Showing 72001 words to 75000 words out of 245004 words
Chapter 25 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
bayan kai baka isa ka hana kanka mutuwa ba?
Kafin Abbansu yace wani abu muryar kanal yusif ta katse su da cewa "Abba ka matso kusa mutane suna son magana dakai,"
Amsa mashi yayi da "toh gani nan zuwa" sannan ya kalli ayaan yace "Abun dayasa na tambaye ke game da junaid kasan halin shi, muddin ya fito yaga halin da fawan ke ciki tofa zai iya sume wa ko ya zauce, dan Allah kusan yarda za'ae ku hana shi fitowa daga ɗakinsa indae yana ciki,"
Ayaan yace "Shikenan abba bari naje na duba shi," cikin sauri ayaan ya wuce upstairs ɗakin junaid, a hankali ya tura ƙopar ɗakin cikin sanɗa ya shiga, abun mamaki samun shi yayi saman gadon shi zaune ya toshe kunnan shi da headphone yana kallo acikin laptop ɗinsa baya jin duk wata hayaniya da akeyi acikin gidan,
Murmushi Ayaan ya saki sannan ya ƙara ja mashi ƙopar ɗakinsa dakyau ya rufe masa ita, sannan ya juya ya sauko down wurin su,
Har wurin dare mutane suna ta zarya agidan sai wuraren ƙarfe 9:30 sannan suka fara raguwa, tuni Sgr ya wuce part ɗinsa saboda ya gyara jikinsa ga matuƙar gajiyar da yayi idonsa ma kansu daƙer yake buɗesu ga yunwa ga bacci, har lokacin zuciyar shi tafarfasa takeyi duk in ya tuna irin artabun da su kayi tare da miyagun nan, duk da sunci nasara akansu sosai, bakomai bane ya tsaya masa aran shi ba face wannan maganar nace wa macace take ɗaukar nauyin tawagar miyagun dake kashe-kashen, yaci alwashin cewa sai ya gano ko wacece ita,
yanayin salon nata ya nuna cewa hada ɗaukar fansa take yi,' 😳😳😳
A asibiti marshal omar ya barsu hussana a hannun Camila kafin zuwa da safe zaisa a sallame su,
shi da major suka wuce izuwa gida saboda kiran wayarsa da ake ta faman yi ga kuma tsananin damuwar daya shiga game da halin dasu Fawan ke ciki,
daker sehrish tasamu ta fito sam tagaza samun natsuwa ta ko ina, ta damu da yanayin da taga Sgr da kuma halin da fawan ke ciki, a ƙopar ɗakin azmee ta tsaya sannan ta kwankwasa tare da jiran ta buɗe mata,
tana tsaye azmee ta bude ƙopan tana kallonta tace "kin gama kukan?
Shiru kawai tayi tana wasa da yatsun hannunta,
"hmmmm me kike yi ma kuka ne ɗazu"?
Cikin sanyin murya tace"babu komai Aunty azmee kawai nadamu ne da halin dana ga fawan,'
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "gsky yaji jiki sosai, nima na tausaya masa bawan Allah, Yakamata muje mu duba shi, dama na jira ne mutane su ɗan rage sosai,"
Sehrish tace "ae nagama babu kowa a falon bansan inda suka kai shi ba,"
"Sun kwantar dashi ne, a ɗakin da suke kwantar da mara lafiya, bari nazo mu tafi tare, inyaso in mun dawo sai mu jera masu dinner ɗin duk da nasan abune mai wuya ma a samu wanda zai iya cin abincin, don duk suna cikin damuwa," tana fadin haka tashige cikin ɗakin bada jimawa ba ta fito sanye da mayafi, sannan suka jera da sehrish izuwa ɗakin dake anan downstairs,
A buɗe suka same shi don haka su kayi sallama, muryar kanal yusif ce ta amsa masu tare da cewa "ku shigo ciki mana,"
shiga ciki sukayi sehrish har tsoran kallon jikin fawan takeyi, wanda ke kwance saman gadon idonshi arufe alamar ya samu bacci,
Ayaan da jahad ne zaune daga gefen gadon sai kanal yusif dake atsaye,
Azmee tace "Yusif ashe haka abu ya faru? Mu ba mu sani ba"!
