Showing 192001 words to 195000 words out of 245004 words
Chapter 65 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
irin bugu jin tambayar da Aunty azeema tayi mashi,baisan dalilin dayasa tayi mashi wannan tambayar ba,
A ɗan ruɗe yace"Mommy meyasa kikayi mun wannan tambayar"?
shiru ta ɗanyi kamar mai nazarin wani abu kafin taci gaba da cewa"junaid bibiyar rayuwarka akeyi!"
Hankali atashe junaid yace"Ni kuma mommy azeema,to meyasa ake bibiyar rayuwata?su wanene ke bibiyar rayuwata,me nayi masu?kuma me suke so atare dani?"gaba ɗaya ya gama ruɗewa,
"Just calm down ur mind,ba wani abu bane na tashin hankali ba,banaso ka sanya damuwa a ranka junaid,amma ya zama dole na sanar dakai,akwai wata baiwa da Allah yayi mun,duk in nayi mafarki yana xama gaskiya,bawan da yasan da hakan sai ni,abubuwa da yawa kafin su faru acikin gidan nan,ni nake fara ganinsu acikin mafarki na,Allah yana nuna mun...'ajiyar zuciya ta dan sauke tana kallon junaid daya kasa kunne yana sauraronta,
kafin taci gaba da cewa"Nayi mafarki akan ka junaid,mafarkin ya tsoratar dani sosai,wannan dalilin ne ma yasa na nace akan saina zo,ba don komai ba sai don na ganka naga wani hali kake ciki......'
gaba daya hankalin junaid yayi mugun tashi muryar shi na rawa Yace"Mommy azeema,dan Allah ki fahimtar dani wani kalar mafarkine wannan?wani mummunan abune zai faru dani ne?mutuwa zanyi ko?dama najima ina ji araina cewa bazanyi tsawancin kwana ba.........'bata bari ya ƙarasa maganar ba,tasa tafin hannunta ta rufe mashi bakinshi,tsit junaid yayi jikinshi na rawa,zuciyarshi naci gaba da bugawa da ƙarfi da ƙarfi,
Cikin sanyin murya tace"Junaid,babu wanda ya isa yayi maka abunda Allah baiyi maka ba!tabbas rayuwarka na cikin hatsari sosai saboda duk wani dake son ganin bayan zuri'armu ta wurinka zai biyo junaid,dole sae da kaine za'a iya cutar damu junaid saboda kaine lagwon kowannanmu,kaine farin cikin mu gaba ɗaya.....' ƙarasa maganar tayi tare da zame hannunta daga bakinshi,
Jikin junaid yayi mugun sanyi,bakomai ya faɗo mashi aranshi ba face wannan ɗigon jinin dake ɗigowa daga hancinshi,da kuma daren ranar nan daya farka tsakar dare yaga wani baƙin hayaki ya fito daga cikin madubin ɗakin Abbansu,ya tunkaroshi ya shiga ta ƙopar hancinshi,a lokacin bayan ya farka washe gari,duk tunaninshi mafarki ne yayi ba gaske ba,amma yanzu da Aunty azeema tayi mashi wannan maganar sae wani tunanin ya faɗo mashi aranshi,tun daga daren ranar da hayaƙin nan ya shiga ta ƙopar hancinshi,a washe garin ranar jinin nan ya soma ɗiɗdigowa daga hancinshi,tabbas akwai wani 6oyayyen abu dake shirin faruwa dashi,
Tuna wannan abun yasa junaid ɗagowa idanunshi awaje yana kallon mommy azeema yace"Nashiga uku!mommy ina cikin tashin hankali!mutuwa zanyi bazan rayu ba...kashe ni zasu yi....bazasu bar ni da raina ba ..zasu rabani da Abbana'
Ganin yarda junaid yabi ya gigice yasa ta ruƙo hannunshi sosai tace"Ka natsu junaid!ba kayi imani da Allah bane?
