Showing 240001 words to 243000 words out of 257722 words

Chapter 81 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

wannan zuwan naku ba kuma" Hajiya Fatima tace "Gaskiya ba lafiya ya kawo mu ba tsohuwa, duk da zuwa muka yi cikin lumana ba tare da wani tashin hankali ba" Nenne ta ɗaga kai ta kalleta baki bude, cikin nutsuwa Mami ta fara magana tace "Ni ce Mahaifiyar Jawwad, kuma Jawwad shi kadai Allah ya bani a duniya, a burikan da nake da shi kan Jawwad a duniya babu auren bazawara ciki, ko kuma auren wata kabila can baya ga cikakkiyar Hausa Fulani, tun daga neman auren da aka zo aka yi na ɗa na har saka rana bani da masaniya akan ko daya, sannan duk wani bautatawa da kashe uban dukiya da Jawwad ya dinga yi akan er ku da ma ku kanku babu wanda ban sani ba, amma duk ba wannan ne damuwata ba, kuma bazan ce zan amshi duk wani abu na alkhairi da yayi maku ba, kamar yanda nace maku mun zo cikin aminci ne babu tashin tashina, don haka tun da girma da arziki ku cire ran auren er ku da ɗa na Jawwad idan ba haka ba wallahi duk wani mummunan matakin da na dauka a kanku ku kuka siya, er ku ba sa'ar auren Jawwad bace don shi din ɗan gidan sarauta ne, ɗan sarki jikan sarki babu abinda zai yi da er ku bazawara, kai ko da ba bazawara bace wallahi babu abinda zai yi da wata kabila warce ba ma na kasar nan ba, ina sake jaddada maku tun da girma da arziki ku janye batun auren er ku da ɗa na...." Cousin sister din Aunty me suna Aunty Nafisa tace "Iya tatsarsa da ku ka dinga yi ma ya isa haka, don hidimar da yayi maku in muka ce yafi na miliyan dari biyu tsaf bamu yi karya ba, da ace tsiya ya kawo mu hatta gidan nan wallahi sai mun kwace amma mun zo maku cikin lumana don mu din ba kananun mutane bane kuma mun fi karfin dukiyar da Jawwad ya kashe maku, kawai abinda za ku yi a zauna lafiya shi ne ku janye batun auren nan cikin ruwan sanyi tun kan tijara ya biyo baya" Har sannan Nenne ta kasa rufe bakin da ta hangame zaune kan Carpet with shock, Aunty Farida tayi wani murmushi tana kallonsu daya bayan daya tace "Mu janye batun aure sai kace mu muka je neman auren Jawwad din? Ina ce wa enda suka zo neman aure su za su dawo su janye sannan su amshi kudin da suka kawo, kuma ni a iya sanina ba mata bane suka zo neman auren Khaleesat, mazan nan dai da suka zo neman auren su nake tunanin za su sake dawowa su ce sun janye a maido masu da kudin ɗan su, ko kuma mafi sauki in kin isa da ɗan ki ai tun daga gida zaki masa umarnin ya janye ba sai kin zo mana nan ba, a yanxu mu dai bamu da sauran magana da ku sai dai iyayenmu maza su saurari wakilan Mai martaba, duk da dai ban san ko gidan sarautar taku har dankwali da dankwali na zama batun neman aure ba" A tare Hajiya Fatima da Hajiya Nafisah suka mike suka daka mata wani tsawa suna nunata da ɗan yatsa, Hajiya Nafisah tace "Ke karamar er iska mu kike gaya ma magana? Kin san su waye mu? Who the hell do u think you are?" Aunty Farida ta ja wani dogon tsaki ta juya ta bar