Showing 183001 words to 186000 words out of 245004 words

Chapter 62 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download

17 Mar 2025

25296

saman sofa ɗin ya nufi hanyar fita,duk suka zuba mashi ido,
Sai da yakai bakin kopar fita sannan ya ɗan juyo tare da kallon inda Hajiya azeema take zaune yace"Allah ya huta gajiya,"yana faɗin hakan yasa kai ya fuce daga ɗakin,
  Girgiza kai Abbansu yayi tare da cewa"Rafayet sai addu'a abun nashi ƙara gaba yake yi,"murmushi kawai azeema tayi aranta tace"Jinin Alexandra kenan,in har rafayet baiyi mun haka ba,bazan tabbatar da cewa nononta ya sha ba,
Ganin rafayet ya fice yasa Omar miƙewa tare da yi masu sallama ya fuce yabarsu donsu samu damar tatttaunawa atsakaninsu yasan sunyi kewar juna sosai,

Bayan fitar Omar,azeema ta kalli abban nasu tare da cewa"Yaya hossein,ya maganar zuwan Abusufyan din?dagaske ne yau ɗin shima zaizo?kasan fa ya jima yana samana ran cewa zaizo sai kuma yaƙi zuwa daga baya,abun na damuna sosai,"fuskarta ɗauke da damuwa tayi maganar,
  "ya tabbatar mun da zuwan nashi,kuma ina da tabbacin cewa wannan karan dagaske yake mana ba wasa ba,inaso yazo saboda akwai abubuwa da dama da nake son muyi magana akai,na damu dashi sosai,na damu da halin da yake ciki,"
Jinjina kai tayi tace"amma abba,akwai wata alfarma da nake nema awurinka,"
   "Wace alfarma kenan"?acewar abban nasu,
  Cigaba da magana tayi"idan Abusufyan yazo nigeria wannan karon banso ku bari ya koma turkey,dan Allah ka ruƙe shi anan,ya zauna akusa dakai,banason yanayin nesa dakai,har yanzu akwai sauran yarinta atattare dashi,shi ne ƙarami acikinmu akwai buƙatar mu janyo shi ajikinmu,don muji menene ke damunshi,meyasa baya son zama ƙasar nan,ni nasan akwai dalilin da yasa abusufyan yake gudun zama anan,tabbas akwai damuwa atattare dashi,"
   Abba yace"dama ni bazan barshi ya koma can ba,bazan ƙara yin gangancin barinshi yayi nesa dani ba,koda can daya bar ƙasar batare da sanin mu ya tafi ba,narasa gane mashi ni kaina,ba yarda banyi dashi ba akan yadawo nan gida amma yaƙi saurare na,wannan karan dae mun ci sa'a ya amince zaizo,kuma insha Allah idan yazo bazan barshi ya koma ba,zan ruƙe shi awurina,'
  Ajiyar zuciya azeema ta sauke,hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba,dama ita burinta Abusufyan yadawo kusa da Yayansu hossein su zauna atare da ƴa'ƴanshi,tafi son taga sun haɗa kansu wuri ɗaya,ita kanta ba da son ranta take zaune a lagos ba,sabo ne kawai sai kuma harkokin kasuwancinta da suka fi yawa acan,
   Sun jima suna fira tsakaninta da ɗan uwanta,kafin daga bisani yayi mata sallama tare da fucewa daga ɗakin,komawa azeema tayi tare da kwantawa saman gadon,nan take bacci yayi awon gaba da ita,

