Showing 48001 words to 51000 words out of 245004 words
Chapter 17 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
ki samu matsayi acikinsa, saina san yarda zanyi in tarwatsa komai har inyi sanadiyar korarki acikin gidan nan," ya faɗi yana kallon sehrish rai a6ace yana faman tura dambun nama abakinsa har yana shaƙewa,
Kanal yusif kuwa murmushi ya saki sannan yaci gaba da cewa "Allah ya yarda Sehrish,Nima inason ki zama Abun alfaharin mu gaba ɗaya," ya ƙarasa maganar tare da sanya hannu ya ɗauki glass cup dake ɗauke da Lemu mai sanyi yakai bakinsa yana kur6a,
ƙasa-ƙasa da murya junaid yayi tare da cewa "sehrish nima fa naso nayi maki nasiha akan zuwanki makaranta, amma kash sai gashi Yaya yousouf ya riga ni, amma duk da haka ban makara ba, don Allah sehrish karki canzamun koda kin fara zuwa school don nasan zaki ƙara wayewa sosai..........'
Murmushi sehrish ta saki jin abunda junaid yace, kafin tace "Insha Allah junaid hakan baxata ta6a faruwa ba,mu aminnan juna ne zamu kasance atare ako wane hali na rayuwa, kaine abokin shawara na,"
ajiyar zuciya junaid ya saki aransa yana ƙara samun kwanciyar hankali jin bayanan da sehrish tayi masa,
wayar haroon ce dake acikin aljihunsa ta soma ringing taken waƙar nan da ake cewa "ɗan duniya hayaƙin taba," jin ringing ɗin wayar yasa kanal yusif girgiza kai tare da cewa "Allah ya shirya ka,"
Haroon yace "Ameen don son Annabi," sannan yayi saurin tashi daga dining ɗin yakama hanyar fita daga falon yana zaro wayar daga aljihun wandonsa, ɗaga kiran yayi tare da karawa a kunnansa yana cewa "Shegen bisa ashe har ka isa hotel ɗin, ae ko gani nan zuwa Yanzun nan Allah yasa ka taho mana da harkar nan..........' ya yi maganar da dariya a fuskarsa kafin yasa kai ya fuce,
Bayan sun kammala dinner ɗin junaid suka wuce masallaci tare da kanal yousouf jin ana kiran isha'e,.
Itama Sehrish bayan ta kammala dinner ɗin tare da azmee suka kwashe kayan da sukayi amfani dasu izuwa kitchen, Sehrish ce ta wawwanke su tare da jerasu a ma'ajiyarsu,
Bayan ta fito suka ci karo da azmee tace " Inaso naje na kwanta,pls kada ki bari bacci ya kwashe ki, idan Twins sun dawo ki tabbatar kin kai masu dinner ɗinsu, Shima Abbansu pls ki kaimasa nasan ƙila sai wurin 12 zasu shigo,.
Sehrish tace "To aunty azmee insha Allah baxanyi bacci ba, zan kai masu in sun dawo,"
daga nan azmee ta wuce ɗakinta, itama sehrish bedroom ɗinta tashiga, sai da tafara shiga toilet ta kuskure bakinta, dama da alwalarta,
Fitowa tayi ta ɗauki hijab ɗinta da ta ajiye saman gadonta, ta kabbara sallah
_________________________________________________
Tuni General ishaq ya iso gidan ya cika tab da mutane tare da jami'an sojoji da suka rakosa, su Aunty babba sai faman rawar kai akeyi miji ya iso gari, a lokacin hafsat har ta shirya kanta itama tsaf ta kimtsa cikin haɗaɗɗen cord lace Ash colour mai adon duwatsu,rigar mai dogon hannu sai skirt ba ƙaramin kyau kayan su kayi mata ba, gashi dama takware wurin iya kashe kallabi, tare da Mommyn nata da wasu daga cikin abokanan aunty babba da suka zo dana hafsat suke taimakawa wurin tarbar baƙi da abunsha dana ci,
"Jahad ya Omar shiru kodai ya manta damu ne"? Hussana ta faɗi fuska tamkar zatayi kuka tana kallon jahad suna zaune dab da juna daga gefen gadon hafsat,
"Hussana bana tunanin hakan, Ya Omar yana son mu sosai ni ina da tabbacin yana sane damu,kuma zaizo ne insha Allah," acewar jahad
Hussana tace "Ni inajin tsoron a rabamu da ya Omar, wlh banso banso....'