Cikin shessheƙar kuka yace"nayi Imani da Allah mommy azeema,amma ni bana so na mutu yanzu,inaso na rayu ko don nacika ma abbana burinshi da kuma burin da nake dashi... '
Katse shi tayi da cewa"tunda kayi imani da Allah,to inaso kasa aranka cewa babu wani mahaluƙi daya isa ya cutar dakai a faɗin duniyar nan face da izinin sa,sannan inaso ka dage da addu'a na sanka junaid baka ba addu'a mahimmanci sosai,kuma ita addu'a da kake gani takobin mumini ce,ka tashi tsaye ka dage da addu'a ka yaƙi duk wani wanda ke son ganin bayanka,kayi mun alƙawarin hakan,nima kuma zan tayaka da addu'ar,sannan zanyi ma abbanku magana akan ya dinga tashin ka tsakar dare kunayin sallah atare koda ace shi bai tashi ba,in har ka farka to ka shiga toilet ka dauro alwala kayi sallarka,sannan kuma zan sanar ma sauran ƴan uwanka duk zanyi masu magana akan su tayaka da addu'a Allah ya tsare mana babynmu,'
Wani irin sanyi yaji ya ratsa zuciyarshi,kalaman Aunty azeema ba ƙaramin sanyaya mashi zuciya su kayi ba,ya samu ƙwarin guiwa sosai awurinta,har ya daina jin damuwa a ranshi,
"Kana da budurwa"?cike da zolaya tayi mashi maganar,don ta kawar da damuwar dake aranshi,
Sunnar da kai junaid yayi tare da cewa"am...um....eh..'
Dariya Aunty azeema tayi tana cewa"wai kunya ta kake ji ne?dalla faɗamun ni inji,"
Hannu yasa yana ɗan sosa ƙeyarshi yace"mommy azeema,akwai wadda nakeso sosai,kuma itama tana sona sosai,acikin gidan nan take,tare da Aunty azmee suke aiki,yau ta sanyani farin ciki sosai mommy,ta kar6i soyayyata,aure kawai ya rage yanzu inyi ma Abbanmu magana.....'kasa ƙarasa maganar yayi ganin yarda Azeema ta saki baki galala tana kallonshi,
Cike da jin kunya junaid ya kifa kanshi asaman laps dinta yana faman tiƙar dariya,
Suna cikin wannan rahar,wayar Hajiya azeema ta shiga ruri,tsagaitawa tayi daga yin dariyar da take,sannan takai hannu tare da ɗaukar wayar dake ajiye gefenta,ta duba mai kiran nata,a fili tace"Abbanku ne ke kirana,bari na ɗaga naji me zaice mun,"ta ƙarasa maganar tare da kara wayar a kunnanta,
Lamo junaid yayi kwance saman laps ɗinta,ba komai yake tunawa ba face soyayyar da suka sha tare da rishi ɗinsa acikin mota,soyayyarta ƙara ninkuwa takeyi acikin zuciyarshi,musamman da ta kar6i soyayyarshi hannu bibbiyu kuma ta amince zata aure shi,yanzu bai da sauran damuwa,dama itace damuwarshi kullum fargabarshi taya zai tunkareta da zancen soyayyar,zata amince ko bazata amince ba!?
Yana cikin wannan zancen zucin nashi yaji muryar azeema tana cewa"Alhamdullillah!Alhamdulillah mun gode ma Allah daya sauke su lafiya,ba don na tara gajiya ba,da ba abunda zai hana nima na biku Airport din mu tarboshi ..'
cike da farin ciki junaid ya ɗago yana cewa"Mommy,Uncle ɗinmu ne ya ƙaraso nigeria"?
Fuskarta dauke da murmushi tace"Eh,yanzu Abba ke sanar dani cewa sun shirya zasu tafi airport ɗauko shi,jirgin nasu bai kaiga ƙarasowa ba,amma kafin su isa airport din zai ƙaraso da yardar Allah,
Cikin sauri junaid ya sauko daga saman gadon jikinshi na rawa yace"Mommy azeema,ki ajiye mun gift ɗina a wurinki,zanzo na kar6a anjima,inaso zanje airport ɗin nima tare dasu Abbanah,'ko amsarta bai saurara ba,ya fuce da sauri da sauri,
Murmushi Azeema tayi yayin da take bin bayanshi da kallo har ya fuce,
Goggon katsina
Da gudun gaske ta fito daga cikin ɗakinta,hannunta ruƙe da wayarta saboda tsabar farin cikin jin zuwan Abusufyan ɗinta da abbansu junaid ya sanar mata,
Adai dai lokacin Saude da dr haris suna manne da juna saman 3 seater a falo suna shan soyayya,yana ƙoƙarin manna mata kiss asaman wuyanta,kwatsam sai ga goggon katsina ta faɗo cikin falon tana murna ganinsu yasa ta aza hannu akai tana cewa"La'haula masalli ila!acikin gidan nan ake wannan baɗalar?
