Showing 63001 words to 66000 words out of 245004 words
Chapter 22 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
sai zuwa ake ana kwashe sudents ɗin ita gatanan tsaye zugudum babu alamar wani zaizo ya ɗauke ta,
tana cikin wannan tunanin motar JUNAID tashigo cikin makarantar adai² inda take tsaye yayi parking ɗin motar tare da zuge glass ɗin motar yace "madam muje ko," ajiyar zuciya ta saki ba ƙaramin daɗin zuwan shi taji ba, buɗe motar tayi tashiga sannan yaja motar suka fita daga makarantar,
Miƙar hanya yayi dasu yana cikin driving ɗin yaji sehrish ta faɗo masa a kafaɗarsa ta langwa6e, saboda shock ɗin daya ji har saida yaɗan ci burki a tsakiyar titin, aza idonsa yayi akanta, wani irin wahalallan bacci ne ya ɗauke ta batare da saninta ba, shine ta faɗo masa a shoulder ɗinsa, gaza janye idonsa yayi akanta yadda take ta faman sharar baccin ta ba ƙaramin kyau tayi masa ba, ya jima yana kallon kyakkwawar fuskarsa, sam.ya manta cewa a tsakiyar titi suke, sai go slow suke haɗawa batare da saninsa ba, har sai da wani babban mutun yayi masa magana ta waje, sannan ya tashi motar yaci gaba driving ɗinsa cikin kasala,
har suka ƙaraso gidan adai² parking space ɗinsu ya ajiye motar, sannan yajuya ya kalli sehrish tare dasa hannunsa ya shafa gefen fuskarta tare da ambaton sunanta"Sehrish mun iso gida fa, wake up pls ," ya furta yana kallon yadda take motsi da idonta alamun zata tashi,
daker ta iya buɗe idonta tana kallon shi sunyi jawur dasu ga bacci ga yunwa, junaid yace "reesh kamar baki lafiya fa? Look at ur eyes fa sun janza kala,
A kasalance tace "yunwa nake ji sosai banci komai ba tunda naje school, ga wani wahalallan bacci da nake ji," ta ƙarasa maganar tana faman yin hamma, har time ɗin suna acikin motar,
Tun da tasoma magana junaid ya saki baki yana kallonta har sai da takai ƙarshen maganarta sannan yace "Kina nufin wai baki ci komai ba a school to saboda me? Ya tambaya yana kallonta
Yamutsa fuska tayi tare da cewa "junaid ban fa da ko sisi balle na sayi abinci, shiya sanya,"
Wani irin kallo junaid ke bin ta dashi kallon na tausaya maki, ga takaicin daya hanasa yin magana,jin yayi shiru yasa ta cewa "ka tashi mu shiga ciki, kuma naga kana kallonta,"
A ƙule yace "Haushi kika ban ne,shiyasa nagaza magana, reesh waya ce maki sai kin biya kuɗi zaki ci abinci? An fa riga anbiya kuɗin komai na school ɗinki, tun daga school fees har kuɗin abincin ki dana school bus da zaki dunga hawa har na tsawon 3 months fa,"
Jin haka yasa sehrish zaro ido waje baki asake tana mamakin ashe itace shashashar batasani ba ta hana kan ta cin haƙƙinta, ashe an biya kuɗin komai ita kanta takaicin ne yasa ta yin kasaƙai,
Fitowa sukayi daga motar atare suka shige cikin gidan a babban falon suka rabu ta wuce bedroom ɗinta shi kuma ya wuce upstairs ɗakinsa, babu kowa acikin gidan abunda ya ɗaure mata kai,
tana shiga ciki tayi wurgi da school bag ɗin sannan tashiga tu6e uniform ɗin suma duk nan tayi watsi dasu saman gadonta, bayan ta kammala ya rage daga ita sai half vest da gajeran wando, toilet tashige shaf shaf tayi wanka tare da ɗauro alwala tafito, cikin hanzari ta buɗe wardrobe ɗinta ta zumbula doguwar riga, sannan ta zura hijabi tare da shimfiɗa darduma ta kabbara sallar, tana kammala sallar ko addu'a bata tsaya yi ba, ta haye saman gadonta ta baje tashiga sharar bacci maganar yunwa kuma wata'kil saita tashi sannan tashiga neman abinci,
