Showing 147001 words to 150000 words out of 245004 words
Chapter 50 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
ɗaura alwala sannan suka fito tare dashi,
Don tsabar gatanci ma Omar ya goya shi abayan shi kamar wani ƙaramin yaro ahaka suka tafi dashi,duk wannan budurin da akasha Haroon na la6e yana sauraronsu babu wanda yasan dashi daga shi sai short ajikinshi,murmushin takaici yayi tare da cewa"kun makaro,aikin gama ya gama,dole ku rasa junaid,"
***************washe gari**********
Sehrish
A washe gari da wannan yanayin data kwanta dashi ta farka,daƙyar ta iya nufar toilet tayi wanka tare da fitowa ɗaure da towel,shaf shaf batare da 6ata lokaci ba ta kammala shirya kanta cikin school uniform ɗinta riga da wando bayan ta kammala shafe jikinta da body oil ɗinta,bin ko'ina tayi na jikinta tana feshe shi da turare gaba ɗaya hankalinta na akan Sgr,abunda ya faru jiya tsakaninsu,har yanzu ji take kamar mafarkine abun nan daya faru,yarda 6awon ayaba ya ja shi ya sul6e zai faɗi ta taro shi suka faɗa saman gadon,murmushi ta ɗanyi tare da cewa"wani ikon Allah,tunda nake kai mashi fruits ban ta6a kai mashi ayaba ba batare da na 6areta ba na yanka mashi ita ba,kamar yarda nake yanka sauran kayan marmarin amma jiya rabon ayi saina manta na kai mashi ita a haka,lallai 6awon ayaban nan ba ƙaramin aiki yaso yayi ba,da ace ya faɗi bansan wani irin buguwa zaiyi ba,"
tsayawa tayi da tunanin nata na wani lokaci,ɗago da idanunta tayi acikin mirror ɗin tare da sakin wani irin ƙayataccen murmushi tace"ɗaya daga cikin amfanin 6awon ayaba kenan wanda mutane basu son dashi ba,wato ƙulla allaƙar soyayya,"
Ƙarasa maganar tayi tare da fashewa da dariya,mayar da flower bomb ɗin tayi ta ajiye shi asaman mirror ɗin,sannan ta ƙarasa saman gadonta inda ta ajiye short hijab ɗinta tare da ɗaukar shi ta zura ajikinta,bata dauki school bag ɗinta ba saboda tana son zuwa kai mashi breakfast ɗinshi before ta wuce school,
Slippers ta zura a ƙafarta sannan ta buɗe ƙopar tare da ficewa izuwa cikin kitchen ɗin,tunkan ta ƙarasa ta hangi Hayaam acikin kitchen ɗin tana taya Azmee girki,nan take taji gabanta ya faɗi,ɗaurewa kawai tayi tare da sa kai cikin kitchen ɗin bakinta ɗauke da sallama,
Juyawa Azmee tayi daga tsayen da take agaban gass tana kallonta fuskarta ɗauke da murmushi,cikin sauri sehrish ta gaishe ta"ina kwana aunty azmee fatan an tashi lafiya,"
"Lafiya lou,Alhmdllh yau kinsha bacci ko leƙowa kitchen bakiyi ba,har nayi tunanin cewa ko baki jin daɗine,shiyasa ban tashe ki ba,"
Sunnar da kai sehrish tayi tare da cewa"Aunty azmee nikaina bansan ya akai nayi bacci dayawa har haka ba,naso ace nashigo kitchen ɗin da wuri don na tayaki aiki,"daƙyar sehrish ta kai ƙarshen maganar tata,ganin yarda hayaam ta zuba mata ido kamar zata haɗiyeta,tana a tsaye gaban choppping board tana yanka vegetables din da zasu yi amfani dashi,
"Yanzu junaid kike jira ya kai ki school ɗin kenan?naga har yanzu ma bai fito daga bedroom ɗin nashi ba,'
Kafin sehrish tace wani abu,Hayaam tayi karaf ta amshe da cewa"Junaid kuma?shine drivernta kenan?school ɗinsu babu bus ne"?ta jefa ma azmee tambaya,
Shiru sehrish tayi batace komai ba don batasan amsar da zata bata ba,
Azmee ce tace"ae da yake bata jima da fara zuwa school ɗinba,har yanzu bata saba da wasu abubuwan ba,amma nan bada jimawa ba,zata fara hawa bus ɗinne,"
Yatsina fuska hayaam tayi tare da mayar da idonta akan kayan lambun da take yankawa,
ganin yarda Sehrish tasha jinin jikinta yasa Azmee cewa"ba zakiyi breakfast bane?
