Showing 204001 words to 207000 words out of 257722 words

Chapter 69 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

Farida tace "Ki gama rabe raben tsaraban ki je ga ruwa can zan juye maki kiyi wanka sai ki karya" Khaleesat dai sai kirga Chocolates din take don har da na Step Siblings dinta take son ta cire. Karfe sha biyu da yan mintuna Nenne ta shigo gidan fuskarta babu yabo babu fallasa, har ta cire gyalenta zata rataye saman igiya ganin tsakar gidan cike da hayaki don su Mama Shatu na ta girkin siyarwan su ta fasa ta nufi dakin Umma da gyalen a hannu, ko amsa gaisuwan su Mama Shatu bata yi, tun da Umma taji muryar Nenne ta fara ma Khaleesat mita tace "Sai da nace ki je ki gaisheta kafin ta samu labari kin dawo, yanxu sai abinda ta manta ne bazata fada mana ba" Khaleesat dai na kwance saman gadon Umma tana danna wayarta, tun da tayi breakfast take son tayi bacci amma yan unguwan sai shigowa dakin Umma suke wai yi mata sannu da zuwa, alhalin da yawansu gulma ce ke shigo da su ba komai ba, ga Sha'awa da taki tafiya tun da ta shigo dakin kusan awa daya da rabi kenan, har da wasu makotansu biyu duk sun zauna sun ki tafiya ko me suke jira oho, Nenne na tsaye daga bakin kofa don labulen dakin a ɗage yake tace "To Zahra'u sai me don Khaleesah ta dawo anki zuwa a gaya min ko kuma a turata ta gaisheni har sai da almajirina ya shigo ya gaya min, naga dai ba don ni ba ai ko iyapot bazata sake zuwa ba balle har ta koma wata Amurka, kuma ba wani ya haifar min uban nata ba dai da za a dinga nuna min an fi ni iko da ita" Khaleesat dai tayi murmushi ta sauko daga kan gadon ta zauna kasa tace "Sannu da zuwa Nenne" Nenne ta kauda kai ta tsirtar da yawu ta kalli su sha'awa tace "Su kuma wa ennan fa? Baku ganin dakin babu sarari gashi duk ya dume bayin Allah sai shaƙan numfashin juna ake, ke sha'awa zanin daddawan naki kika shigo dakin mutane da shi kika zauna? Haba ki dinga ji tsoron Allah mana sha'awa" Mikewa sauran makotan biyu suka yi suna kallon Khaleesat suka ce "Allah ya huce gajiya Khaleesah" Daga haka suka nufi kofa suna gaida Nenne suka fita, Nenne ta tsirtar da wani yawun tace "Tabɗijam...." Sha'awa ta mike tace "Nenne shigowa ta kenan babu dadewa na zo yi ma Khaleesah sannu da zuwa, ashe ma tun da safe ta iso, ina can na gama curin daddawa ban san ta dawo ba" Nenne ta bata hanya da sauri don kar ta goga mata jikinta, a haka Sha'awa ta fita daga dakin, Nenne ta kalli Umma tace "Lallai Zahra'u kina da aiki, ke ba kazama ba ki bar mata kazamai su shigo maki daki su cika da warin jiki har da me daddawa? duk dakin ki ya dume ba dadin shaƙa? yanxu da kin yi bakon kunya ina zaki ajiyesa, ga daki ba daki ba kamar zuciyar talaka, halan ina parida ta tafi don dai nasan da tana nan da tuni ta fatattake yan iska ta koresu, to dai duk komai ya zo karshe, Alhamdulillahi tun da Khaleesah ta dawo lafiya zuwa nan da yan kwanaki kadan sai mu tattara mu bar tsinannen unguwan nan mu koma inda bawon Allahn can ɗan albarka Ahmad ya siya mana, dama dai ni ce nace lallai sai an jira ta dawo tunda ta dalilinta aka yi mana wannan abun arziki baza mu yi mata butulci mu tare a gida