na sauka idonta. Har dare Khaleesat na dakinta abun duniya ya taru ya mata yawa, wajen karfe sha biyun dare har ta fara bacci taji an bude kofar dakinfa, a hankali ta bude idonta, wutan dakin taga ya kunna sai kuma ya kashe, ita dai tana kwance bata juyo ba, ya karaso inda take kwance ya cire duvet din jikinta ya cire hulan kanta yana shafa dogon gashinta ya kai fuskarsa kusa da nata murya can kasa yace "You gave me Neither lunch Nor dinner today, saboda kinfi karfin a gaya maki gaskiya ko?" Ita dai bata ce komai ba duk da tana jin sa, dagota yayi zaune ya rungumeta yace "Then let me have you since you are not giving me what u cook" Bai jira abinda zata ce ba ya fara kissing dinta, Sosai Abdul ya bata lokaci wajen romancing dinta irin yanda yasan zai gigita ta, in ba ita ba ma babu warce ya taɓa romancing har haka, ko lube din bai dauko ba yau don baya ganin zasu bukace sa ma, a wannan moment din Frustration dinsa yafi na kullum don sosai ya kai zuciyarsa nesa bai kai mata hannu ba, yana wani irin huci ya fixgota da karfi yace "Why are you doing this to me Khaleesat? Why are you frustrating me?" Kasa ce masa komai tayi jikinta na rawa hawaye na zuba idonta, ta gaji da ce masa ita bata san abinda ke faruwa ba, cikin daga murya jikinsa na rawa yace "Ki bani amsa? Me na maki kike wahal dani kike cutata haka?" Khaleesat dai ta kasa ce masa komai jikinta na rawa don tsoron magana ma take ya gaggaura mata mari, yana wani irin huci ya turata yace "Ki jika abun ki ki sha" Yana fadin haka ya sauka daga saman gadon ya saka Pajamas dinsa ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Khaleesat dai ta jawo duvet ta rufe jikinta har sannan zuciyarta na bugawa ta fashe da matsanancin kuka, bayan kusan minti goma taji fitar motarsa a gidan gaba daya. Da yammacin ranan Momy na parlonta da Godiya sai ga Abdul ya shigo kamar an hankado sa, Momy na kallonsa tace "A'a Babana, sannu da zuwa" Juyawa yayi ya fice daga parlon ganin Godiya, Momy ta ɗan zaro ido tana kallon Godiya sai kuma ta mike da sauri ta tafi kusa da kofar ta bude tana leka corridor taga bangaren Abbansa ya tafi, ita ta dade bata gansa cikin irin wannan yanayin ba ma, ta kulle kofar ta dawo tana kallon godiya tace "Anya Godiya Malamin nan ba maye bane kuwa, kin ga dama yace Abdul zai zo yau gashi kuma ya zo din kamar an jefosa" Godiya tayi wani dariya tace "Ke ma dai wallahi sai kace yau Danger ya taɓa maki aiki da zaki yi mamaki? Yanxu dai sai ki tashi kije ki dora masa girkin da ya fi so da maganin" Momy tace "Ikon Allah, in dai kana da kudin ka zaka ga aiki da cikawa kawai, yanxu ki dubi yanda ya shigo mana a firgice kamar mara lafiya" Godiya tace "Ina kuwa lafiya dama an hanasa angwancewa da amarya, sai kace baki san maza in suka kwallafa rai kan wannan lamari ba" Suka kwashe da dariya gaba daya har da kyakyatawa, Momy tace "Toh yanxu zan tura cikon aikin nan na karshe, yaushe zaki koma wajensa mu je tare in masa godiya" Godiya tace "Nan da kwana uku in sha Allah, kin ga bari in tashi in tafi mai gidana na hanyar dawowa yau" Momy tace "Haka fa kika ce, toh shikenan sai mun yi waya dai kawai" A haka Momy ta raka Godiya har gun motar ta sannan ta dawo cikin gidan ranta fari ƙal, bangaren Alhaji ta nufa ta tarar da Abdul kwance a parlor idonsa a lumshe, zaunawa tayi gefensa tana kallonsa cikin kwantar da murya tace "Babana baka da lafiya ne?" A takaice yace "Hutawa nake yi Momy, i need privacy pls" Momy tace "Toh shikenan, bari in sa a daura maka favorite din ka, ina Mamata fa?" Shiru yayi yaki ba Momy amsa, Momy ta mike ta nufi kofa ta fita daga dakin ta kullo kofar, sai a sannan tayi wani murmushi ta koma bangarenta zata dau maganin da Godiya ta kawo mata wanda zata zuba a cikin girkin abinda Abdul ya