Showing 90001 words to 93000 words out of 245004 words
Chapter 31 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
motar yayi control dinta, Amma saita janyoshi jikinta ta kankame suka bar motar Tana control din kanta,
Cikin ikon Allah motar ta kashe kanta adai dai bakin bishiyar ƙiris ya rage su gabje ta da ba ƙaramin buguwa zasu yi ba,
Ajiyar zuciya suka shiga sauke wa tare da dagowa atare suna kallon bishiyar, Allah ya takaita wahala da motar ta kashe,
Sai faman zazzare Ido suke Yi su duka biyun, sun ji kamshin mutuwa, juyawa Sehrish yayi tare dasa hannu ta zuge glass din motar Don taga wanene ya bugi motarsu,
wata bakar motace Mai black tunted kirar range Rover, Kamar jiranta suke ta leƙo,suma na cikin motar suka zuge nasu glass din motar,
Gabanta ne yayi mugun bugawa daraaam !! Ganin mutanen dake cikin motar, giggan Yan iska ba Imani a fuskarsu bakeke ne wulik, kana ganinsu kasancewa turo su akayi, da gangan suka bugi motar Junaid din,"
duk Tasha jinin jikinta, ɗaya daga cikinsu ne ya ɗago mata hannu tare da cewa"hi We're sorry guys mun bugi motarku batare da mun sani ba,kuyi mana afwa,amma yakamata kija masa kunne ya dinga kulawa wurin yin driving yana yin tukin ganganci, hakan zai iya halakar daku wata rana,"
Suna faɗin hakan suka ja motar tasu da gudun gaske suka bar wurin,
Ajiyar zuciya ta sauke tare da juyawa ta kalli junaid wanda yayi wuri wuri da ido, duk a tsorace yake da abunda ya faru dasu,
Murya asanyaye tace "junaid kayi sauri mubar wurin nan,"
daker ya iya tashin motar sannan yaja ta da baya baya suka baro jikin bishiyar, ya hau kan titi dasu sannan ya miƙi hanyar gidan,.
gaba ɗaya sehrish jikinta ya gama yin sanyi saboda ta hasko wani abu game da bugun motar junaid da sukayi,maganar da sukayi mata tamkar gargaɗi ne sukayi mata akan wani abu da zai faru dasu,tabbas tashiga ruɗani,
A hankai suka shiga babban entry din gidan, yayi parking motar sannan suka fito atare kowa na faman sauke ajiyar zuciya,atare suka jera suka nufi cikin gidan
ɗan kallon sehrish yayi ganin tamkar ranta ya 6aci don haka yace "am sorry rishi laifina ne,nayi ganganci dana kunna mana waka acikin mota har muka shagala sosai,"
fuskarta a yamutse tace "its not ur fault junaid, ba ka yi tuƙin ganganci ba,da gangan suka bugi motar mu,karka sama kanka damuwa ni bana ganin laifinka, Allah zai saka mana ma,"
tuni yaji sanyi ya ratsa ransa, bayan sun shiga babban falon ta wuce bedroom ɗinta, shima kuma ya wuce nasa ɗakin,
Shaf shaf ta tu6e uniform ɗinta, asaman gadon tabarsu tare da school bag din duka, toilet ta fada tayi wanka tare da dauro alwala, tana fito wa ta bude wardrobe dinta tare da ciro wata gown mara nauyi ta zura, sannan ta shimfiɗa carpet ta zura hijab tare da kabbara sallah, anatse tayi sallarta, bayan ta kammala bata ko nemi abinci ba saboda taci tayi hani'an a school, gado kawai ta haye tare da baje wa tana bacci,
Shima junaid daya wuce nashi dakin nashi ya faɗa toilet ya yi wanka tare da canza kayan jikin shi izuwa riga da wando,
Yana kokarin fitowa daga ɗakin sai ga su twins sun faɗo ciki atare sun ɗau wankan jeans da t shirt,
Yana ganin su ya saki fara'a tunkan su fara magana yace "maganar kiran mommy ce ko"?