Turo ƙopar Azmee tayi ta sameta tana ta jan minshari bin ko'ina tayi da kallo ganin yarda tayi wurgi da school bag ɗinta ga uniform ɗinta data watsar saman gadon, murmushi kawai tayi tare da girgiza kai tace "ƴan makaranta kenan, tun yau anfara wurgi da shool bag ga uniform a watse saman gadon maimakon ta ninke su," ta faɗi da murmushi a fuskarta sannan taja mata ƙopar ta fuce,
ta jima tana bacci sai wuraren sallar la'asar sannan tafarka da wata irin matsiyaciyar yunwa ba arziƙi ta fito ta wuce kitchen, har time ɗin babu kowa, roƙon da take yi Allah yasa babban yaya ba us suka koma ba,
Acikin tray ta haɗa abincinta sannan ta zauna a kitchen ɗin tana ci tana tunanin duniya,'
**********Twins***************
Duk yinin ranar ba inda suka je saboda tashin hankali sam sun rasa inda zasu tsoma ransu, tun da sanyin safiya bayan sun dawo daga sallar asuba, haroon ya faɗo masu ɗaki domin ya ƙara jaddada masu akan buƙatun daya nema a wurinsa, Jahan ya tsawatar masa akan cewa ko nawa yake so zasu bashi amma kada ya sake yayi kuskuren cewa zai ƙara kusantar ɗaya daga cikinsu, da jin wannan maganar sai haroon yace ya amince amma bisa sharaɗin cewa zasu ƙara mashi miliyan 80 in har suna son ya daina bibiyarsu Kuma cikin sati guda kacal ya basu in ba haka ba zai tona masu asiri 😥😳
tun safe basu ci komai ba, ko fitowa ba suyi ba daga bedroom ɗinsh, kuma babu wanda ya lura da hakan illa junaid da yayi ta tambayarsu har ɗakinsu sai da yazo yayi ta faman knocking yana kiran sunan su, suna jin shi tamkar zasu yi kuka amma basu amsa mashi ba,ƙarshe yayi tunanin cewa basa nan yayi tafiyarsa,
Ayaaan ya sha kuka aduk lokacin daya tuna abunda ya faru dasu daren jiya sai yayi yunƙurin amai, yanzu haka ma yana zaune gefen gadon idonsa jawur ya ɗago ya kalli jahan dake ta faman safa da marwa acikin ɗakin yace "Dan Allah jahan mu hanzarta mu sama mashi kuɗin daya buƙata, if not wlh so yake ya kashe mana rayuwa," ya faɗi yana faman matse hancinsa da yayi jawur saboda matsar daya sha da hannunsa,
Jahan ya dubesa cikin damuwa tare da cewa "Ayaan bansan ya zanyi ba ! Wa zan fara tunkara game da kuɗin nan? duk wanda zamu tambaya acikin brothers ɗin mu ko Abban mu dole sai sunji me zamuyi dasu kafin su bamu, daga baya ma zasu tambaye mu ina abunda muka siya dasu, don haka Mommy ce kawai nake tunanin zata iya bamu kuɗin amma matsalar shine tana fushi da mu saboda bama kiranta a waya muna gaishe ta," Jahan ya ƙarasa maganar tare da samun wuri ya zauna kusa da Ayaan ɗin,
"Jahan mom ita kaɗai ce solution, mu jaraba kiranta kawai mu sanar mata mu ji mai zata ce,"
"Video call zamu kira ta, may be tafi tausaya mana in taga yanayin mu" Acewar jahan, yayi maganar tare da miƙewa ya ɗauko laptop ɗinsu dake ajiye saman drawer ɗinsu, komawa yayi ya zauna dab da Ayaan sannan ya zaro wayarshi tare da buɗe laptop ɗin, duk ayaan na zaune zugudun yana jiransa ya kira,
zama su kayi suka ƙurama screen na laptop ɗin ido suna jiran mommyn nasu ta ɗaga kiran cikin sa'a ta ɗaga masu kiran, har haɗa baki suke yi wurin cewa "Mommy," tana zaune cikin haɗaɗɗen garden saman gujera hannunta ɗauke da cup na coffee da alama sha takeyi, ta jima tana kallonsu sai daga bisani tace "sai yau kuka ga damar kira na"?
