Showing 210001 words to 213000 words out of 245004 words

Chapter 71 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download

17 Mar 2025

25232

akan Sgr ta fara shan mari,ta jima tana mamakin yarda ya ɗaga hannu ya kwasa mata mari,duk irin yarda ta ɗau wanka,ta bayyana surar jikinta don taja hankalinshi amma hakan baiyi tasiri akanshi ba,kwallin data shafa kuma ya tashi abanza saboda bai kalli cikin idonta ba bare asirin ya kamashi,
  ɗagowa tayi daƙyar take iya buɗe idanunta,wayarta ta ɗauko dake ajiye saman side drawer na gadonta,layin Aunty babba ta kira,wayar ta shiga ringing,
Cikin sa'a ta ɗaga kiran,Aunty babba nayin sallama,hayaam ta 6are baki ta fashe da wani sabon kukan,
  Tunda Aunty laila taji kukan hayaam hankalinta yayi mugun tashi,daga zaune take saman kujera amma tana jin kukan hayaam ta miƙe tsaye tana tambayar lafiya!
  Cikin shessheƙar kuka hayaam tace"Aunty lailai,yau Sgr ya gama dani,ya wulakantani kuma ya tozarta ni,yayi mun abunda wani ɗa namiji bai ta6a yi mun ba!'
  Hankali tashe Aunty babba tace"Me yayi maki ne!kiyi mun bayani yarda zangane,kuma kidaina wannan kukan da kikeyi,"
  dakatawa da yin kukan hayaam tayi sannan taci gaba da magana tana cewa"Mari na fa yayi,banyi mashi komai ba ya ɗaga hannu ya kwasa mun mari agaban waccen ƙaskantacciyar yarinyar ya mare ni....'
  Tunkan ta ƙarasa maganar Aunty babba tace"Ƙarya kike hayaam!Sgr bazai ta6a marinki ba batare da kinyi mashi laifi ba!dole akwai dalilin dabyasa ya mare ki,don nasan halinki baki da hankali,kuma baki da kamun kai,halan ƙoƙarin kai mashi hari kikayi saboda gajen hkr!!"
  Cikin en ena hayaam tace"nifa banyi mashi komai ba,kawai da safe ne nashiga ɗakin shi lokacin ya fito daga wanka,nayi ƙoƙarin jan hankalinshi ne da surar jikina,amma ko kallo ban ishe shi ba,shine nayi hugging nasa nayi ƙoƙarin ta6a short ɗin jikinshi don in tayar mashi da sha'awar shi,amma shine kawai ya kwashe ni da wani mahaukacin mari.....'
  dafe kai Aunty babba tayi tana cewa"ka ji tsiyar!wlh kin ban kunya hayaam!bansan ke wata irin mace bace!sam baki da kamun kai,idan jarabarki ta motsa, me yasa bazaki iya control din kanki bane agabanshi!wannan mutumin fa da kaina nayi maki alƙwarin cewa mijinki ne shi,idan kikayi haƙuri nan da ɗan wani lokaci zaki mallake shi duka,sae kiyi yarda kika ga dama dashi,amma tun yanzu saboda gajan haƙuri irin naki kin gaza jurewa,kina ƙokarin lalata mun shiri na!bazaki ta6a burge Sgr ba,saboda shi irin mazan nan ne da basa ra'ayin mace mara kamun kai ballagaza,wadda bata iya 6oye zalamarta akansu......'