Kamar daga sama suka ji Muryar Aunty babba tace "Saboda ƙanin ubanki ne ko? ta faɗi ayayin da take shigowa, arazane suka miƙe tsaye su duka suna kallonta, su biyu suka shigo cikin ɗakin ita da wata hajiya, amma ita ta tsaya daga baya
Kusa dasu taje sannan tasoma magana "Ko da gigin wasa bana so wata daga cikin ta leƙo da kanta daga cikin ɗakin nan ! Saboda Mijina ya dawo kuma banaso ya gan ku, ina fata kun gane?
Cikin sauri suka haɗa baki wurin cewa "Insha Allah aunty bazamu fito ba,"
ta6e baki tayi sannan ta juya bayanta ta kalli matar da suka shigo tare tace "Hajjaju gafa yaran nan da nake faɗa baki, Omar yakawo min cikin gidana,"
ƙarasa shigo wa ciki matar tayi jikinta na sanye da shadda gezna green colour tasha uban aiki a wuyan rigar, tayi ɗaurin ɗan kwalin ture kaga tsiya sannan ta yarfa gyalenta a kafaɗarta,
Alokacin da matar ta ƙaraso Jahad taganta nan take gabanta yayi wani irin bugu zaro ido tayi tana kallonta saboda son tuna inda tasan fuskarta,
Hajjaju kuwa tana ganin su hussana da jahad farat ɗaya ta gane su, a ɗan razane ta dafe ƙirji tare da cewa "Kaiii !!!" taja maganar da ƙarfin tana kallonsu cikin mamaki da al'ajabin wannan Ikon Allahn,
tuni aunty babba tagama ruɗewa ganin yadda hajjaju ta razana da ganinsu, da kuma yarda jahad ta firgita itama wannan alama ce dake nuni da sun san juna kenan ko yaya,
Cike da mamaki Aunty babba tace "Wai meke faruwa ne hajiya rabi? kinsan su ne?
Cikin sauri hajjaju tace "A'a bansan su ba, Kamar dae nata6a ganin mai kama dasu ne,"
tayi maganar tare da ruƙe hannun Aunty babba taja ta, suka fuce daga ɗakin,
Kallon jahad hussana tayi tare da cewa "Jahad wacece wannan matar? Naga kin razana da ganinta,"
"Nima so nake na tuna inda nasanta," Jahad ta faɗi tana faman cizon akaifar hannunta da takai abakinta,
Hajjaju kuwa da taja Aunty babba suka fuce can suka nufa wurin kitchen suka tsaya, ga mutane sai faman shige da fuce suke,.
"Dan Allah ki faɗamun gaskiya hajjaju raina na bani cewa kinsan yaran can ko? Aunty babba ta tambaya tana kallonta cike da son jin ƙarin bayani daga wurinta,
Jinjina kai Hajjaju tayi tare da cewa "Yau naga ikon Allah, Lallai ne duk zakaran da Allah ya nufa da cara,to fa sai yayi ta, haƙiƙa nayi matuƙar mamakin yarda akai har Allah ya haɗa Omar da waɗannan yaran , kai kaga wani ikon Allah nan ! mai matuƙar ban mamaki da Al'ajabi?
Hajjaju tayi maganar cikin nuna mamakinta,
Aunty babba kuwa cewa take yi "Hajjaju kin barni acikin duhu, wlh har kinsa hantar cikina ta kaɗa dan Allah kisanar dani me kika sani agame dasu?
dariya hajjaJu tayi tare da tafa hannayenta tace "Ana bura'uba a lagos! yo ke laila da kike cewa zaki sa a zubar maki da waɗannan yaran don ki nisanta su da Omar, idan Kin toshe wannan hanyar to ita waccen ɗayar hanyar da ta ruga isa inda bakya so ya zakiyi da ita?
gaba ɗaya fa Aunty babba ta gama rikicewa da bayanin hajjaju, cikin tashin hankali tace "wai me kike nufi ne hajjau, kiyimun bayani mana yadda zan fahimta !!!
