Showing 207001 words to 210000 words out of 257722 words
Chapter 70 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar
ba, tana ta tsoron kar ya samu labarin ta dawo ma, Nenne tace "Sabili da haka cikin dubara a kira makota duk a basu sadakar abubuwan da baza mu koma sabon gidan da shi ba, irinsu rubabbun tukwanen ku da katifa da tarkacen kwanukan ku, don babu abinda yaron bai zuba mana a gidan ba har kujeru da kayan gado, sannan na aika aje kasuwa a kira min Ali yayi maza ya dawo babu lafiya, so nake ya dawo mu ji yanda zai yi da matansa don baza su bi mu gidan nan ba gaskiya, in ma kauye zai maida su ya dinga zuwa can duk sati yana duba su to" Daga Mama Zubaida har Mama Shatu suka juya suna kallon Nenne, Nenne tace "Don ban ga inda za a kunna icce ko kuma a dafa abincin talla a wannan tanfatsetsen gidan da yaron nan ya siya mana ba, ko ina tas ne malale a kasa, komai sabo dal" Umma dake ta kallon Nenne tace "Ki dai yi hakuri Nenne don da mu da su Shatu duk daya muke a wajen Malam, dakuna shidda ne a gidan banda gini daban me daki daya da parlor da bandaki da kitchen, duk zai ishe mu Nenne" Nenne tace "Ke in baki da hankali ni ina da shi Zahra'u, banda karamin tunani irin naki kinga gidan yayi kalan Shatu da Zubaida? Kinga alamar kazanta zata samu muhalli a wannan tanfatsetsen gidan kamar a kasar waje?Na kirga dakuna biyar a gidan da katon parlor sal wawakeken kitchen, sannan har da bangaren me gida duk a cikin gidan, shima naga parlor ne sai daki da bandaki, to wannan na Ali ne, ke kuma ki dau daki daya, Farida daki daya, Khaleesah daki daya, yan biyunki ma a basu daki daya, daki daya da ya rage ya zama na saukan baki, ginin dake waje dama nace nawa ne ni zan zauna ciki kada wanda ya saka ma ginin ido, to a ina kika ga dakunan da za a zuba su Zubaida da 'ya yansu rakacaa idan ba dai baki de nankali ba? Ai babu guri a gidan, kai ko da wurin ma ni sam bazan amince in zauna da su Shatu ba sai dai ni in hakura da tarewa a gidan inyi zamana a Mariri har wa'adin da Allah ya dibar min a duniya ya cika in koma garesa, in kuma ance lallal lallai sai sun bi mu ta sai dai Malam Ali ya siyar da wnn gidan da nawa ya tafi unguwan yaku bayi ya siya masu gida me dakuna uku ya ajiye su da 'ya yan su, amma wannan gida kam ta silan Khaleesah aka siyesa ba wani shege ba, yau in tace níma bazan shiga ba ya zauna balle wasu yan iska Zubaida da Shatu, da ma suna ganin mutuncin mijinsu ne balle ni, balle ke karan kada miya da suka rena, yau watanni kusan hudu kenan babu abinda Ali ya rage su da shi a gidan nan, tun da Allah ya saka ma hatsin da ya fara siyarwa a kasuwa albarka bai ragi iyalinsa da komai ba komai korrai yi masu yake, amma sun ki dena abincin siyarwa don su yi ta ja masa zagi a gari, kudin makarantan yara idan ya basu sai su bi su kwace su bar yaran suyi ta yawo kamar almajirai a unguwa suna talla, to ina amfanin matan nan? Shi dai wannan yaro da ya basa jari Allah yayi masa albarka..." Nenne te kalli Khaleesat tace "Ya sunan abokin Ahamad din nan mara fara'a?" Khaleesat ta daga ido ta kalli Nenne, Umma dai tayi shiru