Showing 246001 words to 249000 words out of 257722 words
Chapter 83 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar
bazawaran dama ai kince tare kika ganta da Junaid din a Amurka" Aunty ta ɗan bude ido jin abinda Mami tace, da sauri tace "A'a ba sai an kai ga haka ba Fulani, kin ga wannan ai babban magana zai zama a masarautar nan da ma garin Bauchi baki daya, mu dai bakinmu alekum mu yi abinda ya kamata hankalin Jawwad ya dawo jikinsa ya mance da wata bazawara" Mami tace "To shikenan Fulani, Nagode kwarai da gaske" Aunty tace "Haba ai yi ma kai ne, banda ma yan zugi sun shiga tsakaninmu a masarautar nan ai ke din mutuniyata ce a shekarun baya, yanxu dai ki nuna ma Jawwad kin ji kin amince sati ukun da yace sai yaje yayi ma ubansa Mai martaba magana a ɗaga auren" Mami tace "Zan sanar masa in sha Allah, bari in je ko breakfast ban yi ba" Daga haka Mami ta mike ta nufi kofa ta fita, Aunty ta kyabe baki murya can kasa tace "In bari a juya aure kan Junaid? Ashe ina ma son sa da alkhairi in har na bari aka yi haka, ai sai dai in sa a aura masa warce zata zamo ajalinsa in ma na bari yayi auren kenan...." Shiru Mai martaba yayi yana kallon Jawwad bayan ya gama sauraronsa, after a while ya sauke ajiyar zuciya yace "Fulani ce tayi maka wannan tsarin ko?" Jay ya sauke idonsa yayi shiru don bayan sun gama magana da Mami few hours ago sai da ta jaddada masa kar ma yace ma Mai martaba yayi magana da ita, Mai martaba yace "Nasan duk tsarinta ne wannan, so kana nufin yanxu in sake turawa a sanar masu na canza maganar da nayi shekaranjiya kenan?" A hankali Jay yace "Ai ba sai an tura ba ranka shi dade, ta waya ma idan aka sanar masu ina ga ya wadatar" Mai martaba dai yayi shiru yana kallonsa, bayan wasu mintoci yace "Baza a ɗaga daurin auren nan ba Jawwad, ranan Juma'ah kamar yanda na tsara za a daura auren, nothing is going to change that" Jay ya daga kai yana kallonsa a sanyaye bai iya yace komai ba.... Ko da ya koma bangaren Mami ya sanar mata yanda suka yi da Mai martaba kuka ta sakar masa tace "Ni kuma in dai ba nan da sati hudun da muka shirya da kai ba wallahi Ahmad kayi aure ne ba da yawu na ba, ba kuma da amincewata ba, kuma bazan taɓa saka maka albarka a wannan aure ba" Sosai jikin Jay yayi sanyi yace "Don Allah Mami ki yi hakuri, ni nasan yanda zan yi convincing Mai martaba zuwa lokacin da kika ce kina son ayi auren" Cikin kuka Mami tace "Da dai yafi maka, duk da bana son auren nan haka na kai zuciya nesa na amince amma nace ga yanda nake son ayi min a matsayina na mahaifiyarka nan ma sai a tauye ni a nuna ban isa ba?" A hankali Jay yace "Kiyi hakuri, yanda kike so in sha Allah haka za ayi" Ba karamin Courage Jay yayi gathering ba ya sake komawa gun Mai martaba bayan Magrib, ya risina kai cikin ladabi yace "Ka gafarce ni ranka shi dade, i don't mean to disobey or disagree with you in any way, amma kayi hakuri ranka shi dade ka ɗaga wannan aure zuwa nan da wata daya kafin nan nayi shirye shiryen da zan yi a tsanake" Mai martaba ya ɗan yi murmushi ya jinjina kai bai dai ce masa komai ba, shigowar Aunty Parlon yasa Mai martaba yace "Zaka iya tafiya Ahmad, I've heard you" Jawwad ya mike yayi ma Aunty barka da yamma sannan ya fita daga parlon. Wajen karfe tara Ajay ya shiga Bedroom din Jay yana kallonsa yace "Don me zaka samu Mai martaba kace a ɗaga auren?" Jay yace "I have no Choice Ajay, haka Mami tace take so" Ajay yace "Must you listen to everything?" Calmly Jay yace "C'mon Ajay, she is my mother, ta yaya zan yi aure babu blessings dinta? Yanxu ba cewa tayi bata son auren kwata kwata ba kamar yanda tace few days ago, kawai so take sai na fara auren Hadiyah da 4 weeks sannan in auri Halysaah, idan ina son ganin dai dai ai abinda tace take so shi zan yi" Ajay ya girgiza kai yace "Ina me tabbatar maka wannan wani plan ne nasu suka hada ita da Aunty cause ita ke zugata...." Jay