A 6angaren sehrish kuwa tunda taje school,fuskarta babu annuri ko kaɗan duk tabi ta takure kanta asaman seat ɗinta,ko magana batasan yi,juyowa Amrish tayi ta kalli fuskarta tare da cewa"wai meyake damunki ne Sehrish?duk kin bi kin canza,ki faɗamun mana in akwai damuwa,may be ina da shawarar da zan iya baki,"
   shiru tayi na wani lokaci kafin tace"Zan faɗa maki,but pls kada ki sanarwa kowa,"
  "Insha allah,i will keep ur secret bazan bari kowa yaji ba,"amrish tayi maganar tare da mayar da hankalinta kan sehrish,
   matsowa sehrish tayi kusa da amrish tayi ƙasa ƙasa da muryarta sannan tace"Amrish,babban yayanmu ne ya datse mun gashin kaina,dana kwallafa rai akanshi,na jima ina gyara gashin kaina,sai da yayi tsayi sosai yayi kyau,shi kuma ya datse mun shi da almakashi,baki ga wanda yabar mun ba,ɗan guntu ko parking ma bayayi,in nasa ribbom ma zamewa yakeyi,baya ruƙe gashin,'
   Hankali tashe Amrish tace"Are u serious!shi da kanshi yayan naku ya yanke maki gashi?baisan cewa gashi tsada yake yi ba,?amma garin yaya hakan ya faru?ta tambaya tana jiran amsarta,
  shiru ta ɗanyi kafin tace"ni kaina bansani ba Amrish,da safe ne naje kai mashi coffee,yana cikin sha wani abu ya sarƙe mashi a throat ɗinshi,ashe gashi ne ya faɗa ciki,kuma ni banawa bane,nayi ƙoƙarin nayi mashi bayani akan hakan,amma bai saurareni ba,kawai yasa almakashi ya datse mun gashin,'ƙarasa maganar tayi muryarta tamkar zata fashe da kuka,
  hannu amrish tasa tare da dafe goshinta tace"Ya salam,amma banji daɗi ba wlh,ni babban abunda nafi takaici shine,wazai aure ki a haka da guntun gashi,kinsan fa mazan yanzu sunfi son mace mai dogon gashi,"cike da zolaya amrish tayi maganar tana ƙumshe dariya abakinta,
  Harara sehrish ta watsa mata tare da cewa"Oh abun ya zama na zolaya ko?ina faɗa maki damuwata maimakon ki tayani jimami shine kike mun dariya,'
   "No,ba haka bane sehrish,nadamu nima sosai,rai na ya 6aci amma kada ki sa damuwa aranki,zan iya taimaka maki da hular gashi in kinaso,'
   Cike da farin ciki sehrish tace"dagaske kike ko wasa"?
  Amrish tace"am serious,ina dasu ajiye a gida zan ɗauko maki ɗaya daga cikinsu,amma bisa sharaɗin zaki kawo mun gashin kanki da babban yayanku ya yanke maki,inaso zanyi amfani dashi wurin haɗa wata hular gashin,ba ƙaramin kuɗi zamu samu ba,'
   murmushi Sehrish ta saki tare da cewa"shikenan insha Allah,zan kawo maki gashin gobe in zanzo school,'
   "Allah ya kaimu lafiya,"Amrish ta amsa mata,ci gaba da fira su kayi atsakaninsu har sae da malamarsu ta shigo sannan suka dakata da yin surutun nasu,

_💋Boss Bature💋_

Ana gab da za'a tashe su daga school,ciwon ciki yazo mata mai tsananin gaske,gaza jurewa tayi hakan yasa ta miƙe tare da zuwa wurin Aunty ɗinsu ta nemi izinin fita a wurinta,bayan ta amince mata ta fito daga class ɗinsu,sai faman sauri takeyi,hannunta ɗauke da school bag dinta,wani corridor ta nufa inda toilets din makarantar suke a jere,ɗaya daga cikin toilet din ta buɗe tare da shigewa ciki ta rufo shi,juyawa tayi tana kallon cikin toilet din komai na cikinshi fari ƙyal atsaftace,hannu tasa tare da zuge zip ɗin jakarta,ta ciro pad din da tazo da ita guda ɗaya,dama tun last week take jin alamun zuwan al'darta amma baizo ba,sai dae stomach pain da take ta fama dashi,wannan dalilin ne yasa take yawo da pad a jakarta just in case,