don bata san me zata ce ba kuma, Aunty Farida ma dai is speechless, Nenne ta mike tsaye tace "Duk ki fito da tarkacen ki Zahra'u a bada su sadaka, in sha Allahu baza mu kwana a gidan nan ba, gwara mu koma gida me get yanda sai an kwankwasa ma za mu bude, shi kuma Ali ya dawo yasan yanda zai yi da matan nan nasa, bari inje in fara harhada nawa kayan, ina nan dawowa nan ba da dagowa ba, ni dama ba shirgi ne da ni ba, ai 'ya mace abar alfahari ce in dai ka tsaya kayi mata tarbiyya yanda ya dace, da Khaleesat bata da tarblyya uban wa zai kalleta balle har ayi mana wannan abun arzikin ta dalilinta, wannan kadai ya ishi yan baya izini, in za su tsaya su tarbiyyantar da 'ya yansu su zama na kwarai to su za su ci riba ba wani ba" Nenne na kai wa nan ta kalli Aunty Farida tace "Dauko gyalenki mu tafi ki tayani parida, in akwal abinda zan bayar kawai aiken ki zanyi kiyi sallama gida ki kira matar gidan ku taho tare, cikin sirri nake son ayi komai" Daga haka ta fice daga gidan, Aunty Farida ta mike ta dauko Hijab dinta ta bi bayanta ta fita, Bayan yan mintuna Mama Zubaida ta mike ta tafi ta bude kofar gidan tana leka waje taga Nenne da Aunty Farida har sun sha kwanan gidanta, dawowa tayi tsakar idanta, gidan tana ma Umma matsiyacin kallo tace ""Aikin banza, aikin hofi, kurı zauna kun tsara kayan ku shine kike son ki mayar da mu yan iska ke ga er slyasa, bayan duk kin san da tsarin, kin ga wannan sabon gidan In anyi duniya don manzon Allah sai ya zame maku bala'l da fitinar da yafi karfin ku, sai kun gwammace ba a baku ba, kuma waye bai san me Khaleesah tayi aka bata gidan ba? Mu duk bamu yi mamaki ba don mun san ba yanxu ta fara karuwanci ba, kuma muna nan dake sai ta jajibo maku abun kunyan da har ku mutu bazai goge ba daga ke har Nennen, bakin cikin abun kunyan ne kuma zai kar ki har lahira" Umma ta mike tana murmushi tace "Ni dai kullum ina maku tuni da ku koma islamiyya ko za ku samu saukin jahilcin nan, in sha Allahu kuma ni da zuri'ata babu abinda za mu gani sai alkhairi, Allah ya baku lafiyan cutar hassadan dake neman nakasa maku zuciya..." Mikewa Shatu tayi, Umma bata sake bi ta kansu ba ta shige dakinta, Khaleesat dai murmushi kawai take ta mike ta wuce daki ita ma, hayaniya Mama Zubaida da Mama Shatu suka dinga yi a gidan suna batanci da fadin mugaven kalamai har sal da makota suka shigo bada hakuri, ita dai Umma tuni ta sake labulen dakinta tayi kamar bata san da ita suke ba. Bayan la'asar Nenne ta dawo gidan da Aunty Farida, sai ga sha'awa da wasu makotansu Umma su uku sun shigo gidan su ma, duk Nenne ce tasa Aunty Farida ta shiga gidajen su ta kirasu, Nenne na tsaye har Umma ta gama fiddo duk kayan da zata bada, Nenne ta dau zannuwan gado biyu ta wurga ma Sha'awa da wata tukunyar Umma, haka ta dinga rarraba kayan tsakanin makotan da tasa aka kira mata suna girmamata awa enda ke ganin mtuncinta suna girmamata a unguwan, bayan sun kare ta mike tace "Toh gasu nan saboda Allah, shirgi ne suka mata yawa take bayarwa..." Su Mama Zubaida dai na tsaye bakin kofar dakin su fuskokinsu a murtuke suna kallon ikon Allah, Nenne