"Sorry mom ba haka bane.....," suka faɗi atare, girgiza kai alexandra tayi tare da cewa "to menene? halan wani abu ku ke buƙata shiyasa kuka kira ni"?
Shiru su kayi suna kallonta ba bakin magana, tsoki taja tare da cewa "if u can't talk to me, i will reject the call right now"!
Cikin sauri jahan yace "pls mommy don't reject the call, zamu yi magana, pls Ayaan kayi mata bayani" ya faɗi yana kallon Ayaan shima murya tamkar zaiyi kuka yace "Jahan i don't know what to say, kai kayi mata bayani pls," mamaki ne ya kama Alexandra ganin yadda suke ta jayayya akan wanda zaiyi mata bayanin dangane da kiran da sukayi mata,
tsawa ta daka masu tare da cewa "bana son shiriri James! kuyi mun bayanin kiran da kuka yi mun within 5 mins if not zan kashe kiran "
Natsuwa su kayi gaba ɗayan su sannan jahan ya soma cewa "Mom dama.....um......kuɗine...muke....so...awurin ki, ki bamu,"
tana jin haka ta fashe da dariya hankalin su ba ƙaramin tashi yayi ba jin yarda mommyn nasu ke 6a66aka dariya,
Ayaan yace "mom why are u laughing pls, don Allah ki tausaya mana mommy muna cikin wani hali ni da Jahan....' dakatawa tayi sannan ta soma magana anatse "Har nawa ne kuɗin"?
Jahan yace "80million,"
ɗan zaro ido tayi tare da cewa "har 80m? what are going to do with it?
Ayaan yace "mom dan Allah kada ki tambaye mu me zamuyi dasu, saboda ba zamu iya yi maki ƙarya ba, kawai ki taimaka ki ba mu,"
Murmushi ta ɗan saki tana kallonsu na wani lokacin kafin tace "Ni a wuri na miliyan tamanin tamkar naira tamanin take, naji zan taimaka na baku amma bi sa sharaɗi ɗaya"! Har sun fara sakin fara'a amma jin maganarta ta ƙarshe yasa su dakatawa da murna,
Jiki asanyaye Jahan yace "what mom"?
alexandra tace "Inaso ku sa ROMEO ya kira ni a waya, sannan ya kira ni da sunan mommynsa Kuma ya bani haƙura na bijire mun da yake yi, kiran yakasance video call ne, in har ku ka sa romeo ya amince ya kira ni awaya,i promise to give each one of u 50 50millions,' tayi maganar tare da jaddada musu,
Zaro ido suka yi gaba ɗayansu ga samu ga rashi, domin kuwa sunsan cewa Junaid bazai ta6a kiran mahaifiyarsu ba harya bata haƙuri kuma ya kirata da sunan mommynsu tabɗijancan,
gaba ɗaya sun tafi zurfin tunani suka ji tace "i will be waiting to hear from u guys," tana faɗin hakan ta kashe video call ɗin,
Hannu ayaan yasa ya rufe laptop din sannan ya kalli jahan wanda shima kallonsa yake yi yace "Yanzu ya zamuyi jahan? ga samu ga rashi ! duk da nasan junaid yana son mu sosai kuma yana yi mana biyayya zai iya yi mana komai amma banda wannan ALFARMAR,
zugudum su kayi cikin tsananin tashin hankali da kuma tunanin yarda zasu tunkari junaid da maganar! 😥
***********JAHAD***********"**
a hankali ta soma buɗe idanunta biji² ta dunga gani a idonta, daker take motsa su zata buɗe su, sai faman ambaton sunan Allah take yi a hankali,
lokacin da taƙarasa buɗe idanun nata mamaki ne ya kamata ganin ta kwance a wani ɗaki, komai na cikinsa fari ƙal a tsaftace, ga mutanen dake tsaye akanta farare fat hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, gaba ɗaya ranta ya bata cewa mutuwa tayi ne, saboda yanayin wurin da ta gani fari ga mutanen dake tsaye akanta farare, hawaye ne suka soma zubo mata a idanunta cikin kuka take cewa "Ya Allah kasa ba mutu nayi ba,nabar hussana aduniya wurin wancan fasiƙin mutumin, nashiga uku wa zai taimake ta acan, meyasa mutuwa bata ɗauke mu, mu biyu ba atare? Sai ta ɗauke ni nikaɗae tabar hussana a waccen duniyar mai cike da ruɗani," gaba ɗaya jahad ta fashe musu da kuka, Hankalin nurse ɗin dake tsaye da likitan ba ƙaramin tashi yayi ba, cikin sauri su kayi kanta, ko da jahad tagansu sai ta ƙara sautin kukan tana cewa "innalallahi wa'inna ilaihirraji'un,! dan Allah su wanene ku farare haka, ina hussana take,
zama nurse ɗin tayi daga gefenta sannan tace "Sannu da jiki ƴar uwata, ni ce nurse ɗin dake kula da ku, sunana Camila ke fa"?
