Showing 219001 words to 222000 words out of 245004 words
Chapter 74 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
take baida burin daya wuce afita yawo tare da ƴan mata akashe masu kuɗi,kullum yana manne dasu,shi dai kawai yaji mace akusa dashi ba namiji ba,kuma bawai don yayi wani abu da ita ba,sam shi wannan bai agabansa,
Ana haka su Abusufyan suka samu hutun makaranta,atare da dr haris suka je kai ziyara zariya wurin danginsu,
Bayan tafiyarsu ne,Hajiya Amina da Mijinta alhaji nuraddeen suka tafi umra,dama tun kafin su tafi alhaji ya sallami mai gadin gidansu baba buzu don yaje ƙasarsu niger ya gano danginshi kafin su dawo,
Ba ƙaramin daɗi yaji ba,saboda dama atakure yake na rashin ganin ƴar shi tilo da yake da ita,kullum yana cikin damuwar rashin yarinyar a kusa dashi,saboda halin da ya barota acan,basu da kowa danginsu duk sun tarwatse ba haɗin kai,ga talauci dake damun kowannansu,ita kanta yarinyar ya barta ne a hannun matar babanshi,tunda baida kowa iyayenshi duk sun rasu,matar nan ta tsani yarinyar ta takurama rayuwarta gata irin tsoffin nan ne masu mitar tsiya,duk wani aiki yarinyar take ɗauramawa,girki,sharar gida,wanki,ɗebo ruwa,kuma ƙarama ce alokacin bazata wuce 16 years ba,
Koda baba buzu yazo niger ganin gida,zuwan bazata yayi masu bai sanar ma kowa da maganar zuwan nashi ba,saboda yana so yaba Abu mamaki kuma yaga irin farin cikin da zatayi idan ta ganshi,kwatsam yana shiga gidan ya samu matar baban nan tashi zaune saman abu ta danneta a tsakar gida,yarinyar sai ihu takeyi tana wutsil wutsil da ƙafafunta,ita kuma matar sae sambatu takeyi tana cewa"Babu abunda zai hana inƙi kasheki acikin gidan nan Abu,dan ubanki ni zakiyi ma asarar tsintsiya?kin barta a ƙasa har ruwan sama ya jiƙata baki ɗauketa ba!ko don kina taƙamar ubanki ne ke turo mana da kuɗi muna siyan kayan abinci....'
Hankalin baba buzu ba ƙaramin tashi yayi ba a wannan lokacin,ganin zai rasa ƴarshi ɗaya tilo akan tsintsiyar shara da bata wuce naira hamsin ba,ba ƙaramin fusata yayi ba,a ranar ko zama gidan baiyi ba ya ɗauki ƴarshi ya tafi da ita gidan wani amininshi,tamkar ya zubar mata da hawaye haka yaji a wannan lokacin,yarinyar duk ta rame ta fige ta ƙanjame kamar ba mutun ba,yarinyar da duk garinsu babu wanda ya kama ƙafarta a wurin kyau,tun lokacin da mahaifiyarta ta haifa mashi ita,Allah yayi mata rasuwa tabar mashi ita ƴar jinjira da ita,shi yaci gaba da kula da yarinyar,mutane sunsha zuwa suna nuna mashi kuɗi don ya bar musu yarinyar su ruƙe awurinsu amma yaƙi amincewa da hakan,saboda son da yake yi mata,
Bayan hajiya Amina sun dawo nigeria ita da mijinta,Baba buzu ya shirya tafiya tare da ƴarsa abu,babu yarda abokinshi baiyi dashi ba akan ya bar mashi Abu suci gaba da kular mashi da yarinyar a hannunsu,amma ina yace ae ƙafarshi kafar abu,bazai ƙara gangancin barinta a wurin wani ba,kwara ta kasance atare dashi,yana jin motsinta a kusa dashi,zaifi samun kwanciyar hankali,
