Showing 39001 words to 42000 words out of 257722 words

Chapter 14 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

yansa, ana haka aka shiga kotu ko lauya baban Khaleesat bashi da tunda bamu da halin daukan Lauya, rana na farko da aka kawo Malam Ali kotu daga prison ni da Khaleesat da kishiyar yayata Mama Shatu ce muka je kotun don sauraron karan, to a ranan Abdul yaje kotun shi ma a matsayin daya daga lauyoyin mahaifinsa ashe shi ma Lauya ne, sarai na ganesa da na gansa a kotun don ranan karshe da muka je gidansu har ce ma masu gadi yayi in muka sake dawowa su rike mu yan sanda ne za su zo su tafi da mu, zaman kotu da akayi a wannan rana babu wani positive outcome da ke nuni da cewar da nasara a case din, kwata kwata babu alamun nasara tunda Malam Ali ba kowa bane, kuma ba shi da kowa bai da komi, bashi da wanda zai tsaya masa, haka aka dage shari'ar zuwa wani watan shi kuma za a maidasa prison cikin motar da ta kawosa ko belinsa anki badawa, Khaleesat ta dinga kuka sosai a haraban kotun tana kallon yanda aka shigar da babanta motar prison, nima ina rungume da ita ina hawaye, wanda wannan ne ya ja hankalin Abdul da fitowarsa daga kotun kenan zuwa kanta, ba shi ba hatta sauran jama'an wajen kallonta suke, Alhaji Musa babban mutum ne kuma me kudi wannan yasa har da yan jaridu a haraban kotun, wani ɗan jarida ya nufo mu yana tambayar me za mu iya cewa game da zaman da aka yi yau a kotu, budan bakin Khaleesat cikin kuka sai cewa tayi Allah ya saka ma babanta sharrin da aka masa, ina tunanin a nan ne Abdul ya fahimci er gidan wanda suke ƙara ce Khaleesat, duka duka shekarunta sha shidda a sannan amma duk wanda ya kalleta sai ya sake kallonta, ranan ma tsautsayi yasa ta fito babu Nikab duk da ba a shiga da Nikab amma duk inda zata bata fita babu Nikab, in ma bata sa ba uwarta zata tilastata ta saka, hatta nima bana fita babu shi haka Mahaifiyarta saboda bakin jama'a, kun ji inda Abdul ya fara ganin Khaleesat, a sannan kuma kawai motarsa ya shiga, sai wani Lauya me zaman kansa ya nufo mu, ya ja mu gefe yana kokarin calming din Khaleesat, nan ya tambayeni me ya faru, me ya kawo mu kotu, nayi briefing din masa komai nima ina kuka, ya tambayeni zuwa yaushe aka daga karan, na sanar masa, yace to in basa lambata in sha Allah anjima zai kirani yaga abinda za ayi akan case din kuma mu kwantar da hankalinmu, ko wayar bani da shi a sannan, instead sai na basa Address din unguwanmu Mariri, ita dai kishiyar yayata na zaune karkashin bishiya tayi tagumi, a haka muka bar kotu ranan rai babu dadi muka koma gida, bayan kwana biyu ranan da yamma wajen karfe shidda muna zaune tsakar gida ko wacce na fafutukar abinda zata dora ta ciyar da kanta da yaranta, don yanzu kowa takai takai a gidan, kishiyoyin yayata har sun sake 'ya yan su maza kanana suna fita almajiranci suna ciyar da kansu, matan kuma a dora masu talla su tafi can bakin kasuwa, yayata dama ina taimaka mata muna sana'a a gida, kudin waec din Khaleesat ne dai muka kasa hadawa gashi saura kwanaki kadan a fara, kamar daga sama sai ga Mahaifin Khaleesat ya shigo gidan kamar an jefosa, Khaleesat ce ta fara ganinsa ta tafi da gudu ta rungumesa, duk muka mike tsaye a tsorace muna kallon ikon Allah baki bude, yayata tayi karfin halin tunkararsa tana tambayarsa daga ina yake haka, kar dai gudowa yayi daga gidan yari, Baban Khaleesat yace kawai shi dai ce masa aka yi an bada belinsa daxu da rana, sai gashi kuma aka daukosa aka kawo har gida aka ajiyesa, tsabar mamaki duk muka kasa cewa komai a tsakar gidan, yayata ta kama hannunsa hawaye cike idonta ta kai sa dakinsa don shi ma duk a firgice yake kana ganinsa kasan ba karamin wahala ya sha ba, sai a sannan yaran gidan suka fara ihu suna murnan dawowan mahaifinsu suna ta tsalle tsalle, sauran matan duk suka bi bayan yayata zuwa dakin Baban Khaleesat"