Jin tayi mata magana raɗau da hausa yasa jahad dawowa cikin hayyacinta sosai tana kallonta da mamaki, kana kallonta ka ga english woman, Cos majority na ma'aikatan asibin sgr daga u.s suke, wasu daga india, wasu kuma ƴan nan nigeria, akwai kwararrun likitoci da nurses acikin asibitin,
ƴunƙurawa jahad tayi zata tashi cikin sauri Camila tasa hannu tare da mayar da jahad kwance tace "Ana miki ƙarin jini ne, ko baki lura ba ne"? ta faɗi tana kallonta da murmushi a fuskarta,
ɗan juyawa jahad tayi ta kalli ledar ƙarin jinin da akeyi mata,
sassauta muryarta tayi sannan tace "sister dan Allah ina ne nan? Kuma waya kawo ni nan?
Murmushi Camila tayi sannan tace "nan asibiti ne, sannan yayanki ne ya kawo ki domin mu baki kyakkyawar kulawa!"
Cikin mamaki jahad tace "Yayana kuma? ae ni bani da kowa aduniyar nan ƴar uwata ce kawai hussana nasani, dan Allah tana ina"? tayi maganar tana jiran amsa,
duk tattaunawar da suke yi dr Emran na tsaye yana jin su , kafin Camila ta buɗe baki tace wani abu sai ga MARSHAL OMAR ya shigo ɗakin shida Major, gaisawa su kayi da dr emran, sannan ya matsa wurin da jahad ke kwance,
tsayawa yayi yana kallonta fuskarshi asake saboda ganin yarda ta wartsake alamar tasamu kyakkwar kulawa awurin Nurse ɗin,
Sam jahad bata lura da marshal omar ba dake atsaye har sai da ya ambaci sunanta "JAHAD,"
A razane ta wurga kwayar idonta akan shi, ganin Ya Omar ɗinsu yasa ta zabura zata tashi zaune da sauri Camila ta mayar da ita, duk tabi ta zazzare idonta tana nuna shi da hannu tana ambaton sunan shi cikin tsananin mamaki,
tashi Camila tayi taba Omar wuri donya zauna kusa da jahad saboda ta lura yarinyar nason magana dashi,
Zama Omar yayi saman chair ɗin dake facing medical bed ɗin da jahad ke kwance asama sannan yace "Ya jikin naki"? tana jin haka ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, hannunta tasa ta ruƙe hannunsa tana cewa "Ya Omar ina ka shiga tsawan kwanaki kabar mu, bakasan halin da muke ciki ba..........' tana magana muryarta na shasshaƙewa saboda kukan da take, sam Omar ya gaza cewa komai tuni idonsa sun cicciko da kwalla,
Jahad taci gaba da cewa "Ya Omar har yanzu nagaza yarda cewa kaine! dan Allah kayi mun magana taya akai haka tafaru ya omar, kuma ina hossana take? mutumin nan ya gudu da ita ya omar..........." kasa ƙarasa maganar tayi saboda hannunsa daya sanya ya rufe mata bakinta........................................