babu ita ba, shi ne nace lallai ita zata jagorance mu zuwa sabon gidan a bude mu shiga cikin farin ciki, saukan al-qurani dama na saka anyi yafi a kirga a gidan, shikenan Allah ya rabamu da masu warin unguwan nan kuma haka" Nenne ta ajiye kwanon hannunta tace "Ga shi nan kwadon zogala na maki da naji ance kin dawo, to Ahmad din fa?" Khaleesat tace "Sai anjima zai shigo" Nenne tace "Ai ko bari in maza in tafi in ɗora masa tuwon shinkafa da miyar agushi, in bada dubu biyu a siyo min nama me kyau in zuba a miyar" Daga haka ta juya da sauri tana yafa gyalenta ta nufi kofar fita daga gidan, Umma dai murmushi kawai tayi, Khaleesat ta kalleta tace "Dama Nenne ce tace baza a koma gidan ba Umma?" Umma tace "Gashi nan ta gaya maki kuwa, babanki ma bai yi na'am da gidan ba har yanxu" Mikewa Khaleesat tayi bata ce komai ba, ta dauko kwanon da Nenne ta ajiye mata ta bude, ai ko taji dadin ganin zogalen don hadadden hadi Nenne tayi masa. Wajen karfe hudu da rabi Jay ya zo gidansu Khaleesat, bayan sun gaisa da Umma da Aunty Farida Khaleesat ta dauko masa bottle water din da ta siyo masa ta ajiye masa, Aunty Farida dai sai godiya take masa ya ma kasa kallonta yana ɗan murmushi kawai, Khaleesat ta zauna gefen Ummanta tana kallonsa babu ko kiftawa, tsadadden Gezna ne fari jikinsa, kayan sun masa kyau ba kadan ba, anya ta taɓa ganinsa da manyan kaya kuwa, ya fito sak Hausa Fulani yau, Aunty Farida tace "Za ku karasa can gidan Nenne da shi ai ko?" Khaleesat ta gyada mata kai sannan ta mike, Hijab dinta ne har kasa jikinta dama, ta dau nikab ta ɗora, ta fita tsakar gida tana jiransa, after almost 5 minutes ya fito daga dakin, step mothers dinta dake tsakar gida duk suka kafesa da ido kamar yanda suka yi san da ya shigo, Khaleesat dai ko kallonsu bata yi ba ta nufi kofar fita gidan ya bi bayanta, sai da suka fita kofar gida ya kalleta yace "What is this u are covering ur face with Halysaah?" Dariya tayi tace "Nikab ne baka sani ba?" Kallonta kawai yake suna tafiya, can yace "Tell me why you are covering ur face?" Tana murmushi tace "Saboda kallona za ayi ta yi a unguwan, kuma na saba sakawa in zan fita dama" Murmushi kawai yayi bai ce komai ba, a hankali tace "Ko in cire?" Ya kalleta yace "A'a, gwara haka, kinga za a rage kallon ki" A haka suka isa gidan Nenne, Nenne ta rasa inda zata sa Jay tsabar tarba, ta kinkimo masa gaba daya coolern tuwon da tukunyar miyan ta dire a gabansa, lemon kwalba kuwa dama guda biyar ta sa aka siyo masa da ruwan gora biyu, shi dai sai murmushi yake gashi ba yunwa yake ji ba, Khaleesat ma sai murmushi take, can ta cire nikab dinta ta ajiye, Nenne tace "In ma kunyata kake ji bari in shiga makota ka ci tuwonka ka koshi, don kai kadai nayi tuwon nan wallahi in ma baka ci da yawa ba wallahi bazan ji dadi ba, wanda ka rage ma a leda zan juye maka ka tafi da shi, ni ko gurin Zahra'u sai in je anjima ta tsam min tuwon daren ta..." Daga haka Nenne ta yafa gyalenta ta fita daga gidan, Khaleesat sai kallonsa take tana murmushi, ya cire hulan kansa ya ajiye gefe don har ya fara zufa ganin abincin da aka dire masa, yana kallon tuwon yace "Ya za ayi da tuwon