Da daddare suka ƙaraso nigeria bayan uwar tafiyar da suka sha agalabaice suka iso cikin gidan,ruƙe da hannun Abu ya shigo cikin falon gidan,lokacin hajiya ameena na zaune saman kujera mai mazaunin mutun uku tana kallo a tv,tun da sukayi sallama ta dago ta kellesu ganin baba buzu yasa ta saki fara'a tana cewa"marhabun lale ƙaraso ciki mutumina,ashe kana kan hanya banyi tsammanin zuwan.....'bata ƙarasa maganar ba,saboda ganin yarinyar dake ruke da hannunshi,
.mikewa tayi tare da zame farin glass ɗin dake a fuskarta tace"baba buzu wannan yarinyar fa?yar waye kazo da ita,"
bai bata amsa ba,sae da suka ƙarasa wurin kujerar da take tsaye,suka zauna kasa saman carpet,sannan ya soma magana"hajiya shannunku da dawowa,ya gajiyar tafiya,'
"Lafiyalou Alhmdulillah,"
Taƙarasa maganar har lokacin idanunta na akan abu,komawa tayi tare da zama saman kujerar sannan tace"bakayi mun bayani game da yarinyar nan ba,"Tayi maganar tana nuna Abu dake ƙankame jikin abbanta
Fargabarsa kada ya sanar dasu cewa ƴarshi ce,suƙi kar6arta baisan inda zai kai yarinyar ba,ya kwaso yarinya ya kawo masu batare da ya sanar dasu ba,
dakyar ya iya buɗe baki muryarshi kamar zaiyi kuka yace"yarinyar wurina ce hajiya sunanta Abu,ina neman alfarmar ku taimaka mun ta zauna awurina,saboda bata da kowa acan niger,dama a hannun kishiyar babata take zaune,matar bata da imani naje na shame ta tana gallazama yarinyar nan,ban ta6a sanin abunda ke faruwa ba,sai da nayi masu zuwan bazatan nan.......'komai ya kawashe ya sanar ma hajiya ameena,
Kamar jira takeyi ya kai ƙarshen maganar tashi,nan ta rufe shi da faɗa tana cewa"Amma baba buzu ka bani mamaki wlh,yanzu duk irin shaƙuwar dake tsakaninmu dakai,duk irin yarda muka ɗaukeka tamkar ɗanuwanmu,hakan baisa ka sanar damu cewa kana da ƴa ba,meyasa tun lokacin daka fara aiki agidan nan baka ɗauko yarinyar ka kawota gidan nan ba!....'ta inda take shiga bata nan take fita ba,
Jin waɗannan kalaman na Hajiya ameena yasa baba buzu fashewa da kuka yana cewa"na cuci kaina da ban sanar maku ba,ban ta6a tunanin cewa zaku kar6i yarinyar nan hannu bibbiyu ba hajia,da tuni na jima da kawo maku ita,kullum ina cikin takaicin rashinta a kusa dani,saboda itace kaɗai nake gani inji dadi aduniyar nan......'sosai baba buzu ke zubda hawayenshi,
Abu kuwa ganin mahaifinta na kuka yasa itama ta fashe da kukan,jikin hajiya ameena ne yayi sanyi,tausayinsu duk ya kamata,
tausasa muryarta tayi tace"baba buzu kukan ya isa hakanan,naji daɗin dawowarka musamman daka kawo mana wannan ƴar kyakkyawar yarinyar taka,kuma insha Allahu zamu bata kyakkyawar kulawa,zata zama tamkar ƴar cikina,dama kuma banda ƴa' mace,gashi inason ƴa mace,Ashe da rabon zan samu......'
