Showing 225001 words to 228000 words out of 257722 words
Chapter 76 - Halysaah Book 2 By Khaleesat Haydar
har lokacin ta dinga kallonta don tana ganin idanuwanta ta gane bata yi bacci ba daren jiya kuma tayi kuka, Khaleesat ta zauna kusa da ita ta gaisheta cikin sanyin murya, Umma ta jawo ta jikinta a hankali tace "Bana son ki tada hankalin ki Khaleesah, in sha Allahu babu wani abu da zai sake hadaki da Abdul ina nan ina maki addu'a kema ki dage da addu'a kinji?" Hawaye ya cika idon Khaleesat ta gyada ma Umma kai kawai... Aunty Farida na zaune dakin Nenne tana kallonta tana ta koro mata jawabi, Nenne ta kare jawabinta da cewa "Don haka kema ki hada kayanki kala uku ko hudu zuwa nan da gobe mu kama hanya kawai, sam ban ga ta zama ba wallahi Parida, dole ko nawa ne in bada a min addu'a a dauke hankalin tsinannen yaron nan akan jikata ya rabu da ita na har abada, zuwa anjima kuma ki kira min Murja in sanar mata gamu nan zuwa Bauchi gobe, dama ina ta cewa zan je kwanan nan to ga babban dalili zai kai ni yanxu, ke ina ga ma har da Khaleesar za mu tafi don gwara mu je da ita aga warce za ayi ma addu'a ido da ido, in akwai wani taimako da za a bata tayi amfani da shi sai a bata in tsareta tayi, banda Ali ɗan banza ne da wani idon yake son mu kalli yaron nan dake ta mata hidima saboda soyayya, ai sonta yake Ahamad din, to kanin ubanmu ne shi zai mallaka mana kantamemen gidan nan haka babu dalili? Don haka maza mu shirya gobe mu tafi Bauchi mu samo mafita, farkon zuwan Ali furson ai can naje kishiyar Murjan ta rakani gun babanta ya bani taimako, babban bawan Allah ne mutumin a kauyen, kuma gun iyaye da kakanni ya gaji wannan baiwa tasa, in muka ce za mu biye Zahra'u da Ali to fa Khaleesah na cikin gararin rayuwa, miji wawa mata wawiya ga su matsoratan banza, don haka gwara mu rufa ma kan mu asiri Farida kar a mana dariya, naga ke da wayewar ki kuma kina da wayo, sannan hankalina bai kwanta ma ace mu tafi ba Khaleesah ba kar shegen yaron ya sake lallabowa ya dauketa tunda ba addini ne da shi ba, gwara mu je da ita kawai ayi abinda za ayi" Aunty Farida ta sauke ajiyar zuciya tace "To Allah ya kai mu goben Nenne" Nenne tace "Allah ya maki albarka, ku hada kayanku a akwati daya ke da Khaleesar, Ni kuma zan zuba ko a bacco bag ne mu kama hanya" Alhaji Musa ne zaune parlon sa wajen karfe sha dayan safe yana waya, Momy dake zaune ta hakikance kan kujera sai kallonsa take har ya idar da wayar ya ajiye, rai bace tace "Yanxu suna nufin su ce uban yaki amincewa kenan Alhaji??" Alhaji Musa ya sauke ajiyar zuciya yace "Gashi kuwa kina jin yanda muka yi a waya da Deputy, ban taɓa tunanin zai yi turning down din maganar nan ba duba da irin mutanen da suka je har gida suka samesa, idan Abdallah zai yi hakuri ya saka ma ransa salama ina ga zai fi alkhairi, this was the only option I tot will work" Momy tayi mitsi mitsi da ido tace "Amma wannan mutumi anyi tsinannen talaka, ko duba girman mutanen da suka je har gabansa suka zauna bai yi ba, banda Abdul ya nace har