Showing 132001 words to 135000 words out of 245004 words
Chapter 45 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
bata amsa,
Jahad tace"Okey,yanzu nake shirin tashi na shiga kitchen in girka mana abunda zamu ci,amma kafin nan ki fara ɗaukar fresh milk a fridge sai ki haɗa da wani abu kisha,sannan in kin kammala kiyi sallah,gashi har time ma ya wuce,'
amsa mata tayi da toh,sannan ta miƙe tare da fucewa daga bedroom ɗin,
Murmushi jahad tayi tare da cewa"nan ba da jimawa ba zamu sha bikin Amarya hossana tare da bride ɗinta ya Omar,"
Yunƙurawa tayi tare da miƙewa daga saman sallayar, hannu takai zata cire hijabin jikinta, nan take ta tunano da maganar da mahaifiyarsu ta ta6a yi masu a lokacin da suke tare da ita,
"Burin da nake dashi kafin nabar duniya Allah ya nuna mun ranar Aurenku,kamar yarda na haife ku arana ɗaya haka nakeso na aurar daku ku duka ukun arana ɗaya kuma a lokaci ɗaya,zan cigaba da yi maku addu'a Allah ya baku mazaje nagari,"
Cikin sauri jahad ta ƙarasa cire hijabin tare da ajiyeta nan saman gadonsu,sannan cikin sauri ta fito cikin falon anan tasamu hossana zaune saman 3 seater hannunta ɗauke da sinkin bread tare da fresh milk sai cusawa abaki takeyi tana haɗawa da madarar,
jin alamar tafiyar mutum yasa ta ɗagowa tana kallon jahad dake tunkarota,
Ganin yanayinta yasa hossana cewa"jahad meya faru naga kamar kina cikin damuwa"?
jiki asanyaye jahad tace"hossana mun manta ba muyi ma Ya Omar maganar SEHRISH ba!banji daɗi da muka manta da batun nemanta ba,baiwar Allah bamusan wani hali take ciki ba,"
cike da damuwa Jahad ta ƙarasa maganar tare da samun wuri saman hannun kujera ta zauna,
Nan take yanayin hossana ya canza,lokaci guda taji komai ya fita ranta, ba don komai ba sai don tunawa da Sehrish,
murya na rawa ta soma cewa"inason ganin sehrish sosai jahad, zan sanarwa ya Omar ya nemo mana ita,bazan ƙara mantawa ba insha Allah,"
"Nima bazan manta ba, da zarar yazo zamu sanar dashi,". a cewar jahad,
Daga haka ta miƙe tare da wucewa kitchen,
**********************
Wuraren ƙarfe biyar na yamma,motar sofwan ta shigo layin gidan,tun a bakin Gate security guards suka tsayar da motar tasu,kamar wasu zakuna haka sojojin suka tunkari motar shi,hankali tashe ya juya tare da kallon hayaam dake manne ajikinshi tana bacci ta aza kanta asaman kafaɗarshi,jikinta na sanye da dogon hijabi har ƙasa ta sanya niƙab a fuskarta,kamar wata Malamar Addini,
da ƙarfi ya ambaci sunanta"Hayaam!!Hayaam!!"har cikin kanta ta dinga jin kiran nashi,daƙyar ta iya buɗe baki tare da cewa"wai menene"?
"Mun ƙaraso gidan fa,dan Allah ki tashi kiyi ma waɗannan dakarun bayani,nifa a tsorace nake dasu,".
guntun tsoki taja ta janye jikinta daga nashi,sannan tace"haba sofwan bafa yau ka fara zuwa gidan nan ba,menene abun tsoro aciki,sai kace ba namiji ba,"
wani irin kallo yayi mata tare da cewa"ba yau na fara zuwa gidan ba,amma ae ko lokacin da na ta6a zuwa ɗaukarki a iya bakin babban gate ɗin nan nake tsaya......'
Bai ƙarasa maganar ba,saboda bugun glass ɗin motar daya ji anyi daga waje,muryar wani basamudan soja ce ta karaɗe kunnansu da cewa"Oya wind down ur glass,"
A hanzarce Sofwan ya sauke glass ɗin motar,yana ta faman mazurai kamar wani mara gaskiya,
tambayarsu yashiga yi"Su wanene ku!kuma wurin wa kuka zo,?