A firgice suka ɗago suna kallonta hankali tashe,kamar yarda itama take kallonsu hankalinta atashe,
sunnar dakai ƙasa sukayi suna ƴan kame kame,
Jinjina kai tayi tare da cewa"munafukan Allah,yau asirinku ya tonu,dama abunda kuke aikatawa kenan duk in nashige cikin ɗaki ko?cike da tuhuma tayi masu maganar,.
buɗe baki saude tayi da niyar tayi magana,goggo tayi mata dakuwa da hannunta tace"Ungo nan,ja'ira dama kar nake kallonki,munafuka ashe shiyasa kullum nace zan maidaki rugarku sae kiyi mun narai narai da ido kamar na mujiya kina cewa bakison ki koma kiwon shanu,ashe kina nan kin kama wani shanun kina ta tatsa,ina nan sake da baki,Allah kaɗae yasan me kuke aikatawa,ni ban yarda daku bama Allah,ka fadamun gaskiya Harisu iya shinshine-shinshinen kuka tsaya ko kun zarce nan? Tayi maganar tana wurga mashi harara,duk kunya ta gama rufe shi,
Cike da jin kunya suka sunnar dakai ƙasa atare suna sauraronta,sae da takai aya sannan Dr haris yace"Mommyna ni fa ba abunda ya shiga tsakanina da ita,wannan ma da Allah yasa kika gani sharrin shaiɗan ne, ba yin kanmu ba......'bai ƙarasa maganarba,goggo ta tsige kallabin dake kanta,ta wurga mashi shi kafin ya ƙarasa saman fuskarshi,cikin sauri saude ta tarbe kallabin goggon a hannunta,
Baki asake goggo tace"Saude! don tsabar iya rashin kunya da tsageranci akan idona kike kare mashi don na jefe shi da kallabina?wato ya saba baki kina sha shiyasa kika raina ni ko"?
Waro ido waje Saude tayi tana kallonta hankali atashe tace"nashiga uku goggo,me kike nufi daya saba bani ina sha"?
Harara goggon katsina ta watsa mata tana murguɗa mata baki tace"nima bansani ba,nasan dae kina bashi kuma shima yana baki,Allah ya shiryeku in masu shiryuwa ne,sae yanzu nagane kuskuren danayi na barin ki acikin gidan nan,batare da an shafa fatihar Auranku ba,gashi yanzu kuna ƙokarin haifo min ɗan gaba da fatiha.....'fashewa tayi da kuka,cikin shesshekar kuka taci gaba da cewa"Allah sai kin bar gidan nan saude...bazan cigaba da zama dake ba,kina lalatamin yarona,kafin zuwanki gidan nan harisu ko kalmar kiss baisani ba,amma sae gashi yau na same shi yana ƙoƙarin manna maki kiss kamar wani maye,yabi ya kanenayeki don tsabar jaraba irinta ƴaran zamani,acikin gidajen iyayensu ma bazasu iya kame mutuncinsu ba,ni bandamu ba duk abunda zakuyi kuyi,amma ba agaban idona ba.....'