yana neman yi ma kansa illa ya ja min asara don Allah yaushe za mu zubar da girman mu da mutuncin mu haka a gaban talaka fakiri?" Alhaji Musa ya sauke ajiyar zuciya yace "Yanxu ke a matsayin ki na uwarsa babu hanyar da zaki bi ki masa magana ya saka ma ransa salama ya mance wannan yarinya ya hakura?" Cike da damuwa Momy tace "Wallahi Alhaji nayi, ba irin yanda ban bi da shi ba a matsayina na uwarsa amma abun yaci tura, ko baccin kirki Alhaji bana iya yi saboda halin nan da Abdul ya jefa kansa kan wannan er talakawan, ace mutum bazai ci abinci ba kullum gashi nan gashi nan dai ne kamar wanda ya fara samun matsala a kwakwalwa to ina lafiya a nan Alhaji? Kar wani abu ya samesa fa mu shiga uku shi Kenan garemu a duniya, shi yasa na kawo maka shawaran ka hada kan manyan abokanka ka nemi alfarman su je maka su samu matsiyacin uban yarinyar amma daga karshe dubi abinda yayi ma masu, nasan su kansu za su ga sun zubda mutuncinsu gaban mutumin da bai wuce drebansu ba" Alhaji Musa dai girgiza kafa kawai yake don shi kansa halin da Abdul ke kokarin jefa kansa ciki ba karamin damunsa yake ba, ya kira Malam Ali yayi sau uku tun ma lamarin Abdul din bai yi worst haka ba amma bai daga kiransa ba bai kuma biyo sa ba, har yayi zuciya ya goge numbersa, da ya ga dai Abdul bazai taɓa hakura ba yasa ya hada kan manyan abokansa ya turasu kamar yanda Momy ta basa shawara amma duk da haka babu wani fruitful result, mikewa Momy tayi ta fita daga dakin ranta a dagule ta tafi dakin Meemah, cike da damuwa tana kallonta tace "Meemah yanxu menene shawaranki akan wannan hali da ɗan uwanki ke kokarin jefa kansa? Yanxu haka fa tun jiya da safe yaki bude daki, ba ci ba sha, ban san wani hali yake ciki ba, tsorona kada wani abu ya samesa fa in shiga uku Meemah shikenan gare ni a duniyar nan" Sai kuma ta zauna gefen gado ta dafe kai ta fashe da kuka sosai, Meemah ta sauke ajiyar zuciya, ita fa ko kadan halin da Abdul ya jefa kansa ba wani damunta yayi ba in dai akan er talakawan can ce, ace duk class da girman kai irin nasa amma kan er matsiyata ya nemi maida kansa kamar mahaukaci zautattace, Cikin rawan murya Momy tace "Wallahi kwanaki da naga abun nasa yaki ci yaki cinyewa har kudi na bada a min aikin da zai maido hankalin yarinyar kansa amma a banza Meemah, in ba dai zuwa zan yi in tone abinda nace maki an bani na binne a garden ba in ƙone su" Meemah ta wani kalleta, can tace "Kema dai wallahi Momy, ki tone me kuma? Don Allah ki rabu da Abdul zai dawo dai dai nasani, lallai ne sai mutum ya samu abinda ya kwallafa rai dama in ba don yaga kuna biyesa ke da Daddy ba, ai abun nasa har da iskanci, ita kadai ce mace a duniya bayan ga mata wa enda ma suka fita komai" Wani tsawa Momy tayi mata tace "Tun ba yau ba nasan baki da imani baki da tausayi Meemah, kuma mugun nufinki akan Abdul sai dai ya kare maki wallahi, in dai dawowar yarinyar garesa ne zai dawo masa da farin cikinsa to ina maraba da hakan wallahi, da nasan wannan abun ne zai biyo baya yaushe har zan raba su ta karfi