Showing 30001 words to 33000 words out of 257722 words

Chapter 11 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar

shaye wannan, gaskiya duk yanda za ayi a raba auren nan domin ceto yarinyar nan daga halaka, yanxun nan zan kira farida kuwa" Gaje ta rufe bakinta da sauri tace "Ki kirata kice mata me? Rufa mana asiri ba wanda yasan tana nan, ina me tabbatar maki kilan yanzu an tafi da Awdul din police station, kinga ai dole ya kai yan sandan gidansu Khaleesat don wanke kansa su tabbatar matarsa ce, in kuma yayi haka ai za a bazama nemanta ne a gari" Maman Fu'ad tace "Ba komai Gaje, ki tafi kawai ki kyaleta a nan kar su je can gidan naki baki nan" Gaje ta mike da sauri tace "Don Allah ki bata ruwan zafi in kina da shi tayi wanka" Maman Fu'ad tace "Kar ki ji komai Gaje" A haka Gaje ta bar gidan, yanda Khaleesat taga daren jiya wannan daren ma haka ta gansa, ga ciwon kai, ga ciwon ido, ga zazzabi duk ta rasa inda zata sa kanta taji dadi, she don't even know who to speak to at this point. Washegari karfe tara Gaje ta shigo gidan, tun daga bakin kofa ta fara ba Maman Fu'ad labarin abinda ke faruwa tace "Sadiyah wajen karfe goma suka zo nemanta a gidana wallahi jiya har da shi Awdul din, ni dai jikina sai rawa yake don tare yake da yan sanda, yanxu haka daga can Mariri nake, uwarta na can hankalinta a tashe ko bacci bata yi ba sai koke koke, uban kuma yace da hadin bakin uwar Khaleesat ta gudu, babu kalan tijaran da Awdul bai yi ba jiya, keee abun dai babu kyau, ni dai hankalina ya tashi sosai, ina tsoron kar a gano ni na ajiyeta Awdul ya hadani da hukuma, shine na zo kawai ta shirya tayi hakuri ta koma gida duk abinda Allah yayi dai dai ne" Khaleesat dake jin duk abinda Gaje ke cewa ta fashe da matsanancin kuka tace "Don girman Allah kar ki ce masu ina nan Baaba Gaje, wallahi har duka zai iya min" Maman Fu'ad dai na tsaye da atamfar mutane da zata yanka ta hau kan keke ta kasa cewa komai sai zazzare ido take, ita ma tsoro take kar daga karshe ace ai a gidanta aka boye Khaleesat, ta ina zata fara ma Baban Fu'ad bayani in aka zo tafiya da ita gashi bai gari, Gaje tace "Toh ya kike so inyi Khaleesah, Awdul fa ya maida maganar nan babban magana wallahi, wai kin tozartasa a cikin mutane jiya kin sa an tafi caji opis da shi, ba ki da kowa da zai tsaya maki a lamarin nan sai Allah, Malam Ali na can kamar zai haukace shi ma ya saka uwarki a gaba sai ta fito dake" Khaleesat ta hade kanta da gwiwa tana shesshekan kukan, Gaje ta make hannun Fu'ad dake ta jan yakunannen gyalenta sannan ta ja kujeran tsugunno ta zauna ta rafka uban tagumi tace "Ni dai ban san kuma yanda zan maki ba Khaleesah, ina talaka da ni Awdul yasa a daureni wa zai cece ni, sai ma Kinga kallon da yake min jiya kamar bai yarda da ni ba" Khaleesat ta dago da kyar tana kallon Baaba Gaje hawaye na sauka idonta, Baaba Gaje dai zai zazzare ido take tace "Ni ban ma yarda bai sa CID unguwar nan su kula da shige da fice na ba, yanxu hka sai da na zaga kamar zan je Yan kaba sannan na taho gidan nan" Cikin sanyin murya Khaleesat tace "Don Allah Baaba Gaje ki min alfarman dauko min jakana a can gidanmu" Baaba Gaje ta gwalo ido tace "Wani jakar?" Khaleesat tace "Karamin jakata, akwai wayata a ciki zanyi amfani da shi" Baaba Gaje tace "Um um Khaleesat, ta yaya zan dauko jaka ana gani na da rana tsaka?" Khaleesat ta girgiza mata kai tace "Karamin jaka ne bai da girma, ko a gyalenki zaki iya boyewa don girman Allah ki rufa min asiri ki taimakeni Baba Gaje ki dauko min, har da kudi cikin jakan, zaki ga