   ajikin towel hanger,ta rataya jakarta,sannan ta zame dogon wandon jikinta,pant ɗin ta curo tana dubawa taga ko ya fara zuba,babu ajikin pant ɗin,amma da taje wurin yin tsarki bayan tayi fitsari sai ga ɗigon jinin ya fito,cikin sauri ta sanya pad din ajikin pant dinta,sannan ta sanyashi ajikinta,ta ɗauko dogon wandon ta mayar ajikinta,sai da ta zura shi ajikinta,ta ɗauko jakarta tana ƙoƙarin fita daga cikin toilet din kenan,cikinta ya murɗa mata,wani irin raɗaɗi mara daɗin ji,nan take ta zukunna ƙasa hannunta dafe da cikinta,zufa ce ta shiga gangaro mata agefen fuskarta,daƙyar take fitar da numfashi,lokaci guda gaba daya ta galabaita ta fita hayyacinta,anan ta faɗi kwance saman tiles tana juyi ita kadae acikin toilet ɗin,babu wanda yasan abunda ke wakana.

*💋Boss Bature💋*



Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1




قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖


*Na sadaukar da wannan zazzafan page din,ga dukkan masoyan littafin Abban sojoji,especially members na paid grp dina,Abban sojoji paid grp,Father of soldiers,Abban sojoji Vip grp,da kuma Junaid romeo Much luv Allah yabar zumunci anatare insha Allah (08103884440)*😍😘



*Bazan manta daku ba,waɗanda suka ƙarfafamun guiwa wurin rubuta littafin nan,har yau ina alfahari daku,
Fadeela lamiɗo da kuma sadeeq abubakar CEO na Lafazi writer association,da kuma auntyna takaina,bazan fadi sunanta ba,sai na nemi ixninta saboda tsaro🤣😂😅
Da kuma sauran members dinda akayi fadi tashi dasu,suma duk zan fadi sunayensu nan gaba*

*Abban sojoji paid book ne,duk maison siye zaiyi mun magana kai tsaye ta layina,but pls banda kiran waya,only message ta whatsapp,bana shariya muddin mutun ya turamun saƙo zan duba ne,indae ina free,in mutun yayi payment zan tura mashi duka na baya da aka wuce shi har inda muke so*


❤🤍❤


*Junaid*


Tun bayan daya kai Sehrish school ya biya gidansu wani abokinshi,wanda tun suna secondry school suke tare,acan ya yini har bacci yayi awon gaba dashi asaman gadon mamarsu abokin nasu,saboda tsabar gatanci bama gadon abokin nashi ba,a ɗakin mamarsu yayi baccin,daga shiga su gaisa da ita,ya samu ta shiga cikin toilet,shi ne ya ɗan kishingida saman gadon ya shiga sharar bacci,wuraren ƙarfe daya ya farka ganin lokacin tashin su sehrish daga school ya kusa yi,nan yayi sallama da mutanen gidan,jiki na rawa ya shiga motarshi tare da barin gidan,
  da gudu ya fisgi motar saboda ya ƙarasa gida da wuri,ba don komai ba sai don alkawarin da yayi ma sehrish na cewa in zaizo ɗaukarta daga school zai nuna mata wankan da zai ɗauka na shaddar shi,
   yana ƙarasowa cikin gidan bayan yayi parking din motarshi,ya wuce cikin main palour ɗin,a lokacin duk sun fita yin sallar azhar da ake cikin kira,bedroom dinshi ya shige tare da rage kayan da ke jikinshi ya faɗa cikin toilet,shaf shaf yayi wanka cikin minti goma sha biyar,ya fito daga cikin toilet din,jikinshi sanye da bathrobe,
    Gaban dressing mirror dinshi ya zauna,yadda kasan mace haka ya zauna yana gyara jikinshi,sai da yabi ko'ina na jikinshi ya shafe da mai,sannan ya shiga gyara sumar kanshi,bayan ya kammala ya miƙe tare da komawa wurin wardrobe,ya buɗe tare da ɗauko shaddar,a natse ya shiga zura kayan ajikinshi bayan yasa vest da short farare kal,rigar takai masa har guiwarshi,sai wandon,lokacin daya kammala sanya shaddar ajikinshi dawowa yayi tare da tsayawa gaban madubi yana kallon fuskarshi ta ciki ya Allah!shi kanshi sai da ya tsorata da irin kyan da yayi,kamar shiya zana kanshi don kyau,shaddar ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,sae faman salƙi take ajikinshi kamar wani sabon ango,kyakkyawan murmushin nan nashi ya saki tare da cewa"junaid kenan yakamata ka zama namiji mana,ka cire duk wata fargaba yau ka tunkari sehrish gaba da gaba ka bayyana mata irin son da kake mata batare da jin shakkar komai ba,'
   shiru ya danyi aranshi yana cewa"gaskiya ina jin fargaba fa,anya reesh zata amince da son da nake mata?in tace bata sona fa?tabbas zan iya rasa raina,amma zan jure yau dae na fahimtar da ita tsananin son da nike mata,'
  Ƙarasa maganar yayi tare da ɗauko hula mahadin kayan wadda take tsadaddar gaske sai daukan ido take itama ash colour ya aza saman kanshi,hmmmm abun ba'a magana madarar kyau ba kaman da sumar kanshi ta dan fito daga baya.
  Zura takalmanshi yayi masu kyau da tsadar gaske suma mahadin kayan,sannan ya koma gaban dressing mirror ɗin ya ɗauko turarenshi ya shiga feshe jikin shi dashi ko'ina saƙo da lungu,nan take ƙamshin ya gauraye ko'ina na ɗakin,
  Key ɗin motar shi ya dauko sannan cikin sauri ya fito daga ɗakin nashi ya sauko downstairs,babu kowa a falon duk sun tafi salla,