Ɗaure fuska hayaam tayi jin yarda Aunty babba ke ta zaginta a fakaice,
Rai a6ace tace"Aunty laila nifa ban kiraki don kici mun mutunci ba,sae faman gaya mun magana kikeyi ta inda kike shiga bata nan kike fita ba,ni da na kawo maki kukana maimakon ki share mun hawaye na,Amma shine kike ta zazzaga mun masifa!wannan abun fa ba laifina bane,ko kece kika ganshi a yanayin dana same shi dole ki kai mashi attack balle ni da nake budurwa........'
  Waro ido waje Aunty babba tayi rae a6ace tace"Hayaam don ubanki ni kike gayama wannan maganar!ashe ke daƙiƙiyace baki da hankali!an gaya maki ko wace mace irin ki ce mara aji da zata dinga kai kanta wurin namiji har tana ƙokarin ta6a jikinshi!ni tunda nake arayuwata ban ta6a kusantar mijin da banawa ba,duk irin mugun halin da nake dashi kuwa,a iya miji na natsaya ban zarce nan ba!amma ke fa?kullum kina yawon biɗiɗi wurin raba jikinki ga kowane ƙazamin namiji yayi amfani dake,don ki samu kuɗi,ki faɗamun wace riba kika ta6a samu a yawon barikancin naki!acikin mazan da kikayi mu'amala dasu akwai shegen daya ta6a cewa zai aure ki ne!!saboda baki da wani amfani awurinsu,tamkar totuwar masara kike da zarar sun cinye masarar jikinshi ya gama amfani sae su jefar dashi ƙasa,ni kuwa kinga ina da daraja tunda ina da aure kuma a ƙarkashin kulawar mijina nake,shiyake amfani dani kuma shi yake bani kuɗin da zanyi abunda nake so,riba biyu ga kuma lada ina samu......'
  Wani irin huci hayaam ta shiga fitarwa saboda tsabar 6acin ran kalaman da Aunty babba ta gaggaya mata,
Muryarta har shaƙewa takeyi wurin cewa"Aunty Laila!!ni kike faɗama waɗannan munanan kalaman!yau da kanki kike yi mun gori?Ya salam!wlh bazan ƙyale ki ba,kamar yarda kikayi mun gorin aure,nima zan raba auran ki Da Ishaq,ki dawo bazawara,"
fashewa da dariya Aunty babba tayi tana girgiza kai kafin tace"ni zan aje waya,kada ki manta kisha maganinki na rana,don da alama kin manta jawabin da likitan mahaukatan nan yayi maki,akan kula da shan magungunan ki akai akai,"ta ƙarasa maganar tare da kashe wayar,
  Wani irin ihu hayaam ta zabga tare da aza hannunta saman kanta,tana fadin innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...."

Zafi biyu,gana marin da Sgr yayi mata ga kuma na zafafan kalaman da Aunty babba ta gaggaya mata,zuciyarta tamkar ana rura mata garwashin wuta haka ta dinga ji,wani irin zazza6i ne ya lullu6eta,nan ta baje saman gadon tana ta faman birgima a ranta tana cin alwashin ba zata bar gidan ba har sai taga bayan Sehrish don ita taja mata duk wadannan abubuwan da suka faru da ita.

 
 


 
 

 *💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*




*Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*,






Wuraren ƙarfe 4:30 gaba ɗaya matasan gidan sun hallara a baban falon gidan wanda yasha decorations abun ba'a magana,yayi kyau over tamkar wani babban hall na taro,an ƙawata shi sosai hada wasu kujerun aka ƙaro,an tsara komai na wurin anyi table arrangements,kowane table yana zagaye da Kujeru guda uku uku wadanda ke dauke da seat cover haka ma tables din,a jere Ayaan da Jahan irfan da khaleed da kuma jabeer da fawan,suka shigo main palour ɗin kowannansu ya ɗau wankan tsadaddiyar shadda ajikinshi,bayansu sae kanal yousouf shima ya fito cikin nashi wankan,ba ƙaramin ƙyau sukayi ba,sai hotuna suke ɗauka da wayoyinsu,kafin camera man ɗinsu wato junaid ya kammala shirin nashi ya fito ya ɗauke su hotuna,dama shine maiyi masu hoto duk in suka shirya walima irin haka,acikin gida,