dariya su kayi atare, ayaan yace "ashe dae ka gane,Allah yasa bamu takura maka ba,"
girgiza kansa yayi tare da cewa"a'a yanzun nan zan kirata insha Allah,"
Jahan yace "yawwa masoyi junaid mai son farin cikin ƴan uwan shi,pls idan ka kirataa wayar,kayi mata biyayya kaji? kada kace zaka ƙi mata magana, ita mahaifiyarmu ce,idan bata son ɗaya daga cikin mu ae bazama ta ɗauki cikinmu ba balle har ta ruƙe sa na tsawon wata rana, kuma tayi naƙudar haihuwarsa,nasan kai mai ilmi ne junaid kasan hukuncin wanda ya sa6a ma iyayensa dan Allah ka manta da komai," yarda jahan ke yi masa nasiha cikin daɗin rai yasa shi jin sanyi aransa harma yaji cewa ya ƙosa ya kirata a wayar,
"Shikenan ya jahan da ya ayaan,zan kirata yanzun nan amma ba a gabanku zanyi wayar ba,idan nagama dae zan sanar daku duk yarda mukayi da ita,"
Cike da farin ciki suka ce "yawwa ɗan ƙanin mu, yanzun nan kuwa zamu fita daga ɗakin,sai mun ji ka," suna fadin hakan suka juya tare da fucewa daga ɗakin hada rufo masa ƙopar da kyau,
ɗan murmushi junaid yayi sannan ya koma gefen gadonsa ya zauna tare da kai hannu ya ɗauki wayarsa dake asaman side drawer,
Zuba ma screen ɗin ido yayi yana tunanin ta yarda zai fara kiran mommyn tasu, for the first time zaiji muryarta,a lokacin baya kusan kullum saita kirashi awaya bai ɗauka don ko saving na numbarta baiyi ba,saboda haushin ta da yake ji,
A hankali yashiga danna wayar, kai tsaye cikin messages yashiga saboda akwai last messages da ta tura mashi, buɗe sakon yayi ya ƙara karanta shi "Thanks 4 ignoring me, i won't call u again bye,"
tanan ya ɗauki number tare da danna mata kira, ta shiga ringing,
Almost 3 times tana ringing ba'a ɗauka ba,ana huɗunne yana ƙara kira tayi picking,shiru yayi baice komai ba,har sai da tashiga tambayar wanene jin anyi mata shiru, yanayin muryarta akasalance saboda bacci,
Cikin harshen spanish take tambayar wai wanene,
Sai a lokacin junaid ya ambaci sunan "Mommy," shiru tayi tana nazari don ta gano muryar wacece wannan acikin ƴa'ƴanta,bakowa bane ya faɗo mata aranta ba face Romeo ɗinta duk da basa waya amma abbansu na turo mata voice ɗinshi da yake mata recording aduk lokacin da suke fira dashi ko kuma lokacin da yake tsaka da shagwa6a,
tuna wannan yasa Alexandra cewa "Romeo ɗina ne"? Ta tambaye shi donta tabbar cewa shiɗinne da take hasashe,
Ashagwa6e yace "junaid ɗin abbana ne,"
Jin hakan yasa alexandra tashi daga kwancen da take asaman shimfiɗeɗen gadonta, cikin sauri takai hannu ta kunna bedside lamp, bedroom ɗin nata ya ɗanyi haske tamkar zata iya gashinin zahiran agabanta, cikin tsananin farin ciki tace "allah yasa ba mafarki nake ba,romeo da kan shi yau ya kira ni a waya, harya kirani da sunan mommyn shi, cikin tsantsar farin ciki take maganar,
Duk junaid na sauraronta sai da takai aya sannan yace. "Mom ki ƙaddara cewa mafarkine, saboda bashi da banbanci da mafarkin cos i called u by force ba don son raina ba, ya faɗi with angry face tamkar yana agabanta,
murmushin takaici tayi kafin tace"na sani dama saka akai ka kira ni,koma manene laifina ne nasan fushi kake yi dani,baka sona romeo ni kuma nadamu dakai sosai.....' ta faɗi cikin muryar kuka,
"Mom ba ki sona,da ace kina sona da baki tafi kinbarni ba a lokacin da bansan komai ba soyayyarki kawai nake buƙata da kulawarki, amma duk wannan bai dame ki ba,kin tafi kinbar ɗan jinjiri ya yi rai ko kar yayi duk bai dame ki ba,kashe ni kika so kiyi............'