jakar kusa da akwatina a gefen katifar Umman mu" Maman Fu'ad dai sai baza ido take taji Khaleesat zata bar gidanta amma shiru bata ji ba, can dai tace "To ke ina kika nufa daga gidan nan yanzu?" Khaleesat na share hawayenta a hankali tace "Idan ta dauko min jakar zan san inda zan je in sha Allah" Maman Fu'ad ta sauke boyayyen ajiyar zuciya, faridan ma bazata kira ba kar daga karshe a gane ita ta ajiye Khaleesat a gidanta ta shiga uku, Da kyar Baba Gaje ta yarda zuwa Mariri dauko jakan don duk a tsorace take, shi ma sai da Maman Fu'ad ta saka baki tunda taji ance in dai aka dauko jaka to za a bar gidanta, shi sa tayi ta lallaba Gaje taje Mariri dauko jakar, bayan kusan awa daya sai ga Gaje da jakar ta kudundunosa a gyalenta, Khaleesat ta amsa jakar ta bude ta ciro wayar Jay dake ciki, ta ga dollars din da ya bata suna ciki har sannan, Call log ta shiga sai kuma ta kalli Maman Fu'ad tace "Don Allah ki ara min wayarki bani da Sim card a nawa" Maman Fu'ad tace "Ai ko babu kati, tunda ga wayar Gaje bari in bada dari biyu a siyo sai ki saka a nata wayar ki kira" Nan duk dubara Maman Fu'ad tayi kar a ga Khaleesat tayi kira da wayarta idan bincike yayi bincike, Gaje ta mika ma Khaleesat wayarta ta fita ta amso mata katin dari biyun da Maman Fu'ad ta dauko ta bada, Khaleesat na saka katin ta fara dialing number Jay, ta kira yafi sau biyar sai dai kiran ya dawo mata alamar bai je ba, bata hakura ba still tayi ta kira baya shiga bata san ko katin ne yayi kadan ba kuma Number sa na Nigeria yake using a can din ma, wasu sabbin hawayen suka fara sauka idonta ta sake shiga call log din wayar tana scrolling slowly, number AJ ta gani shi ma Nigeria Line dinsa, ta ɗan yi jim tana kallon number, sai kuma tayi dialing tana share hawayen dake zuba idonta, ringing ya fara yi har ya katse bai daga ba, ta sake kiransa, sai da ya kusa katsewa sannan yayi picking, muryarta na rawa tace "Good Afternoon" Shiru yayi, kafin yace "Wacece?" Ta sauke idonta tace "Ni ce" Yace "Ke wa?" Da kyar tace "Plss i want to speak to you" Kawai ta fashe da kuka uncontrollably, shiru yayi for almost 15 seconds, can yace "What happened?" Tana kuka tace "I need to speak to you pls" Ya kara yin wani shirun, can yace "Where are you?" Tace "Hotoro" He still kept quiet for some seconds kafin yace "Address" Katse wayar Khaleesat tayi ta tambayi Maman Fu'ad address din unguwan, Maman Fu'ad ta gaya mata sannan ta tura masa ta message, Gaje dake zaune kan kujera tace "Wanene wannan din da kika kira?" Ita dai Khaleesat tayi shiru wasu hawayen na taruwa idonta, Baba Gaje tace "Gashi idon naki sai kara ja yake yi, wallahi makantar da ke kawai yayi niyyar yi matsiyacin nan" Bayan kusan 35 mins wayar Gaje ya fara ring, Gaje ta mika ma Khaleesat da sauri tace "Ko wanda kika kira ne?" Khaleesat ta amsa tana kallon wayar taga AJ ne ke kira, dagawa tayi yace "I am outside" Khaleesat ta ajiye wayar sannan ta kalli Maman Fu'ad tace "Aunty don Allah kina da Nikab?" Maman Fu'ad tace "Yaushe rabona da Nikab, bani da shi yanzu kam" Khaleesat ta mike tana rike da handbag dinta da wayar Jay ta fita daga gidan, not far away from the house yayi parking, yana jingine jikin motar ya rungume hannunsa looking at a different direction, tana tafiya a hankali ta nufesa tana kallonsa, tana isowa kusa da shi ya juya jin Footstep, ya gyara tsayuwarsa ya dinga kallon idonta babu ko kiftawa, she tried her best na ganin bata fashe da kukan da ya taho mata ba amma ta kasa daurewa ta hade kanta da jikin motar ta fara kuka har da shessheka.