Kanal yusif yace "Wlh kuwa aunty azmee abun babu daɗin ji, ƴan ta'adda ne su kayi masu kwanton 6auna, amma anci nasarar Cafke wasu daga cikinsu,"
Cikin nuna jimami aunty Azmee tace "Allah ya kiyaye gaba, ya tonu asirin waɗannan mutanen, wlh duk jikina ya mutu dana ga fawan acikin wannan halin bawan Allah, Allah dae ya tashi kafaɗunsa,"
Suka amsa mata da ameen, sai lokacin sehrish tace "Yaya yusif ya mai jiki"?
Yace "Alhamdulillah da sauƙi sosai harma ya samu bacci,"
Tace "Allah ya bashi lafiya,"
"Ameen ," suka amsa mata
Kanal yusif yace "Aunty azmee ku matso kusa dashi kuyi mashi addu'a yana buƙatarta sosai," matsawa su kayi atare kusa da fawan suna yi masa addu'a tare da tattofa masa, daga bisani su kayi masu sallama suka fito waje
Kitchen suka wuce atare don sun shirya abincin dining azmee tace "bari na haɗa maki, ki kaima babban yayansu nasan zai buƙaci wani abun,"
"Toh," ta amsa mata, suna cikin kitchen ɗin haroon ya shigo cikin babban falon daga waje ya shigo ciki hango sehrish da yayi yasa shi wuce wa cikin kitchen ɗin, kamar yarda ya saba fado masu batare da sallama ba haka ya shiga,
ɗagowa su ka yi suna kallon shi hankalin shi kwance tamkar baisan meke faruwa ba, azmee tace "haroon me kake buƙata ne"?
tsoki ya ɗan ja tare da cewa "tun yaushe nake ta faman zarya ina jiran a jera mana abincin dare amma shiru babu, so ake akashe ni da yunwa ne"? yayi maganar fuska aɗaure yana kallon sehrish wadda tuni ta kawar da kanta,
Azmee tace "kayi haƙuri haroon, saboda halin da su fawan ke ciki ne ga kuma mutane shiyasa ba mu samu damar fitowa ba mun jera,"
Uban tsoki ya kuma bugawa wanda har sai da suka ɗan razana suka kallesa yace "And then so what? Mutuwa fawan ɗin yayi ne da zaku fake da cewa halin da yake ciki ya hana ku jerawa mutane abincinsu"? Ya tambaya a ƙule
Mamakine ya kamasu jin abunda yace yadda ya nuna ko ajikinsa halin da fawan ke ciki,
nuna sehrish yayi da hannu tare da cewa "Ke! ki kawo mun abinci na yanzun nan a bedroom ɗina ina jiran ki,
Cikin sauri sehrish tace "Ni babban yaya zan kai mawa yanzu, sai dai ko in aunty azmee ta jera a dining ka zauna ka ci,'
Zaro ido haroon yayi afusa ce yace "Ke! Ni kike fadama cewa wani wai babban yaya zaki kaima abinci"? Ke ga futsararra ko"? ya tambaya yana faman huci
da ido azmee tayi ma sehrish alamar tayi shiru da bakinta, tsit tayi bata kuma cewa komai ba,
cike da bada umarni yace "Ina jiran ki ki kawo mun idan kuma ba haka ba zaki ga mai zai biyo baya," yana faɗin hakan ya fuce daga kitchen ɗin,
Murya tamkar zatayi kuka tace "Aunty azmee nifa bazan kai masa ba Allah,"
Azmee tace "sehrish ki daure ki kai masa, nikaina na tsorata da yarda yake mana magana, ina tunanin kamar yayi shaye-shaye ne baya cikin hayyacinsa,"
"Aunty azmee nifa bazan kai masa ba,kema da kan ki kince baya cikin hayyacinsa yanzu in naje zai iya kai mun bugu,"
ganin ta dage akan cewa ba zata je ba yasa Azmee cewa "to shikenan bari ni nakai masa, ke kuma ki kaima Sgr nasa," ajiyar zuciya sehrish ta saki tare da cewa "to,"
