Showing 138001 words to 141000 words out of 245004 words
Chapter 47 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
tana faman 6a66aka dariyar mugunta,abun mamaki shiru babu alamar Amal zata saki ihun jin saukar ruwa ajikinta,.
Hakan yasa dariyar abra ta soma komawa ciki,ganin yarda bargon ya lafe ajikin katifar,yasa ta gane cewa babu mutum asaman katifar,
Hankali atashe ta saki bokitin ƙasa tana faman kwala ma Amal kira,
Shiru bata amsa ba,cikin sauri ta fito tana nemanta a tsakar gidan,babu inda bata duba ba daga kitchen har cikin toilet ɗinsu duk bata nan,
da gudun gaske ta koma ɗakin mamynsu a firgice mammyn ta ɗago tana kallonta ganin yarda ta faɗo mata yasa tace"Abra lafiya meke faruwa ne"!
Muryarta har wani shakewa takeyi wurin fadin"Mammy!babu Amal acikin gidan nan!Amal ta gudu!dama saida raina ya bani cewa zata iya guduwa,'
jin hakan yasa mammy cewa"hakan na nufin itace ta kwashe kuɗin da Sofwan ya bani?
"Mammy dagaske baki ga kuɗin ba!aiko indae hakane toh Amal itace ta kwashe kuɗin,innalallahi bansan ya akai wannan daƙiƙiyar yarinyar har tayi tunanin guduwa ba,ina mata kallon shashasha....'
Katse ta mammy tayi da cewa"amma shegiyar yarinyar nan ta gama dani wlh!naci buri akan kuɗin nan,maimakon ta gudu tabarmin kuɗin shine ta haɗa dasu ta gudu,insha Allah a wulaƙance rayuwarta zata ƙare,Allah ma yasa kidnappers su ɗauketa su kwace kuɗin,sannan su lalata rayuwarta....."
"Subhanallahi!!me nake ji haka!"
Muryar Abbansu Abra ce ta karaɗe kunnansu,shigowarshi kenan cikin gidan ya same su suna ta tsinar Amal,
wani koɗaɗɗen mutum ne,tamkar baya a cikin hayyacinshi haka zubin shi yake,tsohon yadi ne ajikinshi duk yayi uban squeezing,kamar kanshi farau talauci,
ƙarasawa bakin kofar dakin yayi yana tambayar lafiya menene ya faru,
Tsawa mammy ta daka mashi tamkar ba mijinta ba haka tashiga ɗura mashi zagi
"Munafukin banza,munafukin wofi kazo kaji abunda muke tattaunawa ne!Anya bakaine kayi ma Amal hanyar guduwa daga cikin gidan nan ba!wlh ban yarda dakai ba!ka faɗamin gaskiya taya akai Amal tabar cikin gidan nan!?don nasan hakanan banza Amal baza tayi tunanin barin gidan nan ba!dole da taimakon wani,
Tuni yasha jinin jikinshi,saboda mugun tsoranta yake ji,gaba daya ta gama asirce shi,shiyasa baida ikon yin komai sai da Umarnin ta,
tsawa ta daka mashi tare da cewa"ba zaka faɗamun gaskiya ba!taya akai amal tabar gidan nan!