*Thanks for ur patient, and thank you all for checking up on me*



*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah and u send ur evidence of payment 07087865788 👈🏻, it's better ki ji tsoron Allah ki sauke nauyi kiyi karatunki cikin kwanciyar hankali don littafin na kudi ne, in kika karanta with no payment i owe you 500*

kema kına cikin matan da kullum sedai su bawa miji abinci?? Ko kema kullum lunchbox na yaranki shinkafa ce?
Sarari yummy treat ta sauqaqamiki
Frozen snacks are always available a wajenmu
Samosa
Spring rolls
Meatpie ( to fry)
Duk yawan yanda kikeso hajiyata xaki samu

Ga kuma sallah ta matso
This year kibar wanna cincin din ki canjamai da samosa, Cup cake, Spring rolls, Doughnuts, Meat pie, sannan akwai frozen, fried ko kuma samosa wraps din @2800👌🏻
Kawai fillings dinki xaki hada ki nade ki soya Nation wide delivery
09014996620
https://wa.me/message/VBRYP3DYFYNME1


HALYSAAH 30

Ajay bai ce mata komai ba sai da tayi kukan me isarta don kanta tayi shiru, tana share idonta ta daga kai ta kallesa taga kallonta yake har sannan, Calmly yace "He did all this to you?" Kai ta gyada masa wasu hawayen na taruwa idonta, yayi shiru for a while kamar me nazari, sai kuma yace "Ɗan kano ne?" Nan ma ta gyada masa kai, yace "A ina yake a kano?" Muryarta na rawa tace "I don't really know" Zai yi magana Baba Gaje ta leko kofar gidan kamar munafuka tana zazzare ido, Ajay ya ɗan sauke kansa ya gaisheta bayan sun hada ido da ita, fitowa tayi da sauri tana kalle kallen Unguwan tace "Lafiya lau ɗan nan, wallahi yarinyar nan tana cikin mummunan masifa, bata da kowa sai Allah, ta dawo daga turai ta tarar an daura mata aure da lafcecen yaron nan ɗan iska, dama kuma duk mun san ɗan iska ne muke kauda kai tunda bamu da yanda za mu yi, ashe bai ma yi shawara da ita ba kansa tsaye ya taho ya samu iyayen da ya raina suka daura aure shekaranjiya, to tunda tace bata son auren in dai ba tsinannen mutumi ba ai sai ya kyaleta ga mata kaca kaca a duniya, wani mugun kuduri ne a ransa haka da yasa aka daura auren a gaggauce ko shiri babu? dubi fa abinda ya mata a fuska daga ya dannata a mota taki bin sa, yanxu haka duk ya baza CID a unguwan nan ana nemanta, sai kaga tijaran da yaje ya ma iyayen nata jiya da daddare, shi sa ka gan mu duk a tsorace" Tun da ta fara magana Ajay ke kallonta ko kiftawa baya yi, mamaki ne sosai kwance a fuskarsa, can ya kalli Khaleesat dake kuka kamar Baaba Gaje na dada tunzurata, ya sake kallon Gaje yace "Aure kuma Mama?" Gaje tace "Wallahi da gantalallun igiyoyinsa har uku a kanta yanxu haka, tun jiya ta gudo nan bayan ta samu ta tsere da kyar daga hannunsa" Gaje ta fashe da kuka tana matsar kwalla da gyalenta tace "Wallahi bata da kowa sai Allah, iyayen basu da bakin magana, basu da ta cewa, ni kuma ba kowa bace makociyarsu ce mun yi zaman Mariri tare kuma ni talaka ce, ni ko taimaka mata ne kayi ka kai ta wajen masu kare hakkin ɗan Adam ta kai masu kukanta su kwato mata