Share hawayen shi ya shiga yi yana yi mata godiya,
"Yanzu abunda nakeso dakai,ka wuce ɗakinka kayi wanka zansa akawo maka abinci,nasan kun kwaso gajiya sosai kuna bukatar hutu,ita abu kabarta awurina,zan gyara maka ita sosai da anjima zata zo ta gaishe ka,"
Cikin shesshekar kuka baba buzu yace"hajiya bansan da wani irin kalamai zan gode maku ba,kunyi mun abinda bazan iya saka maku ba,kun jima kuna ɗawainiya dani kuma yanzu gashi zaku ɗauki ɗawainiyar yarinyata,Allah yasa ka maku da mafifincin alkhairinsa.....'sosai baba buzu ya shiga yi masu addu'o'i hakan ba ƙaramin dadi yayi ma Hajiya ameena ba,
Tun daga wannan lokacin Abu tazama tamkar ƴa awurin hajiya Ameena,baka ta6a gane cewa ba ƴar cikinta bace saboda yadda suke ruƙe ta hannu bibbiyu duk wata ɗawainiyarta tadawo kansu,hatta makarantar islamiyya dana boko babu wanda basu sakata ba,dama yarinyar akwai hazaƙa sosai,akwai son karatun addini,kullum zaka ganta rungume da kur'ani a hannunta tana karatu,ko aiki takeyi zaka ji tana ta rero karatun haddar da aka basu,bata ta6a zama bakinta shiru batare da tana karatu ba,wannan abun ba ƙaramin burge hajiya ameena yake ba,shiyasa batajin wuyar kashe mata kuɗi,saboda ita ta ɗauko malamin da zai dinga zuwa gida yanayi mata karatu,malamin makarantar islamiyyarsu wanda suke kira da Ya sayyadi,tun da zainab tafara zuwa makarantar islamiyyar asatin farko kullum sai yazo gaishe da hajiya ameenatu,idan yazo yayi ta zuzuta zainab awurinta yana yaba irin ƙoƙarin dake gare ta,hajiya Ameenatu najin daɗin hakan,Amma mahaifin Abu,baba buzu mai gadi mutumin bai kwanta mashi araiba,ya tsani yaga malamin nan yazo wurin Abu zai koya mata karatu,shisshigin da yake yi ma yarinyar yayi yawa,kullum sai yazo da ɗan rugwagwar mashin ɗinshi ƙopar gate din gidan wurinta,hakan ba ƙaramin ƙona ma Baba buzu rai yake ba,shiru kawai yake yi don bai da yadda zaiyi ya hana shi zuwa gidan,tunda hajiya ameenatu ta ɗauke shi amatsayin malamin da zai dinga koyama Abu karatu,tun Abu na da wata daya acikin gidan haris ya dawo batare da Abusufyan ba,saboda shi yace bazai dawo ba sai daddy mijin Aunty ameenatu ya bashi haƙuri,saboda yace shi yake 6ata tarbiyyar Haris,rashin jin maganar shi yayi yawa,koda haris ya hadu da Abu acikin gidan saiya mayar da ita tamkar ƙanwarshi,idan aka bata assignment na school shike zama ya fidda mata shi,harma ya koya mata karatu.
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖*
*Ga duk maison karanta littafin Abban sojoji,zai biya 300 ne,za'a tura mashi tundaga farko har inda muka tsaya,kuma zai cigaba da samun update dinshi akai akai,ga wanda ke buƙata zai tura mun message ta whatsapp ɗina (08103884440) kada ku bari abaku labari*,
Bayan wani lokaci
Tafiya takeyi tamkar batason taka ƙasa,jikinta na sanye da uniform na islamiyya,dogon hijab Brown colour har wuce guiwarta,wandon kuma milk colour,ta rufe fuskarta da nikab,yayin da hannayenta ke ruƙe da jakar makarantarta,da gudun gaske wata danƙareriyar mota ash colour ta faɗo cikin layin da take tafiya,gadan gadan mai motar ya tunkari inda Abu taja ta tsaya,waro ido waje tayi tare da ja da baya jikinta na kerma,koda mai motar nan ya ƙaraso inda take,sai ya shiga zagaye ta da motar gaba ɗaya ya tada mata ƙura,
Ƙanƙame jikinta tayi gabanta ya faɗi rass,tsoronta kar ace sace ta aka zo yi,
Sai da ya tabbatar da cewa ta gama tsorata sannan ya tsayar da motar wuri guda ta tsaya cak,
A ɗan tsorace abu ta buɗe idanunta tana kallon motar cikin ranta tana tunanin wanene wannan bawan Allahn daya firgitar da ita haka,
Bata ƙarasa zancen zucin nata ba taga ya zuge glass ɗin motar,lokacin da tayi arba da kyakkyawar fuskarshi sae da gabanta ya faɗi rasss!matashi ne wanda bazai gaza shekara 20 ba zuwa ashirin da daya,kana kallonshi zaka ga ƙuruciya atare dashi,jikinshi na sanye da crazy jeans sae farar t shirt agaban rigar an rubuta Am crazy,'da alama bashi kaɗae bane acikin motar,akwai wani agefen shi,
Muryar mace tajiyo daga cikin motar tashi tana cewa"Hey,ƴan mata,mun tsorata ki ko?ki yi haƙuri Babyn nawa ne sae a hankali,wai kin burge shi ne,shiyasa yayi maki wannan wasan,'.
