Showing 72001 words to 75000 words out of 257722 words
Chapter 25 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar
kallonta yake without blinking, sauke idonta tayi tana wasa da karamin cokalin dake cikin mug din shayinta, ya dauke shayin ya mayar gefe, taga ya kai hannu shoulder dinta zai sauke siririn hannun rigar dake jikinta, sosai hankalinta ya tashi amma bata ce masa komai ba gabanta na ci gaba da faduwa, ya sauke rigan gaba daya yana kallon bare chest dinta, hawaye ne ya cika idonta taki yarda su hada ido, can dai tayi karfin hali muryarta na rawa tace "Toh baka sha shayin ka ba zai huce" Yayi kasa da murya yace "Wa ennan zan sha... " Momy ce tsaye parlor tana kallon Meemah dake rusa kukan bakin ciki uwa er yarinya, ga trolley dinta a gefenta, bacin rai ne karara kwance fuskar Momy da idanuwanta suka ƙankance tana huci, mai aikin gidan ce ta shigo parlon rike da bowl din pepper soup din da tayi ma Momy, cikin ladabi ta risina tace "Hajiya ga farfesun nan ya kammala" a fusace Momy ta figi throw pillow ta jefa mata tace "Don ubanki wuce ki ban waje ke da farfesun, baki ga magana nake bane zaki shigo min parlor kai tsaye, yau ga jahilar mata kai" a tsorace mai aikin ta juya da sauri ta bar parlon ta koma kitchen ta kullo kofar, Momy tace "Na kusa daina daukan tsinannun masu aikin nan don sun isheni haka kuma, na kori wancan shegiyar da ta shigo min parlor da yan uwan Alhaji da suka zo daga kauye babu izinina yanxu kuma an kawo min wannan jakar da ko kwana biyu bata yi ba ta fara nuna halayyan dabbobi" Ita dai Meemah kuka kawai take tana fyace hancinta da handkerchief, tsabar kuka idonta har sun suntume, Momy ta kara kankance idanuwanta tana kallon Meemah tace "Shi Abdallahn ne yayi maki haka Meemah?" Meemah ta hadiye wani abu da ya tokare mata wuya don bakin ciki tace "Momy da kin ga tijaran da Abdallah yayi min akan yarinyar nan ko, hmmm, ki bari kawai Momy, Momy kare bazai ci abinda Abdul yayi min ba, bayan zagi da cin mutunci wai ni ya kora a gidansa, kora irin ta walakanci" Momy ta zauna kan kujera with disbelief, duk da AC dake aiki a parlorn sai zufa take yi dama ga ta narkekiya, tana gyara zama tace "Ko dai ya sha wani abu ne Meemah??" Cikin rawan murya Meemah tace "Babu abinda ya sha wallahi Momy don lafiyan Allah ya dauko ni a airport muna ta hira, tare fa da ni duk aka yi tracking yarinyar nan tunda akwai wani tsohon saurayina wanda aikinsa kenan, amma wai yau akanta Abdallah zai min irin wannan tijara haka tun ba aje ko ina ba, duka duka fa kwananta yau hudu da shiga hannunsa, amma ya rufe ido ya zazzageni ya ci min mutunci ya koreni" Momy tayi wani murmushin takaici tana girgiza kafa tace "Kin ga abinda nake ta gudu kika kasa ganewa kenan ai ko? Dama ance duk abinda babba ya hango yaro ko uban me zai hau bazai taɓa hangowa ba wallahi, ba ya kwana da ita ba dole ki ga abinda yafi haka ai, babu yanda banyi in lalata batun auren nan ya hakura ba amma sam Meemah kika ki bani hadin kai ki ka koma bayan Abdallah, har da bin wasu malamanki da basu taka kara sun karya ba duk don yarinyar ta shigo hannunsa, to ai ta shigo kuma kin ga abinda ya biyo baya daga shigowarta, to wallahi zai kai ya kawo wataran Abdallah yace bai san mu ba akan yarinyar nan, ni na haifesa ba wani ya haifar min shi ba sarai nasan abinda zai iya aikatawa" Meemah ta dinga kallon Momy babu ko kiftawa don ita sai yanxu ta kara fahimtar dalilin Abdul nayi mata irin wannan mugun tijara kan yarinyar da yake ta ikirarin zai koya ma lesson idan ta shigo hannunsa, sarai kuwa ya kwana da ita dole ya birkice haka ya haukace kanta, dama buzaye da aka sani da mugayen asiri, Meemah tayi wani murmushin takaici tace "To kuwa yanda nayi ruwa nayi tsaki har sai da yarinyar nan ta shiga hannunsa to haka zan yi har sai ya rabu da ita a kwanan kuwa ba da jimawa ba" Momy ta kwado ma sabuwar me aikinta kira, matar ta taho a guje har sai da tsantsin tiles ya kwasheta sbda ruwan dake kafarta sai ga ta a kasa timmm, A fusace Momy tace "Wallahi tallahi kika kuskura kika illata min tiles sai na cire cikin kudin albashinki, yau naga er iskar mata kawai, kullum na kiraki sai kin azabtar min da tiles saboda kauyanci? Wannan wace irin mata Adama ta kawo min haka da sunan me aiki?" Har kasa mai aikin ta zube tana ba Momy hakuri, cikin tsawa Momy tace "Miko min wayata dallah ki fita ki bamu waje, er kauyen banza" Mai aikin ta kalli wayar dake kan center table dab