hakkinta da ake neman tauyewa" Har sannan Ajay ya kasa cewa komai, can ya bude gaban motarsa yana kallon Khaleesat, Baaba Gaje ta fara tura ta ciki tace "Maza shiga ku je ya kai ki ofishinsu, in ma rike ki za su yi su rikeki ki zauna har sai sun bi maki hakkin ki, amma kar ki ce nasan komai, kar ma ki saka ni a maganar" Khaleesat dai kuka kawai take ta shiga motar, Baba Gaje ta amshi wayarta dake hannunta ta kulle motar gbamm tace "Maza ku je" Ajay dai ya zaga ya bude driver seat ya shiga, Da sauri Baaba Gaje ta koma gate din Maman Fu'ad kamar ba daga kusa da motar ta taho ba, ta makale tana kallonsu har suka fita daga layin, driving kawai AJ yake idonsa a kan titi, gaba daya he look speechlesss, tunda ya kalleta sau daya bai sake kallonta ba, ita dai Khaleesat ta rufe fuskarta da Hijab dinta saboda hasken rana dake damun idonta kuma tana tsoron kar ace su hadu da Abdul dan motar babu Tint, har sannan bata daina kukan tashin hankalin da take ba, after driving for 20 mins AJ ya kalli wayarsa dake vibrate, Number Jay ne ke kiransa, hakan ya sa ya rage tafiyar da yake ya gangara gefen titi yayi parking sannan ya dau wayar yayi picking ya kai kunne a hankali yace "Jay" Khaleesat ta zame hijab dinta daga fuska jin sunan da ya kira ta juya ta kallesa, Calmly taji yace "I am cool" tambayarsa Jay yayi ko ya bar Kano, AJ yace "Am still around, when are you leaving Maryland?" After few seconds AJ yace "Alright, we will talk later" Daga haka ya katse wayar ya ajiye ya jinginar da kansa jikin kujerar motar ya kafe titi da ido for almost 2 mins, can ya sake daukar wayarsa don duba available flight to Abuja ranan, yaga jirgin karfe uku kuma saura just few seats, National ID card dinta da passport dake motarsa tun ranan da suka dawo US da drivern su na Lagos ya amsa a wajenta don mata booking ticket to kano, ticket ya siya mata immediately na zuwa Abuja sannan ya ajiye wayar, Aunty na nan gidansu na kano sun zo biki shi sa ma bazai fara kai ta can gidan ba, juyawa Khaleesat tayi da kyar ta kallesa tana dafe kanta pleadingly tace "Kanwar Ummata tana Lagos, don girman Allah ka taimakeni i want to go to her plss" Shi dai kallonta kawai yake, Calmly yace "Where in Lagos?" Tace "Zan kira in tambayeta, amma bani da numberta ne" Ya ga alamar gaba daya she is confuse and in fear, yace "Ta yaya zaki kirata baki da numberta?" Wayarsa ta dauka da sauri ta shiga call logs dinsa tana duba number Baaba Gaje, dialing tayi yana fara ring Baaba Gaje ta daga, da sauri Khaleesat tace "Baaba Gaje don Allah number Aunty Farida za a duba a wayarki sai a turo ta wannan layin" Baba Gaje tace "Har kun je wajen kare hakkin ɗan Adam din?" Khaleesat tace "Ki dai turo min don Allah yanxu Baaba" Baaba Gaje tace "Toh bari in je makota kin san ban san kan wayar ba ai" Khaleesat ta gyada kai da sauri tace "To ina jira" Katse wayar tayi ta jinginar da kanta jikin kujera tana sauke numfashi, wani dishi dishi take gani tsabar kuka, Shi dai