Zuru yayi da ido sai faman kyafta ido yakeyi yana mazurai kamar mara gaskiya,
tsoki abra taja tare da cewa"mammy dama kin daina wahalar da kanki,Abba bai ma da cikakken hankalin da zai iya taimakon Amal wurin barin gidan nan!6ata mana lokaci kawai zaiyi,ni ina ganin ki fito kawai muje mu nemo ta acikin gari,
harara Mammy ta watsa mashi tare da fitowa daga ɗakin ita da Abra suka kama hanyar fita daga gidan,
Bayan sun fuce daga cikin gidan,matsawa abi yayi tare da kai hannu ya ɗauki kujera ƴar tsugunno ya zauna asamanta,
Muryar Amal ya tuna acikin kunnan shi,ashe sun haɗu da ita akan hanya sai faman sauri take yi tamkar zata tashi sama,kamar daga sama taji an ruƙo mata rigar jikinta a firgice ta juya tana kallon shi,ganin Abbansu ne yasa ta fashe da kuka don tasan cewa zai iya mayar da ita gida,cikin shessheƙar kuka tace"Abie nasan inda Aunty amani take,bazan cigaba da zama acikin gidan nan ba,kana gani zasu kashe ni,amma ba ka iya tsawatar masu akan su daina cutar dani,dan Allah Abie kabarni in tafi,kada ka sanar ma mammy cewa ka ganni akan hanya,ka nuna cewa bakasan komai ba,"
tsananin tausayinta ne ya kama shi,nan take yaji cewa zai iya taimakonta gudun karta faɗa hannun mutanen banza,tun da ƙaramar yarinyace mai ƙananun shekaru tsaf za'a iya yi mata wayau,
"Kiyi haƙuri Amal akan dukkan abunda ke faruwa,nima bada son raina bane,bani da yarda zanyi ne gaba daya mammy ta addabi rayuwata,ta hanani dukkan wani farin ciki na rayuwata,tun bayan da Allah yayi ma mahaifiyarku rasuwa ban ƙarasamun kwanciyar hankali ba,komai na duniyar nan ya fita raina Amal,mammy ta jima tana cutar da rayuwata da kuma rayuwarki,yanzu ina da kwarin guiwar iya taimaka maki!dama abunda yasa tuntuni banyi hakan ba saboda bani da ikon yin magana dake acikin gidan,inaji ina gani an rabani da ƴata kuma ana cutar da ita akan idona,babu komai akwai ranar sakayya,"
Yana kai karshen maganar tashi ya ruƙo hannun Amal tare da janta suka tafi,da kanshi yakaita tasha sannan ya damƙa ma drivern amanarta,kasancewar drivern ɗaya daga cikin abokanshi ne ana mutunci sosai,agaban motar drivern yayi mata wuri ta zauna kusa dashi,
Sai lokacin drivern yake tambayarshi inda zasu sauke ta a abujan,shi kanshi abie baisan inda amani ke zaune ba acan,
Cikin sauri Amal tace"ina da numbar wayar Aunty amanin,idan mun isa sai ya kira mun ita awaya,nasan zata zo,"
Murmushi abie yasaki yana tsaye daga waje yashiga tofa mata addu'o'i tare da yi masu fatan sauka lafiya,
tuni Amal taji hawaye sun wanke mata fuskarta,ji take kamar ta fito daga cikin motar tabi mahaifinta,haƙiƙa ta tausaya mashi sosai,haka ta dinga jin raɗaɗi azuciyarta har motar tasu ta kusa barin tashar,ya jiyo muryar Amal tana kwala mashi kira,
"Abie!!Abie!!"
da saurin gaske ya ƙarasa inda motar take,kowa na cikin motar tsayawa yayi yana sauraron muryar yarinyar,
murmushi ta sakar mashi,tare da zura hannu cikin aljihun rigar Abra dake ajikinta,zaro kuɗin nan tayi kusan dubu arba'en,sannan ta zura hannunta ta saman glass ɗin murfin motar ta miƙa mashi su,
ganin ya tsaya yana kallon kuɗin yasa tayi saurin cewa"Abie dan Allah kada ka tambaye ni ina nasamu kuɗin,in dai ka yarda dani to ka kar6a kawai nasan kana buƙatarsu,"
Murmushi yayi tare da sanya hannu ya kar6i kuɗin,sannan a hankali glass ɗin ya soma dagawa sama,