cikin sanyin murya tace"A'a Aunty azmee bana jin yunwa,in naje school zanci acan,amma inaso kafin na tafi in kaima Babban yaya nashi breakfast ɗin in akwai abunda kuka kammala.....'
Wani irin kallo hayaam ta watsa mata wanda hakan yasa ta ƙarasa maganar adabarbarce,
"Babu buƙatar ki kaimashi breakfast ɗinshi,ke da zaki school salon kawai shiririta don kiyi late ko?to ki tafi kawai ni zan kai mashi breakfast ɗin nashi," cike da isa hayaam ke magana batare da jin wani ɗar azuciyarta ba,
Ba sehrish ba hatta azmee tayi mamakin yarda hayaam ke magana a gadarance,duka duka jiyan nan tazo gidan amma zaƙewarta harta fara yawa,
jiki asanyaye sehrish tace"shikenan,Aunty azmee ni zan wuce,"
azmee bata ji daɗin abunda ya faru ba saboda tasan yarda sehrish ke kwallafa rai akan son kai ma Sgr abincin shi,
gyaɗa kai kawai tayi tare da cewa"Adawo lafiya,"
juyawa sehrish tayi kamar wadda aka zare ma laka,
Shu'umin murmushi hayaam ta saki tare da cewa"kaɗan kika fara gani,gayyar soɗi kawai," ƙasa ƙasa tayi maganar don kada azmee taji,
Bayan sehrish ta fito daga kitchen ɗin tsayawa tayi a main palour ɗin tana jiran ganin ko junaid zai fito,ita kanta tayi mamakin rashin fitowarshi da wuri saboda har zumuɗi yake yi nasan kaita school,babbar damuwarta shine batasan inda zata samu school bus ɗinsu ba saboda wurin ƙarfe 8:00am take kammala daukar student a areas ɗinsu,yanzu kuma har da rabi ta buga already bus ɗin ta kammala kwasar ɗaliban,bazata same ta ba,
jin shiru bai fito ba yasa ta juya tare da komawa cikin bedroom ɗinta,kusan minti 5 ta fito hannunta ɗauke da school bag ɗinta,ta kuma sanya sandals ɗinta,
tafiya take tana waiwayon twin stairs ɗin wai ko zata ganshi ya fito amma babu alamar shi,aranta tace kodai yana a bedroom ɗin Abbansu ne?amma kuma ae da asuba yake komawa ɗakin shi don ya shirya in zai kaini school,"
tana cikin wannan tunanin sai ga junaid yana saukowa down stairs fuskar nan tashi ɗauke da ƙayataccen murmushin nan,wankan pakistani ya ɗauka ajikinshi farare sai ya fito wani handsome dashi yayi fresh ga wani haske daya ƙara,
washe baki sehrish ta shiga yi kamar taje ta rungumo shi saboda tsabar farin ciki,dama abunda take zullumi kenan wazai kaita school in ba junaid,gashi ko sisi bata dasu balle tace zata tsaida taxi takaita,
Hannunshi na ruke da key ɗin motar shi,yana ƙarasowa batare da 6ata lokaci ba ya ruƙo hannunta acikin nashi suka fuce daga cikin gidan,
Ran hayaam ba ƙaramin 6aci yayi ba saboda ta hangi junaid tare da wannan yarinyar da ta tsone mata ido,ta wani 6angaren kuma tayi mamakin girman junaid ba ƙaramin kyau yayi mata ba,
Bayan sun shiga motar a hankali ya tashi motar tare da fito da ita yajata da gudun gaske saboda time dayaga yana ƙurewa,
Satar kallon gefen fuskarshi tayi tare da cewa"ko kasan cewa kyau kake ƙarawa"?
