Showing 96001 words to 99000 words out of 245004 words

Chapter 33 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download

17 Mar 2025

25252

daga ciki mana ka zauna na kira maka ita don itama hossana a ƙagare take data ganka,"
  Omar yace"sauri nake na koma gida yanxu,ki gaishe mun da ita dae,ko kuma zan kira wayane ae akwai telephone sai mu gaisa," jinjina kai tayi tare da cewa"shikenan zan sanar mata,amma nasan zatayi kuka in taji cewa kazo kuma ka tafi bata ganka ba,
   juyawa yayi yana faman sakin murmushi har ya kusa fita daga falon tace "ya omar," juyowa ya kuma yi yana kallonta,
  "Tun jiya inata so in kazo inyi maka ya mai jiki,abun yana araina ɗan uwanka daka sanar mun cewa bai lpy,"
   Omar yace"oh fawan da sauƙi jikin shi sosai,kada ki damu zan bashi waya inyaji sauki ssae sai kiyi mashi ya jiki,"
  Jinjina kanta tayi alamar toh daga nan sukayi sallama ya fuce daga falon,
  Ajiyar zuciya ta saki tare da wuce wa ciki fuskarta asake 😇

****AUNTY BABBA******

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.

_💋Boss Bature💋_







********AUNTY BABBA************

Zaune take agaban dressing mirror ranta a matuƙar 6ace fuskar nan tayi jawur saboda kukan da taci,ta zabga uban tagumi zuciyarta sai faman tafarfasa take yi,bakomai bane ya haddasa mata wannan 6acin ran ba face General ishaq daya hanata zuwa abuja,duk yarda ta kwallafa rai akan zuwa abujan ya hanata,sai da ya bari tasha wankanta ta kimtsa cikin leshi ta yafa mayafi ta ruƙo jakarta, tana fitowa ta same shi zaune a falo jikin shi sanye da gajeran wando baki,wani irin kallo yabi ta dashi tare da cewa"Ina zuwa,"
washe masa baki tayi tare da cewa"Abuja mana,kai fa kace zamuje duba jikin fawan,"
kai tsaye yace"ae nafasa wannan,ni kaɗai zanje inyaso ko a waya ne kun kira Abba kuyi masu Allah kyauta,"
Tur6une fuska tayi tare da cewa"dan Allah idan wasa kake mun ka daina,"
  Shima ya tamke fuskarshi yace"ba wasa nake ba,ni kaɗai zanje inyaso saina wakilce ku,"
  Hankali tashe tace"Haba Abban hafsat sai da na kammala shirina, tafiya kawai ta rage zaka ce wai an fasa gaskiya ni sai naje," ta faɗi tare da ruƙe qugunta tamkar zata buge shi,
  Miƙewa ishaq yayi fuskarshi ba wasa yace"to ki sani muddin kikasa ƙafarki kika bar gidan nan without my permission hmmmmmm ke kinsan mai zai biyo baya,
  Yana faɗin hakan ya fuce ma daga falon yabarta,
  da gudu ta koma bedroom ɗinta a ƙasa ma tayi wurgi da handbag ɗinta saman gado ta faɗa tadinga shan kukan baƙin ciki har bacci ya kwashe ta,
Ta jima tana baccin kafin ta tashi cike da kunci ta koma gaban mirror ta zabga tagumi rai a6ace,

ta jima tana tunanin meyasa general ishaq ya hanata zuwa gidansu don ta duba jikin fawan,abun ya ɗaure mata kai saboda shi da kansa yace zasu je dubiya atare amma ya canza ra'ayinsa yanzu,
   tsoki ta buga tare da kai hannu ta ɗauki wayarta dake agaban mirror ɗin,contact ɗinta ta shiga ta lalubo numbar wayar HAYAAM ta danna mata kira,ringing ta shiga yi kusan sau uku ba'a ɗaga ba,

tana a cikin toilet kiran ya shigo a lokacin wayar na hannun wani matashin saurayi dake zaune saman wani haɗaɗɗen gado, daga shi sai shorts ajikin shi ya baje abun shi, ganin sunan Aunty Layla ya bayyana akan screen ɗin wayar yasa shi ɗaga murya tare da cewa"babe!babe!ur phone is ringing,
  Daga cikin toilet ɗin tace"wanene ke kirana?in dae mommy ce ko Abi ka kashe wayar gaba ɗaya bana son takura,
  "No basu bane,wannan auntyn naki ne Layla,"