Murya na rawa sofwan yashiga nuna hayaam yana cewa"am..yalla6ai..itace zatayi jawabi,bani ba,"
girgiza kai hayaam tayi tare da kai hannu ta ɗauko purse ɗinta dake ajiye saman laps ɗinta,cikin sauri ta ciro wayarta tare da ruƙe ta a hannunta,nan fa tashiga tunanin wa zata kira acikinsu don yayi masu magana subarsu su shiga,
"Madam ke muke jira,bama son 6ata lokaci and remove dat thing u covered ur face with" muryar sojan ce ta sake katse ta,yana nuna nikab din da yatsansa.
Tuni taji zufa ta soma karto mata a fuskarta da sauri tasa hannu ta cire nikab din,contact ɗinta tashiga tare da dialing numbar Kanal Yousof,cikin rashin sa'a wayar tashiga ringing amma ba'a ɗaga ba almost 3 times,cikin sauri ta kuma lalubo numbar Junaid,har ta gama ringing junaid bai ɗaga kiran ba,da alama shima baya kusa da wayar tashi,
Hankalin Hayaam ba ƙaramin tashi yayi ba,dama su biyu kawai take da numbarsu a wayarta gashi duk sunƙi ɗaga kiran,
ganin zata 6ata masu lokaci yasa sojoji bashi umarnin yaja motar shi yabar wurin,
Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta,ba ƙaramin 6acin rai tashiga ba,amma babu yarda zatayi dolenta su koma,
Sofwan na ƙoƙarin tashin motar su bar wurin,sai ga motar Sgr ta kunno kai daga cikin babban gate ɗin gidan,
Zuba ma motar ido sukayi gaba ɗayansu musamman hayaam da take jin cewa sauƙi yazo mata,don tasan kowanene zai bada Umarnin abarsu su shiga ciki ne,
"Sir I think something is wrong here," Amstrong ne yayi mashi magana,
Don haka sgr ya bashi command ɗin ya tsayar da motar tasu don jin meke wakana,
A daidai saitin motarsu Hayaam Amstrong ya dakatar da tasu motar,sannan a hankali a wani irin slow glass ɗin motar suka soma saukewa atare,
Waro ido waje hayaam tayi nan take zuciyarta tayi wani irin bugun bazata,ba don komai ba sai don ganin mutumin da tajima bata sashi a idonta ba,wato abun harinta,
A hakimce yake zaune a back seat ɗin motar,ba ƙaramin kyau yayi ba yayi wani fresh dashi,musamman wankan daya ɗauka,Red shirt ce ajikinshi,tare da black trouser,
launin rigar ya ƙara fito da wannan hasken fatar nashi sosai fari sol kamar ka ta6a jini ya zuba,sumar kan nan kuwa tana ɗaure abayanshi,yayin da idanunshi ke lumshe tamkar mai jin bacci,
Cikin sauri sojan ya ƙarasa inda yake tare da buga ƙafa ya sara mashi sannan yace"Sir,wasu baƙin fuska ne ke son shiga cikin gidan,kuma basu da shaidar da zamu iya barinsu su shiga cikin gidan,shiyasa muka dakatar dasu,
kusan 5 mins bai buɗe bakin shi ba,babu alamar cewa zaiyi magana ma,kowa yayi tsit yana jiran jin ta bakin shi,kai har sai da sojan ya fidda rai da zaiyi magana sannan Calmly yace"What about asking their details?