Lokacin da Abbansu ya fito jikinshi sanye da shadda fara taji aiki ajikinta,koda sukayi arba dashi da sauri suka ƙaraso wurinshi suna yaba wankan daya ɗauka,
  "Abba harka fi mu yin kyau wlh,gaskiya bamu yarda ba Abba,'
  Dariya sosai Abban nasu yayi yana kallonsu one by one,wani irin farin cikine ya lullu6e shi ganin ƴa'ƴan nashi gaba ɗayansu agabanshi,duk da ba wasu acikinsu,amma yasan duk zasu hallara ne suna ciki suna shiryawa,
  "Abba,bari mu fara ɗaukar hoton tare dakai kafin Baby junaid ya ƙaraso,"
  fawan ne yayi maganar yana kanga wayarshi saitin fuskar Abban nasu,
dakatar dasu Abba yayi yana tambayar ina Abusufyan yake ne?bai fito bane?
Kanal yousouf yace"naje bedroom ɗinshi lokacin yana acikin toilet ɗinshi,amma ina da tabbacin zuwa yanzu ya kammala wankan ƙila ma harya shirya shima,"
  Jinjina kai abban nasu yayi tare da cewa"Gaskiya sae dae kuyi haƙuri to,babu wanda zanyi hoto dashi har sae naga ɗan uwana akusa dani,dashi nake son na fara ɗaukar hoton nan,don haka ku jirani yanzun nan zamu fito tare,"
  Bashi wuri sukayi ya wuce ɗakin Abusufyan,tura ƙopar yayi yasa kai ya shiga ciki,a lokacin Abusufyan yana tsaye gaban dressing mirror yana maƙala links ɗin hannun rigar shaddar daya sanya,madarar kyau,gezner ce ajikinshi green colour,sae faman salƙi takeyi,yayi kyau Over,ta cikin madubi ya hangi shigowar yayan nashi,
  Ƙayataccen Murmushi ya saki tare da cewa"Yaya hossein,yanzu nake shirin fitowa nima,wlh bacci ne ya ɗan dauke ni bayan mun dawo daga sallar la'asar,shiyasa na makara ban kimtsa da wuri ba,"
  Ƙarasawa ciki Abba yayi yana cewa"tun ɗazu nake ta baza idanu inga 6ullowarka,amma bangani ba,shine nace bari ni nazo da kaina na janyoka mu fita tare,don na sanar dasu cewar babu wanda zan ɗauki hoto dashi har sai naga ɗan uwana mun fara yi dashi ,'
  juyowa Abusufyan yayi a lokacin ya kammala sanya links ɗin ya kalli abba yace"yaya hossein bansan da wasu kalmomi zan iya bayyana maka irin farin cikin da nake ciki ba,wlh sai yanzu nake danasanin yin nesa da ƴan uwana,domin kuwa babu abunda yafi kasancewa tare da ahali daɗi aduniyar nan,'
Abba yace"ae bazan ƙara yin gangancin barinka kabar ƙasar nan ba,wancen lokacin ma satar hanya kayi ka gudu batare da saninmu ba,amma wannan karon zan sanya tsaro sosai akanka,ko nan da bakin gate zaka je sai da izinina,zan sanya security guards ɗin da zasu dinga bibiyarka a 6oye,"
Dariya sosai Abusufyan yayi kafin ya tsagaita da yin dariyar yace"Ya hossein nima bazan ƙara maimaita kuskuren da nayi ba,na tafiya nabarku,nasan ban kyauta ba,wlh naji ba daɗi sosai lokacin da junaid ya ƙankame ni yana murnar zuwana hada hawayenshi,sae naji wani iri araina,na tafi na barshi yana ƙarami bai mallaki hankalinshi ba,amma yanzu dana dawo na same shi ya girma sosai,a waya ne kawai nake jin muryarshi,iya wannan shaƙuwar da mukayi ta waya itace tasa ya ruƙe ni sosai aranshi,insha Allah bazan ƙara tafiya nabarku ba,nayi alkawarin hakan,"
Ba ƙaramin farin ciki Abba yayi ba,da jin kalaman ɗan uwan nashi,ruƙo hannunshi yayi acikin nashi tare da janyo shi suka fito daga cikin bedroom din,
Kamar jira suke Abban nasu ya fito tare da uncle Abusufyan da sauri suka nufesu fuskar kowannansu ɗauke da farin ciki mara misaltuwa,nan fa suka shiga ɗaukar hotuna,