Tana jiyo muryarshi yana cewa"ki kula mun da kanki,sannan in Allah ya haɗaki da ƴar uwarki Amani,ki gaishe mun da ita,kice Abbanta yana gaishe da ita sosai,
har motar tabar tashar Amal bata daina leƙenshi ba ta glass ɗin motar,haka zalika shima yana atsaye yana kallon motar tasu,har sai da ta 6ace ma ganin shi,sannan ya haƙura ya juya tare da kama hanya ya soma tafiya yayin da idanunshi ke akan hannunshi yana kallon kuɗin da Amal ta bashi,
Ba ƙaramin daɗin kuɗin nan ya ji ba,yaushe rabon daya ruƙe naira dubu tashi ta kanshi harya manta,ba damar ya samu kuɗi yashiga gidan shi,da zarar mammy ta gani zata amshe kuɗin,ko sisi bata son taga ya ruƙe a hannun shi,tafi son taganshi a matsiyacin shi yana yawo,wannan ba damuwarta bace,
Sanin cewa zata iya ganin kuɗin a hannunshi ta kwace mashi su hakan yasa baiyi gangancin zuwa gidan dasu ba,kai tsaye ya wuce wurin wani abokin shi mai siyar da nama abakin hanya,wuri yasamu ya zauna bayan sun gaisa ya bashi ajiyar kuɗin duka,sannan yace ya zuba mashi naman na dubu uku yaci,bai bar wurin ba sai da yaci ya ƙoshi sannan sukayi sallama da mai naman ya wuce gaba,
Murmushi abie ya saki bayan ya kammala tunanin nashi yace"Allah sarki Amal!kin taimaki mahaifinki,ba don ta bani kuɗin nan ba,da yau haka zan kwana da yunwa,"
Mammy da abrah tamkar zasu yi hauka wurin neman Amal,gida gida haka suka dinga bi suna nemanta,saƙo da lungu ba inda basu duba ba,har bayan sallar magrib suna waje wurin nemanta,a ƙarshe dasuka gaji agalabaice suka koma gidan suna faman haki kamar waɗanda suka sha gudu,tun acikin zauren gidan mammy ta yanke jiki ta faɗi a sume,saboda tsabar baƙin cikin Amal data gudar mata da kuɗinta,
. hankali atashe abra tashiga zabga ihu tana kuka tana ambaton sunan mammy,
Da alama dae mammy sai anyi jinya,
****************************
Around 11pm,
fitowa tayi daga cikin toilet jikinta na sanye da sleeping dress riga da wando,white colour,da alama tayi shirin kwanciya,tun acikin toilet take jin wayarta na ringing,hakan ne ma yasa tayi hanzarin fitowa,ƙarasawa tayi cikin sauri tare da kai hannu ta ɗauki wayar dake ajiye asaman mirror,duba sunan mai kiran tayi,ganin baƙuwar number yasa taƙi ɗaga kiran,sai tayi rejecting ɗin kiran,kafin ta ajiye wayar sai ga wani kiran ya ƙara shigowa na baƙuwar numbar,
Cike da mamaki tace"Wai wanene ke kirana a irin wannan lokacin,kuma da bakuwar number,salon ajamun bala'e,bari dae in ɗaga inji,picking call ɗin tayi tare da karawa a kunnanta,muryar namiji ce taji ya zabga mata sallama,aikuwa cikin sauri ta katse kiran tana faman dafe saitin zuciyarta,ta tsorata da jin muryar me kiran nata,koma wanene ba ƙaramin mutum bane,
tsayawa tayi tana tunanin wa tasani da wannan muryar,bata ta6a jin mai irinta ba,
tana cikin wannan yanayin sai ga message ya shigo cikin wayarta,cikin sauri takai hannu tare da janyo saƙon daya shigo daga saman screen din wayar tashiga karantawa kamar haka
_baiwar Allah,ina ta kiran wayarki kin ƙi ɗagawa,dama ƙanwarki Amal ce ta ban numbarki don na kira na sanar dake cewa kizo ki ɗauke ta,ni ne drivern daya kawota abuja,idan ba damuwa ki kira kuyi magana da ita,don kiji muryarta_
Wani irin bugu zuciyarta tayi,cikin tsananin mamaki tashiga maimaita sunan Amal,muryarta na kerma tashiga cewa'Amal!wata Amal yake nufi!ko dai Amal ƙanwata!!!
Cikin sauri ta danna ma numbar kira,yatsun hannunta har kerma sukeyi don aƙagare take da taji bayanin mutumin daya turo mata saƙon...........