yace "What ever, ni dai nasan wata dayan da tace bazai cika ba ta canza min magana, shi yasa ban damu ba" Ajay ya sauke ajiyar zuciya yace "Abba isn't happy with this, he wasn't expecting this from you, considering the fact that he supported you from the onset..." Jay yace "I have no choice kamar yanda nace maka Ajay, Mami ce ta sa inyi haka and I did that for peace to reign" Ajay ya ɗan yi murmushi yace "At the end ina ga fa sai dai tayi hakuri ta saka albarkan nan da tace bazata saka ba daga baya cause I am assuring you come Friday sai Abba yayi abinda ya tsara, saboda wani reason mara ma'ana bazai canza maganarsa ba a maida shi karamin mutum, come Friday you will be groom to 2 bride...." Jay na kallonsa da damuwa yace "Haka Abba yace maka?" Ajay ya ɗaga kafada bai ce komai ba ya juya ya fita daga dakin, Jay ya rasa ma me zai yi ko kadan bai son bacin ran Maminsa gashi har da kuka tayi saboda shi, nazarin maganganun da zai sake samun Mai martaba da shi ya fara yi, ya fi minti ashirin pondering on what to say to the king for the third time, daga karshe ya mike ya fita with the hope that wannan karan Sarki zai janye batun auren zuwa nan da wata daya. Karfe goma saura Jay ya tafi bangaren Ajay, a parlor ya samesa yana kallon kwallo, Jay ya sauke ajiyar zuciya ya zauna yana kallonsa yace "Daga wajen Mai martaba nake" Ajay ya ɗan kallesa, sai kuma yace "Ya ku ka yi da shi?" Jay yace "I am just hoping he consider all what I said"
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah*
07087865788
HALYSAAH 98
Washegari da safe Jay ya tafi bangaren Maminsa don gaisheta, bayan ta amsa gaisuwarsa tana kallonsa tace "Ya ku ka yi da Sarki?" Jay ya sauke idonsa yace "Mami sau uku ina yi masa magana...." Mami tace "Ba sau nawa kayi masa magana nake tambayarka ba Jawwad, cewa nayi ya ya ku ka yi da shi daga karshe?" A hankali Jay yace "Kinsan bazai yi magana me tsayi ba Mami, he was quiet at the end kuma yace min ya ji, i am just hoping he is convinced kuma zai yi considering duk abun da na gaya masa, don haka ko da zaki ga wani abu daban Mami ki sani i tried my best in maki yanda kike so, duk yanda nake jin nauyin Mai martaba i confronted him thrice just to please you Mami" Sallaman Aunty yasa Jay yayi shiru ya daga kai yana kallonta, Aunty ta karaso cikin parlon tace "Fatan mun wayi gari lafiya Fulani" Mami tace "Lafiya lau Alhamdulillah, ya kwanan su Zuwaira?" Aunty ta nemi kujera ta zauna tace "Alhamdulillah" Jay ya sauke idonsa ya gaida Aunty ta amsa sannan ya mike yana kallon Mami yace "Zan ɗan fita Mami, sai na dawo" Aunty tace "Zaka ɗan fita ko dai za ku fita, Boss din naka na can naga ai ya shirya yana jiran ka kaje ka ja maku mota" Ko kallonta Jay bai yi ba har ya fita daga parlon, Aunty ta taɓe baki tana kallon Mami tace "Tare fa za su fita da Junaid don naga Junaid din ya fito yana rike da makullin mota" Mami dai bata ce komai ba don abinda ya dameta daban a ranta, ba kadan maganar auren nan ya tsaya mata a rai ba, Aunty ta gyara zama tace "To yanxu yaya ake ciki? Mai martaban ya yarda a ɗaga daurin auren ko kuwa?" Mami ta girgiza kai tace "Ina tantama Fulani, don sau uku Jawwad din ke samunsa da maganar amma yaki ce masa komai, kin ga kuwa bai amince ba kenan" Aunty tace "Sai kace ba Sarki ba, ai ni nasan ko don ya nuna mana iyakar mu fa sai yayi abin nan da yaga ba ma so, ga abu ya zo a kurarren lokaci balle a bi ta kasa a lalata, amma dai kin san abinda zai faru?" Mami na kallonta tace "A'a sai kin fada" Aunty ta mike ta koma gefenta ta zauna tana kallonta.... Ko kallon Jay Ajay bai yarda yayi ba ya nufi motarsa, Jay ya bi sa da kallo yace "Ni zaka walakanta?" Sai a sannan Ajay ya juya ya kallesa yace "Since when did I become ur driver Jay, if you are not too fine to drive ga drebobi sai wanda ka zaba a gidan nan, why do I have to drive you, on a serious note bazan je unguwan