da yaji?? Ai da sai dai in ta gana mata azaba a gidan nan, amma ina neman rasa yarona akan mace kice kar in damu, to wallahi zan je in tono layun in Kona, sannan in har sato ta ne kadai mafita ni da kaina zan basa shawaran yayi hakan, dama wancan karan ma ai sato ta din yayi daga Lagos, ko ba a daura auren ba ya tafi duk inda zai tafi da ita kawai, yanxu ai jin ƙan ta take budurwa shi yasa zata yi ta iskanci tana rawan kai, kawai na cuci ɗa na a banza a hofi saboda dalilina mara tushe" Tana kai wa nan ta fice daga dakin, Meemah ta wani kyabe baki tana ci gaba da danna wayarta, da wuka Momy ta tafi garden din kamar dai zata yanko vegetables, tayi bake bake ta tona ramin da ta binne layun ta ciro tana kare masu kallo, sannan ta tafi kitchen zata ƙonasa saman gas... Tun da Khaleesat ta sanar ma Jay mutanen da mahaifin Abdul ya aiko wajen Babanta hankalinsa bai sake kwanciya ba kamar yanda nata hankalin ke a tashe tun daren jiya, gaba daya yaji zaman Abujan ma kamar a ƙaya yake, at first bata ma gaya masa ba sai da suna waya da yaji mood dinta da yanda take responding sai ya tambayeta abinda ke damunta shine har ta gaya masa, bayan la'asar Ajay ya shigo daki rike da Glass cup na Smoothie da Ammi tayi masu, ya ajiye ma Jay nasa yana kallonsa yace "Anything?" Jay ya kallesa kamar bazai ce komai ba, after a while kawai ya gaya masa abinda Khaleesat ta sanar masa, Ajay yayi shiru na kusan minti daya after listening to Jay, can ya kallesa yace "I think kawai ka samu Mai martaba da maganar, since Mami ta nuna maka she is fine with ur choice, gobe da safe sai mu koma Bauchi ka gaya masa ta amince.... But i will advise you duk yanda ku ka yi da Mai martaba kar ka gaya ma Mami, don nasan shi idan ya tashi zartar da ko wani hukunci sai ya gama zartarwa yake sanar da kowa" Jay dake kallonsa yace "Amma me yasa kace kar in gaya ma Mami yanda muka yi da Mai martaba?" Ajay yace "Just an advice, Ina ga kamar in baka gaya mata ba process din zai fi tafiya smoothly kuma da sauri, baza a tsaya wasu sirfa ba or anything of such, You know our mothers and exaggerating of things" Jay dai yayi shiru bai ce komai ba, Ajay ya ɗan yi murmushi yace "Dama nasan gayen nan bazai hakura ba, and he can do anything silly, I don't even think she is safe in kano...."
*Halysaah is 500 via 3276052019 fcmb Hauwa Bello Jiddah* ur evidence via 07087865788
*TAKAICIN UBA…….*
Na
Nazeefah Sabo Nashe.
08033748387.
8….
Masu buƙata daga farko su yi following channel ɗinmu.
https://whatsapp.com/channel/0029Va5fqs7E50UpMpXolU1T
Driving yake yana sauraron Karatun Alkur’ani daga k’ira’ar sudais. Shi ka’dai ne abinda yake saurare ya rage masa zugi da ra’da’din rashin Hibbarsa. Ko da ya yi parking a makeken wajen shak’atawar kasa shiga ya yi ya shiga cusa hannayensa cikin tarin sumar gashin kansa da ya gadota daga gurin Ummeeynsa. Ya dinga cukuikuye gashin yana jin kansa na sara masa kafin ya mayar da seat ‘din kujerar ta sa ya koma ya kwanta tunanin rayuwarsu da Hibba na sake bujiro masa….