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*





Alhamdulillah! Shin kunada labarin MG’s Beauty Lounge zai buɗe a ranar Litinin, 2nd June 2025 – daidai lokacin Sallah!😍

‘Yan mata da mata masu son kyau a Kaduna, lokaci yayi da za ku haskaka a wannan Sallah!
MG’s Beauty Lounge ya buɗe da kwalliya, tsafta da ƙamshi irin na sarauniyar zamani!

Ga abin da zaki samu idan kika ziyarce mu:

Gyaran gashi da kitson zamani

Kwalliyar Sallah mai ɗaukar ido

Wanke ƙafafu da pedicure mai sanyaya rai

Kayan gyaran fata na gaske

Lalle mai kyau da salo na zamani

Tura-turai, humra, incense da ƙamshi masu daɗi

Shirin amare da na musamman


Ba kawai gyara muke ba – kulawa ce ta musamman ga kowace sarauniya.
Zo ki ji daɗin wanke ƙafa, lalle, kwalliya, ki saya kayan kyau da ƙamshi – komai a wuri guda mai kyau.

Adireshi: Block 21, Nnamdi Azikiwe by Makarfi Road, bayan gidan Indomie, kusa da Sorera Restaurant, Kinkinau, Kaduna.

Tambaya/Booking:
WhatsApp: 08062991549
Kira: 09016108092 / 08064532391

Ki zo ki gani da idonki – ki ji daɗin sauyin MG’s Beauty Lounge.
Bi mu a IG & TikTok: @MGsBeautyLounge

*Gaisuwa da fatan alkhairi zuwa ga me kasuwar garin Dutse Hajiya Aunty Zahrah da Hajjaju Sadiya Chamo Ex in-law, Hajiya Nafeesah Mom twins da Ummu Zainab Maman Ramla, Aunty Maryam Dan Ladi nasidi kema na gaisheki da katon murya, Hajiya Zainurah Boss Lady, Hajiya Jumare da Hajiya Asmy me kayan amare, Oum Nabeelah, Mardiyyah, Uwar Janan, Halysah Garba😂 i hail you all with respect yan Palace*

Manyan Membobin _❤‍🩹Khaleesat's Citadel_❤‍🩹
*Su Meenah parrot🐔, Oum Noor, Nafeesah Jawwad, Rukayya, Fidomashi, Siyam, M manal, Mrs Barrister, Shanono Esq, Ummilos, Na'imatu, Zulaiha, Ummu Abdrhm, Khaleesat Haiydar is saying a big thank you to you all for ur support always, Allah ya bar min ku*🥰