nan Housemate, Ni fa na ci abinci kafin in fito wallahi" Khaleesat tayi dariya tace "Haka nan zaka tuttura ka ci, kasan tun yaushe take maka girkin nan kuwa?" Plate ta jawo ta saka tuwo daya, ya zaro ido yace "I can't finish even quarter of this Halysaah, a koshe fa nake" Dariya kawai take bata tankasa ba ta bude tukunyar miyan dake ta kamshi ta zuba miyar a wani bowl daban, ta saka nama yanka hudu, ta maida tukunyar miyar gefe tace "Oya gashi" Ya kalleta yace "Where am I going to start from? Billah I am full, ki ci don Allah..." Khaleesat ta wanke hannunta ta dau cokali ta dibi tuwon da miya tana kallonsa tana murmushi, yayi kasa da murya yana kallonta shi ma yace "Ko feeding dina zaki yi?" Murmushi tayi ta sunkuyar da kai don hakan take son tayi amma kunya ya hanata yi, yace "In dai zaki yi feeding dina zan ci wallahi" Dakewa tayi ta kai masa tuwon baki ya amsa yana murmushi, nan da nan yaji ya samu appetite din cin tuwon.... Bayan kusan minti talatin sai ga Nenne ta shigo gidan, cikin dubara Khaleesat ta ɗan matsa daga kusa da Jay, Nenne ta bude Cooler din tana kirga tuwon ciki tace "Kana nufin guda daya kacal ka ci tuwon?" Jay yayi dariyar da bai yi niyya ba yace "Ai na koshi ne kaka" Bata san tare ma suka ci guda dayan da Khaleesat ba, Nenne tace "Ban ji dadi ba gaskiya, duk tunanina zaka tashi da malmala biyu, ai don kai nayi tuwon wallahi" Khaleesat na murmushi tace "Ba ya cin abinci da yawa fa Nenne" Nenne tace "To wa ya sako da ke, Allah ya sa ma bake kika sa guda dayan a gaba kika ci ba" Jay ya shafa kai yace "A'a Kaka, ni na ci" Nenne ta nemi waje ta zauna tace "To sai a juye maka sauran a leda ka tafi da shi kawai" Shi dai murmushi kawai yake, Nenne tace "Ya labarin innar ka, da fatan tana lafiya, da yan uwa da abokan arziki" Yace "Alhamdulillah Kaka" Nenne tace "To madallah, Allah Ubangiji ya maka albarka, ka ce min a can Bauchi kuke da zama ko?" Jay yace "Eh can muke" Nenne tace "To kuwa in sha Allahu za ku gan ni a Bauchi kwanan nan don zan je duba wata 'ya ta, tana da yarinya me laluran shafar aljanu, gashi er ta zama budurwa abun dai ba dadi, in de na shiga Bauchi zan neme ka, dama in zan je Parida ke min rakiya tunda da wayewarta, a wace unguwan ku ke a Bauchi?" Jay na murmushi ya kira mata sunan wata unguwa daban, don har sannan dai Nenne bata san ɗan wani family bane, Nenne tace "Ai ko cikin kwanan nan zan shigo garin naku, rabona da zuwa yau kusan shekara biyu kenan" Jay yace "Allah ya kai mu lokacin Kaka" Nenne tace "Ameen" After some seconds ya daga kai ya kalleta yace "To yanxu Kaka tunda ta dawo yaushe za ku koma can Tudun Yolan?" Nenne tayi kasa da murya tace "Ai in sha Allahu nan da kwana uku za mu bar unguwan nan da daddare, don mutan unguwan ba yan arziki bane, bana son ma su san inda muka koma, kaga da daddare ai yafi sirri, zuwa gobe zan kira yan uwa da dangi duk a basu adireshin sabon unguwan mu hade a can ba sai sun taho nan yi mana rakiya ba tunda bama son yan unguwan su san inda za mu koma, shi dai Malam Ali har yanxu dar dar yake banda ni da nake tausan sa gaskiya da bazai bar unguwan nan ba, don yana gudun abinda zai je