💋Boss Bature💋

Tabarakallahu ahsanul khaliqin!Azmee ce ta ambaci hakan yayin da take kallon sehrish dake tsaye,sanye cikin tsadadden cord lace red colour yasha adon duwatsu ajikinshi,riga ce har guiwa sae zani,azmee da kanta ta ɗaura mata ɗankwalin golden colour tamkar gwargwaro haka ta ɗaure mata shi a kanta,fuskar nan tasha make-up ɗan light ba over ba,ta gyara jagirar idanunta duk da ta ƙara zana ta da eye pencil brown colour,ta ko'ina kwalliyar ta fiddo mata da zunzurutun kyawun fuskarta,hancin nan yayi tsayi,ga bakin nan nata yasha jan janbaki,yadda kasan wadda zata gasar sarauniyar duniya haka ta fito ɗass da ita,wasu matsiyatan takalma ƴan ubansu azmee ta ɗauko mata daga cikin shoe rack dinta,ankle strap masu tsinin gaske golden colour ne suma,launin head dinta,wayyo Allah bournvitar kyau just imagine it,
Wuyanta na sanye da ziririyar sarka golden colour,haka earrings dinta,da kuma rings ɗin da ta zura a hannunta duk launi ɗaya ne,
Kai jama'a!,ga zanen fulawar da azmee tayi mata a hannunta na jan lalle,yayi mata kyau sosai hannun nata kamar a lashe don kyau,

"Juya a hankali ki kalli madubi,"Azmee ce tayi mata maganar tana faman sakar mata murmushi,
Ajiyar zuciya sehrish ta sauke tare da juyawa awani slow ta kalli kanta acikin mirror ɗin,
Gabanta ne taji yayi wani irin bugu lokaci guda,zuba ma kanta ido tayi tana kokwonton Anya itace kuwa!?
Yarfa hannu tashiga yi aruɗe take cewa"Aunty azmee wai dagaske ni ce!dama haka nake da kyau kamar macen aljanna! Am just speechless oh my God!! 🤣😂
Maganar sehrish ba ƙaramin dariya taba Aunty azmee ba,kama hanyar fita tayi daga cikin ɗakin tana cewa"Bari naje na fara jera abincin a falo,pls kada ki fito yanzu sai nan da 15 mins nake son ki fito saboda inason inga reaction ɗin matansan gidan idan sukayi arba dake,"tana kai ƙarshen maganar ta fuce,
Ƙayataccen murmushi sehrish ta sakar ma kanta tana kallon kyakkyawar fuskarta acikin madubin,lokaci guda Sgr ya faɗo mata acikin ranta,lumshe idanunta tayi tare da buɗesu a hankali tana ƙara bin jikinta da kallo,
Sae ta dinga jin kanta tamkar amarya a wannan lokacin,amaryar kuma ta Sgr,
"Ya Allah ka nuna min wannan ranar da nake ta mafarkin zuwanta,ranar da zan kasance mallakinshi,shi ma kuma ya kasance mallakina,a wannan ranar nayi ma kaina alkawarin cewa ko bacci ba zanyi ba,zan kwana ina sallar dare,ina miƙa godiya ta ga Allah daya cikamin burina,a washe garin ranar kuma zan tashi da azumi,'
ta ƙarasa zancen zucin nata tare da samun wuri saman kujerar gaban madubin ta zauna,