A hankali yake driving din motarshi fuskar nan dauke da annuri,sae da yafara tsayawa masallaci yayi sallah,sannan ya miƙi hanyar makarantarsu sehrish,shiga ciki yayi tare da yin parking ɗin motar sannan ya fito ya tsaya tare da jingina bayanshi a jikin motar,zuba ido yayi yana jiran fitowar sehrish amma babu ita babu alamarta,ga students sai fitowa sukeyi,wasu na hawa bus wasu kuma ana zuwa ɗaukarsu,
   Gajiya ya fara yi da tsayuwar,
"Wai ina reesh ta shige ne,ta barni tsaye ina ta faman jiranta,'rai aɗan 6ace yayi maganar,
   Juyawa yayi tare da kifa kanshi ajikin motar ya ɗan lumshe idanunshi,
   adai dai lokacin Jahad ta fito hannunta ruƙe da school bag ɗinta,tana neman hossana duk atunaninta zata same tane a wurin da suke jiran osman yazo ɗaukarsu amma babu ita,da alama ma Osman ɗin bai ƙaraso ba,
  guntun tsoki taja tare da juyawa zata koma ciki,karaf idonta suka sauka akan Junaid,cike da mamaki take kallonshi,tana ɗan leƙen fuskarshi daga inda take,

Bakomai ne ya faɗo mata aranta ba,face alƙawarin da tayi ma hosana nacewa zata nemo mata ya Omar,aranta tace"ya Omar yace ƙaninshi ne wannan,kodae naje na tambaye shi ina ya Omar yake,may be ya taimakamun wurin haɗa ni dashi,
  ƙarasawa wurin motar junaid tayi ta ɗan tsaya daga bayanshi,tare da yi mashi gyaran murya don ya juyo,
   jin shiru bai juyo ba yasa tayi mashi sallama"Assalamu Alaikum,"
  Nan ma bai juyo ba,hannu tasa ta ɗan ta6a bayanshi a hankali,aikuwa a firgice ya juyo,ita kanta jahad sae da ta ɗan tsorata taja da baya ganin yarda ya juyo kamar ya tsorata,
    Murmushi ta sakar mashi tare da cewa"am sorry,naga kamar ka razana,tun ɗazu nayi maka sallama baka ji ba,'
   harara junaid ya watsa mata,har sae da tasha jinin jikinta,rai a6ace yace"yanzu abunda kikayi mun kin kyauta!kinsan tun yaushe nike atsaye nan ina jiranki!"
   Gaba ɗaya jahad ta gama ruɗewa jin abunda Junaid ke cewa,
Cikin sauri tace"dama...am..inaso ne na tambayeka game da yayan.......'
  Kafin ta ƙarasa maganar tuni junaid ya gama hasala,ruƙo hannunta yayi tare da buɗe motar,yace mata wuce ki shiga,
   Murya na rawa jahad tace"bangane me kake nufi ba?
  A tsiwace yace"Ni ki wuce mu tafi,'
  duk yarda jahad taso ta fahimtar da junaid cewar ba ita bace wadda yake nema ba,amma yaƙi fahimta,shi duk atunanin shi sehrish ce,
  Tursasa mata yayi har sae da tashiga cikin motar,sannan ya shiga yaja motar da gudu ya fisgeta suka fuce daga cikin makarantar,