fi so, sai da ta kori mai aikinta can compound sannan ta fara girka masa Pounded yam da Vegetable soup, cikin miyan ta zazzage duk maganin da kyauta ta kawo har kala uku, wajen karfe bakwai ta gama ta dau abincin ta kai masa dining table ta ajiye, dama iya cin sa kawai ta girka wato malmala daya kuma ba babba ba, miyar ma ɗan tsut yanda zai cinye gaba daya, sai bayan isha Abdul ya ci abincin da Momy tayi masa, ya bar ma mai aiki ta kwashe sannan ya wuce sama zuwa dakinsa, Momy ta fito dakin Meemah kenan ta bi sa da kallo har ya shiga dakinsa sannan ta bi bayansa, tana shiga dakin tace "Wai lafiya Babana? Ko dai akwai wani matsalan da kake boye min ne" a takaice yace "Ba komai, zan shiga wanka" Yana fadin haka ya fara cire kayan jikinsa, Momy tace "To ka ci abincin?" Yace "Na ci" Momy na murmushi tace "You like it?" Yace "Miyan yayi dadi, but it's little" Tana murmushi tace "To maa sha Allah, amma ai ya isheka dai" Yace "Ya isa" Tace "Toh je kayi wankan ka nima bari inje in ci abinci" Fita tayi daga dakin ya shiga bandaki, Momy na zaune parlonta tana cin farfesu dake cike cikin bowl din hannunta Abdul ya shigo, kallonsa tayi ganin yanda ya shirya sai zuba azababben kamshi yake, tace "Har zaka tafi Babana" Yace "Eh, sai da safe" Tace "To ko in zuba maka farfesun ka kai ma Mamata" A takaice yace "A'a ni ba gida zan kwana ba" Momy tayi murmushi tace "To Allah ya tsare Babana" Yace "Ameen" Daga haka ya fita daga gidan. The next 10 days a gidan Abdul was a living hell for Khaleesat, gaba daya Abdul ya sauya mata a gidan ya dawo kamar wani monster, dukanta da yace ya dena sai dai bai samu slightest opportunity din yin hakan ba, kawai ya maida ta punching bag dinsa a gidan barin in ya zo gareta bai samu biyan bukata ba, kuma bai fasa zuwa mata da bukatar tasa ba amma as usual sai dai kawai ya doketa ya fita bai cimma burinsa ba, kwata kwata ya dena cin abincin gidan, ya dena kwana sai sanda ya ga dama, duk wani ingredients din girki ya dena siyowa sai dai tayi ta cin indomie, hatta bottle water ma da ya kare yaki siyowa, kuma ko Satchet water yaki siya ya ajiye, sai dai ta sha ruwan pampo, gaba daya Khaleesat ta fita hayyacinta a gidan ta dawo kamar ba Khaleesat ba, ga karyewa da gashinta ya dinga yi sosai saboda tsananin damuwa, kana ganinta kasan tana cikin jarabawan rayuwa, bata da aiki sai kuka sai kuma addu'a da sallan dare, gaba daya ta maida duk lamarinta ga Allah, kullum haka take kwana ta tashi da zazzabi amma ina taga fuskar ce masa bata da lafiya, sai dai tayi ta daurewa a haka, in ma ta gaya masa don ya zagi iyayenta ba komai bane a wajensa, in zazzaɓin ya rufeta sai dai ta kwanta har sai sanda zata ji dama dama sannan ta daure ta tashi. Ranan Friday tana dakinta a kwance ko breakfast bata yi ba har kusan karfe sha biyu da rabi, zuwa yanxu ta gaji da cin indomie da ma tana da dakakken yaji sai ta dinga yin ko shinkafa da mai da yaji ne amma babu, indomie duk ya fita a kanta bata iya ci ko ta dafa, gashi haka take dafasa babu yaji balle albasa, bude kofar dakin nata yayi ta mike zaune da sauri tana kallonsa gabanta na faduwa, kamar zai fasa mata dodon kunne taji yace "Ina Cufflinks din da na bari a parlor shekaranjiya?" Sauka tayi daga kan gado, ita dai ta gyara parlon ta goge ko ina jiya da yau amma bata ga wani Cufflinks dinsa ba, a hankali tace "Toh bari in duba a parlon" Wani mugun kallo yake mata hakan yasa ta raɓa tabi ta gefensa ta fita daga dakin zuciyarta na bugawa ta tafi parlor tana dudduba Cufflinks din, da alama masallaci zai je don yin sallan juma'a, babu ta yanda za ace iya Cufflinks din da yake tambayarta yake da shi a gidan, amma sbda neman hanyar da zai musguna mata yake shi yasa zai saka ta gaba ta fito da abinda bata gani ba, kuma