Jin sunan Aunty laila yasa ta yin wuff ta fito daga cikin toilet ɗin, doguwa ce sosai fara sol babu ko tabo ajikinta kai kana ganin fatar nan zakasan cewa ba ƙaramin kuɗi take kashe mata ba saboda yarda take ɗaukar ido,

ta ko'ina Allah ya bata ga dogon wuya,
Bin ta da kallo saurayin yayi sam yagaza janye idonshi akanta sai kace batare suke rayuwa acikin gidan ba,
Towel ne kawai ta ɗauro ajikinta cikin hanzari ta miƙa hannunta tare da kar6ar wayar tana cewa"nashiga ukuna Aunty laila kuma a awaya?yanzu zata rufe ni da faɗan ba gyara ba dalili mtswwwwww
  Ta ƙarasa maganar tare da ɗaga kiran ta kara a kunnanta tana faman zazzare manyan idanunta,
A ƙule aunty babba tace"ina kika je ne inata faman kira ba'a ɗagawa?
Cikin en ina tace"Nashiga toilet ne yanzu na fito na sami wayar tana ringing asaman gado,
aunty babba tace"hmmmm kina a gida ko kina awaurin yawon gantalin naki?
Cikin sauri tace"am....ina a gida......" bata bari ta ƙarasa ba a tsawace tace"Karki kuskura kiyimun karya Hayaam ina sane da duk wani yawon gantali da kikeyi ana sanar mun da komai,saboda tsabagen iya shege da fitsara idonki ya buɗe wuyanki ya isa yanka hada tattara kaya da komawa gidan saurayi da zama koba haka akai ba? Ta tambaya azafafe tamkar tana a gabanta,tuni ran Hayaam ya 6aci juyawa ta ɗanyi ta kalli Sofwan dake kallonta bai sauraron me suke cewa amma ya lura da yanayin fuskarta daya canza saboda hayaam bata iya 6oye 6acin ranta duk mun ƙanƙantarsa,
  sassauta muryarta tayi tare da cewa"Aunty layla mgnr da kika faɗa gaskiya ne,i can't hide it 4 u ni bazan iya rayuwa a cikin gidan nan ba saboda baida marar raba da kwango a wurina,fentin gidan duk ya ƙoƙe kamar munfi kowa talauci a layinmu,bama wannan ba ɗakinmu bai da banbanci da kwankon ashana katifa ce kawai duk ta gwaigwaye sai akwatin kayan mu, ko na fidda kuɗi na siyi furnitures mommy bata barin komai sai dae kawai nadawo na taras ta siyar da komai ta hanani jin daɗin rayuwa kuma kinsan ni macace mai son rayuwar hutu rayuwar ƴanci wannan shine dalilin dayasa nabar masu gidan don wlh ko abincin da suke ci ynx 6ata mun ciki yake yi saboda wannan yarinyar ƙanwar Amani ita suke ba girkin gidan,yarinyar da bata wuci 14years duk wani aiki na gidan ita take yin shi har yanzu mommy bata haƙura ba akan ɗaukar fansar abunda mommynsu tayi mata" yadda take magana kaɗai ya isa ya tabbatar maka da cewa ba ƙaramar ƴar duniya bace magana take tana faman wurga ido tana kora jawabi
Jinjina kai aunty babba tayi tare da cewa"ae ni tayimun dai dai,wato wayewa tasa kin manta da irin azabtarwar da matar nan tayi mana shine har kike ganin laifin mommynmu,kwara su kashe yarinyar ma kowa ya huta ae ni nafison su wulaƙantata," ta fadi tana faman huci kamar tana agabanta,
Ganin wayar tasu ba mai ƙarewa bace yasa Sofwan tasowa daga saman bed dinsa ya sauko, takawa yayi izuwa bayan Hayaam dake atsaye ya rumgumota tare da zagayo da hannayen shi ta waist ɗinta sannan ya kwantar da kanshi daga gefen wuyanta yana cewa"babe yaushe wayar zata ƙare?nifa a ƙagare nake,
ƙasa ƙasa da murya tayi tare da cewa"pls karkaja min bala'e,"
Muryar aunty babba ce taci gaba cewa"Yanzu abunda nakeso dake kibar komai da kike yi ki tafi abuja gidan surukaina acan nakeso ki cigaba da zama,
  Ƙiris ya rage hayaam ta saki wayar dake a hannunta saboda jin sa6on da auntyn nata ke faɗi, cikin ruɗu tace"haba dae Auntyna amma dae wasa kike yi ko?if not ni mai zai kaini gidan in-lows din mu da zama abun ma babu daɗin ji........,
