Showing 183001 words to 186000 words out of 257722 words

Chapter 62 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

give me, she's very beautiful, is she Halfcast?" Ajay yace "Meet Jay about that Femi" Femi ya gyara zama yace "Jay no get joy at all, he isn't as straight as you" Ajay yace "He will listen, since it's about you marrying his sister..." Femi yayi dariya sosai yace "I will definitely visit Bauchi soon be that" Ajay dai bai sake ce masa komai ba.
A kwana a tashi lokacin Exams din su Khaleesat ya matso don satin da za su shiga za a fara jarabawan, tun ranan da ta mari Abdul har zuwa yau bata sake ganin ko giftawarsa a school din ba, ita dai har sannan hankalinta yaki kwanciya don gani take kawai jira yake ta koma Nigeria before doing anything to her, sosai tayi da ta sanin marin da tayi masa, she wish bata yi hakan ba, da kawai ignoring dinsa ta dinga yi since he is not harming her, da ta tuna sati biyu kawai za su yi suna jarabawan sannan ta koma Nigeria sai taji jikinta yayi sanyi sosai, During all this time haduwanta da Jay ya ragu sosai ba kadan, ko apartment din nata sai in zai kai mata abu yake zuwa kuma ba dadewa yake yi ba, but tayi masa uxuri tunda yace mata su ma a wannan period din ne External defense dinsu may be he is concentrating on that and also giving her space to concentrate on her own studies too, amma abinda ke bata mamaki kafin taga Ajay da laptop ko wani abu da zai nuna karatu yake sau daya to ta gansa da remote din TV da bowl din fruit yana ci yana kallon football ko wrestling sau goma, gashi kamar baya bacci, abokansa kuwa in suka xo baya shigowa da su apartment din.... Ranan Friday Khaleesat na school tare da Safiyyah suna studying course din da za su yi exams dinsa ranan Monday, hadari ne sosai a garin, Khaleesat tace "Mu je apartment dina sai mu ci gaba da karatun a can ko?" Safiyyah tace "Tabb, ni ce zan je apartment din ki wannan Uztaz din na nan? Ni har yanxu kin ki gaya min dalilin da yasa suka yi switching da Housemate din ki" Khaleesat na kallonta tace "To ta yaya nima zan sani, na tambaye Housemate dina yace kawai sbda he is busy because of his upcoming defense ne baya samun time sosai he is always in the Library" Safiyyah tayi dariya tace "Shi kadai zai yi defense din? Shi ma Ajay ba defense din zai yi ba ko ba lokaci daya za su yi bane? Ni har na gano dalilin da yasa yaki zama a apartment dinki wallahi" Khaleesat tace "Meye dalili?" Safiyyah tayi dariya tace "Gaskiya na kara respecting Housemate dinki, wallahi iya da addini da sanin ya kamata, kinga a baya ai babu komai tsakaninku shi yasa ku ke zaune kowa na harkar gabansa a tsohon Apartment din ki, iyaka kuyi mutunci, yanxu kuwa da ya fara son ki yana tsoron kada shaidan yayi using Opportunity din zaman ku gida daya ya cuce ku, kinga hakan bazai haifo ɗa me ido ba, gaskiya yaya Housemate iya da addini" Ita dai Khaleesat tayi shiru bata ce komai ba sai ma murmushi da tayi kawai, Safiyyah tace "Abinda ya guje ma kenan kawai ba wani abu ba, don shi zuciya ba shi da ƙashi, shi kuma Ajay masifarsa da fitinarsa kadai ma bazai sa ya shiga harkar ki ba a gidan, shi fitinarsa ma zai iya zuke mutum wallahi" Khaleesat na maida wayarta cikin jaka tace "Sai ka masa abinda baya so yake masifa ai, he just love being on his own kar a shiga harkarsa that's all, but he is kind, caring and down to earth, sai da muka zauna yanxu na gane haka" Safiyyah ta saki baki tana kallonta, can ta gyara zama tace "Ikon Allah, yau ke kike yabon Ajay da kanki, to me da me yayi maki da kika ga he is caring and kind zaman ku a apartment din naki" Khaleesat ta daga ido ta kalleta, can tace "Kilan baza ki yarda ba idan na fara gaya maki wallahi" Safiyyah tace "Ai ina jin ki, gaya min yanda aka yi kika gane hakan in ga ko zai yi convincing dina..." Wayar Khaleesat ya fara vibrate a jaka, ta bude jakar ta ciro wayar, Safiyyah ta leka screen din don ganin me kiranta, sae kuma ta riƙe haɓa tace "Ikon Allah"



_Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa bello jidda Ur evidence_
07087865788