HALYSAAH 33

Aunty Farida ta numfasa a hankali tace "Da yake Abdul shi kadai ne namiji gun mahaifinsa, mahaifin ya dauki son duniya ya dora masa kuma bai jin maganar kowa sai nasa, duk abinda Abdul yake so shi mahaifinsa ke so, bayan yaga Khaleesat a kotu babu tantama zuwa yayi ya samu uban ya nuna yana sonta zai kuma aureta, wannan dalili yasa babu bata lokaci suka janye kara a kotu suka bar maganar miliyan dari da sharadin Malam Ali zai ba Abdul auren er sa Khaleesat, mu dai har yau bamu san ko da wata yarjejeniya da aka yi a kotun ba ko babu, mun dai san an janye kara kawai kuma duk muka yi farin ciki sosai da hakan, burin mu kawai Malam Ali ya dawo gare mu ko da bazai tsinana mu da komai ba amma mu dinga ganinsa a tare da mu a matsayin kantangar gida, balle duk mun san yayi ma iyalansa hidima dai dai gwargwado ya kuma kyautata masu yanda ya kamata, jarabawa ce kawai ta fada masa, bana mantawa Khaleesat ta shiga damuwa sosai a lkcn tana ta koke koke wai ita bata son Abdul tun ma bata san kalansa ba bata gansa ba tace bata sonsa bazata iya aurensa ba, mu kam idonmu duk ya rufe da son ganin an wanke Malam Ali daga laifin da ake zarginsa da shi, ni da uwarta muka yi ta bata baki muna kwantar mata da hankali muka ce ko tafi son a maida mahaifinta prison ne, ko don mahaifinta bazata hakura ba ta amince da bukatar Abdul na son aurenta don case din ya mutu gaba daya, gashi tun bayan dawowar Malam Ali yayi ta rashin lafiya ko kudin kai sa asibiti babu, duba da hakan ne ma yasa muka yi ta karfafa ma Khaleesat gwiwa muna bata baki, a haka dai muka samu muka lallabata ta fara hakura, nan kishiyoyin Ummanta suka fito da baƙin cikinsu da hassada a fili tunda su ma ai suna da 'ya ya mata sa'annin Khaleesat da ma wa enda suka girmeta amma shine Abdul zai ce sai Khaleesat, nan fa duk suka hau gaba sosai da yayata saboda ɗan mai kudi ya ga Khaleesat yace yana so, ranan farko da Abdul ya fara zuwa unguwan cewa yayi shi bazai shigo da motarsa layin ba ta fito bakin titi ta samesa, gashi daga gidan zuwa bakin titi akwai tafiya sosai, haka nan uwar ta lallabata ta shirya ta saka nikab dinta kannenta biyu suka rakata har bakin titin ta samesa, a ranan kuma ya bata babban waya ya kuma hadata da dubu hamsin, ba ma ita ta amsa ba don nuna masa tayi bata so shine ya ba kannenta yayi tafiyarsa, da kudin aka samu aka biya mata waec dinta tunda ba mu da yanda za mu yi, a kaf tarihi ban taɓa jin wanda yake neman yarinya da isa da gadara da walakanci kamar Abdul ba, for almost 2 months in Abdul zai zo unguwan mu sai dai dole ta fito titi ta samesa shi bazai shiga layin da motarsa ba, watarana ne ya kira bata da lafiya shine da ya tashi zuwa dubata da yamma ya shigo layin a karo na farko tunda ya fara zuwa gurin ta, daga nan kuma ya dena cewa ta fito bakin titi in ya zo sai dai ya karasa ciki da motarsa, ya kai ya kawo har cikin gida yana shigowa, tun a wannan lokacin Abdul baya raga ma Khaleesat, fadan yau daban na gobe daban, bashi da fahimta bashi da uxuri, ga nuna isa da gadara abinda yace yake so dole shi zata yi, haka nan yarinyar nan ke hakuri da halinsa duk don saboda mahaifinta, rana daddaya ne baya sa ta kuka, sai dai ni da uwarta mu yi ta bata hakuri muna ganin duk me sauki ne tunda har yana sonta kuma yaji zai aureta ya zauna da ita wataran zata canza sa da kanta, ni dai a sanda na fara sarewa da lamarin Abdul jikina yayi