ta faɗi tare da ɗan jan guntun tsoki, Murmushi hajjaju tasaki sannan tace "Ni baza kiji mutuwar sarki abakina ba!kawai abunda nakeso ki sani shine babu wanda ya isa ya hana ruwa gudu sai Allah! Bakin alƙalami dai ya ruga daya bushe, Amma fa waɗannan yaran da kike gani wlh ikon Allah ne su, tunda har Allah ya haɗasu da Omar aikuwa magana ta ƙare, Yakamata kisan abunyi,'
Hajjaju tayi maganar tare da wuce wa ciki tabar Aunty babba tsaye abakin kitchen baki asake, lokaci guda taji ta ƙara tsanarsu hussana da jahad tabbas suna tattare da wani abu yaran, duk da bata fahimci inda maganar hajjaju ta dosa ba,
ranta ya gama 6aci tsoki ta buga tare da cewa "ta tsaya tayimun bayani amma ta tsaya yimun wasu sambatun banza dana wofi,ni duk tasa hankalina ya ƙara tashi, kuma wlh goben nan zansa a Kwashe mun su aje can azubar dasu tsakar daji, sai dae abunda bangane ba acikin maganar hajjaju wacece ɗayar hanyar da take nufi wadda ta isa inda banaso!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!!? ta tambayi kanta sai dae kash babu amsa hakanan ta koma ciki tana faman sambatu aranta,
Zumbur !! Jahad tayi tare da kallon husana tace "Wlh nasanta!! Nagane ta !! Itace matar da ta taimaka mana a asibiti har ta biya kuɗin gadon Ki husana, wlh itace matar da tasama ma SEHRISH aiki, hakan na nufin ta son inda sehrish take.....!!
Cikin tsananin farin ciki jahad tayi maganar, hussana ma aɗan raxane tace "dagaske jahad itace tasama ma sehrish aiki? Ke nan itace kawai zata iya faɗa mana inda ƴar uwarmu take kenan,.
jahad tace "eh itace, nagane ta yanzu ya za'ayi muyi magana da ita, gashi aunty ta hanamu fita, amma ni dae inason magana da ita kodan saboda ta faɗa mana inda sehrish take,' jahad tayi maganar fuskarta tamkar zatayi kuka,
Cikin sanyin murya hussana tace "Jahad kada ma musa rai don nasan bazata faɗa mana ba, ita fa ƙawar Aunty ce, kuma kinsan muguwace idan halinsu ɗaya fa? Bazata ta6a faɗa mana ba, Ni tsorona ma kada ta faɗa ma wannan muguwar auntyn inda sehrish take, suna iya zuwa su cutar da ita, Allah yasa sehrish tana lafiya banaso wani abu yasame ta.........'" tayi maganar cikin shessheƙar kuka,
"Da gaskiyar hosana,Nima ina tunanin hakan Allah yasa karta faɗama auntyncan inda ƴar uwarmu take, amma dai ni inason naga matar na roƙeta akan ta faɗa mana inda sehrish take,yakamata musan inda take, wane hali take ciki, gashi yanzu sai mutuwa akeyi Ya Allah kasa sehrish tana araye har mu haɗu," tayi maganar idonta cike tab da hawaye,
daga bisani ta kalli hosana tace "ki zauna hosana kada ki fito bari ni naje nayi magana da matar na roƙe ta, ta faɗamun inda rishi take,"
Hosana tace "toh," sannan tasamu wuri ta zauna gefen gadon tana faman sauke ajiyar zuciya,
Cikin sanɗa jahad ta futo daga kopar ɗakin ta tsaya tana ɗan leƙa kanta, mutane tagani gasu nan sai faman zarya sukeyi acikin babban falon,
A hankali ta miƙi hanya ta soma tafiya tana faman waige-waigen neman hajjaju, ta ɗanyi nisa a tafiyar ta ta, tajiyo magana daga bayanta ana cewa "Nasan cewa ni kike nema ko"?
Cikin sauri jahad ta juyo bayanta, hajjaju ce tsaye tana kallonta fuska ɗauke da murmushi,
Ajiyar zuciya jahad ta saki sannan itama ta mayar mata martanin murmushin tare da gaishe ta, hajjaju ta amsa mata da cewa "Nayi mamakin ganin ku, anan gidan ko ba'a faɗamun ba nasan cewa kunsha wahalar rayuwa don nasan Laila sarai muguwace bata da Imani,kuma tana sanar dani game daku a waya sai dai bansan cewa ku bane,"
Jinjina kai Jahad tayi tare da cewa "Munsha Wahala sosai tamkar ba zamu rayuwa ba,dan Allah ki faɗa mana ina Sehrish take? Munyi kewarta sosai, rabon mu da ita, tun da ta tafi aikin nan da kika sama mata,bayan wasu kwanaki hosana ta 6atar mana da wayar da muke amfani da ita wurin kiranta, shikenan rabuwarmu da ita......' jahad ta ƙarasa maganar idonta cike tab da kwalla,
ɗan shuru hajjaju tayi tana kallonta gwanin ban tausayi kafin tace "Kiyi haƙuri, amma bazan iya shaida a ina sehrish take ba nikaina,saboda nasaba hulɗa da yara ina sama musu aiki, bazan iya tuna a wane gari nakai sehrish ba, bazan iya tunawa ba......'