Atare Dr da saude suka kalli juna cike da mamakin jin abunda goggo tace,wato komai zasuyi suyi amma ba'a gaban idonta ba,tashin sense,
Miƙewa haris yayi tare da takawa inda take ya ruƙo hannunta,cikin lallashi yace"Goggo pls komai ya wuce,kuskure ne mun riga da munyi,kuma bazamu ƙara ba,kiyi haƙuri kinji mommyna"
fisge hannunta tayi daga cikin nashi tace"kada ma Allah yasa ku daina,ni wannan ba damuwata bace,yanzu ni bani da sauran damuwa zan tattara nabar maku gidan,idan kunga dama kuyi aure,in baku ga dama ba ku cigaba da abunda kuka saba,Allah dae na kallon mutun,'
Tayi maganar tana wurga ma saude harara,haushinta takeji kamar ta rufeta da duka,
"Mommyna,ina zakije ne?naji kina cewa zaki bar mana gidan"?cike da damuwa yayi maganar
Murguɗa mashi baki tayi tare da cewa"gidan Abba mana,zanje inga Abusufyan ɗina ne,yanzun nan zan shirya in tafi,'
"Mommyna pls ki bari sae gobe zan kaiki da kaina har can ki ganshi,amma yanzu marece yayi fa,naji kamar ana kiran sallar magriba ma,dare zai yi mana a hanya,'cikin lallami yake yi mata magana,don yasan halinta bamai iya mata,
Turo bakinta tayi tana gunguni kamar wata ƙaramar yarinya tace"Allah bamai hanani zuwa,sai naje naga Abusufyan dina tare da ƴa'ƴanshi,'
ɗaure fuska babban likita yayi tare da cewa"Muddin kikasa ƙafa kika bar gidan nan,akwai karnukan layi na nan suna ran gadi acikin anguwar nan,da zarar sunyi arba dake hmmmmmm Allah kaɗae yasan mai zai biyo baya,
tunda taji ya ambaci sunan karnuka,nan take jikinta ya shiga kerma,saboda mugun tsoransu take ji,bata ƙara tanka masu ba,jiki na rawa ta wuce bedroom ɗinta,
Ajiyar zuciya Dr haris ya sauke tare da juyawa ya kalli saude dake ta faman sakin murmushi yace"wlh naji kunya sosai,mommyna bata da saiti,komai yazo bakinta faɗinshi takeyi,yadda kasan rakwa6a66iyar motar da burki ya kwace mata,'.
Fashewa da dariya sukayi,daga bisani Saude ta tsagaita da yin dariyar tace"babyna,addu'a yakamata muyi mata akan Allah ya bata lafiya,idan tadawo dai dai mu kanmu zamuji daɗi sosai,saboda goggo tana da kirki sosae,'
Murmushi Dr haris ya kuma yi tare da cewa"insha Allah zamu cigaba dayi mata addu'a Akan Allah ya bata lafiya,'
_💋Boss Bature💋_
Wuraren ƙarfe 6:30 jirginsu Abusufyan yayi landing a Nnamdi Azikiwe International Airport Abuja,
gaba ɗaya su Abba sun gama hallara a airport ɗin suna jiran saukowarsu daga cikin jirgin,kowannansu a ƙagare yake daya ga fuskar Abusufyan da suka jima basu sanyashi a idanunsu ba,nikaina wlh amatse nake dana ga wannan Abusufyan ɗin da kowa yake ta ɗokin ganinshi,
Gaskiya namatsu,namatsu namtsu, inga wannan ɗan tahalikin,
daga cikin waɗanda suka hallara domin tarbar shi akwai Abbansu tare da junaid,kanal yousouf da kuma Irfan,jabeer,khaleed da kuma fawan,bayansu kuma akwai Twins suma duk suna zazzaune asaman waiting seats na airport din suna jiran ƙarasowarshi,suna zaune suka ji ana annoucement din ƙarasowar jirgin daya zo daga ƙasar turkey,
Tsantsar farin cikine ya bayyana a fuskokinsu,duk suka zuba ido suna jiran 6ullowarshi,
Passengers ne suke ta fitowa daga cikin jirgin kowannansu fuskarshi asake,sae bullowa sukeyi ta ko'ina,
Sannu a hankali ya aza kafarshi asaman matattakalar benen,masha Allah sae dae muce tabarakallahu ahsanul khaliqin,