da inda Momy ke zaune, ta karasa da sauri ta dau wayar ta mika ma Momy, Momy ta warce, mai aikin ta bar parlon, Momy ta mika ma Meemah wayar tace "Dubo min lambar Godiya, glasses dina yana daki" Meemah ta amshi wayar ta dubo number aminiyar Momy sannan tayi dialing ta mika mata, a kashe suka ji wayar, Momy tace "Tayi tafiya me muhimmanci kenan, bari zuwa anjima in sake kiranta" Meemah da kanta ya gama kullewa tace "Tabddi jam, lallai nayi babban kuskuren da ban taɓa yin irinsa ba Momy, sai ma fa kinga kayan dake jikinta da naje gidan, tana kitchen tana soye soye" Momy dai tayi shiru tana girgiza kafa don bakin ciki da takaici, can tace "Dauko min gyale da jaka a daki, ina zaman zamana kin janyo min kashe kudin da banyi budgeting ba Meemah, duk ke kika ja min wannan masifa da kika ki jin maganata wallahi, in hada iri da matsiyata akan wani dalili? A farko dai na hakura na zuba masa ido da yaki jin maganata, amma yanxu kuwa wallahi sae ya rabu da yarinyar nan, babu dalilin da zai sa in hada zuri'a da ita, ga kuma rashin adalcin da aka yi ma Alhaji ga asara ga biyan tara" Tashi Meemah tayi ta tafi dauko ma Momy gyalenta da handbag, all this while dama ita ke ta shiga malamai don Khaleesat ta shiga hannun Abdul Momy ko bin ta kanta bata yi tunda dama ba son auren take ba, Momy na ficewa daga gidan da driver dinta Meemah ta tafi dakinta da wayarta tayi dialing number Malamin da tasa yayi mata aiki. Runtse ido Khaleesat tayi bayan taji duk maganganun da Abdul yayi, yana rungume da ita saman gadonsa kamar zai maidata jikinsa, it's past 8pm na dare, jin taki cewa komai s hankali yace "Khaleesat" Bude idonta tayi wasu hawaye masu zafi suka silalo fuskarta tace "Um" Yace "Say something" Still tayi shiru hawaye na zuba idonta don bata ma san me zata ce masa ba at this point, ya dago kanta yana kallonta yayi kasa da murya yace "Say something pls" Da kyar muryarta na rawa tace "Ban san me zan ce ba" Yace "Say anything" Shesshekan kuka ta fara yi masa tana jin zafi a zuciyarta, me kuma yake son ta ce masa, tunda yace bazai taɓa rabuwa da ita ba ko me zai faru, meaning dole ko tana so ko bata so haka zata ci gaba da rayuwa da shi a matsayin mijinta, so me yake son ta ce, ta dai dake da kyar har sannan muryarta na rawa tace "Kawai alfarma daya zan nema wajenka" Murya can kasa yace "Say it Khaleesat" Tayi karfin halin cewa "I don't want you to hurt anyone because of me...." Kasa ci gaba tayi tana kuka a hankali, ya dinga kallonta don sarai yasan su wa take nufi, Calmly yace "Ohk u mean ur Body Guards that sue me?" Ita dai kuka kawai take, Ya ɗan yi wani murmushi yace "I don't think i will leave dem cause they started everything first, they intruded in what wasn't der business, basu baki labarin harbin da aka yi ma wani dake da alaka da su ba, I mean Salem..." Khaleesat ta daga kai da sauri ta kallesa hawaye na sauka idonta gabanta na faduwa, lkci daya ta tuna sanda Aunty Farida ke sanar mata Ajay yace mata an harbi wani abokinsu a kano, yana wani murmushi yace "To su ma ana nan ana targeting din su, amma in kince in kyalesu i will do that under 2 condition..." Khaleesat dai kallonsa kawai take ta kasa cewa komai duk jikinta yayi sanyi, yace "The first condition is that.... zaki yi magana ta waya da su ki gaya masu ke za ki zauna da mijin ki they should back off, sannan ki gaya masu su janye karan da suka kai kotu..." Bata san sanda ta fashe da matsanancin kuka ba, ya dinga kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Baza ki yi ba kenan?" Muryarta na rawa tace "Ban ce bazan yi ba" Wayarsa ya dauko ya mika mata yana kallonta, da kyar tace "Bani da number ai" Yace "Amma aunt dinki na da shi ai... Call her and ask her to send you the number" Ta girgiza masa kai tana jin kamar numfashinta zai dauke sbda rikicewan da tayi bayan ya fadi conditions dinsa, cikin kuka tace "Bani da numberta offhand" Yace "Ni ina da shi, i will call her now sai ki gaya mata ta turo maki number daya daga cikinsu, and mind you kada ki kuskura ki ce mata komai, number kawai zaki yi requesting ta turo maki" Ta fashe masa da kuka sosai tace "Why are you doing this plss Ya Abdul" Yace "Ohk, i will revenge and nothing is gonna stop me, i promise you this, shi abokinsu da aka harba ai yayi surviving, i hope they survive too....." Tana kuka sosai tace "No plsss..." Wayar ya dauka yayi dialing number din Aunty Farida yana fara ringing ya mika mata yana kallonta.