Sojan yace"ban tambaye su wannan ba,amma bari naje na tambaye su,"
juyawa yayi tare da ɗan matsawa kusa da motar Sofwan yace"yana buƙatar bayani a wurinku,ku gabatar da kanku don yasan su wanene ku,"
jin shiru hayaam bata ce komai ba yasa sofwan juyawa zaiyi mata magana,sakin baki yayi yana kallon ikon Allah,gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan Sgr,ba ƙaramin tafiya da imaninta yayi ba,
Nan take yaji wani irin kishi ya rufe shi,acikin ranshi yace"haba no wonder,sai yanzu na gane dalilin dayasa hayaam ta haukace mun akan wannan Namijin,mutum kullum ƙara kyau yake yi,kamar shi yayi kanshi don kyau,muddin irin wannan na yawo agari tofa bazamu ta6a yin kasuwa ba,"
"Don't waste our time"! muryar sojan ce ta katse mashi tunanin nashi,
Cikin sauri yace"Hayaam!magana fa ake maki,kiyi masu bayanin alaƙarki da mutanen gidan,"
Ajiyar zuciya hayaam tasaki,sannan anatse ta soma magana"ka sanar dashi cewa ƙanwar matar yayansu ce hayaam,"
Juyawa sojan yayi tare da komawa wurin motarsu Sgr yace"yalla6ai tace ita ƙanwar matar yayanku ce kuma sunanta Hayaam,"
a hankali sgr ya ɗan buɗe idanun shi,
Hakan yasa Hayaam dake hangen shi ta soma washe baki,ba don komai ba sai don ita atunainta sgr ya gane jawabin da Sojan yayi mashi,
Cike da ƙasaita yace"sam wannan bayanin bai kwantamin araina ba!infact,I don't know any person wit dat name hayaam or what...,ban ta6a jin sunan ba,Sergeant!!a sallamesu su koma,nd add more security!!"
Yana ƙarasa maganar tashi,glass ɗin motar ya ɗaga sama sannan a hankali Amstrong ya tashi motar,anatse yake driving ɗinshi har suka bar wurin gaba ɗaya,
dariya ce ƙumshe abakin sofwan amma ya gaza fitar da ita saboda tsoran 6acin ran hayaam,sam yaƙi yarda su haɗa ido da ita,saboda tsoran karta huce akanshi,
Kamar ta aza hannu akai ta fasa ihu haka taji,zuciyarta har wani boiling take tana burning saboda tsantsar 6acin rai da baƙin ciki,ashe duk haukan nata ma abanxa ne Sgr baisanta ba,baisan wacece ita ba duk zuwan da takeyi gidan a lokacin baya,
daƙyar sofwan ya daure ya cije tare da ce mata"mu juya ko"?
A tsiwace tace"bansani ba!!mtswww" ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki,
Can kuma tace"babu inda zanje wlh,kota tsiya kota arziƙi wlh saina shiga cikin gidan koda kuwa zamu kwana anan ne,don bazanyi tafiyar banza ba,"
Cikin sanyin murya sofwan yace"Hayam ki bi komai a hankali!su fa waɗannan mutanen da kika gani ba kamar sofwan ɗin da kika raina bane,muddin kikace zakiyi masu rashin kunya wlh dukan tsiya zaki sha,kakkarya ƙasusuwan jikinki zasu yi,kuma kada kiyi tunanin cewa zakiyi masu kwarkwasa ko kija hankalinsu da kyanki,don wlh babu ruwansu da mace,su ba mayin mata bane irina,so u ave to be very careful,"
ya ƙarasa maganar fuskarshi ɗauke da dariya,don yau ba ƙaramin nishaɗi yasamu a wurin Sgr ba,ba ƙaramin burge shi yayi ba yanayin acting ɗinsa babu wasa aciki,Namijin ne dae na gaske,
Tsuke fuska hayaam tayi,harara ta watsa mashi tare da jan dogon tsoki batare da tace komai ba,
tunani tashiga yi akan yadda za'ae su shiga cikin gidan,nan take zuciyarta ta bata shawarar ta kira Aunty babba ta sanar mata,tana ƙoƙarin kiran nata sai ga Motar Haroon ta shararo da gudun gaske cikin layin,
tunkan ya ƙaraso wurinsu ya rage gudun motar tashi,sai da yazo dai dai bakin gate ɗin gidan sannan yayi parking ɗin motar tare da sauke glass ɗinta,da alama yasha ya bugu har takai mashi karo,saboda yarda idanunshi ke ta faman rurrufewa sunyi luhu luhu dasu,
dakyar ya iya tsayar da idanunshi akan Motar sofwan,nan take suka hango mashi kyakkyawar fuskar hayaam,ɗaga murya yayi tare da kwala ma sojojin kira,cikin sauri suka tunkari motar tashi tare da sara mashi,
Yatsina fuska yayi ya kallesu a wulaƙance yace"Meke faruwa anan ne?su wanene acikin motar can"?