ya dawo, nace masa da xuciya daya kayi mana alkhairin nan ya cire komai a ransa, ba komai tattare da kai sai alkhairi don kai ɗan halaq ne" Jay yayi shiru don bai ma san me zai ce ba, ko da ya kawo ma mahaifin Khaleesat takardun gidan ƙin amsa yayi ya nuna masa he is much okay with where he is leaving with his family, yasan kawai yana gudun abinda zai je ya dawo ne, shi kuma da zuciya daya ya siya masu gidan ba don yana son anything in return ba, Nenne ta marairaice tace "Mu dai wannan abun arziki da ka mana ɗan nan Allah ya iya maka duniya da lahira, Allah ya raba ka da sharrin masu sharri, yayi maka albarka ya bude maka hanyoyin samu, Allah kuma ya ji ƙan mahaifinka ya sabunta masa rahama" A hankali Jay yace "Ameen" Nenne tace "Iya abinda za mu iya ce maka kenan ɗan nan, kuma babban dalilin da yasa ko yan unguwan nan bana son su san inda za mu koma shine kusan duk bayan kwana biyu sai ɗan iskan yaron nan Awdul ya zo unguwan nan, haka zai samu ubanta yayi ta masa magiya wai mu zai kara yaudara, har nan ya zo min na koresa da tabarya shi ne bai sake zuwa min ba sai dai yaje can gidan Malam Ali da ya raina, kuma ni ban ga alamar nadama a tare da shi ba, sam ba alkhairi ya dawo da shi ba, kaga tunda bamu san me ke baƙar zuciyarsa ba tunda har yarinyar nan ta dawo kasar nan gwara tun wuri mu lallaba mu tashi cikin sirri babu wanda zai san inda muka koma, Shikenan mun rabu da shi lafiya, don wallahi ban yarda da yaron ba, sam babu Allah a ransa, da kyar in ba wani shirin yake ta yi ba, kaga kuwa ai dole mu ba er nan kariya kar ya sake cutar mana da ita" Jay yayi shiru ya kasa cewa komai yana kallon Nenne, sosai hankalin Khaleesat ya tashi jin abinda Nenne ke cewa kan Abdul, ta juya ta kalli Jay a sanyaye, ya sauke ajiyar zuciya a hankali yace "In sha Allahu komai ya zo karshe Kaka"



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
Ur evidence 07087865788

HALYSAAH PAGE 85

Karfe tara da kusan rabi na dare Khaleesat ta shigo dakin Ummanta da sallama tana rike da ledan tsire wanda babanta ne ya siya mata, tun bayan isha'i take wajen baban nata tare da Nenne sai yanxu ta dawo daki, Jay sai da ya jira har Malam Ali ya dawo suka gaisa sannan ya bar unguwan daxu, zaunawa Khaleesat tayi kusa da Aunty Farida tana bude ledan naman tace "Su Islam har sun yi bacci" Umma dake kallonta tace "Nennen "Ne inen ta tafi ne?" Khaleesat ta girgiza kai tace "A'a tana can bata tafi ba" Aunty Farida tace "Baza ki ci tuwon naki ba?" Khaleesat ta langwabe kai tace "Nama zan ci" tuwon masara da miyar kuka Umma tayi, tana ganin tuwon daxu kawai tasan bazata ci ba, Aunty Farida tace "Ina kawarki Hajiya Safiyyah" Murmushi Khaleesat tayi tace "Tana can Maryland" Aunty Farida tace "Haba? Ita bata dawo hutun ba kenan?" Khaleesat tace "Yayanta yace sai next week za su taho gaba daya" Aunty Farida tace "Allah sarki, Allah ya kawo su lafiya, na zata tare ku ka dawo ai... Wai saura wata nawa yanxu ku kare karatun gaba daya?" Khaleesat tace "Bai wuce wata hudu ba, final semester kawai ya rage mana" Aunty Farida tace "Toh Allah Ubangiji ya baku sa'a, ya sa ku gama lafiya, ai kun kusa" Khaleesat