Fashe mata da kuka yayi mai cin rai, nan da nan hankalinta ya tashi duk yadda taso ta lallashe shi ya daina kukan amma yaƙiya,janye wayar tayi daga kunnanta tare da zuba ma screen ɗin wayar ido tana sauraron kukan shi, har cikin ranta ba ƙaramin ɗaci ta ji ba, tama rasa ta yarda zata fahimtar dashi, Sai da junaid yayi mai isar shi sannan ya tsagaita yana faman sauke ajiyar zuciya,
Jin haka yasa tace "pls can i turn it to video call,cos i wanna see u face to face,"
Rai a6ace junaid yace "ban amince ba mommy,if u really want to see my face then come to nigeria,"
Murmushi taɗanyi sannan ta kuma cewa "ka yafe mun junaid ɗin abbansa,ba don bana sonka ba na tafi nabarka, nafi kowa sonka junaid saboda ni na haifeka,duk da nasan cewa a wurinka bancancanta na amsa sunan mahaifiya ba, amma inaso kaa sani nikaina ba'a son raina nabar ƴa'ƴana ba, bakowa bane ya son da wannan ba saboda ba kowane zai yarda dani ba, amma an takuramun an ƙuntatamun ko bacci bana iyayi a ƙarshe ma naji ƙasar gaba ɗaya tafita raina na dinga jin tamkar ƙona fatar jikina akeyi wannan shine dalilin dayasa nabar ƙasar, kai kuma abunda yasa ban tafi dakai ba shine, soyayyar da mahaifinka ke yi maka,idan na tafi dakai ya zai ji a zuciyar shi? shi kan shi bai fahimci hakan ba kowa tunaninsa na tafi don son raina ne amma ba haka bane junaid, akwai wani 6oyayyen lamari dake faruwa acikin gidan nan,nayi ƙoƙarin na fahimtar da abbanku saboda ni ina da masaniya akan wani abu, amma abbanku sai ya nuna mun cewa kawai don na tsani baƙar fata ne yasa nake zargin wasu,bayan ba haka bane ni duk wanda na tsana hakanan batare da wani dalili ba to yana da wata muguwar manufa ne... '
Shiru junaid yayi yana sauraronta, bai cika ɗaukar komai serious ba arayuwarshi amma maganar mommynsa taɗan ta6a shi kaɗan, bazai ce ƙarya take masa ba saboda shi kanshi ya jima yana tunanin dalilin dayasa mom ɗinsa tabarshi, saboda shi ya kasance yaron da kowa ke so mai farin jinin gaske, taya za'ace uwar da ta tsugunna ta haife shi, itace zata ƙisa ta guje shi just without any reason !?
Idan ka samu kaɗan ka gode ma Allah gobe saiya baka mai yawa😁 Cikon page din ɗazu dama 3 page nace zan haɗe maku, sa'an nan ku gyara zama 😱😨
Ina guga ina editing gashi nan har na ƙona mata hijabi ynx jira nake tadawo inga mai zatayi mun😇🤣
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku🤩😍
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
_💋Boss Bature💋_
Murmushi taɗanyi sannan ta kuma cewa "ka yafe mun junaid ɗin abbansa,ba don bana sonka ba na tafi nabarka, nafi kowa sonka junaid saboda ni na haifeka,duk da nasan cewa a wurinka bancancanta na amsa sunan mahaifiya ba, amma inaso kaa sani nikaina ba'a son raina nabar ƴa'ƴana ba, bakowa bane ya son da wannan ba saboda ba kowane zai yarda dani ba, amma an takuramun an ƙuntatamun ko bacci bana iyayi a ƙarshe ma naji ƙasar gaba ɗaya tafita raina na dinga jin tamkar ƙona fatar jikina akeyi wannan shine dalilin dayasa nabar ƙasar, kai kuma abunda yasa ban tafi dakai ba shine, soyayyar da mahaifinka ke yi maka,idan na tafi dakai ya zai ji a zuciyar shi? shi kan shi bai fahimci hakan ba kowa tunaninsa na tafi don son raina ne amma ba haka bane junaid, akwai wani 6oyayyen lamari dake faruwa acikin gidan nan,nayi ƙoƙarin na fahimtar da abbanku saboda ni ina da masaniya akan wani abu, amma abbanku sai ya nuna mun cewa kawai don na tsani baƙar fata ne yasa nake zargin wasu,bayan ba haka bane ni duk wanda na tsana hakanan batare da wani dalili ba to yana da wata muguwar manufa ne... '
Shiru junaid yayi yana sauraronta, bai cika ɗaukar komai serious ba arayuwarshi amma maganar mommynsa taɗan ta6a shi kaɗan, bazai ce ƙarya take masa ba saboda shi kanshi ya jima yana tunanin dalilin dayasa mom ɗinsa tabarshi, saboda shi ya kasance yaron da kowa ke so mai farin jinin gaske, taya za'ace uwar da ta tsugunna ta haife shi, itace zata ƙisa ta guje shi just without any reason !?