A natse yake driving lokacin daya hau saman shantalelen titin,zuba mashi ido jahad tayi tana kallonshi,ta wutsiyar idonshi yake kallonta,ganin yarda ta zuba mashi ido yasa shi ɗan juyowa tare da sakar mata wannan kyakkyawan murmushin nashi,
  mamaki ne ya kama jahad,gaba ɗaya abun ya gama ɗaure mata kai,aranta tace kodae yana da ta6in hankali ne?in ba haka ba, nida bamu ta6a haɗuwa dashi ba amma kuma ya nuna ya sanni har ya tursasa mun na shiga motar shi,yanzu ni bansan ya zanyi na fahimtar dashi ba,kada hosana ta fito tayi ta nemana acikin school,
   "Reesh banji kin yabi wankan nawa ba?ko banyi kyau bane,"yayi maganar a yayin da yake kokarin parking ɗin motar a gefen titi,sannan ya juyo yana kallonta,
  zuru jahad tayi tana kallonshi,hakan ba ƙaramin 6ata mashi rae yai ba,cikin shagwa6a yace"Wai menene haka reesh,duk kin bi kin wani sauya mun,saboda ke fa na ɗau wankan nan don nazo na nuna maki,amma kin zuba min ido kina kallona kamar yau kika fara gani na,'
  A tsorace take da shi,don tagama yarda cewa yana da ta6in hankali,cikin en ina tace"amm...ni fa...ba..' kasa ƙarasa maganar tayi gabanta na faɗuwa,ganin yarda junaid ya matso dab da ita,ya ƙureta gaba ɗaya ƙamshin turaren shi ya gama kashe mata jikinta,
  murmushi ya ɗan sakar mata tare da cewa"kallon ya isa haka reesh,let's talk about serious issue,akwai abunda na jima inason sanar dake,amma inajin fargabar amsar da zan samu a wurinki,'ya ƙarasa maganar yana kallon cikin kwayar idanun jahad amatsayin sehrish,
   a hankali jahad ke bin kyakkyawar fuskarshi da kallo,tun daga kan eye brows ɗinshi,dogon hancinshi da kuma red lips ɗinshi,komai nashi mai kyau ne kuma mai jan hankali,
   Anatse yaci gaba da magana,"reesh,nasan cewa baki ɗauke ni cikakken namiji ba kamar saura,saboda na cika wasa da shiririta da kuma shagwa6a,kuma bani da aikin yi sae zama acikin gida kamar mace, nasan ba kowace mace bace zata so ta aure ni a haka" ya ɗan dakata da maganar yana kallonta,wannan karon babu alamar wasa a fuskarshi,