*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®️_* ✍️
──────────────29
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•
bin idanunta yayi da kallo itama tana kallon nashi hawaye ne cike taf da idonta, bai janye hannunsa daga bakinta ba har sai da ya tabbatar cewa ta samu natsuwa sannan ya zame hannunsa yace "Jahad duk wani abu dake faruwa ni bansani ba,bani da masaniya akai,jiya ne aka turomin saƙo da privet number bansan ko wanene be,let me show the message,
Hannu yasa ya curo wayarsa daga trouser pocket ɗinsa kunna wayar yayi sannan ya shiga wurin messages ya buɗe saƙon ya nuna ma jahad don ta gani,
Zuba ma screen ɗin wayar tayi da ido tana karantawa kamar haka
_"Omar ka yi ganganci daka bar rayuwar yaran nan a hannun Laila, ina baka shawarar ka hanzarta zuwa ka ɗauko su, saboda naji cewa gobe goben nan za'a fitar dasu daga gidan_"
Janye wayar yayi sannan yace"lokacin da message ɗin ya shigo mun bana cikin natsuwa ta, saboda mun shiga tashin hankali,ƙanne na da aka tura aiki miyagu suka farmake su, mun samu nasarar ceto rayuwarsu kuma mun kama wasu daga cikin waɗanda suka farmake sun, yanzu haka da nake maki magana ɗaya daga cikinsu yana kwance a A&E ward, baisan inda kansa yake ba,saboda sai da suka banka mashi kayan miyagun ƙwayoyi sannan suka azabtar dashi, ba don Allah yasa an samu wani daga cikinsu ba yayi mana waya da shikenan ba'asan mai zai biyo baya ba,
Shiru Omar ya ɗanyi na wani lokaci kafin yaci gaba da cewa "tun shekaran jiya da muka fita daga gida muna can wurin cetonsu,a asibitin nan aka kwantar da waɗanda suka raunata sosai daga cikinsu,gaba ɗayan mu babu wanda ya samu runtsawa adaren jiya saboda tashin hankalin kada mu rasa su,kuma a daren jiyan ne acikin asibitin nan saƙon ya shigo mun,duk nabi na rikice saboda narasa yarda zanyi, Major shine babban na hannun dama na, shi na kira na nuna mashi saƙon da aka turomin game daku, koda ya gani sai cewa yayi dama ya jima yana son ce mun wani abu, amma ba zai iya sanar dani ba saboda bayason shiga tsakanina da matar yayana, sai abun ya ɗaure mun kai jin abunda yace,a lokacin ban matsa masa ba akan son sanin wani abu ne yake son sanar dani ba,a time ɗin duk da halin da nake ciki burina kawai inzo in ganku, Major shine yace nabar masa komai a hannunsa kar na damu, sai a washe gari major ya sanar dani cewa mu shirya mu tafi, sannan kuma yaban wata number yace mu bi diddiginta, atare dashi muka fito mu biyu kawai muka miƙi hanya, da wayata nayi amfani wurin bindiddigin numbar daya bani har muka ƙaraso titin da dajin nan yake,mu ka shiga cikinsa kai tsaye, muna cikin tafiya naji an kwala mun kira ta waje "yalla6ai," cikin sauri na zuge glass ɗin motar don naga wanene, shine naga wani saurayi zuƙunne a ƙasa, ga ki kuma kwance a sume duk jini a goshin ki, hankali atashe na zabura zan fito daga cikin motar, kawai sai saurayin nan yace "yalla6ai ya gudu da ɗayar acikin motarsa, gashi can ya miƙi hanyar da tayi dama don Allah ku ceto rayuwarta, " jin haka yasa gaba ɗaya na rikice, cikin sauri major yaja motar mu da gudun gaske muka bi motar wannan tsohon mutumin da gudun gaske har cikin gidan gonarsa, ina shiga najiyo kukan hossana hankalina ba ƙaramin tashi yayi ba, tuni na makance na afka ma ƙopar ɗakin gidan gonar na tarwatsa ta, ina shiga naga hossana a lokacin har yayi nasarar yage mata rigarta ya ruƙe ta a hannunsa, raina yayi mugun 6aci abunda ya hanani yin motsi a lokacin saboda