gaba ɗaya ya tafi duniyar tunanin ya amince da zancen mahaifiyar shi ko kuwa, shessheƙar kukanta daya ji ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa cikin sauri yace "its okey mom,ni banason nayi sanadin da zan zubar da hawayen wani,bare ke da kike mahaifiyata ma,"
Ajiyar zuciya alexandra tashiga saukewa jin kalamansa masu daɗin gaske, muryarshi ce tasake katse ta da cewa "pls wipe ur tears mom,"
Murmushi ta saki tamkar tana agabansa,hannu ɗaya tasa tana share hawayenta kamar yarda ya umarta tayi,
. bayan ta gogesu tace "baka son ganin hawaye ne? amma meyasa baka amsa kirana duk in na kira wayarka, ko na kira wani nace ya baka muyi waya,a duk lokacin da hakan ta faru ina zubar da hawaye na sosai,
Murya asanyaye take magana, har cikin zuciyarshi yake jin maganar mommyn nashi,
"Mommy inaso zan aje waya,i wll call u next time,
Cikin sauri tace "ka haramta mun ganin fuskarka ko? Shikenan my romeo,ka faɗi kome kake so zan maka shi"
"Komai nace kiyi zaki yi ne"? Ya tambaya yana jiran amsa
"zan yi maka shi koma menene,"
murmushi junaid yayi sannan yace"yaya ayaan da jahan suna son wani abu wurin ki, kiyi masu shi, sannan ki dawo gida ki bani kulawar da baki bani ba tun ina yaro,"
Murmushi tayi sannan tace"shi kaɗai kake so"?
Yace "eh,"
Jinjina kai tayi tare da cewa"duk abunda kace zanyi saboda in tabbatar maka da cewa ina tsananin ƙaunarka my romeo,sannan koda daga bayane kaga wani abu kana so ka sanar mun, zanyi maka koma menene shi indae acikin duniyar Nan yake, sun jima suna yin wayar daga bisani su kayi sallama, bayan ya ajiye wayar ya dinga jin wani irin sanyi na ratsa zuciyarshi ga wani irin kwanciyar hankali da yazo mashi yasan cewa duk saboda wayar da yayi da mom in shi ne yasamu wannan natsuwar,
Sai wuraren ƙarfe 4'dai dai sehrish ta farka tana faman yin hamma, ba ƙaramin daɗin baccin taji ba,saukowa tayi daga saman gadon nata ta wuce toilet jim kaɗan tafito da alwalarta, hijab ta dauko ta zura a jikinta sannan ta kabbara sallah, tun tana cikin yin sallar taji ana knocing ƙopar ɗakin nata, don haka tana kammala shafa addu'a ta miƙe a hanzarce ta buɗe ƙopar,gabanta ne taji ya faɗi rass ganin matar nan ta ɗazu,murya na rawa tace "ina yini," murmushi Amani tayi tare da cewa "lpy ya kike,"?