bayan sehrish ta kammala shirya masa a tray ta wuce upstairs part ɗinsa, sallama tayi ba'a amsa ba don haka tashiga daga ciki, babu kowa acikin falon alamar yana a cikin bedroom ɗinsa,
takawa tayi izuwa ƙopar bedroom ɗin nasa tayi masa sallama kusan sau uku sannan ya amsa mata da cewa"Come in,"
Shiga ciki tayi zuciyarta na dar-dar lokacin da ta aza idonta akanshi yana zaune gaban dressing mirror saman chair din dake gaban madubin, ya sanya tafin hannayensa ya tallabo gefe da gefen fuskarsa ya zabga tagumi agaban mirror, sam babu riga ajikin shi daga shi sai short green colour, da alama ma daga wanka ya fito yagaza yin komai shine ya zabga tagumin, Sumar kanshi duk ta barbazo ta rufe masa gefen face dinsa, da wasu siraran gashi da suka sauko ta saman fuskarsa idonshi na arufe saboda gajiyar da ta lullu6e ga66ansa da kuma baccin da yake ji ga kuma yunwa duk shi kaɗai
tsayawa sehrish tayi jiki asanyaye tana kallon shi tsananin tausayin shi ne yakamata ganin yarda ya zabga tagumi da hannayensa biyu, alamar baya jin daɗi
Ta jima tana kallon shi kafin ta ɗanyi gyaran murya tace "dama abinci ne na kawo maka, bansan ko kana buƙata ba," ta fadi adan tsorace gudun kar tayi kuskure a maganarta,
daker ya buɗe bakinsa tare da cewa"keep it on the table, then i wanna see u," gabanta ne ya faɗi rass ! jin abunda yace na yana son ganinta ƙarasawa tayi ta ajiye masa dinner din saman table ɗinsa, sannan ta matsa kusa dashi ta tsaya sannan tace "gani,"
Hannu yasa ya ɗauko wata ƙaramar kwalba ta magani daya ajiye a saman mirror din sannan ya miƙa mata tare da cewa "rub it on my back," ya fadi tare da kifa kansa saman gaban mirror ɗin yadda zata samu damar murza masa maganin,
tama rasa ta ina zata fara shafa masa shi, gaba daya duk tabi ta rikice wai yau itace sgr da kansa ya bata magani don ta shafa masa abayansa, jikinta har kerma yakeyi tsoranta kar ta fasa masa fatar bayansa saboda hasken fatar fes tamkar in kasa yatsa jini zai fito,
Matsawa ta ƙara yi dab dashi sosai sannan ta buɗe mufin kwalbar, tasa yatsa ta lakuto maganin tare da ɗan russinawa ta lakuta masa shi abayan, sannan tasanya hannunta a hankali tana shasshafa masa shi, tun da Allah ya halicce ta bata ta6a jin skin mai tsananin laushi da daɗin tabawa ba irin fatar bayan sgr,
Shi kuwa ajiyar zuciya kawai yake saukewa saboda relief daya fara samu sosai na ciwon da ga6o6insa suke masa, tun sehrish nayi masa da hannu ɗaya har takai ga ajiye kwalbar maganin ta sanya duka hands ɗinta a faffaɗan bayansa tana yi masa massage, a tunaninsa in ta kammala zata cire hannunta ne, amma sai yaga ta zarce gaba ɗaya babu alamar zata daina shafa masa gashi kuma yaji ko'ina na bayansa yaji maganin sosai, shiru kawai yayi bai ce komai ba, almost one hour kenan sehrish na shafa masa magani har sai da ya ɗan ɗago da kansa daga kwancen da yake tare da cewa "Har yanzu maganin bai shafu bane"? Cikin sauri ta janye hannunta tare da ɗagowa tana kallonsa suka haɗa ido ta cikin mirror,
gabanta ne taji ya ƙara faɗuwa rass ganin yarda kwayar idonsa ke shining sai taga tamkar tana canza launi ne daga blue zuwa green,.
