Showing 222001 words to 225000 words out of 257722 words

Chapter 75 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

ganin Ajay ne ta mike don dama ta gaji da zancen da Nenne ke mata, fita tayi daga dakin tayi picking call din ta kai kunne tace "Good evening" Yace "Ke... Ni na aikeki ki siya min Birthday present? Who sent you message? A ina kika samu wannan kudin da kika siyo turaren nan?" Khaleesat dake ta sauraronsa ta kyabe baki tace "For once kayi acting like how every other person will do, kawai godiya zaka min for getting u a present and Birthday card, shikenan...." Yace "To bana so, zan kuma bada a maida maki kayanki" Ɗan murmushi tayi tace "Ka maido min da kudin dai...." Katse wayar taji yayi, ta taɓe baki, dama tasan he will never change kuma ko kadan bata ji haushin abinda yayi mata ba, in ma bai yi bane zata yi mamaki, although she sees him as the senior brother she never had, shi yasa bata jin haushinsa ko kadan, ko barin wajen da take tsaye bata yi ba sai ga Alert din 1M ya shigo wayarta, dakinta ta tafi ta zauna ta dinga dariya kamar taɓaɓɓa, wato har da riba ya kara mata a kai, kamar ta kirasa tace saura Birthday Card din yaushe za a maido mata kawai dai ta kyalesa ta bar wayar a daki ta fita parlor, yaran Mama Shatu ne zaune kasan tiles din parlon suna kallo tunda Nenne ta hanasu zama kan Carpet wai kar yayi datti, Nenne ta fito dakinta tace "Ace har karfe tara Ali yaki shigowa gidan nan, yana can zaune kofar gida kan benchi wani ba sai yace Mai gadi bane" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba don tun dawowarsu gidan har yanxu fa Babanta dari dari yake, yaki sakin jiki da gidan, in yana unguwan to a kofar gida zaka samesa zaune kan Benchi da ya sa kafinta ya buga masa, Nenne tace "Wannan ai salon ya ja mana kallon raini ne a unguwan nan, sai ya nuna ma kowa talakawa ne mu kyauta aka bamu gidan nan sannan hankalinsa zai kwanta, kwata kwata yaki sakin jiki yayi kamar shi ne Mai gidan da ya gina gidan" Khaleesat ta koma daki ta dau mayafinta ta fita compound, ita kanta she is feeling somehow yanda Babanta yaki zama comfortable a gidan, da alama babu yanda ya iya da mahaifiyarsa ne yasa ma yake gidan nan, one thing about her father is bai yarda mutum yayi maka gagarumin kyauta babu wani dalili me karfi ba, shi yasa har yau bai sake yayi na'am da gidan ba, don yace bai san dalilin siyan gidan ba, kamar kullum yana zaune kan Benchi da karamar wayarsa da yake kunna Radio yana saurare ga carbi a hannunsa yana ja, ya juya jin an bude gate, Khaleesat ta karasa ta zauna daga gefensa tana kallonsa tace "Baba bbu sauro a nan kuwa?" Malam Ali yace "Ai shi yasa na saka Safata Jiddah, sauro kam ai ba a rasa su a ko ina" Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace "Amma Baba me yasa baka son ka dinga shiga ciki sai dai kawai ka shiga idan dare yayi sosai, da sassafe kuma ka fita kasuwa" Malam Ali yayi murmushi yace "To ai zaman gida na mata ne Jiddah, ni yaushe zan ta zama a cikin gida tare da mata" Sauke idonta tayi cikin sanyin murya tace "Baba ka kwantar da hankalinka plss, tsakaninsa da Allah ya bamu gidan nan ba don wata manufa ba, trust me pls" Malam Ali yayi wani murmushin ya jinjina kai yace "Ke yarinya ce har yanxu Jiddah, haka kawai babu wani dalilinsa bazai siya mana wannan gida me tsada da komai na more rayuwa a ciki ba, babu yanda na iya da Baabata ne