Showing 249001 words to 250533 words out of 250533 words

Chapter 84 - Kurkukun Kaddara Book 2 Middle Steps By Boss Bature.

18 Feb 2025

116531

damar shigowa estate dinmu dake acike da tsaron sojoji da ƴan sanda”? Zayn ne ya kora jawabin.
Pravin ya ta6e baki haɗi da cewa”macijin fa mutunne wai ya rikide, acewar shi owais....”tunkan ya ƙare maganar, zayn da zaid suka kalli juna da alamun al’ajabi.

“Tayaya haka zai yiwu? Kamar dai ashirin film, ko atarihi ni ban ta6a jin mutun ya rikiɗa ya koma dabba ba” acewar zaid.

Pravin yace”ai shine muma abunda ya ɗaure mana kai, ni dai nafi tunanin yaron aljanine ko kuma wasu miyagunne da suke son cutar da kakanku suka yi amfani da sihiri a jikin yaron donsu kashe shi”
Hankalinsu zayn ba ƙaramin tashi yayi ba, jikinsu har tsuma yake yi,
“Ku shiga daga ciki, ku duba jikin baban naku, Sauran uncles dinku suna a cikin dakin, idan kun shiga ku tayasu jimamin abunda ya samu babanku, sannan please kada ku goyi bayan yaron yaci gaba da zama a estate din nan, tunda shi owais din bai san ciwon kanshi ba, idan ba haka ba taya zai ɗauko mugun abu ya ajiye agidan shi da sunan taimako”? Ranshi amatuƙar 6ace yayi maganar.

Zayn daya gama harzuƙa yace”wallahi bazai yiwu ba daddy, wannan ai ba maganar da hankali zai ɗauka bace, in banda an rainawa mutane wayau taya za’ace wai mutun ya zama maciji? Kuma ya rasa inda zai farmaka sai gidan baban mu, bayan ga sauran gine ginen dane akusa dana shi owais din duk ya tsallakesu Ya nufo nan so ake kawai akashe mana shi, dama ya lafiyar giwa, ga mahaifiyarmu itama da firgici ta kwana bazan lamuntaba dole mu dauki mataki....” Yana huci ya ƙare maganar.

Cikin sanyin murya zaid yace”Allah ne kadai yasan dai dai, kada mu yanke hukunci cikin fushi, bayan bamu da masaniya akan wanene yaron? Menene silar canza halittar shi, da son ranshi ko kuwa ƙaddarace ta afka mashi, duk waɗannan amsoshin zamu same su abakin Yayanmu owais tun da shi yasan komai dangane da yaron....”tunkan ya ƙare maganar, Pravin yai hanzarin katse shi da cewa”babu wata hujja da zamu jira zaid, ka duba kaga fa yadda ya siye zuciyar kawunku Hateem, meye alakarshi da yaron da har zai tura da jet din da zai dauko sheikh imam daga sudan, duk irin manyan malaman da muke dasu A nigeria, basuyi mashi ba sai da ya kashe makuɗan kudi don a dauko mashi sheikh, don baku agidan macijin ya kawo farmaki da baka furta maganar da kayi ba ayanzu, badan Allah yasa Owais Ya kau da macijin ba da tuni Ya sari kakanku saboda shi kadai yake kokarin kaima hari” jin wannan maganar yasa zaid shan jinin jikinshi
“Inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un, wannan wace irin masiface daddy? In sha Allah koma su wanene miyagun da ke son ganin bayanshi bazasu ta6a yin nasaraba, sannan Nima na goyi bayan a kori yaron daga estate dinmu” gyaɗa kai pravin yayi”yanzu naji magana my son”ya faɗa tare da dafa kafadar zaid din”ku shiga dakin baban, Ni yanzu zan je nataho da mahaifiyar taku”Amsa mashi sukayi da toh, kafin suka nifi ɗakin baba obie suka shiga da sallama abakunansu.

*HAJIYA SARATU❤*

Fitowa tayi daga bathroom, jikinta sanye cikin bathrobe fara ƙal, wanka ta samu tayi don taji daɗin jikinta, don tun da safe data farka bata motsa daga kan gadoba saboda fargabar abun da ya faru jiya da kuma damuwar da pravin Ya haddasa mata.
Agaban mirror ta tsaya fuskarta babu walwala, idanuwanta sun ƙanƙance saboda rashin baccin da batayi ba a jiya, hatta kanta ciwo yake yi mata.
Expensive body lotions dinta ta soma shafama skin dinta, bayan ta kammala ta nufi closet din kayanta, jim kaɗan ta dawo harta cire rigar wankan ta maida doguwar riga bubu ta material, turare ta dauka ta feshe jikinta da shi.
Kafin ta kammala wayar ta dake ajiye kan pillow ta soma ringing, yamutsa fuska tayi kamar bazata ɗaga kiran ba, ta nufi wayar ta duba sunan me kiranta, ajiyar zuciya ta sauke kafin tayi picking call din
Ko sallama batayi ba ta furta”daughter, sai yaushe zaki shigo gida”?
On the other hand muryar faryat ta ratsa kunnanta

“Mommy, tun jiya nayi niyar shigowa in kwana anan part dinku, Zulaihat ce ta ruƙe ni wai dole saina kwana a gidansu, mom madina ma tace in tsaya in kwanar masu shiyasa kika ji ni shiru kuma ma bani kaɗai bace, hada su Yusra duk muna agidan”

Ta6e baki hajiya saratu tayi”okey, duk lokacin da kika ga damar shigowa ina jiranki,” faryat ta amsa mata da toh, kafin sukayi sallama, Landline din kitchen ta danna ma kira, Bugu uku Abla tayi picking call din
“Jira kuke yi sainace akawo min breakfast dina”? A faɗace tayi masu maganar
Cikin girmamawa abla tace”Ina bada haƙuri aunty, Yanzu nan zan shirya maki” guntun tsoki taja tare da katse kiran ta wurga wayar kan mattress.