Pls read this👇👇👇
*Assalamu Alaikum,barkanmu da juma'a fatan kowa na lpy,yauwa inaso indan yi wani karin haskene,aduk lokacin da bansamu yin update ba har ranar ta wuce ina kokarin ganin nayi long page don yayi covering da wanda bansamu yi ba,nasan wasu sun fahimci hakan,yayin da wasu kuma basu fahimci hakan ba sai suyi ta maganar page kaza yakamata inyi tunda banyi na rana kaza ba,duk page da nake saki yafi ƙarfin page guda a ƙa'idar page,ina haɗe 2 pages ne sometimes ma yana haura 2 pages, Shiyasa in na sanya short page wasu ke complain saboda sun saba ganin long page,sannan ban kin yin typing sai don uzurin da ba yadda zanyi,da fatan zaku fahimce ni,sannan akwai masu maganata abayan idona nacewa wai ina jan littafi? Allah sarki rashin sani yafi dare duhu,bani da wani burin daya wuce inga na kammala littafin nan ayanzu saboda abubuwa da sukayi mun yawa,bani ke jan littafin nan ba!bada son raina ba kuma hakana ke faruwa ba!yanayi ne dake nake ciki,yakamata mutane su dinga yi mun uziri bai kamata arinƙa yi mun irin waɗannan maganganun ba,duk wanda kuma yake yi Alhakina na akanshi, wai wasu ma har cewa suke yi don naga littafinna yasamu kar6uwa mutane naso. shiyasa nake jan labarin,wlh dana ji wannan maganar kamar na fasa ihu don takaici, hmmmm babu komai akwai Allah,to my real fans nagode kwarae da hadin kai da kaunar littafi na da kuke,godiya mara adadi kuci gaba da yi mun uziru kuma acigaba da yi mun addu'a,shine kawai insha Allah komai mai wuce wane,Littafin nan inaji araina cewa kammaluwarsu tazo zanyi ƙoƙarin tabbatar da hakan!insha Allah*❤
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
_💋Boss Bature💋_
_Zuwa ga masu karkasamun littafin duk wanda ya ƙara haɗamun document,ban yafe ba!babu yarda za'ae ni ina cikin rubuta littafi na biyu,wasu kuma sun haɗamun document na book 3 don iyayi da kuma ƙarfin hali,sai ja mun surutu sukeyi nacewa naja littafi har book 3 duk da idan naga dama har book 5 ma sai inyi bani naji zan iya ba😒😏🙄😒, wasu har gardama sukeyi mun nacewa book 3 suke so complt,bayan ni iya book 2 nake cikin rubutawa ma_
🤍❤💖
Kiran na shiga drivern ya ɗaga,cikin sauri ta kara wayar a kunnanta tare da yi mashi sallama tace"kayi haƙuri bawan Allah,ban fahimci zancen ka bane,dan Allah ka ƙara yi mun bayani yarda zan gane,"
drivern yace"ƙanwarki ce Amal na kawota Abuja,yanzu haka ita kaɗai ta rage acikin tashar nan,kiyi hanzari kizo ki ɗauke ta saboda dare yana yi kuma ni yanzu nakeson na juya,"
Cikin sauri tace"ka turomin da address ɗin wurin gani nan zuwa,"
Amsa mata yayi da toh,sannan ya kashe kiran,ba da jimawa ba sai ga message ya shigo wayarta na address ɗin inda suke,
Da sauri Amani ta ƙarasa wurin wardrobe ɗinta tare da buɗewa ta ɗauko mayafi tayi rolling ɗinshi akanta,sannan ta dawo ta dauki purse ɗinta dake ajiye asaman bedside drawer ɗinta,
gaba ɗaya duk tabi ta dabarbarce ko escort bata nema ba, da kanta ta shige motarta,ta fisgeta da gudun gaske ta fice daga cikin gidan,driving take tana ta faman sambatu"Ya Allah ka tabbatar mun da abunda nake tunani,Allah yasa Amal ce ƙanwata,Ya Allah kasa itace,wayyo Allah da naji daɗi,
ji take kamar motar bata sauri,tamkar tayi fiffike ta tashi sama don ta ƙarasa da wuri,
tun bayan da Drivern ya turama Amani adireshin wurin inda suke shiru bata ƙaraso ba,gashi dare sai ƙarayi yake,kuma babu wani passenger daya rage acikin station ɗin sai ita kaɗai kwallin kwal,sai kuma wasu daga cikin mazauna station ɗin,tana zaune acikin motar baiwar Allah ba ƙaramin galabaita tayi ba,ga gajiyar tafiya ga kuma ciwo da take fama dashi,don har yanzu zazza6in nan bai bar jikinta ba,ganin cewa zasu 6ata mashi lokaci gashi yana da wani uzuri mai mahimmancin da yake so yaje yayi,hakan yasa yace ma Amal ta fito daga cikin motar,daƙyar ta iya miƙewa tare da saukowa daga cikin motar ta fito waje tare da tsayawa tana jiran jin me zaice,