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*
_Assalamu Alaikum yan mata da matan Oga ina me maku albishir da cewa Han-Ash skin beauty ta zo maku da kayan gyaran jiki iri iri wanda zai mayar da fatarki kamar Madara ta yanda duk inda kika shiga sai an kalleki, ki sai mayukan da zesa fatar ki tayi kyau, muna kuma maraba da siyan daya ko sari, i am assuring you that duk wani product dinmu is tested and trusted, ga kuma arha, for more information contact Han Ash via +234 803 810 3096_
HALYSAAH 44
Har Aunty Farida ta ɗaga kiran Khaleesat bata amshi wayar da Abdul ke mika mata ba hawaye na zuba idonta, lkci daya ya hade rai yana mata wani irin kallo, babu shiri ta amshi wayar hannunta na rawa, a sanyaye tace "Aunty" Cikin rikicewa Aunty Farida tace "Khaleesat?" Khaleesat ta sauke idonta tayi shiru, hankali tashe Aunty Farida tace "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, Khaleesat kina ji na? Don Allah kiyi magana, Hello Khaleesat" Khaleesat ta kasa ce mata komai hawaye masu zafi na sauka idonta, kiris ya rage ta fashe mata da matsanancin kuka a wannan lokacin, Abdul ya fixge wayar yayi a hannunta ya katse yana mata wani mugun kallon da ya tsorata ta sosai yace "Are you daring me?" ta fashe masa da kukan da take dannewa tana girgiza masa kai, a fusace yace "Ohk then, since abinda kika zabar masu kenan to ina me tabbatar maki zan aikata hakan nan ba da jimawa ba kuwa, sannan bayan nayi zan sanar maki, don bani da imanin kyale duk wani mahalukin da yace zai shiga hurumina, i don't mind sending that person to his early grave, and mind you.... i will so deal with them yanda in their next life baza su kara shisshigi akan abinda bai shafesu ba, if you think i am bragging watch and see, bani da conscience...." Khaleesat ta girgiza masa kai cikin karfin hali tace "Duk ba sai ka masu komai ba, zan yi abinda kace" Wayar ta amsa a hannunsa ta cire a Flight mode din da ya saka sannan ta sake dialing number Aunty Farida, yana fara ringing Aunty Farida ta daga da sauri tace "Khaleesat, kina ji na Khaleesat?? Hello" Khaleesat ta dake ta hadiye sauran kukanta cike da karfin hali tace "Na'am Aunty" Cikin tashin hankali Aunty Farida tace "Kina ina Khaleesat?" A hankali Khaleesat ta daga kai ta kalli Abdul taga ya wani murtuke fuska yana kallonta kamar bai taɓa fara'a ba a rayuwarsa, ta sunkuyar da kanta wasu sabbin hawayen na zubo mata cikin sanyin murya tace "Aunty Number Ahmad za ki turo min yanxu plss" Aunty Farida da duk ta rude tace "Ahmad kuma Khaleesat? Wanene Ahmad? Kina ina ne yanxu?" Shi dai Abdul wani devilish look kawai yake mata, tayi kasa da murya tace "Aunty Number Junaid zaki turo min" Da sauri Aunty Farida tace "To bari in turo maki yanxun nan" Katse kiran Aunty Farida tayi cikin rawan jiki ta tura ma Khaleesat number Ajay, number na shigowa Abdul ya amshe wayar a hannunta yana kallon number for almost 5 seconds, can yayi wani murmushi ya mayar mata da wayar, cike da isa yace "Kirasa ki gaya masa abinda nayi instructing din ki" It took Khaleesat almost 30 seconds kafin ta iya dialing number Ajay, shi ma saboda irin kallon da Abdul ke mata ne, exactly irin kallon da yake mata in zai gaura mata mari, cikin muryarsa dake tsoratata taji yace "Kika kuskura kika yi magana da wata muryar da ba normal voice dinki ba zaki sha mamaki wallahi, and immediately he picks just go straight to ur point, do not give him a breathing space to say anything to you, go straight and tell him