parlon alamar bata da lokacin ci gaba da basu amsa, Cikin azama Aunty Nafisa ta bi ta a fusace, Mami tayi saurin dakatar da ita tace "Dawo Nafisah, dawo, kyaleta kawai" Umma dake hawaye ta dinga basu hakuri a rikice tana cewa "In sha Allahu duk bazai kai ga haka ba, in dai ta bangaren mu ne babu batun wannan auren da izinin Allah, mu mun janye ba wannan batun in sha Allah, don Allah ku yi hakuri" Mikewa Mami tayi tana kallon Umma cikin nutsuwa tace "Da ya fi maku, don in baku janye cikin lumana ba za ku janye saboda tashin hankali, bana hada ɗa na da kowa, kuma ba don ko wace irin mace na haifo ma ɗa na a duniya ba, in ma wani abu ku ka yi ma Jawwad irin naku na yan kabilar ku to tun wuri ku warwaresa tunda kun tatsi arziki son ranku daga jikinsa har da siya maku gida, to duk nafi karfin abinda yayi maku bazan kuma ce zan amshe ba, kawai dai ina me maku gargadi da babban murya ku raba kanku da ɗa na, ku nisanta er ku daga ɗa na" Mami na kai wa nan ta nufi kofa, sauran matan suka bi bayanta suna yatsine yatsine, rabon Nenne da shiga irin wannan shock din tun da Motar yan sanda suka zo tafiya da Malam Ali farkon case dinsa da Baban Abdul, Umma ta zauna kan kujera ta dafe kanta ta dinga kuka, Mama Shatu dake makale bakin kofar dakinta sai zazzare ido take taki karasowa cikin parlon, Sai a sannan Nenne ta samu bakin sakin salati ta rushe da matsanancin kuka kamar warce aka aiko ma da mutuwa, Duk wannan abun da aka yi Malam Ali dake zaune Balcony yana ji, har su Mami suka fito basu ce masa komai ba suka nufi gate. Sai bayan Magrib Aunty Farida ta samu Ajay a waya, he was shock an speechless bayan ta sanar masa abinda ya faru don sai da ya mike tsaye daga zaunen da yake, gaba daya ya ma rasa me zai ce, after some seconds ya dake yace "Zan kira ki Aunty" Yana katse wayar ya fita zuwa bangaren Mai martaba, Sarki ya fi minti biyar bai ce komai ba bayan Ajay ya sanar masa abinda Aunty Farida ta gaya masa, kana ganinsa kasan ransa ya baci sosai, after another 2 minutes ya numfasa cikin nutsuwa yace "Dau waya ka saka min Number Mahaifin yarinyar" A hankali Ajay yace "Bani da numbersa ranka shi dade" Mai martaba yace "Sa min Number Faridan" Mikewa Ajay yayi ya dau wayar Mai martaba ya saka masa number Aunty Farida sannan ya mika masa, Mai martaba ya amshi wayar yace "Wannan karan zan yi maganin Aseeyah, i have tolerated her for so long for the sake of my late brother, amma zan nuna mata na fi ta iko da Ahmad, kuma juma'an nan mai zuwa in sha Allahu za a daura auren nan" Murya can kasa Ajay ya fara basa hakuri don har ya mance rabon yaga bacin ran Abbansa haka, Mai martaba ya mike yana rike da wayarsa ya shiga dakinsa, ashe duk wannan abun Aunty na tsaye bakin kofa tun da taga Ajay ya taho parlon Abban nasa ta biyosa ta tsaya bakin kofar duk tana sauraron su, mikewa Ajay yayi zai fita yaga Aunty tsaye bakin kofar tana masa wani matsiyacin kallo, sauke idonsa yayi ya canza wata hanyar don kofa biyu ne a parlon.