Bakomai take tariyowa ba face Rashin mutuncin da pravin yayi mata, Ya ƙona mata rai adaren jiyan nan, wai har ita zata kirashi yaƙi zuwa sannan yayi rejecting call dinta? bata motsa daga gaban mirror din ba, ƙarar knocking din ƙofa Ya katse mata zancen zucin nata
Sai da ta mula tasha iska tukunna ta furta”Come in” muryar abla da ƙarfi ta furta”Aunty ƙofar a kulle take” tunawa tayi da ta datse dakin jiya ta ciki, juyawa tayi taje ta buɗe ƙofar, shigowa abla tayi hannayenta biyu ruƙe da wooden tray daga saman shi kayan breakfast ne.

Wuce wa ciki abla tayi, ta daura tray din kan table, Kafin ta juya tana fuskantar hajiya saratu data ruƙe qugu da hannu ɗaya, har saida taji gabanta ya faɗi ganin 6acin ran dake kwance akan fuskarta, cike da jin shakkarta ta furta”ko akwai wani abu da kike buƙata”? Atsiwace hajiya saratu tace”ke nake buƙatar ki fuce min daga ɗaki, kin wani tsareni da ido kina kallona kamar yau kika fara gani na” Jiki na 6ari Abla ta nufi ƙofar fita daga ɗakin bayan ta fuce hajiya saratu ta nufi gefen gadon ta zauna, ta soma cin breakfast dinta, farawa da bismillah kakkauran tea ta ɗauka ta kur6eshi dukanshi, kafin ta rarumi roasted chicken takai baki tana cizgarta atsiyace, daɗina da hajiya saratu damuwa bata hanata cin abincin, adai dai lokacin da ta ɗauki burger da hannu biyu ta gutsireta da baki, Muryar pravin ta dakatar da ita daka taunar burger din da takeyi, lokaci guda yanayin fuskarta ya canza ta haɗe rai kamar baƙin haɗari.

shigowa ɗakin yayi fuskarshi ɗauke da murmushi, yasan tsiyar daya tsula mata shiyasa yake jin shakkar tunkararta
Daga nesa da ita ya tsaya haɗi da goya hannayenshi on his chest cikin muryar lallashi ya furta”My wife, ina neman afwarki, dan Allah ki yafe min nasan ban kyauta maki ba, duk da ba laifina bane, laifin ki ne saboda kece kikaja nayi maki hakan, kin nuna bani da mahimmanci awurinki...” kau da idonta tayi daga kallon fuskarshi, taci gaba da cin burger dinta ta share shi kamar batasan da zaman shi ba.

“Dan Allah kiyi min magana sanyin idaniyata, kamar yadda na 6ata maki rai nima haka raina ya 6aci, saboda tunanin awani hali kika kwana jiya ko runtsawa banyi ba, nayi kewar rashinki atare dani, da pillow na kwana rungume a kirjina ina jin tamkar kece na rungume”

fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yayi mata maganar, duk don ya samu ta yafe mashi, burinshi ta aminta dashi su sasanta tsakanin su, duk don ya tunzurata akan maganar macijin daya tsoratar da ita jiya, yasan muddin saratu ta ƙyamaci zaman yaron a estate dinsu dole kowa ya amince saboda ƙaunar da yayyanta su ke yi mata.

“Bugun zuciyata, please ki kula ni mana, bana son sharenin da kike yi, wallahi ashirye nake dana kar6i duk wani horo da zaki bani ni kawai so nake mu sasanta tsakaninmu bana so kina fushi dashi” ƙara ɗaure mashi fuska tayi batare data juya ta dube shi ba.
Zuƙunna pravin yayi, tare da kama kunnansa Ya soma yin tsallan kwaɗi Yana nufar gaban table dinta Yana fadin”Am sorry my wife, nagane kuskurena bazan ƙara ba”
Tunkafin Ya ƙaraso gabanta, ta tsiyaya ruwan lemu acikin cup mai sanyi, ta ruƙe a hannunta, Yana zuwa dab da table din ta daddage ta watsa mashi ruwan lemun saman fuskarshi, da sauri ya runtse idanuwanshi jin raɗaɗin da ya shigar mashi, burger ta ɗauka ta yunƙura ta kifa mashi ita a fuskarshi, tunda tayi mashi hakan sai taji sauƙi acikin ranta, komawa tayi ta zauna tana dubanshi tace”Ina fata ka tashi lafiya” shiru pravin bai furta komai ba, ƙoƙarin buɗe idanuwanshi yake yi sai dai ya kasa, shu’umin murmushi hajiya saratu tasakar mashi tare da cewa”malam, ka tashi ka shiga toilet ka wanke fuskarka,” babu musu pravin ya miƙe kamar makaho Yana laluban hanya daƙyar ya gano ƙofar toilet......”


*✊💋ALHAMDULILLAH, END OF MIDDLE STEP, FATA NA SHINE ALLAH YA BANI IKON KAMMALA TAKUN ƘARSHE LAFIYA KAMAR YADDA NA KAMMALA TAKUN FARKO DA TAKUN TSAKITA💋✊*

(Domin neman ƙarin bayani a tuntu6i layukan mu (08103884440 0r 08169856268)


Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login