amma wannan gida ba gidan da za mu saki jiki a cikinsa bane mu zauna don komai zai iya faruwa in ma yanxu in ma nan gaba, shi yasa ma nayi amfani da wannan dama wajen fara gyaran gidanmu da muka baro a Mariri tunda babu kowa ciki, yanxu haka har an fara plaster a kasa, kuma duk za a canza zinc din gidan da Ceiling, sannan a kara girman window din dakunan, a fitar da inda ruwa zai dinga fita ya dena taruwa cikin gidan, duk abokaina na can ni bance masu gida aka siya min ba, na dai ce an bani gida in zauna har zuwa sanda zan gama gyara nawa gidan na Mariri" Khaleesat ta kasa cewa komai, amma duk jikinta yayi sanyi sosai, tasan bata da wani kalman da zata sake using wajen convincing Babanta, don his belief will be his belief, ita dai tasan daga ɓangaren Housemate dinta baza a taɓa samun matsala akan gidan nan ba balle tuni ya basu takardun gidan da komai, wasu motoci uku ne suka shigo layin a jere, Malam Ali da Khaleesat suka juya suna kallon motocin da suka dallaro masu hasken fitila, amma lokaci daya duk aka kashe fitilun motar masu haske wanda da alama saboda su aka yi hakan, haka kawai Khaleesat taji gabanta na faduwa barin da taga motocin all halted at the same time a kusa kusa da su, Malam Ali dai ya gyara zama har sannan yana kallon motocin shi ma, after almost 2 minute da tsayuwar motocin, motar dake gaba wani ya bude ya sauko daga front seat da alama dai Security ne, ya bude back seat wanda ke bayan motar ma ya sauko, Malam Ali dai sai kallonsa yake don kara tabbatar da shi din yake gani ko ba shi ba, can ya kalli Khaleesat yace "Tashi ki shiga ciki Jiddah" Gaba daya hankalin Khaleesat ya gama tashi ta girgiza kai tace "A'a baba I will remain here" Guard din mutumin na biye da shi a baya ya nufo Malam Ali da murmushi fuskarsa ya kai masa hannu yace "Assalamu alaikum Alhaji Aliyu" Malam Ali ya mike ya kai masa hannu yana mamakin me kuma ya hadasa da Deputyn garin nan, Khaleesat dai bata ma ganesa ba amma ta mance rabon da ta shiga tashin hankali irin na wannan moment din, me zai kawo su wajen Babanta da daddaren nan da motoci har uku, Deputy ya kalleta yace "Sannu yarinya" Dakewa tayi ta gaishesa ya amsa da fara'a sannan ya maida dubansa kan Malam Ali yace "Idan babu damuwa Alhaji Ali mun zo maka ne akan wani batu me muhimmanci, Allah yasa zaka bamu lokacinka ka saurare mu, in kuma lokacin da za mu dawo zaka saka mana to duk babu damuwa" Malam Ali yace "To ni dai Allah ya sa lafiya ranka shi dade" Deputy yace "Babu komai sai Alkhairi ka kwantar da hankalin ka, ni da abokina ne da sauran manyan mutane muka zo har inda kake muka same ka akan wannan batu da ke tafe da mu, amma sai dai muna baka hakuri mun maka zuwan bazata, and this could be sort of inconvenient....." Malam Ali ya dake don zuwa yanxu kam ya gama ƙaguwan yaji me kuma ya hadasa da manyan mutane kamar yanda Deputy yace, sannan me ya kawo Deputy da kansa inda yake, a ina ma ya san sa?? Duk da yasan Deputy mutumin kirki ne kuma kowa ya shaida amma fa hankalinsa yaki kwanciya, yana gyada kai cikin karfin hali yace "A'a ba komai ranka shi dade, bari a shimfida tabarma sai mu zauna a nan tsakar gida, hakan yayi ko?" Deputy yace "To babu laifi Alhaji Ali" Malam Ali ya kalli Khaleesat yace "Shiga ciki ki shimfida mana tabarma a compound Jiddah" Mikewa Khaleesat tayi jiki a sanyaye ta shiga cikin gidan don yin abinda Babanta yace tayi....