nan me nisa ba da daddaren nan, gwara ma ace hanyar Kano na kama in san tafiya me nisa dama zan yi kawai, haba ai unguwan yayi nisa sosai ga hanyar babu kyau ga dare yayi, throughout the day time me yasa baka ce in raka ka ba sai da daddaren nan, beside i told you i am meeting a friend yana jirana, you met me already prepared to go out balle kace kirkiro fitan nayi" Jay dai kallonsa kawai yake, Ajay yace "Zaka je wajen budurwar ka sai kace sai an raka ka, idan nace bazan je ba kuma ya zama issue, kaje for once kai kadai mana, haba you are stressing me wallahi" Kallonsa kawai Jay yake yaki tanka sa, Jin Jay yaki cewa komai kuma bai fasa kallonsa ba yace "To in har zan je sai ka min full tank, sannan akwai shopping da zan yi online the bill is on you, agreed?" Jay ya wani kallesa, haka nan babu yanda Ajay ya iya suka bar gidan a cikin motarsa yana mita, Jay dai ko kallonsa bai yi ba, karfe tara saura mintuna Ajay yayi parking dai dai kofar gidansu Aunty Murja, Jay ya ciro wayarsa after some seconds ya kai kunne duk da ba kira yake ba don yasan ko ya kirata ba lallai ta ɗaga ba, he tried calling her once yesterday bata yi picking ba kuma bata biyo sa ba, can ya kalli Ajay yace "Can you pls call Halysaah's line, I can't reach her" Ajay ya juya ya kallesa, sai kuma yace "You can't reach her? To ni ne zan iya reaching dinta kenan, ina ce same network muke using, in baka sameta ba ai nima haka, better still ka aika yaro cikin gidan ya kirata mana" Jay ya dau wayar Ajay dake ajiye, shi dai Ajay kallonsa kawai yake, number Khaleesat yayi dailing sai ga suna ya fito anyi saving as Jay's girl, Jay ya daga kai ya kallesa, dariya Ajay yayi, shi kansa bai ma san me ya basa dariya ba, May be the way he saved the contact, can dai ya fixge wayar yayi sending kiran, Jay yace "Sunanta ne baka sani ba?" Ajay yace "Oho, Haseenah kake ce mata ko Haseelah" kiran na shiga bayan ɗan lokaci Khaleesat ta ɗaga amma tayi shiru, Ajay yace "Ke kika saka min katin zaki yi shiru Malama?" A hankali tace "Good evening" Yace "Ana jiran ki a waje" Tace "Wa?" Yace "Kar ki bata ma mutane lokaci Malama" Daga haka ya katse wayarsa ya daga kai ya kalli Jay dake kallonsa, bayan kusan minti shidda sai ga Khaleesat ta fito tana sanye da hijab har kasa, kallon motar kawai take kamar bazata karasa ba can dai tana tafiya a hankali ta nufi gun motar, Ajay ya kunna fitilar cikin motar, shi dai Jay kallonta kawai yake suna hada ido ta sunkuyar da kai, kamar munafuka ta zaga ta wajen driver seat inda Ajay ke zaune, shi kansa kallon mamaki ya bi ta da shi har ta iso side dinsa ta tsaya tana kallonsa tace "Ga ni" Ajay ya juya ya kalli Jay da ya ɗan yi murmushi kawai don ko kadan bai ji haushin hakan da tayi ba, Ajay ya sake kallonta yace "Me zan maki?" Duk da abinda take ji a ranta sai da ya bata dariya amma bata yi ba ta wani kallesa kafin ta saci kallon Jay taga kallonta yake, sunkuyar da kanta tayi, Ajay ya hade rai yace "Malama you are obstructing the air from reaching me, matsa daga nan" Ta wani kallesa tace "To ai kai ne ka kirani" Ajay ya juya ya kalli Jay da yaki cewa komai, can ya bude motar, ta matsa gefe har ya sauko, tsayawa tayi gabansa ganin barin wajen zai yi kamar zata yi kuka tace "Toh ba kai ne ka kirani ba, why did you call me?" Da mamaki Ajay yace "Wai ina wasa dake ne, kinga na saba kiran ki dama?" Juyawa yayi ya bi ta gaban motar ya wuce ta bi sa da kallo, can ta saci kallon Jay suka hada ido, sauke idonta tayi lokaci daya jikinta yayi sanyi, ɗan murmushi yayi ya bude motar ya sauko sannan ya zagayo inda take tsaye, ta ɗan koma baya a hankali tace "Ina yini" Yace "But you know what happened few days ago wasn't intentional right?" Gyada masa kai tayi, cikin sanyin murya yace "To kiyi hakuri Halysaah, it's the work of the devil" Ita dai tayi shiru bata ce komai ba, yace "Kin hakura?" Ta gyada masa kai, yace "Ta yaya zan gane hakan?" Ɗan murmushi tayi ta jingina da motar bata ce komai ba, yayi kasa da murya yace "Kin riga kin ba Ajay insight cewar we had issues ai" Ta ɗan kallesa tace "Ai bazai sani ba...." Yace "Wa yace maki, ur reaction says it all..." Ta girgiza masa kai tace "Zai yi tunanin i am just pulling his leg saboda shi ne ya kira wayana" Jay yace "To shikenan Halysaah, just came to check on you, hope there is no problem" Ta gyada masa kai kawai, a hankali yace "Ki ci gaba da mana addu'a kin ji Housemate? We need it most at this point" Tace "In sha Allah, but...." Yace "But what?" A hankali ta jingina jikin motar cikin sanyin murya tace "No matter what ka zamo me yi ma Mahaifiyarka biyayya, may be aurenmu babu alkhairi ne shi yasa bata so...." Hawaye ne ya cika idonta ta kasa ci gaba, Jay dake ta kallonta da mamaki yace "Saboda me zaki ce aurenmu babu alkhairi Halysaah? Me yasa zaki ce haka? Kuma wa yace maki Mami bata son auremmu, ita kawai cewa tayi ga particular time din da take son ayi auren, Ajay ne ya gaya maki abinda ke faruwa har kika aiko min text din nan few days ago?" Cike da karfin hali Khaleesat tace "Da yaushe muke magana da shi har zai gaya min abinda ke faruwa, Kasan ai baza a boye min abinda Mom dinka taje tayi a gidanmu ba" Jay ya dinga kallonta babu ko kiftawa zuciyarsa na bugawa jin abinda tace, da kyar ya bude baki yace "Gidanku kuma Halysaah? Kina nufin Mamina taje gidan ku??" Khaleesat dai ta dinga kallonsa don reaction dinsa ya nuna kwata kwata bai san Mami taje gidansu ba, hawayen dake makale idonta ya gangaro ta sauke kanta, jingina yayi da motar ya ma rasa abinda zai ce zuciyarsa na bugawa da karfi, Khaleesat ta goge hawayenta cikin sanyin murya tace "Ai ya ma wuce don har Mai martaba ya aika an ba su Babana hakuri, and he spoke to them on phone" Jay was more than shock ya dinga kallonta babu ko kiftawa don duk bai san da haka ba babu wanda ya gaya masa har Mai martaba, a hankali yace "Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un" Khaleesat ta goge idonta cikin sanyin murya tace "I think it's better mu jira har sanda zata so aurenmu, but for now mu hakura kawai, haka Abdul ya aureni Mom dinsa bata so na, yan uwansa basa so na, yanxu kuma...." kasa ci gaba tayi ta fashe da kuka sosai bayan ta tuna abinda Mom din Abdul tayi mata, don yana daga cikin mamakin da har yau ya kasa barin ranta, Lokaci daya Jay ya rikice mata ya fara bata hakuri, zuwa yanxu ta fahimci halin da yake shiga idan yaga tana kuka hakan yasa ta dake ta hadiye kukan nata tana goge idonta, damuwa ƙarara fuskarsa yace "Kina tunanin zan iya hakura dake no matter what Halysaah? Kinsan irin son da nake maki kuwa? What do you think will become of me idan na yarda aka raba mu?" Ita dai Khaleesat ta kasa ce masa komai hawaye na zuba idonta tana gogewa, Yayi kokarin calming kansa cike da karfin hali "Kiyi hakuri Halysaah amma no matter what ni bazan rabu dake ba, in sha Allah komai zai yi dai dai da izinin Allah, zan kira Aunty Farida in basu hakuri, I knew nothing about this babu wanda ya sanar min Billah" Khaleesat ta ɗan yi murmushi tace "Ya wuce fa, abinda nace maka har gida Mai martaba ya aika a basu hakuri, ai kaga ya wuce kenan" Jay was speechless, bai taɓa tunanin abun Maminsa ya kai har haka ba, to menene yasa shi zata dinga masa pretending, wannan abun da take yi ne yake kara weighing dinsa down, shi abinda zata nuna masa daban abinda zata je tayi kuma daban, this is so heartbreaking to him, Ajay ne ya zagayo wajen yace "Pls I can't endure the mosquitoes in this area anymore, in baku gama ba ka samu nearest hotel kawai kayi lodging ni gida zan tafi" Khaleesat ta daga kai ta kallesa, ya hade rai yace "Matsa min in shiga mota" Ta ɗan taɓe baki ta matsa, ya bude driver seat ya shiga, Khaleesat na kallon Jay a hankali tace "Shikenan sai da safe" Da damuwa yace "Ba mu