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*

07087865788

HALYSAAH 96


Aunty farina na zaune tsakar gida da umma da malam Ali,umma dai tayi tagumi ko bakin magana bata dashi idanuwanta duk sun kumbura saboda kuka,Aunty farida sai jira take malam Ali yace masu ga yanda sukayi da maimartaba a waya amma yaki cewa komi,Nenne ta fito daga cikin gida tana rike da wayar aunty farida Don har ita sai da maimartaba yayi magana da ita,Nenne tace," inba adalin sarki ba waye zaiyi haka sai kunga yanda ya ajiye izza da girman kai irin ta sarakuna yana ban hakuri,har saida kunya ta kamani wallahi,yana bani hakuri ina basa hakuri,to ni ai inba shegiya bace ai dole In hakura,Amma zance na gaskiya na tsorata da lamarin uwar Ahamad,taban tsoro sosai banga alamar akwai abun arziki a tattare da itaba,naji kuma ina tsoron auren nan,ace khaleesat tayi auren farko bataji dadi ba nabiyu ma yazo mata a haka? Kunga ai bazamu bari ayi na biyu ba yarinya da karancin shekarunta tayi ta walagigi gidan aure har sai wani cutar yaje ya sameta,gaskiya nidai nasha jinin jikina gaskiya da auren nan gara kawai duk a hakura dan babu alamar alkhairi a cikinsa,tunda har uwar sa ta nuna bata sonta bazata taba sontaba har abada kuwa, sannan fa duk a yau mukejin ashe ba ita daya ma ashe zai aura ba,harda yar uwarsa budurwa itama jinin sarauta kuma duk a rana daya za a daura auren,Ina khaleesah ina kishi da jinin sarauta inba dai hallaka akeson jefa yarinyar ba ga uwar miji tun baayi auren ba ta nuna bata sonta gaskiya jikina ya mutu,akan abun duniya bazamu sake salwantar da rayuwar er mu ba" Cikin sanyin murya umma tace" Damani auren ya fice man arai gaba daya Nenne,Hakura zatayi Allah ya fiddo mata da wani mijin kawai Don babu Alkhairi a wannan auren dama aikowa tayi akazo da sauki akan ta tako da kanta tazo gidannan tayi abinda tayi gwara a hakura kawai.....Nenne ta katseta da sauri tace"Ai bazamu bari wannan ya fito daga bangaren mu ba Zahara'u duba da yanda sarki duk yabimu yayi mana magana ta waya, in bama shi dinba wane sarkin ne zaiyi haka? Ai iyaka saidai yasa na kusa dashi su kiramu su bamu hakuri a gantale Amma badai yayi waya damu muji muryarsa ba,Ki duba lokacin daya dauka yana waya da farida,Sannan yayi waya da malam Ali ma,nima kuma yayi magana dani duk yana kokarin sanyaya mana zuciya akan tijarar da er iskar mata tazo har gida ta mana,kinga ko Don wannan bazamu yarda ace daga wujen mu mukace mun fasa bada yarinya ba,nasan kuma wannan matar er bariki ba hakura zatayi ba gwara ace ita ta ruguza zancen Auren da kanta da dai ace mu muka ruguza,Sam Ahamad baiyi dacen uwa ba gashi yaro mai hankali da nutsuwa ga kirki amma uwa er duniya,mu bazamuce komai ba Albarkacin mai martaba saidai in su suka ce sun janye batun auren shikenan yazo ma kowa gidan sauki ,Aunty farida ta sauke ajiyar zuciya tace"hakane Nenne" Nenne tace Atoh,kai meye shawararka malam Ali?Ana magana sai kayi shiru kamar wani bare a cikin mu,sai a sannan malam Ali ya daka kai a karo na farko yace" Shawara ta shine zuwa gobe ko jibi mu tattara mu koma mariri tunda har an kusan gama gyaran da akeyi gidana baaba,idan mun koma to koma me zai biyo baya me sauki ne..... A mugun fusace Nenne tace "Toka tattara ka koma mana Ali wani ya rike ka ne? Mudai muna nan babu inda zamuje tunda bamu bude baki mun roki yaron nan ya siya mana gida ba,kuma takardun gida na hannun mu balle ace