tace "Ameen Aunty" Aunty Farida tace "To amma me yasa baku dawo har Junaid ba ya riga ku tahowa shi" Umma ta rike haba tana kallon Aunty Farida tace "Ikon Allah, kika san uzurinsa?" Ita dai Khaleesat murmushi kawal tayi bata ce komal ba ta matsar da takardan naman gabanta kusa da Aunty Farida bayan ta debar ma Umma nata.... Bayan Khaleesat taje tayi alwala ta dawo dakin Umma tayi shirin kwanciya, ta kwanta ta dau wayarta zata bude WhatsApp don rabonta da hawa tun da asuba da suka sauka Abuja kuma tasan Safiyyah dole zata yi mata magana, tana shiga WhatsApp din ta ga status din Ajay, sosai tayi mamaki don bata yi zaton yayi saving numberta ba, ta bude status din, daily reminder quote taga ya dora, ta tura masa Sticker sai taga yana ma online, WhatsApp call tayl ma Safiyyah bayan sun gama magana still bal mata reply ba, dama bata sa ran zai yi ba ta kashe data dinta ta kwanta. Washegari Khaleesat na idar da azkar din da take ta kira Jay, don yace mata karfe shidda zai wuce Bauchi kuma driving zai yi, bayan sun gaisa tace "Are you still leaving early?" Yace "In sha Allah Halysaah, har na gama shiryawa ma" Tace "Toh Allah ya tsare hanya, Allah ya kai ka lafiya, don't forget to pray please...." Yace "I won't dear" Tace "Amma kayi breakfast?" Yace "Yea, I took tea, idan na fita gida zan kira ki in sha Allah, ko za ki koma bacci ne?" Ta girgiza kai tace "A'a" Yace "Ohk then, I will call you" Daga haka ya katse wayar. Karfe goma sha daya Nenne ta shigo gidan ta nemi kujera er tsugunno ta zauna tana kwalo ma Umma kira, Khaleesat dake wanke wanke a tsakar gidan ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace "Ahamad din ya tafi Bauchin kuwa, yace min da sassafe zai bi hanya yau" Khaleesat tace "Har ya isa tun karfe goma" Nenne tace "Maa sha Allahu haka ake so, in kun yi waya ki ce ina gaishesa don Allah, ni ba waya gareni ba balle in kirasa, amma kar ki ce masa haka, kawai kice ina gaishesa ina masa bangajiya" Khaleesat na dauraye kwanon hannunta tace "Toh" Sai da Umma ta fito sannan Nenne ta amsa gaisuwan su Mama Zubaida a dakile ba tare da ta kalli inda suke ba, Umma ta zauna kan tabarman dake shimfide ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace "Ina parida" Bata rufe baki ba sai ga Aunty Farida ta fito dakin Umma, ita ma ta gaida Nenne ta amsa sannan tayi kasa da murya tana kallon Umma tace "Zaura'u, ina ga fa lallai lallai yau za mu bi dare mu bar unguwan nan, don daxu almajirina ke ce min yaga Awdul ya shigo unguwan nan da safe" Khaleesat ta daga kai da sauri tana kallon Nenne gabanta na faduwa, Nenne tace "Don haka baza mu biye All ba, In yaga duk mun tattara mun tafi ya biyo mu da dan akwatinsa, don ba irin maganar da ban masa jiya da daddare ba kan ya hakura ya amshi gidan nan da bawan Allahn nan ya siya masa hannu bibbiyu don da zuciya daya ya siya masa, amma tsoro ya hana Ali sakat, yace shi tsoro yake gaskiya...." Umma dai tayi shiru don bata san me zata ce ba, ita kanta hankalinta ba a kwance yake ba tunda Khaleesat ta dawo jiya don bata san wani mugun abun ke ran Abdul

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login