ta sallami makotan duk suka fita gidan suna godiya kaca kaca, sal kuma ta kalli Umma tace "Kin gama hade kayayyakin naku na sa wa dake da yaran ki? Har fa mun je mun samo motar da zata kwashe mu anjima, karfe sha daya da rabi na dare muka yi da me motar" Umma tace "To Allah ya kai mu" Malam Ali ne ya shigo gidan da sallama, Nenne tace "Yauwa Ali, mu dai anjima za mu bar gidan nan kamar yanda na gaya maka jiya, yanxu ya za kayi da shirga shirgan matan nan naka? Kauye zaka tura su zuwa sanda zaka samar masu gidan haya ne ko ya zaka yi da su? Don babu wanda zai saura gidan nan balle Awdul ya samu kishin kishin din inda muka koma" Malam Ali dake kallon Nenne yace "Kauye kuma Baaba, kin fa ce min dakuna bakwal ne a can gidan" Mama Zubaida ta gyada kai tana girgiza kafa alamar atoh dai, Nenne ta saki baki tana kallonsa, can tace "Sai aka yi yaya da nace maka dakuna bakwal ne Ali?" Malam Ali yace "Kawai ayi hakuri duk a koma can din tunda kince a bar unguwan, don ni gaskiya yanxu bani da isasshen kudin kama haya Baaba" Umma ta kalli Malam Ali tace "To kuwa sai kasan yanda zaka yi da su Malam, don wallahi babu warce zata bi mu gidan nan, in ko kace sai sun bi mu sai dai duk a fasa shiga" Nenne tayi wani dariyar keta har da kyakyatawa sannan ta ja kujera ta zauna tana kallon Umma da mugun mamaki kamar ranan ta fara ganinta, Aunty Farida kanta kallon Umma take da mamaki, Balle Malam All da yayi shiruu shi ma yana kaitonta ya kasa cewa komal, Nenne ta sauke wani ajiyar zuciya tace "Allah ya mak albarka Zahra'u, in ya ga dama ya basu kudi ko wacce ta kama hanyar kauye, duk sanda Aliah ya hore masa sal ya nema masu hayan a birni" Malam Ali yace "Toh Shikenan, sai ayi hakan kawai" Mama Shatu ta fashe da kuka tace "Amma ka cucemu ka ci amanar mu Malam, wallahi sai Allah ya mana sakayya" Mama Zubaida ma ta fashe da kuka tace "Kuma kar ka manta hukuncin wanda baya adalci cikin iyalansa, wato ka fifita Zahra'u da 'ya yanta a kan mu kenan kake nufi, alhalin duk matsayinmu daya a wajenka tunda mu ma matan ka ne, kaji tsoron Allah Malam" Nenne tace "Ji bakaken jahilai, Alin ne ya siya gidan ko kurra shi ya zuba kayan cikin gidan da ya maku rashin adalci? Gida al na Khaleesah ne da uwarta kuma yanda suka ce haka za ayi, ko Ali bashi da ta cewa tunda babu biyar dinsa a gidan, balle ni uwarsa, don ma ku ji in gaya maku" Malam Ali dai ya nufi kofa ya fita daga compound din, Aunty Farida tayi murmushi ta koma ta zauna, har sannan Umma bata gaya mata abinda su Mama Shatu suka mata ba shi yasa ma tayi mamaki da action din Umma.... A daren ranan Malam Ali ya ba su Mama Zubaida da Mama Shatu kudin motan zuwa kauye da tulin 'ya yansu, gidan mahaifinsa na can kauyen har yanxu sai dai ginin kasa ne me dakuna hudu kuma babu kowa cikin gidan, sun ci kuka har sun gode Allah, karfe sha daya na dare motar da Nenne da Aunty Farida suka tafi suka yo haya can cikin gari ya iso kofar gidan, aka kwashe su gaba daya sai sabon gida, babban bakin cikin su Mama Zubaida basu san Inda su Khaleesah za su koma ba balle su yada a Mariri kowa ma yasan inda suka