*Hakika duk wacce ta Bari aka barta abaya ita taso domin mu mata da ado da kwalliya aka sanmu. Assalamualaikum, barkanmu dai Yan uwana ma masu albarka, ayau na zo maku da batun sababbin kayan da na kawo Mana masu matukar kyau da kuma inganci,oum eman collection 🤝😍, takawo maku jakunkuna da takalma,hadi da abayas da kuma sarkoki masu matukar kyau da kuma sauki,07018872587 Ena amare da uwayan gida masu capacity's toh duk wacce ta yarda da tacika mace da wacce takeso ta zamo ma abociyar kwalliya toh ta garzayo gunmu domin hadewarki cikin ado da kwalliya kedai nemeni a wannnan number domin kisami kayayyaki masu kyau da kuma quality akan kudi kalilan hajiyata 07018872587 ngd 🤝 ado da kwalliya shine takenmu*

HALYSAAH 79

Khaleesat tayi picking call din ta kai kunne tayi shiru, after some seconds ta mayar da wayar cikin jaka ta kalli Safiyyah tace "Makulli zai amsa" Safiyyah tace "Toh shi ina na shi makullin? Haba, he is a kind of person that is way too organized da har za ace zai manta makulli a gida, ai irinsu are always cautious of everything, ta yaya zai mance abu me muhimmanci kamar makulli, shi dai yasan me yasa ya kira ki amma ba wai makulli ba" Khaleesat tace "To ni dai bai taɓa requesting makulli a wajena ba sai yau, probably he was carried away shi yasa ya manta, waye baya mantuwa" Safiyyah tace "To meye na wani karesa?" Khaleesat tace "A'a ba karesa nake ba, naga kamar you are trying to put meaning into everything" Safiyyah tace "Ko me yasa Housemate zai wani hada ku waje daya salon ku saba, ke dama gashi zuciyarki kamar ta yara mutum na maki kirki sau daya to har abada yana da kirki a wajen ki" Khaleesat bata san sanda ta fara dariya ba tace "Wa yace maki mun saba? An ce maki har yanxu baya masifarsa ne? Kawai dai bayan masifar tasa he will still be kind to you and give u a listening ear that's one thing about him, kin tuna abincin da na kawo school ranan har kika hanani kika cinye duka?" Safiyyah tace "Ehen sai aka yi yaya?" Khaleesat tace "To shi ya dafa" Safiyyah ta bude baki tace "Ban gane shi ya dafa ba, wannan abincin da nayi ta santin sa kina nufin girkinsa ne?" Khaleesat tayi dariya tace "Wallahi.... he can cook so well fiye da tunanin ki, amma iya jollof rice, sai rice and stew da Alfredo pasta kawai ya iya, i notice su ne favorite food dinsa, he can also make you different kind of salad and fruit salad, yana son su sosai...." Safiyyah ta hade rai, sai kuma ta taɓe baki tace "To shi ne ya burge ki kike haƙilon bani labari? Nasan Housemate ma babu abinda bai iya girkawa ba kawai chance ne baki basa yayi maki ba, beside he is always busy ina yaga lokacin wani girki" Dariya sosai Khaleesat tayi tace "See me see trouble, ni kin ji na ce maki Housemate bai iya ba? To in gaya maki bai ma iya din ba, sanda muke old apartment dina ba sai dai in dafa ya diba ba, shi ko wanke wanke bana tunanin ya iya balle shara da gyaran gida" Tana dariya ta kare maganar, Safiyyah ta wani kalleta tace "Abinda shi ba mace bane ta yaya zai iya wanke wanke ko kuma ya fara girke girke a kitchen kamar wani da ya taso cikin mata, girki da gyaran gida ai sai mata, ni tun da aka haifeni ban taɓa ganin Yarima da girki ba ma sai wannan karan, kawai dai wahalalle ne wannan Yariman...." Khaleesat ta kasa daina dariya tana kallon Safiyyah tace "OCD fa garesa, baya cin abincin wanda bai yarda da shi ba shi yasa yake kayansa da kansa, kika sani ko a can masarautar su akwai masu yi masa girki? Even here in America ai yana cin abincin Cook din gidansu...." Safiyyah tace "Ashe ma kawai kina zaune da wanda ke maki kallon gagarumar kazama ne tunda baya cin girkin ki, in ni ce ma bazan zauna gida daya da shi ba yana min kallon katuwar kazama, shi ne har kike bada labarinsa kina babbaka dariya bayan ya gama raina tsaftar ki, to meye abun dariya a nan, sannan