Ajay idonsa na kan titi alamar dai kansa ya gama kullewa, ya kalli agogon wrist dinsa yaga karfe biyu ya gota, driving motar ya ci gaba da yi da tunani iri iri a ransa ya nufi wani eatry ya sauka ya shiga ciki, Khaleesat ta dinga bin haraban wajen da kallo sai kuma ta rufe fuskarta da Hijab dinta da sauri zuciyarta na bugawa, incident din jiya ne kawai ke dawo mata a kai as if she is hallucinating, sai taga kamar yanzu incident din ke faruwa yanda Abdul yayi parking ya fita daga mota ya shiga eatry, kan kace me ko ina na jikinta ya fara rawa taji kamar numfashinta zai dauke, ba a dau lokaci ba Ajay ya fito daga gidan cin abincin da leda a hannunsa, yana shiga motar ya ajiye ledan da sauri yana kallonta yace "Me ya faru??" Ta dago kanta hawaye caba caba a fuskarta, sai kuma ta kamo hannunsa gam tace "I just want to leave here plss, don Allah mu bar nan" Gaba daya ta dawo kamar warce ta zauce, ya fara bin area din da kallo tunaninsa ko Abdul din ta gani, can ya sake kallonta bayan ya zauna cikin motar, cikin nutsuwa yace "Look, stay calm.... You are safe" Ya gyara mata kujeran motar a hankali ta yanda zata ɗan kwanta yana kallonta, sai da ya jira for almost 10 mins yaga ta ɗan nutsu tana sauke numfashi a hankali, lkci lkci yake kallon agogonsa saboda flight din da yayi booking, after a while ya ɗan duba fuskarta yaga kamar ta fara bacci, tada motar yayi ya bar wajen, still sai da ya kara tsayawa a pharmacy ya siya mata magunguna, ko kashe motar bai yi ba don kar ta ma san yayi parking, har yaje ya dawo kuma bacci take, ya ja motar ya dau hanyar airport hoping jirgin bazai tashi kafin su isa ba, suna isa airport din bayan yayi parking yaga saura minti sha biyar kawai jirgin ya tashi kamar yanda suka sa a ticket, tapping din kujeran motar yayi gently don har lkcn bacci Khaleesat take, a tsorace ta farka kamar yanda tayi daxu a eatry tana ganinsa kuma tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya, ya bude ledan abincin da ya siya ya ciro mata takeaway din ya bata yace "Take a little before ur flight..." Ba musu ta amshi abincin tana kallonsa a hankali tace "Lagos din zan je?" Yace "In kin je zaki gani" Sai da ya hade mata rai sannan ta ci abincin cokali uku da kyar tana hadiyewa kamar magani, ya bude drugs dinta ya bata ta amsa ta sha da ruwan goran hannunta, without looking at her ya mika mata wayarsa yace "Saka min number mutumin nan" Zaro ido tayi tana kallonsa, yace "Ko bakya ji na ne?" Kamar zata yi kuka tace "Kiransa zaka yi?" Yace "Amsa ki sa min number sa nace" Hannunta na rawa ta amshi wayar ta saka masa lambar Abdul don tana da shi a kanta, ya amshi wayar yana kallon number sannan ya ajiye wayar yace "Dama an mashi alkawarin aurenki ne?" Ta sunkuyar da kanta cikin sanyin murya tace "Um, tun shekara hudu da suka wuce" Shiru Ajay yayi yana kallonta, but because of how cautious he is with time kar tayi missing flight

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login