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

07087865788

HALYSAAH
PAGE 91

https://chat.whatsapp.com/B5uR4Jfj6fZIIN0EIIHegM?mode=ac_t



Bayan Khaleesat ta shimfida tabarmin da Babanta yasa ta shimfida ta koma parlor ta nufi kujera zata zauna har a lokacin hankalinta ya kasa kwanciya duk da irin approach din deputy toward her dad but she was so tense and confused, gashi ita bata ma san ko su waye ba, Nenne na kallonta har ta zauna kan kujera sannan tace "Yanxu baki lallabasa kun shigo gidan tare ba kika bar sa zaune bakin gate? Haka rayuwa zata ci gaba yana zaman kofar gida kamar Mai gadi kenan?" Ita dai Khaleesat bata ce komai ba, she was trying all possible best to keep calm at this moment, Nenne ta kyabe baki ta dau remote ta danna inda Islam ta nuna mata ana dannawa idan za a canza tashan kallo, tana canza tashar duk yaran dake zazzaune parlon suka juyo suna kallonta, ta tsuke fuska, Mikewa Khaleesat tayi ta bar parlon ta tafi dakin Ummanta ta sameta zaune tare da Aunty Farida sai Mama Shatu dake zaune daga kusa da kofar dakin a zuwan ta shigo hira da Umma, tunda Khaleesat ta shigo Umma ke kallonta, ganin Mama Shatu kawai Khaleesat ta juya ta tafi dakinta, Aunty Farida ma ta bi ta da kallo, bayan kusan minti biyar sai ga Umma ta shiga dakin nata tana kallonta tace "Lafiya Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta har Umma ta karaso ta zauna gefen gado tana kallonta, sai ga Aunty Farida ma ta shigo dakin tana tambayarta me ya faru? Da kyar Khaleesat tace "Baba ne yayi baƙi a motoci ban san daga ina suke ba" Umma ta kasa daina kallonta ita ma a ɗan tsorace tace "A motoci kuma? Ke wa ya gaya maki?" Khaleesat tace "Muna zaune tare a waje sai ga su a motocin" Hankali tashe Umma tace "Yanxu yana ina Malam din?" Khaleesat tace "Ya ce in shimfida masu tabarma a tsakar gida, har ma sun gaisa da baƙin" Juyawa Aunty Farida tayi ta fita daga dakin, ta tafi can compound ita ma dai hankalinta a tashe, ai ko ta hangosu zazzaune saman tabarma su hudu sai Malam Ali na biyar da ya sinne kai ko me suke gaya masa oho, ta juya ta koma cikin gida. Karfe goma saura na daren Khaleesat ta shigo parlon Babanta tare da Aunty Farida, Umma ma na zaune parlon sai Nenne, Nenne ta gyara zama tace "To yanxu Ali ko don wannan girmama ka da yan unguwan nan suka yi suka shigo har gidan nan suka zazzauna a tabarma suna gabatar maka da kansu ya kamata ka rufa mana asiri kar ka sake zama bakin gate kamar Mai gadi, baka ji dadin da naji ba wallahi ganinka a tsakankanin manyan mutane a tsakar gida" Malam Ali dai kallonta kawai yake, can yace "Yanxu Baaba wa yace maki yan unguwan nan ne?" Nenne ta saki baki tace "Ba yan unguwan nan bane? To yan unguwan dake gaba da namu ne ko wanda ke bayan namu?" Malam Ali yace "Ni baƙin da suka zo gidan nan bama su da alaka da unguwan nan gaba dayan ta" Nenne ta zaro ido tana kallonsa tace "Kai haba dai? To a ina ka samo su Ali? Su waye?" Malam Ali ya sauke ajiyar zuciya yace "Dalilin tara ku a nan da nayi kenan