ɗaya daga cikinsu ne yace "Yalla6ai,ba mu san ko su wanene ba,mun hana su shiga ciki ne saboda basu da shaidar da zamu iya barinsu shiga cikin......'
Tunkan ya ƙarasa maganar haroon ya katse shi da cewa"Saboda gidan na ubanku ne!wai ma uban wanene ya kafa wannan dokar ta hana mutane shiga cikin gidan nan ne!"?ni banga amfanin takurawa mutane ba,idan tsaro ne ba Allah ke tsarewa ba mtswwww,
Shiru sojojin sukayi suna sauraron faɗan nashi kamar ubansu,hayaam kuwa tunda taji yana zazzaga masifa yasata ɗagowa tana kallonsu,ganin yarda yake banbamin bala'e akan an hanasu shiga yasa ta soma sakin murmushin jin daɗi,
Sofwan kuwa jinjina kai yayi tare da cewa"ikon Allah,kowanene wancan jarababben da yake ta faman tada jijiyoyin wuya,da alama ba ƙaramin hatsabibi bane,'
Cikin lallashi sojojin suka haɗa baki wurin cewa"Sorry sir!Allah ya huci zuciyarka!"
Hura hanci haroon ya shiga yi kafin daga bisani yace"Ban amince abarsu su shiga da motar da suka zo da ita ba!shi namijin yaja motar ya koma gidan ubansa,ita kuma budurwar kuce mata tashigo daga cikin motata na sauke ta cikin gidan,idan har bata amince ba to su tattara su koma inda suka fito,".
"An gama yalla6ai,"atare suka amsa mashi,sannan suka juya tare da tunkarar motar sofwan,tun kafin su ƙaraso hayaam ta buɗe motar jiki na rawa ta fito saboda taji duk bayaninshi acikin kunnanta,
Hankali tashe sofwan yace"Hayaam ni kuma awani matsayi kika ajiye ni ne"?
Batare da ta waigo ta kalleshi ba tace"Zan kiraka a waya,in nasamu lokaci,ta bude back door ta dau jakanta"
Jiki asanyaye Sofwan yaja motar,yayin da zuciyarshi ke cike da 6acin ran abunda tayi mashi,yasha wahalar kawota,amma ko godiya babu balle yayi tunanin sake samun wani abu awurinta,tuni yaji hawaye sun cika mashi idanunshi,tabbas hayam ta cuce shi sosai ba ƙaramar wahala yasha akanta ba,duk don ya mallake ta amma gashi nan ya tashi a tutar babu!dashi da Zero basu da bambanci ƙwara ma zero yana da amfani wurin yin lissafi,
Shu'umin murmushi haroon ya saki lokacin da hayaam ta ƙaraso jikin motar tashi,hannu tasa tare da buɗe gaban motar tashiga ta zauna tare da rufe motar,sannan ta mayar da idonta akan haroon daya zuba mata ido ko kyaftawa baiyi,
ita kanta saida tasha jinin jikinta da ganin irin zubin shi,cikin sanyin murya tace"Sannu ko,"
ɗan ta6e la66ansa yayi tare da cewa"Yawwa,amma naga baƙuwar fuska ina buƙatar ƙarin haske,"
Cike da kwarkwasa tace"Sunana Hayaaam,ni ƙanwar Aunty laila ce da kuma Aunty Amani,"
murmushin gefen fuska haroon yasaki kafin yace"Wow,no wonder that's why naga kamanceceniyar ki da Aunty laila,ashe ke ƙanwarsu ce,amma fa am really sorry game da abunda ya faru,securities ɗin gidan nan basu son ciwon kansu ba,in ba haka ba taya zasu ga mace kamila irinki sanye cikin dogon hijab kuma su hanaki shiga?