Jin hakan yasa Jahad fashe wa da kuka mai cin rai, matsawa hajjaju ta ƙara yi gab da jahad tasanya hannunta tare da dafa kafaɗunta tace"kiyi haƙuri Jahad, ina mai matuƙar jin takaicin gaza taimaka maku akan halin da kuke ciki, haƙika kun ga rayuwa, amma ni abunda nakeson sani taya akai kuka haɗu da Omar? bayan naji labarin rasuwar tsohuwa ya gigita ni matuƙa, sannan naji labarin cewa ana zargin cewa kune kuka bata poison amma bansan ya ƙarshen labarin yake ba,'.
Cikin shessheƙar kuka jahad tace "bayan tsohuwa ta rasu, mutane suka ce mune muka kashe ta alhalin mu bamu da masaniya akan mutuwarta, shine aka kaimu police station, munsha Wahala sosai saboda bamu da sheda, ana shirye shiryen za'a miƙa case ɗinmu kotu, hussana tayi rashin lafiya shine dalilin dayasa ƴan sanda suka tafi da ita asibiti tare dani, Acan ne Allah ya haɗamu da yaya Omar shine ya kwace mu daga hannun police ɗin kuma ya kashe case ɗin gaba ɗaya......' ta ƙarasa maganar tana faman sauke ajiyar zuciya,
Murmushi hajjaju tasa ki tare da cewa "Allah sarki Omar mutumin kirki ne sosai, yana da tausayi inama ace tunfarko ba nan ya kawo ku ba, wlh da kun more rayuwarku,amma sai dai kash yayi kuskuren jefa rayuwarku cikin haɗari batare da sanin shi ba, Amma insha Allah Laila bazata ta6a cin nasara akanku ba,'
Jinjina kai kawai Jahad ke yi, bayan sun ɗanyi shiru hajjaju tace "Muje ɗakin da kuke,ina son ganin ƴar uwarki danaji kin kirata da hussana, bazan manta ba itace a lokacin kwance saman medical bed ansa mata oxygen tana shaƙar numfashi cikin mawuyacin hali, Amma yanzu naganta taji sauƙi sosai jiki yayi kyau,' hajjaju ta faɗi da ɗan murmushi a fuskarta yayin da suke nufar ɗakin hafsat atare,
Suna shiga suka samu hussana atsaye sai faman zirga-zirga take yi burinta kawai jahad tadawo kusa da ita,
Tsayawa tayi ganin sun shigo tare da matar, Murmushi hajjaju ta sakar ma hussana tare da ƙarasawa inda take ta rungumo ajikinta, tana ɗan bubbuga bayanta tace "nasan ke baki sanni ba,sabosa lokacin kina kwance rai hannun Allah, amma ni nasan ki saboda naganki a lokacin, naji daɗi sosai dana ganki cikin ƙoshin lafiya,
Hajjaju ta ƙarasa maganar tare da janye hussana daga jikinta, ita dai hosana kallonta kawai take yi don batasan ta ba, mayar da idonta tayi kan jahad tace "ta faɗa maki inda sehrish take?
Jahad tace "a'a hosana, tace itama ta manta inda takaita aiki saboda ta saba kai yara aiki bazata iya tuna inda takai su ba,"
Jin haka yasa Hosana fashewa da kuka tana cewa "..yanzu shikenan bazamu ƙara ganin sehrish ba....