Ruƙo hannunta direban yayi sannan yajata izuwa wurin wani benci yace ta zauna anan ta jira ƴar uwarta tazo,kada taje ko'ina,shi zai wuce don yana da uzuri,
Hankalin Amal ba ƙaramin tashi yayi ba ganin direban zai tafi yabarta acikin station ɗin gashi babu wata ƴa mace aciki sai ita kaɗae,
Shi kanshi baiso hakan ba,saboda amanace aka bashi,amma ba yarda zaiyi,ya zamar mashi dole ya juya ya koma da motar,
tana ji tana gani direban nan ya shige motarshi tare da janta yabar cikin tashar da ita,
Lokaci guda wani irin sanyi ya lullu6eta,nan da nan jikinta ya shiga rawar ɗari,hatta haƙoranta sai faman kakarwa suke yi suna fidda sauti kaf kaf suna game wa da juna,ƙanƙame jikinta tayi tana ta faman ambaton sunan Allah abakinta,
Tana cikin wannan yanayin tajiyo takun tafiyar mutane daga gefen hagunta,cikin sauri ta juya don taga su wanene,gabanta ne yayi wani irin faɗuwa ganin wasu giggan tantirai su uku suna tunkaro wurin da take,sai faman nunata sukeyi da hannu da alama ma abuge suke,sun sha takai masu karo suna tafiya suna tangal tangal kamar zasu faɗi,
ganin hakan yasa Amal ta miƙe cikin sauri ta soma tafiya tana waiwayonsu,muryar wani daga cikinsu ne tajiyo yana cewa"kai karfa ta kufce mana,naga kamar tana so ta tsere mana," haba ina ae Amal na jin wannan maganar ta manta da yanayin da take ciki,takai hannu tare da tattare rigar jikinta ta watsa aguje kamar zata tashi sama,suma ganin ta fara gudu yasa suka bi ta aguje don su taddota,
Gaba ɗaya duk tabi ta rikice tana gudu tana waiwayonsu hakan yasa ta hau saman titi batare da saninta ba,kafin tayi wani aune tuni wata mota tayi awon gaba da ita,wata irin razananniyar ƙara Amal ta saki yayin da ta baje asaman titin idonta na kallan sama,jini na zuba ta saman goshinta da kuma hancinta,da la66anta duka sun raunata,
Waro ido waje tantiran nan sukayi ganin abunda ya faru,aikuwa a gaggauce suka zura da gudu don kar ace sune suka kashe ta,
Hankali tashe suka tsayar da motar,sannan atare suka fito daga cikinta da hanzari suka tunkari wurin da yarinyar take kwance,gaba ɗayansu suna sanye da kakin sojoji ajikinsu,
Zuƙunnawa daya daga cikinsu yayi yana kallon fuskar yarinyar dake ta faman faɗin"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"
"bata mutu ba,har yanzu tana numfashi amma tana bleeding ya kamata muyi saurin kaita asibiti,"
Na zuƙunnan ne yayi magana,sannan batare da 6ata lokaci ba,yasa hannunshi tare da sungumarta asaman kafaɗarshi cikin sauri suka wuce da ita cikin motarsu,a back seat ɗin motar ya zaunar da ita,sannan shima ya shiga daga gefenta ya zauna tare da ruƙota jikinshi,
Shi kuma ɗayan ya shiga gaban motar tare da yi mata key,yaja ta aguje suka juya domin zuwa kai yarinyar asibiti,
Adai dai lokacin da Motar tasu take ƙoƙarin shiga shantalelen titin dake a left hand dinsu,Motar Amani ta kunno kai ta titin dake a right-hand ɗinsu, a wani slow Amani ta zuge glass ɗin motarta tana bin tasu motar da kallo saboda kukan mutum da tajiyo acikin motar ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba,aranta tana cewa"Allah yasa dae ba wani mummunan abunne ke faruwa acikin motarcan ba,"
Tana ƙarasa maganar taja motarta da gudun gaske ta ƙarasa cikin tashar motocin,wuri ta samu tare da yin parking ɗin motar,cikin sauri ta fito tana faman gyara mayafin dake ajikinta,hannu tasa tare da ciro wayarta dake acikin purse ɗinta,sannan ta dannawa direban kira,cikin rashin