zaa kwace gidan,ko kuma mu siyar da gidan mu tashi mu koma wani wajen mu siya ba shikenan ba,Amma wallahi babu shegen daya isa ya rabamu da gidannan,ko shi Ahamad din bazai fara tunkarar mu da zancen gida ba tunda saboda Allah yayi kuma jinin marigayi sarki Ahmadu na yawo a jikinsa,mahaifinsa kuwa kowa ya shaida mutumin arziki ne "Nenne na kaiwa nan ta Mike rai bace tana kallon Aunty farida tace" Taso mu shiga ciki muyi shawara parida " Ali da matarsa in kace zaka zauna cikinsu kayi maganar Arziki ranka ne kawai zai baci a banza,ban taba ganin sumbudaddu matsorata irin su ba "washegari har gida maimartaba ya tura akaje ba malam Ali hakuri akan abinda mami taje tayi,Shidai malam Ali Allah ya sani he is not longer comfortable with his daughter getting married to the royal family, Sam hankalinsa bai kwanta da auren ba amma nauyin me martaba yasa ya kasa nuna hakan,gashi wanda sukazo basa hakurin sunce ranar jumaar nan zaa daura auren,shi kansa me martaba ya sanar masa da hakan a maganar da sukayi jiya,gaba daya ya rasa ta inda zai bullo ma lamarin gashi yasan nenne bazata taba tsayawa ta fahimcesa ba balle suyi abinda ya kamata dan ceto rayuwar Khaleesat,baya fatan abinda ya samu ersa a baya ya sake samun ta yanzu,bayan wakilan me martaba sun bar gidan wajen karfe takwas da rabi na dare ya dau wayarsa ya zauna tsakar gida yayi dialing number khaleesat,yana fara ringing khaleesat dake shafe shafe bayan tayi wanka ta daga Kiran,bayan ta gaishesa ya amsa yace "yaushe zaki dawo jiddah"?a hankali khaleesat tace Nenne tace kada su bari in dawo yanxu amma ni ina son ranar Friday indawo ,malam Ali ya danyi shiru sai kuma yace"kina jina jiddah?tace inaji baba,yace farida sun fada maki abinda ke faruwa kuwa?Sosai khaleesat taji gabanta ya fadi ,ta ajiye kwalbar turaren hannunta tayi shiru ta kasa cewa komai,Har saida babanta yace "hello ta kifta ido cike da karfin hali tace "inaji baba,baa gaya min komi ba meke faruwa baba,?Cikin nutsuwa malam Ali ya fara sanar mata duk abinda mahaifiyar Jay tazo har gida tayi,babu abinda yayi mata excluding,daga karshe ya sauke ajiyar zuciya yace you know why I decided to call and inform you about this jiddah?Saboda nasan Nenne zatace kar a sanar maki,Ni kuma abinda yasa nike gaya maki ina son kiyi deciding duk abinda kikaga ya dace da rayuwar ki tunda ba wani zai maki zaman auren dashi ba jiddah,quite alright I knew Ahmad is a good man but come to think of the life you may find your self in with his mother as your in-law,Ni ina jin nauyin sarki ina matukar jin nauyin Ince bazan bada auren kiba beside har gida ya aiko aka ban hakuri akan abinda ya faru bayan Kiran da yayi min ta waya ,bazan iya ja in ja da me martaba ba jiddah amma ina jiye maki wannan auren,hankalina bai nutsu da auren ba bana son abinda ya faru dake a baya ya sake maimaita kansa saboda muna jin nauyin kwatar maki yancinki for the second time kamar wancan lokacin,sarki ba mutumin da zaa tsaya ayi ja in ja dashi bane Don girma da martabarshi ya wuce ayi masa haka koda kuwa bai turo wakilansa ba iya ta waya kawai mukayi magana,balle bayan munyi magana ta waya still ya sake aikowa har gida a bamu hakuri .....tunda ya fara magana khaleesat ke kallon kofar dakin aunty murja babu ko kiftawa dan mutuwar zaune rayi kawai a inda take,sosai maganganun babanta sukayi mugun girgizata taji wani sanyi na shigarta wannan shine dalilin da yasa