koma. Jay na zaune parlon Maminsa yayi nisa tunanin da yake, a karo na farko a rayuwarsa kenan da yaji sa kamar ba a parlon Maminsa ba don gaba daya he is not comfortable ya kasa sakewa, tunani iri iri ne ke yawo a zuciyarsa, tun jiya da ya iso Bauchi kawai gashi nan ne gashi nan dai, lokaci lokaci yake kallon Ajay dake zaune gefensa comfortably yana danna wayarsa, Ajay har ya mance rabon da ya shigo bangaren Mamin Jay a masarautan, duk da bata fiye zama ba sai tayi wata biyu ma bata gidan, Mami ta fito parlon daga Bedroom dinta don tana waya Jay ya shigo dakin sai kuma ya koma parlor shiru shiru kuma bata ga ya sake shigowa dakin ba bayan ta gama waya, dama yace mata da maganar da za su yi daxu saboda hakan ne ma bata fita ba don akwai inda zata, sai bayan da ta fito ne taga ashe shi da Ajay ne, Ajay ya ajiye wayarsa va gaisheta ba tare da ya kalleta ba, kallo daya tayi masa ta amsa sannan ta zauna tana kallon Jay tace "Ina ta jiran ka tun daxu Jawwad, yanxu in tafi inda zan je kenan sai na dawo kawai?" Jay ya daga kai ya kalleta yace "Ai yanxu za mu yi maganar da nace Mami" Marni ta kalli Ajay, sai kuma ta kallesa tace "Yanxu? Ka dai bari da daddare don fita zan yi yanxu gaskiya" Ta fadi hakan ne don bata ga dalilin da zai ce zai mata magana duk da bata san ko na menene ba kuma ya shigo mata da Ajay, tana bakin cikin yanda sam Jay bashi da sirrin kansa kamar tare aka haifosu duniya da Ajay, Ajayn da babu wanda ke sanin komai game da tasa rayuwar, bata jira cewar Jay ba ta mike ta wuce dakinta zata dauko mayafi, kafin ta fito har Ajay ya bar parlon, Jay ya bi sa da kallo, har cikin ransa baya jin dadin yanda Mami ta dauki Ajay, he felt really heartbroken, mikewa yayi kawai ya bi bayansa....
*Pls masu taya ni posting pages din Arewa da suke mayarwa typing ta nan WhatsApp kafin inyi posting su yi hakuri su daina saboda ina yin advert a pages din, be patient idan nayi update sai ku watsa duk inda ku ke son watsawa amma don Allah ku dena posting before I do because of people's advert that I have on ground, although naga pages daya kuke posting din amma dai kuyi hakuri ku dena, thanks...*
https://chat.whatsapp.com/DtKRIBCkfHoGuMzWcuq87V?mode=ac_t
HALYSAAH 86
Khaleesat bata yi zaton gidan da Jay ya siya ma iyayenta yafi yanda ta tsammacesa a hoto ba, she was totally speechless don gida ne lafiyayye kuma a unguwa me kyau sosai, babu abinda ba a zuba a cikin gidan ba, ga wuta da ruwa 24/7 don Solar ne a gidan, maimakon tayi farin ciki sai ta zamto so emotional tana kara jin Jay a ranta, tasan a yanxu dai bata da enough words da zata yi amfani da su wajen fara yi masa godiya tayi expressing how grateful she is, balle ko zata yi hakan ma bazai saurareta ba, Nenne kam baki yaki rufuwa don farin ciki tasa masa albarka tare da iyayensa yafi cikin Kwando, Chalet din da ta mayar nata tsabar murna bata kwana ciki ba, a main building din gidan ta kwana a parlor kan lallausan bargo da sabon Pillow ga AC da ta sa aka kure mata, ai ko da asuba ta tashi hanci duk sun toshe, sai ta ɓige da cewa yawace yawacen da suka yi jiya cikin gari da