"Ina lpy," ta bata amsa ataƙaice,
dan ta6e baki amani tayi kafin tace"naso ɗazu dana ganki da safe muyi magana amma naga kina cikin sauri ne zaki school," ta fadi a wayance
Sehrish tace"eh hakane," duk tarasa natsuwarta, tsoranta me take son ce mata,
Amani taci gaba da cewa"Tun yaushe kika fara aiki a gidan nan ne"? Saboda ni ban ta6a ganinki ba gsky,"
Sehrish tace"banjima da farawa ba,"
"Amma nayi mamamkin yarda shaƙuwa ta shiga tsakanin ki da mutanen gidan har abbansu ya mayar dake ɗiyarshi,kuma naga kina da kusanci ssae da junaid har yana ruƙe maki hannunki kamar wata ƙanwarsa, bayan matsayinki bai wuce na ƴar aiki ba,"
ɗagowa sehrish tayi a ɗan rikice tana kallonta jin abunda tace,
Murmushi amani ta kuma saki kafin tasanya hannu ta dafa kafaɗar sehrish tace"idan ba damuwa inaso in baki wata shawara wadda zata amfane ki, domin na lura kinason jefe kanki cikin hatsari, karfa ki ruɗa kan ki,".
Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"ina sauraronki," amani taci gaba da cewa"ki nisanta kanki daga kowa na cikin gidan nan,ka da ki bari wani ya so ki acikin matasan gidan nan,kuma kada ki kuskura ki bari zuciyarki ta faɗa tarkon son wani,idan da hali ma ki tsaya a iya matsayinki na ƴar aiki,zaki fi samun kwanciyar hankali,"
Tun da tasoma magana sehrish ke bin ta da kallo fuskarta ta nuna alamun rikicewa don sam batasan inda zancen matar ya dosa ba,
"Kada kice na cika ki da surutu,its just an advise in kinyi amfani da ita ke zata amfana,but if u don't hmmmmm u can even lost ur life........'
Wani irin bugu zuciyar sehrish taji saboda abunda amani tace, na cewa zata iya rasa rayuwarta, tuni jikinta ya shiga yin kerma alamomin tsoro sun bayyana a fuskarta, hankali atashe take cewa"meyasa kika ce haka?saboda me zan rasa rayuwa ta?don kawai naso wani ko wani ya so ni acikin gidan nan"? Ta tambaya tana kallon Amanin,
Kafin Amani tace wani abu, muryar Azmee ta katse mata hanzarinta da cewa"tsayuwar me kuke yi ne, ke da nace ki kira mun ita don tazo mu haɗu mu fara girkin da wuri"? Ta tambaya tana kallon Amani,
. cikin sauri Amani ta dan basar tare da sakin fara'a a fuskarta tace"dama muna ɗan tattaunawa ne,kinsan bata sanni ba nima kuma haka, so ina gabatar mata dakaina ne don musan juna,"
Zuba mata ido sehrish tayi kawai baki asake tana kallonta,
Azmee tace"Hakan na da kyau, sehrish wannan matar yayanku ce Abbas sunanta AMANI,ina fata zaki saki jiki sosai da ita domin kuwa tana da mutunci sosai,
daƙer sehrish ta ƙaƙalo murmushi tace"Insha Allah aunty azmee,"
tayi maganar tana kallon Amanin ita ma kallonta takeyi har lokacin,
Azmee ta lura da kallon kallon da suke yi don haka tace"Amani mu wuce kitchen,ke ma sehrish ki ajiye hijabin jikinki ki zo mufara aiki,"
Juya ciki sehrish tayi su kuma suka wuce kitchen ɗin, kanta ya gama ɗaurewa da maganganun da Amani ta gaya mata,amma duk da hakan ba tajin zuciyarta zata karaya saboda wasu ƴan kalamanta,hannu tasa tare da tu6e hijabin ta ajiye ta nan saman gadon, sannan ta ɗauko ɗan mayafinta cikin wardrobe tayi rolling ɗinsa,
A dai dai lokacin da ta fito daga ɗakin ta tunkari hanyar kitchen ɗin sai ga haroon ya fito daga part ɗinsu,sai da taji gabanta ya faɗi don ita yanzu kallon shaiɗan take yi mashi saboda ƙahone kawai babu akanshi,
Ƙarasowa yayi inda take suna facing ɗin juna yace"mutuniyar ba hello ba hi,laifin me nayi maki ne"? Yayi maganar yana ɗaga mata gira tare da kashe mata ido,
Tsuke fuska tayi tare da bi zata wuce cikin sauri yasha gabanta tare da ware hannayensa yace"daga kin ƙara motsowa zan rungume.........' kasa ƙarasa maganar yayi gabansa na faduwa ba don komai ba