Gaba daya duk sun zazzauna saman kujerun yayin da table din ke shaqe da kayan ciye ciye iri²,Abusufyan tare da Abban nasu sae junaid suna a zaune wuri daya,Ayaan da jahan da kuma fawan suna zaune suma a wuri daya suna cin abincinsu,Irfan da jabeer sae khaleed suma suna zaune a table daya,
Kanal yousouf ne ya buɗe masu taron da addu'o'i,kafin su fara kulu washarabu hani'an,sunyi haje haje da naman kaji,farfesu iri iri da sauran kayan maƙwalashe,
,kowa ya mayar da hankalinshi akan abincin dake gabanshi,
  "Wai ni ina Rafayet da Omar ne?naga kowa amma bandasu,"Abusufyan ne yayi ma Abba maganar a yayin da yake ɗaukar cup na lemu,yakai bakinshi yana kur6a,
  "Ina tunanin suna ciki suna shiryawa,kasan su fa manya ne nasu wankan ba irin namu bane,nasan shiyasa suka jima aciki basu fito ba,"a cewar abbansu,
"Naga alama,amma ni ko ina so na tambayeka yaya,wai har yanzu Sgr da Omar basu fara soyayya bane "?yayi tambayar yana kallonshi,
  Murmushi Abba ya ɗanyi kafin yace"Omar dae ya sanar dani cewa akwai yarinyar da yake so,kuma ashirye yake daya aureta,amma shi rafayet har yanzu fa babu wani sauyi yana nan yadda kasan shi,amma kwanan nan na fuskanci kamar akwai wani abu atsakaninshi da yarinyar gidan nan,wadda na faɗa maka cewa tana taya Azmee aiki,kamar akwai soyayya atsakaninsu,duk da dae bani da tabbacin hakan,"
  tunda suka soma magana junaid baisan me suke tattaunawa ba,saboda hankalinshi na can wurin tunanin abu biyu,rishi ɗinsa da kuma zuwan mommynsu a takure yake,gaba ɗaya ya gaza samun natsuwa saboda ya kwallafa rae akan zuwan nata,

Abusufyan yace"yanzu me ka yanke shawara agame dasu ne?zaka tunkari Sgr da maganar yarinyar ne ko kuwa"?