Tsawa aunty babba ta daka mata tare da cewa"ke dalla yi mun shiru!duk ƙoƙarin da nakeyi akanki bakya gani!kina nan sake da baki ga wata can a gidan matsayin yar aiki Abbansu ya mayar da ita ɗiyarshi sun gatanta yarinyar har makaranta take zuwa,idan har kikayi gangancin rasa wannan damar ta komawa gidan da zama ina mai tabbatar maki da cewa Kin rasa cikar burinki na har abada," shiru hayaaam ta ɗanyi gabanta na faɗuwa saboda ba abunda ta tsana fiye da ace zata Rasa SURGEON GENERAL RAFAYET saboda mutuwar son da take yi mashi ta kwallafa rai akanshi a lokacin baya tasa naci sosai akan shi sa'adda suke zuwa gidan sosai,amma tun da ta lura cewa kafin ya ma ɗaga idonshi ya kalli mace aiki ne don sai da ta share 2 weeks a gidan sau ɗaya suka ta6a hada ido shima ɗin by mistake ne ya ɗago a lokacin,abun ya tsaya mata arai, yadda take da kyawun surar nan babu namijin da zaiganta ya kawar da ido batare da ya neme ta ba sai akan SGR,tun a lokacin ta soma fidda rai akan shi amma yanzu aunty laila ta soma dawo da ita kan network,
lumshe idonta tayi tana tuna kyakkyawar fuskarshi har lokacin sofwan na manne da jikinta ya lafe mata kamar wani maye,
  ƙara kara wayar tayi akan kunnanta tace"Aunty laila komai zan iya yi akan na mallake shi,saboda shine namijin daya haɗa komai da nake kwaɗayi nake tsananin so a jikin ɗa namiji,amma abunda bansani ba aunty layla shin kina ganin zasu kar6e ni in naje gidan a matsayina na ƙanwar matar yayansu?
Wani irin shu'umin murmushi Aunty babba ta saki wato anzo dai dai wurin da tafi so, miƙewa tayi daga zaunen da take agaban mirror tashiga zagaye bedroom ɗin nata tana cewa"Hayaaam baki da Matsala indae a gidan nan ne! Kinsan yarda Abbansu ke da son ƴa'ƴa hannu biyu zai kar6eki abu daya kawai nasani shine dole sai da iznin Abi sannan zai kar6eki don haka kibarmun wannan a hannuna ni zanyi magana da mommynmu tunda ita ke juya shi da zarar tayi mashi magana zai amince!abunda kawai nakeso dake hayaam shine kiyi gaggawar komawa gidan da zama acikin watan nan!Ke bama sai kin je da komai ba tsurarki zaki tafi batare da trolly na kayanki ba,saboda inaso ki fara fakewa da cewa kinje duba Fawan ne da bashi da lafiya daga nan kawai saikiyi zaman ki dirshan babu mai tanka maki saboda duk matasan gidan miskilai ne babu ruwansu,da ace dae yana da ƴa'ƴa mata shine za'a samu matsala kinsan mu mata da bakin ciki da hassada muke....'
  Murmushi kawai hayaam ke saki tana faman lumshe ido tare da cizon pink lips dinta saboda shock ɗin da takeji na sofwan dake bin jikinta da hannun shi yana shafa ko'ina,
  "Auntyna indae ni ce just karki samu damuwa,ki ƙaddara cewa gani can ma acikin gidan ina watayawa ta,ita kuma wannan yarinyar da kika sanar mun cewa tana zaune a gidan tuni zansa su yi mata checking out badai ni bace ba hmmmmmm,
  Dariya aunty babba ta saki tare da cewa"har naji sanyi araina,burina na dab da cika,"
  Sun jima suna wayar kafin daga bisani suka yi sallama da junansu,
   Buge hannun sofwan tayi tare da cewa"duk kabi ka takuramin wai kai wani irin jarababben mutun ne mai nacin tsiya haba mtwww,"taja dogon tsoki
  Baki asake yabi ta da kallo tare da cewa"ni kike ma tsoki wai?wato wannan haɗamammar auntyn taki takira duk ta tunzuraki akan abunda bazai ta6a faruwa ba,duk naji mai kuka tattauna da ita,