rai atsananin 6ace take kallon fuskokinsu ta cikin niqab din fuskarta,bakowa yafi bata haushi ba face shi saurayin daya yi mata wannan ɗanyen aikin,arayuwarta ta tsani mutane masu wayewa irin tasu,kallo guda tayi masu ta gane cewa ba mata da miji bane,amma sun manne ma juna acikin motar kamar zasu haɗe su zama ɗaya,
jinjina kai kawai tayi tare da zuƙunnawa ta ɗauki jakar islamiyyarta da ta fadi,cikin sauri ta kama hanyar zuwa gida,biyo ta sukayi da motarsu,hakan yasa hankalinta ya tashi,saboda gudun kada Abbanta ya ga motar dake biye da ita,don kullum yana ja mata kunne akan karta kuskura wani ya tsaidata akan hanya ta tsaya,yanzu in ya ganta tare da wannan jibgegiyar motar dake bin bayanta batasan wane hukunci zaiyi mata ba,dole ya tuhume ta akan ina ta samo su,
"Baby,kana ganin zata faɗa mana address ɗinta kuwa?da alama yarinyar kamar za tayi ji da kai nake gani,kasan ƴan islamiyyan nan,ji su keyi kamar sunfi kowa tsoran Allah,suyi ta kame kansu acikin hijabi,suna yi ma mutane kallon shaiɗanu,'matashiyar dake acikin motar ce tayi wannan maganar,kuma duk akan kunnan Abu,
Saurayin yace"ae ko bata faɗa mana address ɗinta ba,zamuyi ta bin bayanta ne har mu gano gidansu,"
Jin wannan maganar yasa,yarinyar zuƙunnawa tare da kwale takalman ƙafafunta,kafin su ankara ta watsa da gudun gaske kamar zata tashi sama,ko waiwayensu batayi,har ta 6ace ma ganinsu,,
Tun daga nesa Baba buzu mai gadin dake a zaune saman benchi yana sauraron radiyo dake ruke a hannunshi,ya hango ta sai faman tsala gudu takeyi,hankali tashe ya miƙe tsaye yana jiran ƙarasowarta,koda ta ƙaraso a galabaice ta zube agabanshi,saman guiwowinta tana faman haki,
"Abu meya faru ne naga kina gudu haka?waye ya biyo ki"?
Muryar mahaifin nata ne ta dawo da ita cikin hayyacinta,
daƙyar ta iya cewa"wasu ne a mota,bansan kosu wanene ba,sae faman bibiyata sukeyi,shine na watso da gudu don karsu gane gidan da nake,"
Jin wannan maganar yasa ran buzun mai gadin ya 6aci sosai nan fa yashiga zazzaga masifa yana cewa"da kin bari sun ƙaraso don ubansu dana koya masu hankali,shikenan ba dama yarinya ta ɗan fita ɗauko karatu sae an samu wanda ya takura rayuwarta!zan yi maganin koma wane ɗan ja'irin ne yake son cutar mun dake.....'ta inda yake shiga batanan yake fita ba, a ƙarshe dae yace"tashi ki shiga ciki,kiyi wanka kici abinci ki kwanta ki huta kafin akira sallar magariba,ki kwantar da hankalinki kinji Abunah,ina nan ina jiran Koma wane ɗan iskan ne,saina koya masu hankali,'