"A'a,bana tunanin cewa zai amince cewa yana sonta harma ya yarda ayi auren kasan halin shi,yanzu dai akwai wani shiri da nakeyi dama zuwanka kawai nake jira,nan da sati mai zuwa zan sanar dakai insha Allah,"
Murmushi Abusufyan yayi tare da cewa"Allah ya kaimu lafiya,"
Abba ya amsa mashi da Ameeen,
Juyawa abbansu yayi tare da kallon junaid ya ambaci sunanshi,
  Firgit junaid yayi tare da aza idanunshi kan abban nasu yace"Abbana,"
..murmushi sukayi gaba ɗayansu,Uncle abusufyan yace"junaid kodae ka fara soyayya ne?tun ɗazu muke magana amma hankalinka na'a wani wuri,"
  Murmushi ya ɗanyi tare da sunnar da kanshi ƙasa yana kallon plate dake ajiye gabanshi shaƙe da Chips,tun da Azmee ta zuba mashi bai ko ta6a shi ba,
  "Junaid naji kayi shiru kodae dagaske ne abunda Uncle ɗinku yace ka fara soyayya"?Abbansu ne yayi maganar cike da zolaya yana kallonshi,
  Duk kunya tabi ta kama junaid,ba wai abban nasu yake ji ma kunya ba,uncle ɗinsu yake ji ma kunya,don ta Abbansu har zancen aure suna yi dashi in wasan nasu ya motsa,
  yana ƙoƙarin buɗe baki yayi magana,wayar shi ta shiga ringing,jikinshi na rawa ya zura hannunshi a aljihu ya curo wayar yana duba sunan mai kiran nashi,private number ya gani wato anyi hidden ɗin numbar,kallon abbansu yayi tare da cewa"Abba zan amsa waya,"
amsa amshi yayi da cewa"okey,amma kada ka jima,muna jiranka,don bamu gama hotunan ba,"
  Murmushi ya saki tare da miƙewa yabar wurin,sae da yayi nesa dasu sannan ya ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanshi yana jiran jin wanene ke kiran nashi,
  Wata sanyayyar murya yaji ta karaɗe kunnan shi da cewa"babyn abbanshi kana ina ne"?
  Tunani ya shiga yi kodae mommynshi ce don haka yace"ina a gida ne,"
  Matar tace"Idan ba damuwa kazo Airport kadauke ni,na ƙaraso Nigeria amma banaso kowa yasan da maganar,kai kadae kawai nakeso kazo ɗaukana,Kada ka bari kowa ya biyo ka"
  da ƙarfi junaid ya ambaci sunan mommy fuskar nan tashi cike da farin ciki yace"mommy am coming right away"
  Matar tace"okey,idan ka fito daga cikin gidan ka sanar mun,"
  Cike da zumuɗi ya amsa mata da toh,sannan jiki na rawa ya katse kiran tare da zura wayar a aljihun shi,
  Gaba ɗaya ya gaza rufe bakinshi saboda tsabar farin ciki,juyawa yayi yana kallon ƴan uwanshi dake zazzaune kowannansu fuskarshi ɗauke da farin ciki,aranshi yace"kodai na sanar masu cewa mommy ta ƙaraso?kuma dae tace kar na faɗama kowa,gaskiya bazan faɗa masu ba,zan basu mamaki ne nasan in suka ga mommy zasu yi murna sosai,amma kuma inason na sanya rishi a idanuna kafin nabar gidan nan,bari nayi sauri naje naga wankanta na yau,
  Yayi maganar tare da nufar corridorn ɗakinsu sehrish da sauri da sauri ya ƙarasa kopar bedroom ɗin nata,
  A lokacin tana acikin bedroom din nata sae faman zagaye takeyi,tarasa ya zatayi ta fita,kunya take ji su ganta da kwalliyar jikinta,
Jin kwankwasa ƙopar ɗakin nata yasa ta cewa"wanene,"
daga waje junaid ya amsa mata da cewa"Mijinki ne insha Allah,"
  Murmushi ta saki tare da cewa"ka samu iznin shigowa ciki,daga matarka insha Allah,"
  tura ƙopar yayi tare da sanya ƙafa ya shiga cikin ɗakin,koda yayi arba da sehrish nan take yaji gabanshi ya faɗi,kokwonto ya shiga yi yana tambayar kanshi Anya wannan sehrish ce kuwa?
  matsawa kusa dashi tayi tace"meya faru junaid naga ka toge anan?
  "Reesh,kinyi kyau Over,"cikin sanyin murya yayi maganar,don ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,
  Ƙayataccen murmushi ta sakar mashi tare da cewa"saboda kai nayi wannan kwalliyar,launin lips dinka red colour ne,shiyasa nima na sanya jan lace don inyi anko da kai,to ya kaga wankan"?
tayi maganar tare da jujjuya mashi bayanta don ya kalla da kyau,aikuwa ba ƙaramin ruɗashi tayi ba,gaba daya yabi ya susuce,
Kamar yakai mata runguma haka yaje ji,amma ba halin yin hakan jikin shi sae faman kerma ya keyi,
juyawa tayi tare da nufar bedside drawer dinta,ta ɗauko wayarta tare da dawowa saitinshi ta ɗaga wayar tare da cewa"ka shirya in ɗauka?'tayi maganar tana jiran jin amsarshi,
Jin hannunshi ta gefen waist dinta yasa ta ɗan razana kaɗan,sosai ya ruƙo qugunta tare da kwantar da kanshi saman kafaɗarta yace"ki ɗauka,"
Zuba mashi ido tayi ta cikin camera ɗin tana kallon fuskarshi,hakanan ta dinga jin zuciyarta nayi mata wani irin bugu,muryarta akasalance tace"junaid ka buɗe idanunka,taya zan ɗauka dakai ido a rufe"?
Murmushi yayi tare da buɗe idanunshi yana cewa"Reesh,ƙamshin turaran nan naki,kashe mun jiki na yake yi,ba kiji yarda nake ji ba,don Allah reesh,kada ki guje ni kinji"?
Martanin murmushin ta mayar mashi sannan tace"junaid banda hankaline da zan guje ka?angaya maka kai irin mazan da ake gudu ne?kai fa na musamman ne junaid,tun farkon ranar dana fara zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login