rabonsa da gidan tun shekaranjiyan, tana cikin dube dube a parlon shi kuma yana tsaye fuskarsa a murtuke alamar he is loosing his patient aka bude kofar parlon, Momy ce ta shigo da Cousin sis din Alhaji Musa, warce suke kira da Ummu, Yau kwanan Ummu uku a Nigeria daga Dubai inda take aure da yaranta duk a can, kuma a yau zata koma Dubai shi ne ta sa a kawota ta ga matar Abdul kafin a kai ta airport, duk da Abdul yaje ya gaisheta san da ta zo, Khaleesat da duk a rude take ta kalli Abdul a hankali tace "Wallahi ban gansa ba da nake gyaran parlorn jiya da yau, kilan ka sha'afa ko a daki ka bar su ne ka manta" Bata rufe baki ba ya sauke mata wani gigitattcen mari yana huci ya fixgota yace "Ni zaki gaya ma a daki na bar su?" Ta dafe kuncinta hawaye cike idonta tana girgiza masa kai, nan da nan fuskarta yayi ja, ko minding uwar sa da Cousin sis din Babansa da suka shigo parlon bai yi ba, duk suka yi cirko cirko baki bude suna kallon ikon Allah, cikin tsawa yace "Baza ki fito min da shi ba sai na maki dukan tsiya a nan?" Tana shesshekan kuka tace "Nace maka ni ban ga wani links din ka ba wallahi...." Bata rufe baki ba ya sake sauke mata wani wawan marin, Momy da taji ranta yayi fari tass cikin kwantar da murya tace "Subhanallahi, Babana ka bi a hankali, hakuri ake Babana" Ummu ta jefar da handbag dinta kan kujera ta nufesa cikin bacin rai tace "Abdallah?? kana hauka ne kake marin mace haka don uban ka?" Momy ta wani hade rai tana kallon Ummu, Abdul yaki ko kallon Ummu dake masa magana, ya wani haure Khaleesat a mugun fusace har sai da ta fadi kasa, Wani Mari Ummu ta sauke masa a fuska, cikin fushi tace "Ashe kai jahili ne shashasha ban sani ba?" Juyowa yayi yana kallon Ummu da mamaki baya ko kiftawa, Momy ta dinga huci tana kallon Ummu ita ma, nan da nan idanuwanta suka kankance don bacin dai, tunda ta haifi Abdul bata taɓa marinsa ba haka ma ubansa sai gashi yau an maresa a gabanta, Abdul dake kallon Ummu kamar me counting din words dinsa yace "Ummu akan wannan jakar yarinyar kika mareni??" Ummu tace "Na mare ka din, zaka rama ne? Wawa kawai mahaukaci ka saka yarinya karama haka a gaba kana duka? Tarbiyar da aka maka kenan? In na san abinda zan zo in tarar a gidan ka kenan uban me zai kawo ni?" Abdul da idanuwansa suka sauya launi ya kalli Khaleesat yace "Ki je... na sake ki" Yana fadin haka ya dau makullin motarsa ya fice daga parlon kamar zai tashi sama, Khaleesat ta bi sa da kallo babu ko kiftawa kamar bata fahimci abinda yace ba, Momy ta sauke wani bayanannen ajiyar zuciya tace "To Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah" Sai kuma ta kalli Ummu tace "Ke kuma Muhusina kin ci darajar Musa banda haka da babu uban da zai hanani rama ma ɗa na marin da kika masa don tunda na haifesa ban taɓa marinsa ba haka ma ubansa, kuma Abdul yayi min dai dai hukuncin da ya dauka, dama me ake da auren er gidan talakawa er gidan matsiyata? Ai ba class din mu bace ita, kuma duk bama goyon bayan wannan tsinannen auren, kawai irin wannan rana muke ta jira gashi Allah ya kawo mu cikin ruwan sanyi, Alhamdulillah Allah na gode maka, Allah na gode maka, yau zan yi bacci cikin farin ciki da kwanciyar hankali burina ya cika, effort dina kuma bai tashi a banza ba" Momy na kai wa nan ta nufi kofa tana tafiya gansan gansan farin ciki fal a ranta mara misaltuwa tana murmushi ta bude kofar parlon, Khaleesat ta bi Momy da kallo with shock ko kwakkwaran motsi ta kasa tsabar mamaki, maganganun Momy suka dinga yawo a kanta kamar a mafarki, Ummu ta zauna gefen kujera ta dafe kanta tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Sai a sannan Khaleesat taji hawaye masu zafi na silalowa fuskarta, ta mike tana tafiya a hankali ta tafi daki ta dauko hijab dinta har kasa ta fito....