sunnar da kanta tayi ƙasa tana faman haɗe yatsun hannunta dake dankare da maganin data shafa mashi,
lumshe idonsa yayi tare da sake buɗe su yace "kin haɗo mun da coffee ne? ya tambaya a kasalance hakan ba ƙaramin kashe ma sehrish jiki yayi ba, tuni ta nemi natsuwarta tarasa sai ta kama en ena tana faman wurwurga ido
"Its ok, idan babu akawo mun shi," ya faɗi tare da mayar da idonshi ya lumshe su,
Juyawa sehrish tayi cikin sauri ta fuce izuwa kitchen donta haɗo masa, a lokacin har azmee ta kammala shirya masu abincin dinner ɗin a dining amma babu kowa asaman shi alamar basu kaiga fitowa ba,
tayi mamakin hakan duk da tasan cewa duk suna cikin damuwa ne,bata ji daɗin hakan ba, tasa ba ganin mutanen gidan cikin raha suna nishaɗi suna cin abinci yau kuma wayaam babu kowa, Yau da gobe kenan,
tana acikin kitchen ɗin bayan ta kammala haɗa masa coffee din ta ruƙo cup ɗin a hannunta, sai ga haroon ya faɗo mata kamar daga sama cikin sauri taja da baya hankalinta atashe, daga shi sai vest da singlet, shu'umin murmushi ya saki yana kallonta yace "ke shine nasa ki kaimun abinci kika ƙi ko? Ke ga isassa mai walkin sa harni ɗan masu gida zan saki aiki, ki bijire mun," ya faɗi yana kallonta
Murya na rawa sehrish tace "kayi hakuri dama na fara kaima babban yaya ne, kafin na kawo maka nakan......'
Bata ƙarasa ba ya katse ta da cewa "Sorry for your self sehrish! wlh kin shiga uku ! kin jefa kanki cikin masifa, daga rana irin ta yau inaso kullum ki kasance cikin yin sallar dare kina rokan Allah akan ya kare ki daga Sharrina," zaro ido tayi tana kallonsa jin abunda yace cikin tsananin tashin hankali tace "saboda me zaka ce haka"? laifin me nayi maka, dan Allah kabarni inyi rayuwata cikin salama,"
Fashewa da dariya yayi kafin ya tsagaita da cewa "kinsan wani abu?kina da kyau sosai musamman idan kika tsorata idanunki ba ƙaramin fizgata sukeyi ba, idan kika amince a shirye nake dana aure ki, kuma zan shiryu nadaina duk wani abu da nake yi, amma idan kika bijire mun I pity u wlh," cikin sanyin murya yake yi mata magana,.
Tamkar zatayi kuka tace"Dan Allah na roƙe ka kayi hakuri nidai ka fita daga cikin rayuwata, kabarni dan Allah kaje can ka samu mace irinka ka aura, amma ni ina da wanda nake so," tayi maganar tare da bi ta gefensa gabanta na faduwa ta wuce cikin sauri,
murmushi kawai haroon yayi tare da jinjina kansa aransa yace "nasan ba kowa take hari ba face wancan mai zubin ifritan, ni kuma ba zan ta6a bari hakan ta faru ba, target ɗina na farko da zanyi zan fara 6ata sunanki ne a wurinsa," yana fadin hakan ya saki shu'umin murmushi tare da wuce wa room ɗinsa
Maganganun da haroon ya faɗa mata sun tsaya mata arai, tunaninta ya rayuwarta zata kasance nan gaba acikin gidan batasan me haroon zai yi mata ba,
tana tunanin tana tattaka stairs ɗin jiki amace, adai² lokacin Marshal ya shigo gidan cikin sauri saboda yarda yake agajiye shima, har sai da ta juyo daga saman stairs din ta ɗan kalle sa, ta other side ɗin yabi ya wuce part ɗinsa da hanzari sam bai lura a ita ba,
bakomai bane ya faɗo mata arai face yaran da taji yace zasu zauna gidan Uncle Abusufyan ɗinsu, ko ya ɗauko su? ta tambayi kanta
cikin sauri ta wuce part ɗinsa bedroom ɗinsa ta shiga da sallama ya iznin shiga, a lokacin harya dawo gefen bed ɗinsa ya zauna yana cin abincinsa, yau ba sai ya jira anyi saving ɗinsa,