giant ne yana da tsayi da kuma cikakkiyar sura mai jan hankali,ta ko'ina Allah ya hore mashi,a launin fata kuwa chocolate colour ne,kala mai tsada,fatar nan tashi taji hutu ko a ido ka kalleta sae kasan cewa ba ƙaramin hutu taji ba,jikinshi na sanye da Suit maroon colour launin glass ɗin dake manne a fuskarshi,wani irin daddaɗan kamshi ne ke fesowa daga jikinshi,hannunshi na sanye da tsadaddan agogo na diamond,
A hankali ya ɗaga hannunshi tare da kai shi saman fuskarshi ya zame glass ɗin da ke manne a fuskar,lumshe idanunshi yayi tare da waresu a hankali yana kallon mutanen dake shawagi a wurin,
Yayi kewar ƙasar shi sosai,shekara kusan goma sha wani abu,bai taka ƙasar ba,sai yau Allah ya dawo dashi,
"Ƙaddara ta sake dawo dani wannan ƙasar" ya furta hakan yayin da yake ƙara ruƙe trolley ɗin hannunshi,jan shi ya shiga yi yayin da yake ci gaba da saukowa daga saman matattakalar jirgin,
Dirar shi ke da wuya,yaji an ambaci sunan shi da wani irin sauti yaji ance"Uncle Abusufyan! "firgit yayi tare da kai idanunshi wurin da yaji an ambaci sunan,
Waro ido yayi waje fuskar nan dauke da farin ciki ya ambaci sunan Junaid,
Da gudun gaske junaid ya ƙarasa tare da faɗawa saman faffaɗan ƙirjinshi,ya kankame shi sosai kamar zai shige jikinshi,
sosai Abusufyan ke sakin dariyar farin ciki yana ƙara bubbuga bayan junaid da hannunshi yana cewa"WOW MASHA ALLAH MY BABY BOY KAINE KA KOMA HAKA,GASKIYA NAYI MISSING ƊINKA SOSAI JUNAID,AM REALLY GLAD TO SEE U ........'
ya ƙarasa maganar tare dasa hannunshi ya ɗago junaid daga saman kirjinshi yana kallon fuskarshi,yayi mamakin girman yaron lokacin da daya tafi yana ɗan ƙaraminsa ya barshi,
ganin hawaye na sauka asaman fuskar junaid yasa shi cewa"meya faru junaid?kai da zan ga kana farin ciki sae kuma naga hawaye a idanun ka why?
Cike da shagwa6a junaid yace"uncle bakaine ka tafi kabarmu ba,shekara da shekaru ka manta damu,ba ka damu da kazo ka ganmu ba,"
ƙayataccen murmushi Abusufyan ya saki tare da cewa"Am really sorry my boy,nasan ni mai laifine ayimun afuwa pls,shiyasa nadawo nigeria don in goge laifina....'
Yana cikin maganar tashi sai ga su Abba sun ƙaraso wurinsu tare dasu kanal yousouf,
Gaba daya suka ƙarasa one by one suna rungume shi ajikinsu cike da nuna farin cikin ganinshi,
Sae da ya kammala rungumarsu,sannan ya ɗago yana kallon ɗan uwan nashi daya tsaya gefe guda,yana kallon shi fuskarshi aɗaure alamar fushi yake dashi,
Tunkarar shi yayi zai rungume shi,cikin sauri Abba ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga mashi hannu yace"karka kuskura ka ƙaraso nan,bana son ganinka,ni banma san ya akai nazo airport ɗin nan ba,"
Hannu uncle abusufyan yasa tare da kama kunnan shi yana cewa"Am sorry my bro,ayi mun aikin gafara nasan nayi laifi,amma zan gyara kuskure na,yanzu dae ka barni in rungumeka kona ji sanyi araina,'
Buɗe mashi hannu Abba yayi alamar ya taho,faɗawa jikin shi abusufyan yayi sosai suka rungume junansu,tuni hawaye suka cicciko a idanuwan kowannansu
muryar abbansu junaid tamkar zaiyi kuka yace"Hakanan ka tafi ka barni batare da sani na ba,me yasa kayi mun haka abusufyan?duk irin son da nake maka,ka tafi ka barni da raɗaɗin rashin ka acikin zuciyata,abun ba ƙaramin ciwo yake yi mun ba,"
ya ƙarasa maganar a lokacin da yake ƙoƙarin raba jikinshi daga na Abusufyan,
Jikin shi yayi mashi sanyi,duk sai yaji ba daɗi,kuma bai kyauta masu ba,
daƙyar yace"Ka yafe mun ɗan uwana,na cutar dakaina,na raba kaina da ƴan uwana,bawai don bana son kasancewa atare da ku ba......'