kawai daga barin ki da shi a gida shi ne zaki je ki sake masa fuska har haka bayan kin san ɗan uwansa mutuwar son ki yake? Ai kamata yayi tsakanin ki da shi a gidan gaisuwa sama sama, don Housemate dinmu bazai ji dadin ganin kina washe ma Cousin brother dinsa hakora ba" Khaleesat ta hade rai tace "To ni yanxu ce maki nayi abu na hadani da shi a gidan ne wai?" Safiyyah ta daga hannu biyu sama tace "A'a kar ki canza baki Malama, bana son karya, yanzun nan kika gama yaba ma mutum kina cewa he is kind and caring amma kina neman lauye magana, in ba sake masa kika yi ba ta yaya kika san he is down to earth? Wato ke kawai kulasa kike yi kaca kaca a gidan ma kenan" Khaleesat tace "Ni dai wallahi ban ce maki haka ba kece dai baki fahimce ni ba, mutumin da ba magana ma sosai yake min a gidan ba" Safiyyah tace "Oho dai ni har kin bata min rai wallahi, sai kace wata kuturwa meye na dinga cin abincinsa da ya dafa da baza ki dafa naki ba" Khaleesat dai kallonta take, Safiyyah na gyara ɗankwalin kanta tace "Housemate ai bazai ji dadi ba fisabilillahi, ni ma kaina ban ji dadi ba balle shi da baza a rasa sa da kishi ba tunda duk mun san yana sonki" Ita dai Khaleesat bata ma san me zata ce ba, amma da gaske Ajay ko lkcn kulata ma baya da shi a gidan, iyaka yayi masifa in ta debar masa abinci kuma wani lkcn late take komawa gida shi yasa ma bata girkin in taga yayi sai ta debi nasa, kuma kaɗan yake dafawa kamar abincin rowa, can ta taɓe baki tace "Wai ke ance maki yana da time dina ne a gidan, shi fa kawai ya kalli football ko wrestling or boxing sai kuma ya buga PS5 dinsa" Safiyyah ta kalleta da sauri tace "Ke haba, da gaske? yaushe ya kawo PS5 din?" Khaleesat tace "Oho kawai gani nayi nima" Safiyyah tace "Ki ce wataran idan naje gidan baya nan za mu buga" Khaleesat tayi dariyar da bata yi niyya ba tace "Za ki buga dai, ni ba ruwana" Safiyyah tace "Kin tuna na saurayin former Housemate dinki Nancy, a sannan fa kema kika iya, Mutumin kirki haka ya bar mana ps4 dinsa a gidan da yaga muna so, kullum sai naje apartment dinki saboda shi lokacin muna level 2, mu yi ta buga game" Khaleesat tace "Hmm na tuna, ai yanxu ma idan naga yana yi sai in makale in ta kallo, kamar inje inyi" Safiyyah tayi kasa da murya tace "Wani rana da wani rana ne baya zaman gidan?" Khaleesat tace "Every Saturday saboda ina tsayawa school mu yi karatu baya zama gidan sai sanda zan dawo da yamma yake dawowa shi ma" Safiyya tace "Tunda dai ba mu muka kawo karatun nan duniya ba, gobe kawai in kin taho school sai mu koma apartment dinki tare da sauri mu buga PS5 din, abinda ma mun gama karatun course din da za muyi ran Monday in de ba haram za mu kara karantawa ba, kawai mu je mu shoshale a apartment din ki da Ps5" Khaleesat ta zaro ido jin wayarta na vibrate tace "Lahh, na manta ban kai masa key din ba" Safiyyah tace "Je ki kai masa ki dawo mu ci gaba da maganar mu, ai ni ban san yana da ps5 ba" Khaleesat ta mike ta bar wajen, duk da hadarin dake gari Safiyyah ke ce mata taje ta dawo su ci gaba da magana ko a jikinta idan ruwa ya musu duka. Khaleesat bata karasa inda Ajay yayi parking ba aka fara yayyafi, tana isa wajen ta bude front seat ta mika masa makullin apartment din, zata kulle motar yace "Kwana za ki yi a makarantar?" Tayi shiru bata ce komai ba, can tace "To zan je in ma kawata sallama" Yace "Ohk" Juyawa tayi ta koma inda ta baro Safiyyah, Safiyyah na ganinta tace "Kin ga an fara yayyafi, mu koma department mu ci gaba da maganar mu..." Khaleesat tace "Gida ma zan wuce" Safiyyah ta tabe baki tace "Motarsa za ki shiga kenan? Dama abinda yasa ya kira ki kenan ya ga hadari" Khaleesat tace "To ba waje daya za mu ba in ma saboda hakan ya kirani? Dama dawowa nayi in maki sallama sae gobe" Safiyyah tace "Ai shikenan" Khaleesat tace "Ko kuma tunda hanya daya ne mu je yayi dropping