Sunnar dakai Hayaam tayi tana faman sakin shu'umin murmushi,aranta tace"dalilin dayasa na sanya dogon hijabi kenan saboda nasan cewa kowa zaiyi tunanin ni mutuniyar kirki ce,hmmmmm basu san cewa da fuska biyu nazo masu ba,"
(Rashin sani yafi dare duhu!hayaam batasan da wa take magana ba,"
"Kada na cika ki da surutu,bari nashiga dake cikin gidan,"
Ya faɗi tare da jan motar da gudun gaske ya shige cikin babban gate din gidan
(Finally hayaam ta samu nasarar shiga cikin gidan)
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
_💋BOSS BATURE💋_
*Zuwa ga masu karkasamun littafin duk wanda ya ƙara haɗamun document,ban yafe ba!babu yarda za'ae ni ina cikin rubuta littafi na biyu,wasu kuma sun haɗamun document na book 3 don iyayi da kuma ƙarfin hali,sai ja mun surutu sukeyi nacewa naja littafi har book 3 duk da idan naga dama har book 5 ma sai inyi bani naji zan iya ba😒😏🙄😒, wasu har gardama sukeyi mun nacewa book 3 suke so complt,bayan ni iya book 2 nake cikin rubutawa ma,*
Abban sojoji part 2 ❤
Bayan Haroon yayi parking ɗin motar,hayaam tayi mashi godiya tare da ɗaukar bag ɗinta,ta fito daga cikin motar sannan ta nufi cikin gidan,
Shu'umin murmushin nan nashi ya saki yabi ta da kallo tare da cewa"Nifa bana abu don Allah,kowani tsautsayin ne da ƙaddara suka kawo ta cikin gidan nan!Allah yasa ta kwanan mana biyu...." ya jinjina kai tare da cewa "tsuntsu daga sama gasasshee!"ya ƙarashe maganar tashi tare da zura hannun shi cikin aljihun jeans ɗin dake a jikinshi,wayar shi ya ciro tare da duba screen ɗin, missed calls aka mashi da wata hidden number,
shiru yayi yana tunanin taya zai bi kiran saboda kira ne mai mahimmanci a wurin shi gashi dole sai in shi mai 6oyayyiyar numbar ne ya kira ka,
Yana cikin wannan tunanin sai ga kiran ya sake shigowa,cikin sauri yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnan yana jiran jin me za'a sanar dashi
Wata irin muryace ta irin hamshaqan matan nan waɗanda suka ji duniya ta soma magana"Haroon!kana shirin jamin bala'e ko?meyasa ka fiye shiririta ne?ko kamanta plan ɗin mu ne"?
nan take haroon yashiga en ina murya na rawa yace"ban manta ba,inaso nabi komai a hankali......'bata bari ya ƙarasa maganar ba ta kwatsa mashi tsawa"Ya isa Haka! kasani wlh akanka bazan bari nayi gangancin rasa damar da nake da ita ba!haroon zaka iya rasa ranka muddin kace zaka kawomin wasa acikin lamarina!kai kasan wacece NI!bani da imani,"
Wata irin zufa ce ta soma gangaro mashi daga cikin sumar kanshi,lokaci guda duk yabi ya rikice yashiga zazzare idanu,
sautin dariyarta ce ta karaɗe kunnan shi,tsagaitawa tayi da yin dariyar sannan ta sassauto da muryarta wurin cewa"Am sorry fa,na tsorata ka ko?
Nannauyar ajiyar zuciya haroon ya saki tare da cewa"Yanzu me kike so ayi ne,just command me zanyi maki koma menene,"!
"So nake ka kashe JUNAID!saboda shikaɗai ne hanyar da zanbi wurin ƙuntata masu,banaso junaid ya rayu,muddin yana araye toh farin cikin gidan zai cigaba da wanzuwa ne,ni kuma abunda bana so kenan!,"
girgiza kai haroon yashiga yi tare da cewa"Kiyi haƙuri wannan ne karo na farko da kika ban umarni na musa maki tunda na fara maki aiki!junaid is innocent I can't kill him,zan iya kawar maki da duk wanda kikeso acikin gidan nan,Amma