Kasa ƙarasa maganar yayi saboda wani abu daya tuna a rayuwarshi daya ta6a faruwa dashi...,
Jinjina kai kawai Abbansu junaid yayi tare da ruƙo hannunshi yace"Komai ya wuce,tunda kadawo nigeria,kuma inaso ka sani bazan ƙara bari kabar ƙasar nan ba,komai kakeso ka faɗamun zanyi maka shi,in ma akwai wani abu dake damunka duk ka sanar mu,zanyi ƙoƙari wurin ganin na share maka hawayenka,dama ni sae da raina ya bani cewa bada son ranka kabar ƙasar nan ba,akwai wani abu dake faruwa wanda kaƙi sanarma kowa.....'
"Abba,uncle fa ya gaji sosai,ya kamata muyi hanzarin wucewa gida tare dashi,idan ya kwanta ya huta sae mu ƙara gaggaisawa dashi,"
Kanal yousouf ne ya katse mashi hanzarinshi,
murmushi abba yayi tare da janyo hannun abusufyan suka kama hanyar fitowa daga airport din,gaba dayansu suka ɗunguma izuwa wurin da suka ajiye motocinsu,murmushi kawai Abusufyan keta saki yana kallon ƴan uwan nashi kamar ya haɗiyesu haka yake ji,saboda tsabar son da yake yi masu.
Finally Uncle Abusufyan ya ƙaraso nigeria,saura mommynsu junaid da kuma Ammi,su muke jira,
Koda suka ƙaraso cikin gidan,anan main palour din suka zazzauna ana ƙara gaisawa da juna,a ƙarshe abba ya ruƙo hannun ɗan uwan nashi yakai shi izuwa cikin bedroom ɗin da aka tanadar mashi,katafaren ɗakinsa da zai zauna aciki,sae da abba ya tabbatar da cewa Abusufyan ya shige cikin ɗakin sannan yaja mashi ƙopar ya rufe,
Gaskiya zanso kuga irin farin cikin da ahalin nan suke yi na zuwan Uncle dinsu Abusufyan,
Wuraren ƙarfe 11 na dare lokacin komai ya lafa,junaid ya nufi bedroom ɗin sehrish yana nemanta ganin bata fito ba,lokacin daya je,ɗakin nata ya shiga wayam yaga babu kowa,jiki na rawa ya wuce ɗakin azmee yana tambayarta ina reesh take,azmee tace"tun ɗazu dana kai mata lunch ban ƙara sanyata a cikin idanuwana ba,"fitowa junaid yayi daga ɗakin azmee hankalinshi a matuƙar tashe,saƙo da lungu na gidan ya dinga bi yana dubawa bai ganta ba,lokacin daya tabbatar da cewa sehrish bata acikin gidan,jiki na rawa ya wuce ɗakin Abbansu anan ya same shi zaune shi da Uncle abusufyan suna ƙara tattaunawa a tsakaninsu,
Ganin yarda junaid ya faɗo masu ba sallama yasa suka shiga tambayarshi ko lafiya,hankali tashe yace"Abba,sehrish nake nema,na duba ko'ina acikin gidan nan bata nan,'
cike da mamaki abusufyan ya maimaita sunan Sehrish abakinshi,
Abba kuma yace"tun yaushe tabar gidan?baka je ɗaukota daga school bane"?
"Abba naje,dakaina na ɗaukota kuma na kawota acikin gidan nan,amma yanzu na duba ko'ina babu ita,"
Jin wannan maganar ta abba yasa shi miƙewa daga zaunen da yake gefen gadon ya nufi junaid yana cewa"muje wajen,"
Juyawa junaid yayi suka fuce atare,yayin da suka bar Abusufyan azaune cikin ɗakin,
Hankalin kowa fa ya tashi,abun sai ya baka mamaki,ashe ba ƙaramin so sukeyi ma yarinyar ba,duk wanda akace mashi Sehrish ta 6ace ba'a ganta ba,sae kaga ya fito daga bedroom dinshi yadawo falo cike da damuwa,gaba daya sae da kowannansu ya hallara banda Sgr,saboda tun ɗazu yabar cikin gidan,
Hankalin Marshal omar