taketa Kiran housemate baya picking call dinta tun jiya kenan,har take tunanin ko wani laifin tayi masa bata sani ba,daga karshe taji muryar babanta yace hope kin fahimceni jiddah?da kyar ta nemo muryarta dako fitowa sosai bayayi tace "Toh bana,yace kiyi abinda kikaga ya dace for your betterment dear,I want nothing but the best for you,nobody is in the rightful position to decide for you for the second time daughter "kai ta gyada mashi cike da karfin hali har ya katse wayar,sannan taji wasu hawaye masu zafi sun zubo idonta,whatsapp dinta ta bude ta shiga DM din Jay cikin minti daya ta gama rubuta masa abinda zata rubuta hannunta na rawa tayi sending,sannan ta kashe data ta kwanta hawaye masu zafi wasu na bin wasu a kuncinta, ji tayi kamar komi na duniyar sun tsaya mata cak tsabar confussion ,ko minti biyu baayi ba saiga kiranshi ya shigo wayarta,silencing Kiran tayi bata daga ba sau uku yana kiranta bata picking ba daga karshe tayi switch off din wayar gaba daya tana sheshshekar kuka tana jin zuciyarta na mata zafi,karfe goma da rabi na dare aunty murja ta gama shimfide yaranta da sukayi bacci tun dazu,ta tafi ta dauro Alwala ta dawo dakinta ta kashe fitila zata kwanta saiga wani Almajiri yana sallama bakin kofar dakinta tace waye? Yace wai Ana sallama da halysah a waje,aunty murja tace khaleesat da daddaren nan? Wai inji wa? Almajirin yace a mota yake,Duk khaleesat najin aunty murja da Almajirin amma ko motsi batayi ba,Aunty murja ta dau hijab tasa ta fita Don ganin wanda ke Kiran khaleesat a wannan lokacin bayan minti uku sai gata ta dawo dakin tana tashin khaleesat ,tace khaleesat tashi Ahmad na jiranki a waje,meyasa bakice masa yazo da wuri ba yanzu ai dare yayi khaleesat taki juyowa tace, na Riga nayi bacci ace nayi bacci,Anty murja tace haka nan zaki daure ki fita amma karki dade ,kar babansu ya dawo ya tarar dake a waje kije yace sako ya kawo maki,khaleesat taki tashi aunty murja tafi minti biyar tana fama da ita amma fir taki tashi,har saida kishiyar Aunty murja ta leko dakin tasa baki Don tana jinsu,khaleesat ta tashi zaune da kyar ta sunkuyar da kanta Don bata son suga idonta da yayi ja saboda kuka,banda tanajin nauyin kishiyar Aunty murja da babu abinda zai sa ta tashi harta fita kofar gida,hijab dinta ta saka har kasa akan kayan baccin jikinta Aunty murja na mika mata torchlight taki amsa ta fita daga dakin kanta a kasa ta isa kofar gidan ta tsaya daga jikin motar tana jinsa ya bude motar ya sauka sannan ya zagayo inda take tsaye yana kallonta ita dai wani wajen daban take kallo sai kuma ya bude mata back seat pleadingly yace pls ki shiga Halysah ita dai taki ce masa komi kuma taki kallonsa lallabata ya shigayi yana hadata da Allah ta shiga motar yafi minti biyar yana Abu daya ita dai taki cewa komai hawaye na sauka a idonta ganin anata wucewa Ana kallonsu yasa kawai ta shiga motar ya kulle sannan ya zagaya ya shiga ta dayan side din motar ya ajiye wayarsa ya matsa kusa da ita yana kallonta cike da damuwa yace why will you send me such txt halysah?da wanne kikeson inji pls? Meyasa zaki man irin wannan message din? Ta sauke idonta tana jin wasu hawayen na zubo mata kasa daurewa tayi kawai ta fashe da kuka sosai nan da nan ya kara rikice mata yace stop this pls halysah why are you doing this to me? Kuka kawai take taki ce masa komai taji ya jawota

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login