Farida ne ƙuran garin Kano ya saka mata mura, gari na wayewa Nenne aka dinga goge goge da share share a parlon duk da babu ko digon datti, Aunty Farida da Khaleesat kuma na kitchen suna girka breakfast don sun taho da few food stuffs dinsu na can gidan, Umma ta fito parlor zata amshi wayar Aunty Farida ta kira Malam Ali don nata babu kati, Nenne ta matse tsumman hannunta da take goge tsadaddun kujerun parlorn da shi tace "Kinga dai Ali da ya dawo nan ya kwana cikin ni'imar Ubangiji gwara ya kwana a takure cikin zafi da sauron Mariri, ko da yake ban ga laifin sa ba kinga dole zai yi ma su Zubaida rakiya zuwa tasha kuma zai ɗan hada masu hatsin da za su tafi da shi tunda su ma suna da hakki gwara ya sallamesu cikin mutumci su tafi" Ita dai Umma bata ce komai ba, Nenne tayi kwafa tana ci gaba da goge gogenta tace "Dama ai ance mahakurci mawadaci, yanxu da kika yi hakuri Zahra'u baki ga ribar hakuri ba? Ni nasan Allah bazai bar ki haka ba don hakurin ki abun dubawa ne, gashi yau dai kin ga riban hakurin ki, ni dai kullum addu'ata shine Allah Ubangiji ya albarkaci 'ya yan da kika haifa ya tsare maki gabansu da bayansu, gashi wai tun Khaleesah bata fara aiki ba mun fara cin moriyarta saboda kyawawan halayyan uwarta da irin tarbiyyar da aka mata, cikin ruwan sanyi kuma Allah ya rabaki da matsiyatan kishiyoyin ki lafiya duk tuggun da suka maki ya kare kansu, ke kika ci riba" Umma dai ta ɗan yi murmushi bata ce komai ba, amma da Nenne tasan action dinta na ƙin amincewa a taho da su Mama Zubaida jiya har baccin kirki sai da ya hanata da bata ce haka ba, gaba daya rasa sukuni tayi tana jin bata kyauta ma kanta ba tunda ita ma bata san Allah zai bada gidan nan ba, sannan ba dubaranta ko wayonta bane yasa Allah yayi mata hakan, yanxun ma wayar Aunty Farida da zata amsa Malam Ali take son kira tayi masa magana ko zai samu ya lallaba Nenne tayi hakuri su dawo gidan kawai, gudun tsine mata da Nenne zata yi yasa bata gaya mata abinda ke ranta ba kawai ta nufi kitchen ta tambayi Aunty Farida inda wayarta yake, bayan Aunty Farida ta gaya mata ta juya ta bar kitchen din, Aunty Farida na kallon Khaleesat dake juya miyan kan wuta don shinkafa da miya suke dafawa for breakfast, tace "Ina jin ki Khaleesah" Khaleesat dai bata kalleta ba tana ci gaba da juya miyan a hankali tace "Haka muka yi da shi Aunty, ni dai ban ce masa komai ba har yanxu" Aunty Farida dake ta kallonta cikin sanyin murya tace "Amma kina ganin iyayensa za su amince masa cikin sauki duba da status dinki ga kuma irin gidan da ya fito Khaleesat? Bana son ki saka ranki da yawa cause anything can happen, kin ga dai ai baza a boye ma iyayensa status dinki ba a yanxu, in ma aka boye magana irin wannan baya buya Khaleesah" Khaleesat ta kasa kallon Aunty Farida amma sosai taji jikinta yayi sanyi, taji ƙafafuwanta sun kasa ci gaba da ɗaukan ta, all this while ita bata taɓa kawo wannan tunanin a rai ba ko don tasan babu abinda ya shiga tsakaninta da Abdul ne yasa hakan, to amma bayan ita da Abdul din wa ya san ba abinda ya shiga tsakanin su? Aunty Farida ta jingina jikin cabinet ita