Hajjaju tace "Ki daina kuka hosana,wayace maki bazaku sake ganin sehrish ba? Ki daina wannan tunanin Insha Allah zaku haɗu da ƴar uwarku, abunda nakeso daku kawai ku cigaba da addu'a insha Allah zaku dace,"
Jahad tace "kullum muna cikin yin addu'a,Kuma zamu cigaba da yi har illa masha Allah"
Murmushi hajjaju ta kuma yi sannan tace "Ni zan wuce,Ku kula da kan ku,Allah ya Albarkanci rayuwarku, yaci gaba da tsare ku aduk inda zaku kasance arayuwar nan,"
Suka amsa mata da "Amin," sannan tasa kai ta fuce tana mai jin rashin daɗin gaza taimaka masu da tayi na ƙin faɗa masu inda ƴar uwarsu take, bayan ta son inda take,
Komawa sukayi atare suka zauna jikinsu amace, Shin mai zai biyo baya?😥
Bayan wasu lokutta, duka baƙin da suka zo suka tafi gidan yayi tsit ba hayani, suna cikin wannan zaman na jimamin Ga samu ga rashi, na hajjaju da suka haɗu da ita yau, sun son itace kaɗai zata faɗa masu inda Sehrish take gashi itama tace bata sani ba, hakan ba ƙaramin kashe musu zuciya yayi ba, daker suka samu bacci ya ɗauke su,
_______________________
Fitowa daga wanka general ishaq yayi jikinsa sanye da gajeran wando, Closet ɗinsa ya nufa tare da sa hannu ya buɗe ya ɗauko jallabiya ya zumbula ajikin shi, Sarai yasan cewa tana ɗakin Amma sai yayi tamkar bai ganta ba, sai da ya kammala kimtsa kansa sannan yace "Ya Rashin Ji"? Ya tambaya yana kallon kansa acikin Mirror, mamaki ne ya kama aunty babba jin abunda yace, tana zaune daga gefen gadonsa tace "Nifa ce ba hafsat ba," ta faɗi tana kallonsa
Ishaq yace"Nasani ae, dake nake magana, duk rashin jin hafsat ae bata kai ki ba, kefa tamkar 6eran gida kike wurin 6arna da rashin ji,"
ɗaure fuska tayi jin abunda yace rai a6ace tace "Alamu sun nuna cewa ba kayi kewata ba ko? shiyasa kake gayamin magana, ko da yake dama kai ae ba ka iya soyayya ba, Iya ruƙe bindiga kaɗae ka sani,"
......juyowa Ishaq yayi yaɗan kalle ta tare da ta6e bakinsa yace "ban iya soyayya ba, amma gashi nan har kin haifi hafsat dani ko? Naga wannan ma ae wani sashe ne na soyayya,"
ya ƙarasa maganar tare da wuto wa ya haye saman gadonsa ya kwanta yana cewa "Idan kin tashi fita daga ɗakin kada ki manta, ki kashe mun hasken inaso nayi bacci,"
a ƙule aunty babba ke kallon shi, can kuma ta miƙe fuuuuu ta nufi hanyar fita har takai bakin ƙopar ɗakin ta kuma tsaya tare da juyowa tana kallonsa, abun mamaki sai ta same shi yana ta faman tiƙar dariya,
Bakomai yasa ta tsayawa ba face tsananin son kasancewa dashi da take yi,
dakatawa da dariyar yayi sannan yace "nifa ba korarki nayi ba, zaki iya dawowa kiyi zaman ki,"
murguɗa masa baki tayi aranta tace "shashasha dama nasani ae dole ka buƙace ni,"
shi kuma aransa yace "Mayya, Jibi yarda take ta hau hawa kamar buhun harawa, duk an cinye mun abincin gidana," 😂
Kamar taji mi yace ta ɗan kallesa tare da jinjina kanta tace "bari na kawo maka Tea,"
"Ok i wll be waiting for u," ya faɗi yana faman yin dariya ƙasa-ƙasa, general ishaq kenan tamkar Abbansu haka yake indai wurin iya zolaya ne,
******************************
A 6angaren sehrish kuwa, sam taƙi bari bacci ya ɗauke ta sai faman gyangyaɗi take yi tana zaune asaman kujerar dake gaban mirror burinta kawai su twins su dawo ko tasamu ta kai masu abincinsu, sune kawai suka rage mata takai mawa, domin kuwa ta jima da kaima Abbansu nashi tunda ya dawo,
Basu tashi dawo wa cikin gidan ba sai wuraren ƙarfe Sha biyu da rabi suka shigo suka shigo cikin falon kai tsaye ɗakinsu suka wuce, shaf shaf suka shiga rage kayan jikinsu, sai da ya rage daga su sai shorts ajikinsu, sannan suka shige toilet donyin wanka, sun jima aciki kafin daga bisa ni suka fito kowannansu ɗaure da towel a waist ɗinsa, closet ɗinsu suka buɗe jerin kayansu ne ajere komai iri ɗaya, kamar yadda suke tagwaye haka komai nasu yake iri ɗaya, kimtsawa su kayi cikin sleeping dress riga da wando milk colour,
faɗawa su kayi saman gadon