sanyi shine watarana da ya daga hannu ya mareta har sai da shatin yatsunsa ya kwanta fuskarta, mu dai har yau bata gaya mana me tayi masa da yayi mata haka ba don a cikin motarsa hakan ya faru, nan jikin uwarta ma ya fara sanyi kan lamarin har ta samu Mai gidanta ta gaya masa amma Malam Ali yayi ta kakkarewa har da cewa duk wanda ma ya kara tada maganar Allah ya isa, ana haka har ya biya mata jamb ya kai ta da kansa ta zana don fara jami'a tunda waec dinta ya fito kuma sakamakonta yayi kyau sosai, kawai rana daya kwatsam ubansa ya kira mahaifinta wai ga abinda Abdul yace yake so, wato zai tura Khaleesat Amurka tayi karatu a can, duk kawaicin da yayata take wannan karan sai da ta nuna bata amince da hakan ba, don ana ta bin su a yanda suke so ba hakan ke nufin bamu da ta cewa akan lamarin Khaleesat ba, ba Yayata ba har kakar Khaleesat Nenne ta nuna rashin amincewarta a wannan bukatar tasu, babu ta yanda za a dau yarinya karama haka da ko mallakan hankalinta bata gama yi ba ace za a tura ta har Amurka da sunan karatu, in haka ne kawai a daura auren mana sai ya kai ta duk inda ma zai kai ta tayi karatu, in ko ba haka ba babu inda er ta zata je da sunan karatu sai dai duk abinda zai faru ya faru, a nan dai laifin Mahaifin Khaleesat ne da ya dau tsoron duniya ya dora ma Abdul da mahaifinsa ba kuma tsoron komai ba sai tsoron kar su sake maidasa inda ya baro wato prison, dama tunda ya baro can ya dawo gashi nan gashin nan dai kamar ya ɗan samu matsala a kwakwalwarsa, yau lafiya gobe akasin haka, ya dawo kamar ba Malam Ali ba, a lokacin duk ya gigice yayi ta bala'i wai ina ne ba a tura yaro karatu a zamanin yanxu, yarinya me shekara sha bakwai ce za ace ma yarinya, inda yake shiga ba nan yake fita ba, hakan ya zame masu bacin rai sosai da mahaifiyar Khaleesat har sai da ta bar gidan ta koma gidan Mahaifiyarsa warce ita ma yaki sauraronta, haka nan Malam Ali ya dau Khaleesat ya damka ma Abdul ba tare da amincewar uwarta ba ya kai ta karatu Amurka, Shiru Aunty Farida tayi tana kallon su Ajay dake kallonta duk suna sauraronta, a hankali tace "Tun daga sannan shi yake sponsoring komai nata a Amurka, cin ta da shan ta, da suturanta komai dai shi ne, sai san da ya ga dama ne yake bari ta zo hutu Nigeria, mu tsakaninmu da ita dama sai sanda muka ganta ko kuma muyi magana ta WhatsApp, gashi yaki a daura auren nasu wai sai ta gama karatun wanda wnn ne ke kara daga mana hankali, a haka ake ta rayuwar bamu da kwanciyar hankali, a ko da yaushe fatanmu shine ayi ayi auren don duk wasu iyaye nagari baza a same su da kwanciyar hankali ba ace yau er su budurwa bata gabansu, kusan kullum sai uwarta ta zubda hawaye kan wannan lamari sanadiyar hakan har sai da hawan jini ya kamata, ace bata da iko da er ta sai dai abinda Abdul da ubansa suka tsara gashi mai gidanta ya dau tsoron duniya ya dora masu sai jan sa suke kamar rakumi da akala.... ko wata biyu ba ayi ba ranan yayata ta kirani take sanar min sun kawo kudin auren Khaleesat, duk muka yi farin ciki sosai da hakan, muka yi fatan Allah ya sa hakan alkhairi ne a rayuwar Khaleesat tunda mu ma mun fi son ayi auren kowa ma ya huta, kawai ranan juma'an nan da ta wuce sai ga kiran yayata wai an daura auren Khaleesat da Abdul, nace mata ban gane ba, Khaleesat din ta dawo ne? Sannan dama ana daura aure haka ba shiri? Nan take gaya min ai mahaifin Abdul din ne ya kira Baban Khaleesat