Ajiyar zuciya abu ta sauke tare da miƙewa tayi mashi sallama,sannan ta shiga cikin gidan ta ƙopar gate ɗinsa,
Lokacin da ta shiga cikin main palour ɗin gidan babu kowa,alamar suna can upstairs bedrooms ɗinsu,don haka ta wuce nata ɗakin kai tsaye,
Bayan ta ajiye jakar islamiyyarta,ta cire hijab ɗin jikinta,ta ninketa tare da turata cikin wardrobe na kayanta,shaf shaf ta kammala cire kayan islamiyan nata ta wuce cikin toilet don tayi wanka,
After some minutes,ta fito daga cikin toilet ɗin jikinta ɗaure da farin towel,jikin nan nata har wani ƙalli yakeyi saboda hasken fatarta ga gyaran da take sha,agaban mirror ta tsaya tana ɗaure sumar kanta mai tsayi da yawan gaske,tana da yalwataccen gashin kai wanda yakai har qugunta,tana cikin ɗaure gashin kan nan nata kwatsam taji anyi mata gyaran murya abayanta,a firgice tajiyo don ta ga kowanene,lokacin da tayi arba da mutumin da yayi mata gyaran muryar acikin ɗakinta nan take ta zazzaro ido amatuƙar tsorace take kallonshi,
kwance yake asaman gadonta,ya miƙe ƙafafunshi yayin da hannunshi ke ruƙe da brazier ɗinta da ta cire kafin tashiga toilet,sae faman latsa breast curve ɗin yakeyi cike da tsokana,
Hankali a matukar tashe abu tace"innalillahi wa'inna ilaihirraji'un...Nashiga uku....!'gaba daya taba ma ranta cewa al'jani ne shi,ba kowa bane wannan face saurayin nan daya tsoratar da ita da motarshi akan hanyarta ta dawowa daga islamiyya,shi da budurwarshi,
Muryarta na rawa tace"wa..wanene...kai dan Allah!me kakeso a wurina ne!taya akai kasan gidan mu har ka biyoni ɗakina"?
Ƙayataccen murmushi ya saki tare da cewa"bani da amsar tambayoyinki,ni dai kawai nagani inaso,in kika yi mun biyayya mu rabu lafiya,koda yake bazama mu ta6a rabuwa ba,saboda kinyi mun wlh," ya ƙarasa maganar tare da kai bakinsa ya manna ma bra ɗinta kiss
Runtse ido abu tayi agigice ta fasa ihu tana neman ɗauki,akan azo a fidda mata aljanin dake aɗakinta,
Da gudu ta watsa waje babban falon jikinta na kerma ta shiga cewa"Mommy!!mommy!!ya haris!daddy!!dan Allah kuzo ku taimake ni,Aljani aɗakina saman gadona....'
Jin sautin kukan Abu yasa hankalin Hajiya ameena tashi,da saurin gaske ta sauko downstairs ta nufi wurinta tana cewa"Abu meya faru ne kike ta kwaɗa ihu?
Cikin shessheƙar kuka tace"Wani ne acikin ɗakina saman gadona,bansan ko wanene shi ba,a kan hanyar dawowata daga islamiyya ya tsoratar dani da motarshi,shine yanzu kuma bayan na fito daga wanka na ganshi kwance saman gadona,'
Cike da mamaki hajiya Ameena tace"Wani kuma!acikin gidan nan saman gadonki?taya akai har ya samu damar shigowa cikin gidan nan....'