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*



We sell all kind of children school shoes, school bag, Lunch box, Readymade for children.... Atamfa, Lagos laces, veils, Handbags, shoes, lafaya, jewelries, kitchen items e.t.c.....
All at affordable prices

Akwai adashin kayan kitchen, kayan yara and atamfa with laces if interested....



Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM

HALYSAAH 51

Khaleesat na fitowa parlor suka hada ido da Ummu dake kokarin kiran Alhaji Musa da wayarta cikin bacin rai, sunkuyar da kai Khaleesat tayi tana goge hawayen dake ta zuba idonta, Ummu tace "Zo ki zauna tukunna diyata" Khaleesat tayi shiru bata ce mata komai ba don har cikin ranta bata ji zata iya zama a parlon ba kamar yanda Ummu ta umarceta, amma kar tayi disrespecting matar duba da tsaya mata da tayi sanda Abdul ke ci mata mutunci yasa kawai ta duka kasan carpet kanta a kasa, Sau uku Ummu na kiran wayar Dad din Abdul, daga karshe ya daga kiran, cikin fushi ta fara koro masa abubuwan da ta zo gidan Abdul ta tarar da kuma abinda Abdul ya aikata daga karshe, Alhaji Musa dake ta sauraronta ya jira har ta gama, sannan yayi gyaran murya yace "Ai ina ganin Muhusina wannan ba issue bane da zaki shigar da kanki farat daya, ke da ba ma a kasar kike ba zuwa kawai kika yi, i don't think it's proper kiyi involving kanki sama ta ka, it's not done that way, alright? kuma tunda kika ga ya saketa definitely yana ganin hakan shi ne dai dai so meye zaki damu kanki, ko mu iyayensa we are not in the rightful place to question his act, okay? decision dinsa ne, so just stay out of what u know nothing about Muhusina, ba naji kin ce flight din karfe biyu gare ki ba? Ko kin daga tafiyar taki ne?" Kasa cewa komai Ummu tayi tsabar mamaki, kana ganinta kasan she is speechless, ita dai Khaleesat kanta na kasa don ba handsfree Ummu ta saka wayar ba balle ta san abinda Dad din Abdul ke cewa, a hankali Ummu tayi ending call din ta ajiye wayar a gefen kujera don ba ma ta da amsan da zata ba ɗan uwan nata, sosai jikinta yayi sanyi, yanxu dama Family din Alhaji Musa basu canza ba daga yanda ta san su tun tale tale, don ita sai tayi shekara aru aru ba a ganta a Nigeria ba in ba muhimmin abu bane ya kawo ta, Momy ce ta bude kofar parlon fuskarta a murtuke, ashe all this while tana kofar gida tana jiran ganin Khaleesat ta fito ta bar gidan amma shiru shiru bata ga ta fito ba, Momy na kallon Khaleesat tace "In dai ba gidan ubanki bane ko na uwarki nan din tunda har ya furta ya sake ki ai kya fito ki kama gabanki, ko zaman ubanki kike yi har yanxu? Da wani abinda kika zo gidan da shi ne kika yi waya a zo da mota a kwashe maki ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login