K’arar da wayarsa ta yi ne ya farkar da shi daga wancan tunanin, ba sai ya kalli screen ‘din wayar ba ring tone ‘din ya sanar da shi wacece ‘Ummeey’ ya fa’da yana sakin murmushin gefen kumatu kafin ya jawo wayar ya kanga a kunnensa. Cikin muryar shagwab’a kamar yarda ya saba mata magana ya ce “Hayateey!” Ummeey daga ‘daya gefen ta saki murmushi tana jin da’din sunan da yake kiranta da shi. “Amin ya gida hope dai kana lafiya, muma kwanan mu uku a Nigeria.” Ya ‘dan yi dum da waya a kunne kafin ya ce “Nigeria kuma how comes? Ya aka yi Abeey ya barku kuka je?” Dariya ta yi sosai kafin ta ce “Da kansa ya sauko ya ce mu je. Yauwa ba wannan yasa na kira ka ba, Amin bu’de kunne da kyau ka ji lokaci ya yi da ya kamata ka yi aure.” Wani irin dum ya ji k’irjinsa ya buga, Ummeey zata sake janyo masa wani jidalin kenan shi tun yaushe ya cire maganar aure a rayuwarsa, ya Riga ya gama da wannan babin an gama samun mata na gari tun bayan da Hibba ta rasu. “Ba ka ji ni ba ne?” Ummeey ‘din ta fa’da with a serious tone. Sakin ajiyar zuciya ya yi kafin ya ce “Na ji Ummeey, amma ina neman alfarma, not now please, wallahi ban shirya aure ba, ko kuma na ce na gama buk’atarsa a rayuwata tunda dai Hibba ta haifa min mai yi min addu’a.” Cikin b’acin rai Ummeey ta ce “Ko da nice nake so?” Muryarsa a cunkushe ya ce “Don Allah Ummeey a bar maganar, please!”
“Ka yi k’arya kuwa in bar maganar aure, haka kawai da ranka da lafiyarka in dai ba mu’amala kake da matan banza ba ai ya kamata ace zuwa yanzu ka ajiye iyali, don haka magana ‘Daya da zan maka na samar maka mata y’ar aminiyata ta yarinta da nake yawan baku labarinta wato TALATU, don haka umarni na baka ba shawara ba..” kafin ya ce komai ta katse wayar don ta san idan ba haka ta yi masa ba,
Ba zai ‘d’au zancen serious ba.
Gaba ‘daya ji ya yi zuciyarsa ta karye, ya tabbatar tunda ta fa’da ‘din sai ta cika alk’awarinta. Ya runtse idonsa yana tunanin menene mafita? Wannan karan kam ya zama dole ya bijirewa umarninta, shi kam da zata bar shi haka ma tsaf zai iya rayuwarsa har ya koma ga lillahi babu aure. Wajen shak’atarwa da bai shiga ba kenan, ya da’de a zaune a motar kafin ya ja motar da sauri ya fice daga garden ‘din.
____________
Tun Asuba da ta mik’e bata farka ba, ta shiga gyaran gidan da abincin da ta san Amma ta fiso, gurasar larabawa da alkubus sai kunu da k’osai. May be idan Amman ta ga wannan hidimar da ta mata ta sassautawa zuciyarta daga fushin da ta tsiri yi da ita tun jiya da bak’uwarta da ta kira bak’ar bak’uwa ta zo gidan.
Sai da ta jera kayan akan dinning table da taimakon mai aiki. Sannan ta kunna sunnah t.v tashar da ta san Amman ta fi muradin kallo a koda yaushe.
Tsaf ta fito cikin shigar alfarma. Ta dinga bin falon gidan da kallo ganin yarda aka canja masa tsari. Ga dadda’dan k’amshi da aka baje falon da shi, na abinci da na k’amsashshen turaren wuta mai sanyaya ruhi na mutanen chad. Murmushi ne ya so sub’uce mata sanin cewa Ayra ce duk ta shirya hakan sarai ta san neman sulhu take tun jiyan tana lura da ita fushin da take da ita yana damun zuciyarta, sai dai ba zata bari ta fuskanta ba.
Ta zauna tana sake addu’ar fatan alheri ga Ayran kamar yarda ta kwana tana yi a cikin sujuda, ji take kamar warwarar matsalar Ayran ce ta zo. Ita kanta ta ji tana son Ayran ta yi wannan auren ko da sonta ko ba son ranta.
Tana jin takun tafiyar Ayran, ta kawar da waccan fuskar tata mai yalwar fara’a ta saka wacce ta aro tun yammacin jiya, mai wuyar kallo a wajen Ayran mai fa’dar mata da gaba da sakata ‘dimuwa. Zuciyar Ayra ta buga sosai ganin har a lokacin waccan caku’da’ddiyar fuskar tana nan tare da ita. Ta yi k’asa da kanta tana jin yarda zuciyarta take bugu a hankali take furta ‘Wannan bak’uwa ta cuceni na shiga uku, ban tab’a ganin fuskar mahaifiyata a haka ba kamar yau.’