  natsuwa jahad tayi tana sauraran shi,
   Hannayenshi yakai tare da ruƙo nata cikin nashi,nan take jahad taji gabanta ya faɗi,
  ɗagowa yayi awani irin yanayi yaci gaba da magana"duk wannan abun da nake reesh zan daina in baki so,idan har kika amince mu kayi aure,xan zama kamar yarda kikeso,nidae burina ki amsa mun cewa kina sona,kuma zaki aure ni,ni ban ta6a son wata ƴa mace ba in bake ba,na shaƙu dake sosai kuma ina da tabbacin cewa in mukayi aure zaki bani kyakkyawar kulawa,pls reesh tell me will u marry me"?
   Tamkar zai yi kuka haka yayi mganar yana jiran amsarta,
  Shiru jahad ta ɗanyi tana yanke shawara da zuciyarta,tunda dae bai da cikakken hankali bari na jaraba biye mashi kona samu mu rabu lafiya
Ƙarasa zancen zucin nata tayi tare da mayar da idanunta akan nashi tace"bana tunanin cewa akwai macen da zata samu namiji kamarka ta nuna bataso,kai na daban ne,kana da komai da mace zata buƙata a wurin namiji,kayi mun sosai kuma ka kwantamun araina,tayin soyayyar da kayimun na kar6a hannu bibbiyu,kuma na amince zan aure ka.....'
   Tsantsar mamaki ne ya kama junaid bai ta6a tunanin cewa rishi zata amince da soyayyarshi ba,cikin sauƙi haka batare da ta wahalar dashi ba,ajiyar zuciya ya shiga saukewa wani irin farin cikine ya lullu6e shi,mara misaltuwa a hankali ya shiga furta"Alhamdulillalh Allah nagode maka daka nuna min wannan ranar,dama sae da raina ya bani cewa reeshi ɗina bazata gujeni ba...."
  Fuskar jahad ɗauke da murmushi take kallonshi har lokacin hannunshi na ruƙe da nata,
   farin cikin da tagani a fuskarshi yasa taji aranta dama dagaske ita yake so,da ta bashi kyakkyawar kulawa,amma da alama akwai wadda yake so,tunda taji ya ambaci sunan reesh wannan ne yasa jikinta yin sanyi,

"Allah yasa ba mafarki nake ba,in ma mafarki nake kada ki tashe ni,'yayi maganar yana dariya tare da zame hannun shi daga nata,ya tallabo fuskarta da tafin hannayenshi,yana ƙare mata kallo,hakanan ya dinga jin kamar ta canza mashi,ƙura mata ido yayi kamar mai son gano wani abu,
  "Reesh kin canzamin sosae,sai nike ganin kamar bake ba,'
   Shiru jahad tayi tana cigaba da kallonshi,sakin fuskarta yayi tare da zura hannunshi cikin hijab ɗin jikinta,ae kuwa a firgice jahad ta ƙanƙame jikinta dake ta faman kerma cike da tsoran abunda zaiyi mata,
   Cikin lallausar suman kanta yakai hannunshi yana shafa gashin kanta yace"meyasa baki ɗaure gashin kanki ba?bai takura maki ahaka?
   atsorace jahad tace"ni na cire shi,yana acikin school bag ɗina,"
   Zame hannunshi yayi daga cikin hijab ɗin nata,
  "Zan ɗaure maki shi,ki ɗauko ribbom ɗin naki,"
  Kamar karta ɗauko mashi amma tunawa da cewar yana da ta6in hankali in ranshi ya 6aci zai iya kai mata bugu,hakan yasa ta janyo school bag ɗin tare da zuge zip ɗin,ta curo mashi ribbom din ta miƙa mashi sannan ta mayar da jakar abayanta,
  kar6a yayi tare da zura shi a cikin hannunshi,sannan ya ƙara matsawa kusa da ita sosai,cire hijabin jikinta yayi sannan ya janyota asaman chest ɗinshi,gaba ɗaya jahad ta gama rikicewa,ba ƙaramin yanayi junaid ya jefa ta ba,
  lamo tayi ajikinshi tana shaƙar daddaɗan ƙamshin turarenshi,
  Xuba ma yalwataccen gashin nata ido yayi yana kallonshi,kafin daga bisa ni ya sanya hannunshi tare da tattaro shi wuri guda,ya ɗaure mata shi da ribbom ɗin,
   muryarshi taji acikin kunnanta yana cewa"Reesh,ya akai naga launin gashin kanki ya canza?ba brown colour bane?yanzu kuma naga ya koma dark black,?kodai idona ne ke nuna min ba daedae ba'?shiru jahad tayi batace mashi komai ba,saboda bata da amsar da zata iya bashi,
  jin tayi shiru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login