  ya fadi yana faman sakin hucin 6acin rai,murmushi hayaam ta saki tare da cewa"Sofwan zamana dakai ya ƙare!!!!!!!
  Zaro ido waje yayi yana kallonta hankali atashe yace"saboda me hayaam?kada kiyimun haka don Allah!amma dae nasan wasa kike mun ko?
  ƴar dariya tayi kafin tace"na ta6a maka wasa irin wannan?zanje na nemi namijin duniya ne!cikakken namiji jarumin gaske wanda ya kasance burin kowace ƴa mace ne shi bazanyi gangancin rasa cikar burina ba sofwan.......
Bata ƙarasa ba ya dauke ta da mari ji kake faaaauuuu!
  Rai a 6ace yace"Wlh baki isa ba hayaam ki katse mun jin daɗina ba!!saboda ke dakikiya ce sam bakisan meke maki ciwo ba wannan wani irin abun kunyane zaki kwasa kawai ki koma gidan surukanku da zama?Anya kuwa yayarki ba mahaukaciya bace.....
   bata bari ya ƙarasa maganar tashi ba ta zame hannunta data dafe kuncinta dashi ta daddage ta zabga mashi zafafan maruka har guda uku sannan tace"karka kuskura ka ƙara kiran auntyna da sunan mahaukaciya!!maganar tafiya kuma ba fashi sofwan inka ga ban tafi ba to wlh numfashi na ne ya tsaya don ko ba ƙafa saina je,😳
  Tuni sofwan ya rikice ganin yarda hayaam ta zabga masa mari batare da jin komai ba,duk irin yarda yake tarairayarta don karya rasa ta amma lokacin guda auntynta ta canza mata tunaninta,
  Kallonta ya shiga yi yana girgiza mata kai yayin da idonshi suka cicciko da kwalla muryarshi a kasalance yace"Hayaam kada kiyimun haka dan Allah!saboda ke na wulaƙanta iyayena na baro komai nawa don muyi irin rayuwar da kikeso,wannan gidan fa duk don saboda ke na gina shi hayaam,ki duba gidan da iyaye na suke ciki duk ya rakwakkwa6e amma saboda ke na gidan wannan katafaren gidan ko don saboda wannan pls hayamm kada kibarni komai kikeso zanyi maki shi," yayi maganar tare da zubewa saman guiwowin shi a gabanta yana faman sharara hawaye,amma maimakon yaga alamun tausayi a idonta saima ta fashe mashi da dariya tashiga tafa hannaye tana cewa"sofwan kaifa dakanka kace ka wulaƙanta iyayenka saboda Ni?shin ni wacece a wurinka?mutumin da bai daraja iyayensa ba musamman uwarsa data tsugunna ta haifeshi taci baƙar wahala kanshi!ga kuma mahaifinsa daya fitar da gumi wurin nema masa kyakkyawar rayuwa duk bai duba wannan ba,burinka kawai ka farantama wasu can waɗanda basu son ciwonka ba,waɗanda ko yau ka faɗi ka mutu wlh shewa zasu yi suce Allah raka taki gona,shine har kake mun kwatance da ka wulaƙanta iyayenka don saboda wata banza can Ni?hanyar Aljanna nake sanya ka kota wuta?ko zan taimake ka ne ranar lahira?sofwan haƙƙin iyayenka ma kawai ya isa ya tarwatsa dukkan wani farin ciki na rayuwarka!!idan ma naci gaba da ra6arka nima zan shiga matsala ne don haka kawai muyi break up kawai kowa yayi rayuwarshi,"
  ta ƙarasa maganar tare da ruƙe waist dinta tana kallon shi a tsiyace,
  Miƙewa yayi daga kneel down din da yayi ya kalleta da fuskar tausayi yace"kada kiyi mun haka hayaam indae alaƙata da iyayena ne zan gyara komai...'
  girgiza mashi kai tayi tare da cewa"na yaushe sofwan?hmmm ba don Allah zama kayi masu ba sai don saboda ni abanza kam,shiyasa koda yaushe soyayyar SGR take ƙara ninkuwa araina duk da irin tarin dukiyar dake gare shi hakan baisa ya canza ma iyayenshi ba ko wani nashi,zokaga Namijin gaske mai tsananin biyayya ga iyayensa wanda yasan darajarsu yake binsu sau da ƙafa kaifa? Har yau mahaifinka bai daina siyar da kifi a gefen titi ba, ga Mahaifiyarka cen kullum safiyar Allah sai tafito da murhu kopar gida tana suyar ƙosar da kunu,taya ma zan cigaba da kasancewa dakai!!? Kana da arziƙin da zaka iya ciyar da karuwai ka gina ma iyayensu gida ka kuma gina masu su kansu Amma iyayenka fa!!!?