din ki kawai mana" Safiyyah tace "Wa?? Gwara inyi trekking inje gida, salon ya koreni, kema da kike iyayin cewa in shiga motar ba kyaleki zai yi ba.... Hadawa zai yi ya fatattake mu" Khaleesat bata sake ce mata komai ba suka nufi inda Ajay yayi parking, suna karasawa wajen Khaleesat tayi shiru ta tsaya ganin babu motarsa, can ta ɗan kalli Safiyyah ta gefen ido, Safiyyah dake ta waige waige tana neman motar Ajay tace "Ina motar tasa?" Khaleesat tace "Kawai mu tafi mu hau Uber" Da Safiyyah ta fara baɓɓaka dariya har da durkusawa kasa, tun Khaleesat na daurewa har ta kasa ita ma ta fara dariyan, da kyar Safiyyah ta dago tsabar dariya har da hawaye tace "Har kina min iyayin in shiga ayi dropping dina ke me sabon Housemate, yanxun nan kika gama kakkaresa sai gashi ya shuka maki rashin mutunci, an gaya maki Ajay zai canza halinsa ne" Khaleesat ta taɓe baki ta bude handbag dinta ta ciro waya zata yi ordering ride, har suka rabu da Safiyyah dariya take mata kamar zata shide, ita dai ko tanka ta bata sake yi ba.... Jay na zaune motarsa yana waya da Mami yaga Khaleesat ta sauka daga Uber din da ya ajiyeta, ya bi ta da kallo har ta shiga apartment dinta bata lura da shi ba, Muryar Mami yaji tana ta masa magana, ya ɗan sauke boyayyen ajiyar zuciya a hankali yace "Idan na dawo za mu yi magana Mami it's nothing to be worried about, in less than 3 weeks zan dawo Nigeria in sha Allah" Daga daya bangaren Mami tace "Jawwad kana tunanin da akwai wani abinda zaka tambayeni da zan ki maka ne? Plss tell me what you want, hankalina bazai kwanta har nan da sati uku ba, ko kuma in taho Maryland din ne?" Jay yace "A'a Mami ba sai kin zo, ba wani abu bane da zaki damu kanki, idan na dawo za mu yi magana" Mami dai tayi shiru, alamar bata gamsu ba. Khaleesat na shiga apartment dinta ta ji alamar Ajay yana kitchen, ta karasa kitchen din ta tsaya a bakin kofa tana kallonsa fuska daure tace "Ba sai kace min kar in dawo bazan same ka a wajen ba..." Ba tare da ya kalleta ba yana slicing fruits yace "Saboda ina tsoron ki" Tace "Amma ai da bazan koma wajen ba har ruwa ya doke ni...." Sai a sannan ya juya ya kalleta, lokaci daya taga ya ajiye wukan hannunsa da sauri yana kallon finger dinsa, dariya tayi tace "Dama wa yace maka haka ake slicing abu da wuka?" Ko kallonta bai yi ba har sannan yana kallon finger dinsa, Ita ma dai kallon hannun take don bata ga jini ba, can ta karasa kitchen din tace "Ai ba haka ake yanke hannu ba, idan da gaske ne jini za a fara gani yana zuba" Tana fadin haka ta bude tap ta wanke hannunta da liquid wash ta dau karamin towel ta goge hannun sannan ta karasa kusa da fruit din da yake slicing ta dau wukan tace "Let me just show you how to handle a knife in case of next time" Slicing fruit din ta fara, ya wani kalleta daga sama har kasa, can ta daga kai ta kallesa tace "Hope you are watching how i am using the knife?" Juyawa taga yayi ya nufi fridge ita dai ta ci gaba da yanka fruit din tana kallonsa, wasu fruits din ya debo alamar ya bar mata wa encan din, bata san lkcn da ta jefar da wukar hannunta a gigice ba jin wani sharp pain sai ga jini ya biyo baya, ya juya ya kalleta at first ta so ta daure, kawai taji ya fara dariya irin ta mugunta da yake ma Jay, sai a sannan ta fashe da kuka sosai, ta juya zata fita daga kitchen din ya tura kofa yace "Waye zaki zubar ma jini a parlor, jira ya gama tsiyayewa a nan kar ki bata ma mutane gida" Kuka kawai take zata fita ya tsaya bakin kofar yaki barin ta fita, sai kuma ya hade rai yace "Baza ki je ki wanke hannun ba" Ta koma jikin bango tana kuka a hankali tana kallon finger dinta da ta gaftare, Yace "Sorry... but that serves you right" Tap din kitchen din ya bude mata, bata ko kallesa ba ta tafi ta fara wanke hannun tana duba how deep the

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login