ƙarasawa tayi kusa dashi sannan ta samu wuri agefen plate ɗin abincinsa ta ajiye masa cup ɗin,"
A hankali ya furta "thanks,' a tunaninsa zata tafi amma sai yaga tayi masa tsaye akansa, sam bata son ta tafi tabarshi saboda a ganinta in ta tafi bazai ƙarasa cin abincin bacci zai iya ɗakarsa,
Hannu yasa ya ɗauki cup of coffee ɗin data kawo masa sosae yasha, bayan ya kammala ya ajiye shi, sannan ya gyara kwanciyarshi ya kwanta luf abunsa, ya janyo blanket ɗinsa ya rufe har zuwa chest ɗinsa nan take bacci ya ɗauke sa,
bata bar bedroom ɗin nasa ba sai da ta tabbatar tayi masa addu'a tukunna tasa hannu ta kwashe kayan abincin acikin tray ta fuce dasu a hannunta,
Kitchen ta koma da hanzari ta haɗa ma Marshal Omar nasa shima acikin tray sannan ta wuce masa dashi part ɗinsa,
tana shiga a lokacin ya fito sanye da jallabiya fara wuri ya samu asaman 3 seater ya zauna hannunsa ruƙe da wayarsa ganin sehrish yasa shi sakar mata murmushi tare da cewa "kamar kinsan a yunwace nake abunda nake jira kenan,"
Murmushi ta saki tare da ƙarawa ta ajiye masa tray ɗin asaman table ɗin dake a gabansa sannan tace "Ya mai jiki ya omar, naji abunda ya faru Allah ya kiyaye gaba, ya tonu asirin su,"
"Ameen Ameen," ya amsa mata, hannu tasa ta buɗe warmer tare da ɗaukar plate da saving spoon zata zuba masa abinci taji yace "baki tambaye ni twins ɗina ba"? Murmushi ta ɗanyi tare da ɗagowa ta kalle shi tace "dama ƴan biyu ne"? Yace "eh kamannin su ɗaya sak, ke ma haka fuskarki irin tasu ce sak komai da komai,"
gabanta ne taji ya faɗi jin abunda omar yace dakatawa tayi da zuba mashi abincin tana son tunano wani abu arayuwarta amma sam takasa tunawa, tabbas tana jin cewa akwai wani abu da ta manta arayuwarta mai matuƙar muhimmanci agare ta, a duk lokacin da tayi ƙoƙarin tunawa sai taji zuciyarta tayi mata wani irin nauyi sosai,
"Wata rana zan kawosu ku ga juna, saboda inaso ki ga abun al'ajabin da nake son nuna maki,"
Cikin sauri tace "Shikenan ya Omar Allah ya kaimu lokacin nima zanso nagansu,"
ta jima suna dan fira dashi kafin daga bisani ta bar part ɗin nasa ta koma ɗakinta,
Bayan Omar ya kammala cin dinner ɗinsa fitowa yayi tare da wuce wa ɗakin da suka kwantar da fawan
Yanayin daya samu Twis zaune zun zuba mashi ido ga kanal yusif shima zugudum duk cikin jimami, gyaran murya yayi duk suka ɗan ɗago kana yace "ku tashi ku je ku kwanta, tun da ya samu bacci"
Amsa mashi su kayi da "toh" sannan suka miƙe tare da fuce wa daga ɗakin shima yusif yayi yabi bayansu, zama Omar yayi daga gefen fawan dake ta faman sharar bacci, addu'o'i ya shiga karantowa yana tatto fa masa, ya jima yana yi masa addu'a sannan ya tashi yabar ɗakin tare da tufe masa ƙopa,
****************
Wuraren ƙarfe sha biyu ya fito cikin sanɗa hannunsa ɗauke da pillow yana duddubawa yaga in ba kowa duk sunyi bacci lokacin murmushi ya saki tare da cewa "sheggu saboda wancan ɗan shilan shine duk suka susuce har suka gaza cin abinci, bari na ƙarasa shi lahira sai in ga ya zasu yi, zasu bi shi ne
Yana faɗin hakan ya wuce ɗakin da suka kwantar da fawan cikin sanɗa ya tura ƙopar tare da sa ƙafa yashiga cikin, bin shi yayi da kallo jinjina kansa yayi sannan ya lalla6a ya haye saman gadon tare da ɗaga pillow ɗin ya taushe ma fawan hancinsa dashi , nan take fawan yafarka tare da