Jiki a sanyaye ta isa gefen Amman kamar yarda ta saba ta rab’a jikinta da nata a hankali ta bata sumbata a kumatu “Ammaty Ina kwana?” “Lafiya” ta fa’da tana sake ‘d’aure fuskarta sosai, Ayran gabanta ya fa’di sosai ganin ba sassauci da da ne sai ta janyota itama ta ha’da goshinta da nata kafin ta ce “Lafiya lau Auta ta, kin tashi lafiya.” Ta dinga wasa da hannunta kafin murya a raunane ta ce “Amma I cooked your favourite dish.” Ta ‘dau tsawon lokaci kafin ta yi jarumta ta kawar da tausayin Ayran daga ranta ta ce “Ana sa’im.” Ayran ta dinga kallonta wani iri kafin ta ce “Sa’im kuma Amma? Yau fa laraba idan ban manta ba.”
Zuciya a dake ta ce “Na sani. Kuma ki k’yaleni haka bana son magana.” Tuni idanun Ayra ya fara tsiyayar da hawaye ta dinga bin ta da kallo kafin ta fashe da kuka ta fa’da kanta. Amman bata hanata ba amma fa bata saka hannu ta rarrasheta kamar yarda ta saba ba. Duk da zuciyarta tana bugu haka ta mayar da idanunta kan T.V a zahirance kallon take amma a ba’dinance kukan Ayra ne yake tsaya mata a zuciya. Ta da’de tana kukan kafin Amman ta saki ajiyar zuciya ta ‘dago kanta. Idanunta cikin nata ta ce “Saurareni Ayra, idan kina son ganin walwalata ya zama dole wannan karan ki yi ya’ki da zuciyarka ki amincewa auren nan, idan ba haka ba kin bar ganin walwala ta. A kullu yau min ina gaya miki ba duka maza ba ne halinsu ‘daya akwai wa’danda halinsu ya Sha banban da na mahaifinki yanzu yayyenki ba duk sun yi auren ba, duk da ta ki k’addarar ta fi ta su girma, kada ki manta ni kaina idan na tuna lamarinki abin yana min ciwo wani lokacin kwana nake ban yi barci ba saboda tsananin b’acin rai kuma ma ba wannan ba, ki tuna wani abu ‘daya mana yau ace na mutu na barki ina za ki kama? D’an uwana ‘daya tak da nake da shi kina ganin dai shekaru ashirin ba mu ji labarinsa ba, aurenki fa shine abinda ya fi cancanta..” Hawaye take idanunta ba k’akkautawa ita Kanta Amman danne zuciyarta take bata bayyana nata kukan ba, amma wanda take yi a zuciyarta ya fi na Ayran yawa ya fi shi kuma ciwo. Ayran da sauri ta mik’e ta shige wani k’aramin falo da yake k’asa. Kuka take sosai tana tunanin ina ma zata iya da ta amincewa aurennan tunda yanzu ta lura burin Amma gaba ‘daya ya tattara ga son aurar da ita, sai dai ina har a lokaci zuciyarta bata karkata da neman rushewar wancan adawar da takewa aure ba, ba zata iya ba ba zata iya ha’da makwanci da namiji ba…. Ba zata iya bawa namiji lokacinta ba balle ta masa girki ko ta nuna masa wata kulawa Menene Mafita? Shine kawai abinda take tunani ta runtse idanunta kawai tana hango wata mafita da take tunanin ita ce zata tserar da ita daga wannan auren ba tare da kowa ya zargeta ko ya k’alubalanceta ba…. Ta dinga sakin ajiyar zuciya tana jin cunkoson b’acin ran da zuciyarta ta yi tana warwarewa hankalinta ya kwanta ta mik’e tana ka’de jikinta….
________________
Magriba sakaliya ya shiga gidan nasa. Alh.Sulaiman turaki ya