  shiru Sofwan yayi yana kallonta idanun shi sunyi jawur dasu ga wani ƙululun baƙin ciki daya tsaya masa a maƙoshinsa,
  Wuce wa hayaaam tayi wurin wardrobe dinshi saboda anan kayanta suke nasawa, hannu tasa ta buɗe wurin kayanta tana raira waƙar nan ta namej dayake cewa"ko babu mota ba abun hawa wlh saina jee,"
  A wani irin fusace Sofwan ya cafki hannunta data ruko bra dinta dashi,dakatawa tayi da yin waƙarta ta tace"Malam sakarmin hannu na,"
  Yana wani irin huci yace"Hayaam baki isa kibar gidan nan ba, batare da kin mayar mun da duk wani abu dana kashe maki ba!!wlh bazaki ci bulus ba,duk kin taƙaitani duk ƙarshen wata saina kawo maki kayan abinci kwalin indomie kwalin taliya da sauran kayan abinci, sannan duk ƙarshen sati muna zuwan shopping mall dake nayi maki siyayya kuma mu fita restaurant cin abinci,ga kuma kuɗin mayukan da nake siya maki su kansu kudinsu yakai na dubu dari biyar,in kin ga kin bar gidan nan to ki tabbata kin haɗa mun kuɗaɗe na kin mayar mun dasu," ya ƙarasa maganar yana jifanta da wani irin kallo,
  ta6e baki tayi tare da cewa"Naji duk zan biyaka ni kuma da me zaka biyani jikina da kayi amfani dashi?donni ma bazaka Ci bulus ba tunda ba uwar mutun ta haife ni ba,ka biyani budurcina nima saina biyaka kudinka"A shagale take maganar tana faman sakin murmushi,
  Shiru sofwan yayi yana faman mazurai aransa yana tunanin taya zai biyata virgin dinga da take magana akai?
  tsoki taja tare da buge hannunshi tabar shi tsaye a wurin ta koma daga gefe tana zura brazier dinta,
  Muryarshi ce ta kuma katse ta da cewa"naji wannan tabbas bazan iya biyanki budurcinki ba,amma inaso ki sani bazan bari ki ɗauki ɗaya daga cikin abunda nasiya maki ba da kudina,daga ciki kuma hada kayan sawa don dama a tsiyace kikazo gidan nan,
  harara ta wurga mashi tare da cewa"Matsalarka ce wannan!ae ni abun kunya gaba na bashi ba baya ba,in ka hanani sa sutura sai in tafi a zir abuna,"
ganin tana shirin ɗaura mashi hawan jini yasa shi buga jikin wardrobe din da hannunshi yana kallonta idonshi jawur rai a tsananin 6ace ya fuce yabar mata ɗakin gaba daya,
Murmushi tasaki tana cizon la66anta aranta tace"ƙaramin ɗan duniya har ni zakayi wa barazana,"

*******************

Tsare ta da ido hafsat tayi wadda shigowarta kenan  bedroom din ta,
Ta jima a la6e tana sauraron firar da mommyn nata keyi da Hayaam a waya, sai da tabari ta kammala sannan tashiga daga cikin ɗakin tana kallonta, tunkan tace wani abu aunty babba tayi saurin cewa"to ƴarsa ido uban me yakawo ki dakina?
murmushin takaici hafsat tayi kafin tace"narasa meke damunki mommy!gaba daya naji wayar da kikayi da aunty hayaam,saboda me zaki ce ta tattara kaya ta koma gidansu Abbana da zama?wannan wane irin abun kunya ne ace ƙanwar matar yayansu tana rayuwa acikin gidansu? menene alaƙarta dasu?gsky wannan tsarin sam baiyi ba mommy yakama ki dakatar da hayaam daga zuwan gidansu........'
tunkan taƙarasa aunty babba ta kwatsa mata tsawa tare da cewa"munafuka!!ashe la6e kikeyi mun ni narasa gane meke damunki hafsat!!tunda waɗancan yaran da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login