Baaba, duk za ku ji waye su da kuma me ya kawo su gidan nan" Nenne ta gwalo ido tace "Wani laifin kuma ka sake yi Ali? Mun shiga uku mun lalace, abun arziki bai amshe mu ba, ko kwace gidan suka yi?" Malam Ali ya kara sauke wata ajiyar zuciyar cikin nutsuwa ya fara koro masu bayanin su waye mutanen da suka zo da kuma dalilin zuwan nasu gidan, tunda ya fara magana Khaleesat ke kallonsa babu ko kiftawa zuciyarta na bugawa, haka ma Umma da Aunty Farida that look speechless, Sai da Nenne ta jira ya kai har karshe sannan tayi mitsi mitsi da ido tace "Amma ka ban mamaki kuma ka ban tsoro da baka masu koran kare ba Ali, anya kuwa ba a canza min kai a daki na je wankan jegon ka a banɗaki ba kuwa tunda gidan yawa ne kuma mu uku muka haihu ba wani tazara tsakaninmu??? Ali yanxu kana nufin baka kore su ba ka zauna ka sauraresu har karshe?" Malam Ali yace "In kore su kuma Baaba? Na fa gaya maki su wa da su wa suka zo, ta yaya zan koresu fisabililahi?" Nenne ta mike a fusace tace "To ina ruwana da koma su waye, kai ko shugaban kasa ne in ya gaya maka abinda bai gamshe ka ba ai zaka kama kanka balle ma ba shi bane, yanxu a takaice kana nufin ce masu kayi toh shikenan?" Malam Ali yace "A'a, ni ban ce masu haka ba Baaba...." Nenne tace "Amma daga Awdul din har iyayensa Allah Ubangiji ya tsine masu albarka daga su har wanda ya basu shawaran turo maka manyan mutane su baka hakuri, kai kuma da yake gantalalle ne kai baka san ciwon er ka ba maimakon kace masu ai an sa mata rana biki saura sati daya yanxu haka shine ka zauna da wata safarka a kafa kamar ɗan bigilantee a tsakankaninsu kana sauraronsa, to wallahi idan ban kai karar su kotu ba Allah ya tsine min, ko Awdul ne kaɗai namiji da ya rage a duniya idan na kara basa auren jikata a kirani tsohuwar banza tsohuwar hofi, haba fisabililahi, sannan shi yaron nan da ya siya mana gidan nan kanin ubanmu ne shi ko na uwarmu da zai siya mana katon gida haka idan har ba sonta da aure yake ba, sai ya fito ya gaya mana yana sonta mu wani irin ƙwaƙwalwa gare mu da baza mu gane ba? ai ni ba yarinya bace nasan abinda nake, wallahi sonta yake so kuma na aure, haka kawai ka biye barayin gwamnati su saka ka a tsakiya don su tsorata ka ka sake daukar er ka ka bada a karo na biyu? Ko dai baka da lafiya ne Ali?" Malam Ali dake ta kallonta cikin nutsuwa yace "Yanxu fa Baaba baki saurareni na kai karshen bayani na ba...." A fusace tace "To ina jin ka maza maza tafi karshe" Malam Ali yace "Ni nace masu bazan ma Jiddah dole ba, duk abinda take so shi zan mata kuma shi nake so, in ma shi Abdul din tace take son komawa ni bazan hanata ba sai dai in bi ta da fatan alkhairi, in kuwa tace bata so to hakan ya zauna don bazan mata auren dole a karo na biyu ba" Nenne tace "To maza tun basu yi nisa sun isa gida ba ka bi su kace ai babu wannan zancen ko makamancin sa, yarinya tace bata sonsa ta tsanesa, in kuma wannan karan da karfin mulki za su yi amfani da shi wajen auren nata kamar yanda suka yi da kudi watannin baya to sai su yi mu