kin hakura zaki zauna da mijinki, kin ji me nace maki?" Ita dai bata ce masa komai ba hawayen takaici na zuba idonta, sai da kiran ya kusa katsewa Ajay ya daga, ta ɗan kalli Abdul da bai fasa mata wani irin kallo ba, da kyar ta daure tace "Hello, good evening....." Mikewa Ajay yayi jin muryarta, bata jira ya gama processing ba ta ci gaba a hankali tace "Dama ina son in ce maka ni na hakura zan zauna da mijina, and i appreciate all what you've done for me kai da Yaya Jawwad, thank you so much" Ajay ya juya ya kalli Jay da shigowar sa dakin kenan, as if counting his words yace "Come again!" Yana fadin haka ya saka wayar a handsfree sannan ya nufi Jawwad yana kallonsa, Khaleesat ta kalli Abdul, sai kuma ta sunkuyar da kanta tace "Cewa nayi ni na hakura yanxu, zan zauna da mijina, and thank you for all what you've done for me...." Wasu sabbin hawaye suka hau zarya a fuskarta tana ji kamar ta fashe da kukan dake cin ta, Abdul ya fixge wayar a hannunta ya katse sannan ya kashe wayar gaba daya, Ajay ya kalli Jay that looks speechless and shock at the same time, lkci daya ya jefar da wayarsa saman gado, cikin nutsuwa yace "Nayi da na sanin bata lokacina akan yarinyar nan, i regret wasting my very precious time...." Jay ya ma rasa me zai ce, walking slowly ya karasa gaban window din dakin yana kallon Ajay that was boiling from inside, a hankali yace "Look Ajay, i think those words are not coming from her heart, sakata yayi ta fadi hakan pls mu yi mata uzuri, she is forced to say all what she said, ba mu san situation din da take ciki ba let consider that plss" Ajay ya masa wani kallo yace "Billah na cire hannuna a lamarinta kaji na rantse Jay, i have nothing to do with her case again, after all i was just doing it just for the sake of humanity not because of her, ko kasheta yake ya kamata ta gaya mana haka? Mu zata dauka for granted? Beside she spoke confidently meaning she is okay with what he asked her to say, i am leaving this state first thing tomorrow morning, so unfortunate i waste my time on the brat, don taga mun yi stooping kan mu so low shi yasa ta dauke mu for granted" Yana kai wa nan ya fice daga dakin kamar zai tashi sama, Jay ya lumshe ido ya bude don bai san me zai sake ce masa ba da zai sa ya sauraresa, kuma tunda har ya rantse magana ta kare, ya zare hannunsa kenan babu abinda zai sa ya sake involving kansa, zaunawa yayi gefen gado ya dafe kansa da yaji ya masa nauyi, at the same time letting out a sigh, kalmomin Khaleesat ne suka dinga dawo masa kai, he felt really disappointed in her too, but can kasan zuciyarsa tausayinta ne ya mamayesa ya kuma yi mata uxuri, ya rasa menene yasa shi shiga yanayin da ya shiga a wnn lkcin, da kyar dai daga karshe ya mike ya fita daga dakin yana tafiya a hankali. Daren ranan nan Khaleesat bata yi baccin awa biyu ba cikakke, da bacci barawo ya saceta zata farka a firgice, bata taɓa jin abu ya tsaya mata a rai irin abinda Abdul ya sa tayi ma su Housemate dinta ya tsaya mata ba, gashi ko digon hawaye yaki fita idonta, her heart is just heavy, but did she have a choice? In bata yi hakan ba yayi ma su Housemate dinta wani mugun abu ai bazata taɓa yafe ma kanta ba, tunda har yake ikirarin ba shi da imani babu abinda bazai iya aikatawa ba, tasan kuma sarai zai iya aikatawa din, tunanin sabuwar rayuwar da take kokarin fadawa take, is she going to survive this at all? Is this not going to be her end? A ranta taji kilan lokacin mutuwarta ne ke tinkarota,