da yamma likis yace ga bukatarsu gobe juma'a, babu bata lokaci kuma aka daura auren kamar yanda suka bukata washegarin, nace mata to shikenan Allah sa hakan shine mafi alkhairi, zuwa satin da za a shiga zan shigo kanon tunda tace Khaleesat din ma na Amurka bata dawo ba, ban kuma san komai dake faruwa ba sai ranan Lahadi da kirani, mun yi waya da kai babu dadewa sai ga yayata ma ta kirani tana kuka" Ajay ya sauke idonsa kasa, Calmly yace "Amma dai baki ce mata tana nan ba har yanxu ko?" Aunty Farida ta girgiza kai tace "Ai tunda muka yi waya kace kar in nuna ma kowa nasan inda take wallahi ban nuna ma yayata nasan komai ba, ita kanta har yanxu bata san inda Khaleesat take ba, Nasan Baaba Gaje bazata gaya mata ba ita ma" Ajay ya sauke ajiyar zuciya yace "Shikenan, yanxun ma kar ki nuna tana wajenki, in sha Allah za mu ga yanda za ayi, in ma kudin baban nasa da abinda ya kashe mata na makaranta za a mayar masu wannan ba matsala bane in sha Allah" Aunty Farida ta gwalo ido jin abinda yace, ko dai bai ji amount din da ta kira bane da kyau, a hankali tace "Kudaden ne da yawa ai Junaid, miliyan dari fa banda abinda zai ce ya kashe mata na makaranta da bamu sani ba" Ajay yace "Bazai dai ce ya kashe mata sama da miliyan dari a makarantar ba, mu ma duk makarantar muke ai, in ma yace haka miliyan dari biyu ba abu bane da muke fatan zai gagara a mayar masu, so kawai kar ki ce ma kowa tana wajenki, we will see how things will go in sha Allah" Ita dai Aunty Farida tsabar yanda jikinta yayi sanyi ta kasa cewa komai, dama tun da ya sakko daga mota jiya taga kalansa take ta kallonsa tana mamakin inda Khaleesat ta samo shi, hatta wanda ya kira ɗan uwansa bata ga yayi kalar tsiya ba shima, Shi dai Jay yayi shiru bai ce komai ba idonsa akan buhun shinkafa biyu da babban jarkan man gyada da carton din taliya dake parlon Aunty Farida, kana gani kasan food vendor ce, Ajay ya mike yana kallon Jay alamar ya tashi su tafi, Jay ya sauke boyayyen ajiyar zuciya yana kallon Aunty Farida a hankali yace "Bacci take ne?" Ajay ya wani kallesa sai kuma yayi ficewarsa daga parlon, Aunty Farida ta mike tace "Bari in duba ta" Dakinta ta nufa Jay ya bi ta da kallo, after few seconds sai ga ta ta fito tana kallonsa tace "Ehh bacci take" Yace "Ohk, amma Drip din na raguwa kuwa?" Aunty Farida tace "Eh yana sauka" Mikewa yayi yace "Toh shikenan, sai anjima Aunty, kilan zuwa gobe da safe in sha Allah za mu shigo" Aunty Farida ta ɗan yi murmushi tace "Toh Allah ya kai mu Jawwad, mun gode sosai" Murmushin ya mayar mata ya nufi kofa, har ya fita ya sake juyowa yace "Amma Aunty ki ɗan dinga duba drip din idan ya kare sai kiyi ma makociyar taki magana ta cire" Aunty Farida tace "Ina sha Allah, mun gode Jawwad" Daga haka ya fita daga parlon ya nufi kofar gida, cikin mota ya tadda Junaid har ya tada mota, ya karasa ya bude front seat ya shiga ya zauna ya jinginar da kansa da kujeran motar ya lumshe ido ya bude, saukansa kenan daga America ko hutawa bai yi ba balle ya ci abinci, yayi wanka kawai suka taho gidan Aunty Farida da Ajay, har suka isa gidan Cousin sister din parent dinsu dake Banana Island babu wanda yace komai a cikin motar, it's almost 7pm tsabar traffic din Lagos da ya rike su a hanya, bayan Ajay yayi parking Jay ya sauka daga motar ya nufi entrance din shiga gidan Ajay na biye da shi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login