gani, maza su gaya ma ɗan su ya cire shegun idonsa akan Khaleesah bata sonsa kuma tafi karfinsa nesa ba kusa ba wallahi" Hawaye ne kawai ke zuba idon Khaleesat tana shessheka tana jin wani zafi a ranta, ta jinginar da kanta jikin Aunty Farida cause she is beginning to loose her control, Sosai Aunty Farida ke jin dadin maganganun Nenne don ita ma banda tafarfasa babu abinda zuciyarta yake a inda take zaune, Umma kuwa dafe kanta da yayi mata nauyi sosai tayi, Nenne tace "Ka ji me nace maka ko baka ji ba Ali?? Tun gari bai waye ba ka san yanda zaka yi ka sanar masu babu wannan maganar da suka zo da shi don har an saka ma Khaleesah rana da wanda take so kuma ranan jama'ar nan daurin aure" Malam Ali yace "Shikenan Baaba, su a yanda suka zo ma suna tunanin bayan sun gabatar da bukatarsu nauyin su da ganin girmansu zai sa in amince lokaci guda babu ja in ja, amma wallahi ban yi haka ba, nuna masu nayi ni bani da ta cewa sai abinda 'ya ta tace shine magana don bazan kara mata dole ba, yanxu zuwa gobe suna saurarata su ji ya ake ciki, don haka bazan boye masu komai ba in sha Allah, zance su yi hakuri nayi mata miji" A fusace Nenne ta nufi kofa tana cewa "In Alhaji Musa bai yi hankali ba zan taka har gidan nasa in ci masa mutunci wallahi, tun da saboda shegen ɗan sa aka halitto Khaleesah ba sai ya zo ya sake daura auren ba mu gani, wato ya zo maka da manyan mutanen garin nan yanda zaka yi masu biyayya ga ka ɗan banza ko? To mu zuba da su" Tana kai wa nan ta fice daga parlon, Umma ma ta mike ta bi bayanta don bakin ciki ma bazai bari tace komai ba, shi dai Malam Ali kallon Khaleesat kawai yake, a hankali yace "Kiyi hakuri Jiddah, babu me maki dole in sha Allah, ki kwantar da hankalinki" Ita dai Khaleesat hawaye kawai take ta kasa cewa komai, Aunty Farida tace "Amma Malam tun farko bai kamata ma ka zauna ka ci gaba da sauraransu ba bayan kaji dalilin zuwan su, kamar yanda Nenne tace da kawai sai kace masu ai an saka mata rana kawai" Malam Ali yace "To tunanin nan bai zo min ba wallahi, amma ba komai in sha Allahu zan kira na kusa da Deputy din gobe in gaya masa yanda ake ciki don ya bani numbersa suna sauraran kirana gobe" Aunty Farida tace "Allah ya kyauta" Mikewa tayi ta dago Khaleesat suka fita daga parlon. Daren ranan nan Khaleesat kasa baccin kirki tayi, she was so disturb, ta rasa menene zai sa Abdul ya hakura da ita ya cire ransa a kanta cikin ruwan sanyi babu tashin hankali, dama kullum a ranta tana jin ba fa hakura yayi ba, he is definitely coming back amma bata san ta wannan salon zai sake dawowa ba, ko kadan bata yi mamakin gano sabon gidan nasu da suka yi ba ba don ko dubu biyu suka ba wani a Mariri tsaf zai kawo su tunda kusan kowa yasan inda suka dawo yanxu, sai kusan karfe hudu da rabi ta tashi daga saman darduman da take zaune bayan ta idar da sallolin da tayi sannan ta kwanta.... Da asuba bayan ta idar da Sallah tayi azkar ta tafi dakin Umma ta gaisheta, Umma dake zaune kan darduma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login