Ba ta kaiga ƙarasa maganar ba,sae ga Abusufyan ya fito daga cikin ɗakin abun,fuskarshi ɗauke da murmushi,
Ganin shi yasa abu yin saurin nuna shi da hannu tace"Ga shi nan mommy....wlh shine ..Aljani ne,"
murmushi hajiya Ameenatu tayi tana kallon Abusufyan tace"Son sai yau kaga damar dawowa gidan?irin wannan zuwan bazata haka?ka tafi kabarmu da kewarka ko?ko tunanin makaranta bakayi ba,ka kama hanya ka tafi kan abunda bai kai ya kawo ba,'
Langwa6e kai abusufyan yayi yana tsuke bakinshi alamar an 6ata mashi rai,
...zuru abu tayi tana kallon ikon Allah,aranta tana cewa"Ashe ɗan masu gidan nan ne,ni duk atunanina aljani ne shi,amma dae da alama baijin magana sosai,'
"Pls mom just forget about it,komai ya wuce tunda dae nadawo,"
Jinjina kai hajiya ameenatu tayi,kafin ta mayar da idanunta kan Abu dake tsaye sototo tana kallonsu tace"Calm down ur mind Abuna,wannan da kike gani ɗan yayata ne,sunan shi Abusufyan,bai jin magana amma kada wannan ya hanaki sakewa dashi,shima ki ɗauke shi tamkar Yayanki Haris,'
Jiki asanyaye tace"insha Allah mommy,"kafin ta ɗan wurga ido ta kallo shi har lokacin kashe mata ido yakeyi,hakan ba ƙaramin haushi yake bata ba,har tafara jin tsanarshi,
Tun daga ranar da Abusufyan ya dawo cikin gidan abu ta shiga uku dashi,ya hana rayuwarta sakat,duk inda ta sanya ƙafarta yana biye da ita,toilet ne kawai bai binta shi dai kawai burinshi ta sake dashi kamar yarda take shiri da haris,ita kuma tace bazata ta6a ɗaukarshi yayanta ba,saboda bai da kamun kai,bakomai yaja mashi hakan ba face Abubuwan da yake yi mata na rashin kunya,da kuma ƴan mata da take ganinshi tare dasu manne da juna,hakan ba ƙaramin ƙona mata rae yake yi ba,duk a tunaninta Abusufyan ɗan iska ne kamar yana bin mata,saboda ita tayi believing da abunda idanuwanta ke nuna mata,
Ana haka wata rana malamin nan nasu Sayyadi ya ɗaukota daga islamiyya asaman machine dinsa super cub,tun suna akan hanya motar abusufyan ke bin bayansu saboda ya hangota abayan mashin ɗin malamin,ranshi yayi mugun 6aci wani irin kashi ne ya lullu6e shi,saboda ya lura akwai soyayya tsakaninta da malamin nan nasu,babu yarda abusufyan baiyi da ita ba akan ta bari ya dinga kaita school amma taƙiya,da yake tana da kafiya sosai,mace ce mai wuyar sha'ani,
A bakin gate ɗin gidan sayyadi ya tsayar da mashine ɗinsa,abu ta sauko hannunta ruƙe da jakarta,tsayawa tayi suna ƙara gaisawa dashi,
"Abu har yanzu baki bani amsa ta ba"?
Sunnar da kai ta ɗanyi tana murmushi tace"amsar me kenan"?
sayyadi yace"oh har kin manta kenan?abu kinfa san ina sonki sosai,kuma kema kina sona,bana buƙatar mu 6ata lokaci atare da juna batare da munyi aure ba,banda burin daya wuce wannan, in ganki amatsayin matar aure na,'
Cike da jin kunyarshi abu tace"dan Allah ka ƙara mun lokaci,zanyi tunani akan hakan,'
Kafin sayyadi ya buɗe baki ya ƙara yin wata maganar,suka ji dirar motar Abusufyan agefensu,tun daga kan yarda yayi parking ɗin motar ya tabbatar masu da cewar ba'a hayyacinshi yake ba,
.zuba ma motar ido sayyadi yayi kafin ya mayar da idonshi kan abu yace"wanene acikin motar nan"?
Muryarta na rawa tace"yayana ne Abusufyan,'
ɗan ta6e bakinshi yayi yana jinjina kai,
Atsiyace abusufyan ya buɗe murfin motar ya fito,jikinshi sai faman rawa yake yi,kai tsaye wurinsu ya nufo sai faman huci yake yi,
Wani irin mugun kallo ya jefa mata tare da nuna mata hanyar gida yace"Ke wuce ciki!tun kafin ranki ya 6aci shashasha kawai wadda batasan ciwon kanta ba!ki rasa da wa zakiyi mu'amala sae wannan ƙarmasasshen mutumin,ko uban miye abun so ajikinshi!mutumin da ya kusa tsaran ubanki!"
Hankalin abu ba ƙaramin tashi yayi ba jiki na rawa ta kama hanyar shiga gida,
Muryar sayyadi ce ta dakatar da ita"Abu kada ki tafi!bangama magana dake ba,"
Zuba ido abusufyan yayi yana kallon ikon Allah,tsayawa abu tayi saboda umarnin da sayyadi ya bata akan karta tafi,
Rai amatuƙar 6ace Abusufyan ya daka mata tsawa tare da cewa"ke!har ni zan baki umarni kiƙiyi mun biyayya saboda wannan