Murmushi junaid yayi hankalinshi na akan driving ɗin da yake yi yace"dame dame kenan na ƙara"?
Lissafa mashi tashiga yi"ka ƙara haske sosai,ka ƙara tsayi ka ƙara komai dae hada ak47 ma duk ka ƙara......' bata ƙarasa maganarba saboda jin yarda junaid yaja burkin motar,kallonta yayi a ruɗe yace"rishi kinsan menene ak47 kuwa"?
murmushi sehrish tayi tare da cewa"a'a nima bansani ba,naji kwanakin baya da jimawa,su fawan na jan ka faɗa suna ambaton sunanta shine nace nima bari naja ka faɗa da ita,"
Ajiyar zuciya junaid ya sauke jin abunda tace,dama sai da ranshi ya bashi cewa batasan menene ainihin ma'anar abunda suke nufi ba shiyasa ta furta mashi kalmar,
Tambayarshi ta shiga yi me take nufi ne,aikuwa nan yashiga tiƙar dariya batare da ya bata amsar ba ya tashi motar suka nufi hanyar school ɗin,
**************
"Hossana wai bazaki fito mu tafi ba!?ya osman fa yana waje yana jiran mu,"jahad ce ke ta faman tunatar da hossana dake zaune asaman dining table wanda ke shake da kayan breakfast ɗinsu,tun dazu jahad tabarta tana ta faman cusa abinci a cikinta sam bata ƙoshi,ta haɗa wancan ta kwa6a wancan ta tura abaki,
ran jahad ba ƙaramin 6aci yayi ba lokacin data fito ta samu hossana ko motsi batayi ba gashi ko uniform bata sanya ajikinta ba,iya kayan baccin jiya ne ajikinta,ita kuwa har ta jima ta kimtsa kanta acikin unform ɗinta hatta hijabi ta zura a jikinta,hannunta na ruƙe da shool bag ɗinta,
a tsiwace tace"Hossana!ki ajiye wannan abincin ki tashi mu tafi school!"
Batare da ta ɗago ta kalleta ba tace"dan Allah jahad ki bari na ƙarasa shanye wannan madarar dana haɗa da zuma,"
Tsoki jahad taja tare da wuce wa tana cewa"bazan bari kijamin ba,ni kinga tafiyata,"
"Dan Allah ki jira ni ukuty,kada ku tafi ku barni,"ta ƙarasa maganar tare da tashi cikin sauri ta wuce cikin bedroom ɗinsu don ta sanya uniform ɗinta,"
Fitowa jahad tayi a farfajiyar gidan ta samu Motar Osman yana jiransu,cikin sauri ta ƙarasa tare da buɗe back seat na motar tashiga daga ciki tana gaishe shi "
Amsa mata yayi sannan yace"ina ɗayar take ne"?
"Nabarta aciki,idan zata 6ata mana lokaci mu tafi kawai,"acewar jahad,
Suna cikin maganar saiga hossana tafito da saurin gaske harta kammala shiryawa cikin nata uniform ɗin,hannunta na ruƙe da school bag ɗinta,
Tana ƙarasowa ta wuce front seat ta buɗe tare da shigewa ciki ta zauna,
Murmushi osman ya ɗan saki tare da kallonta yace"ta gaban mota,yau ba gaisuwa ne,"
ɗaure fuska tayi tare da cewa"banason magana ni,ko ƙoshi banyi ba an taso ni,makaranta makaranta kamar in nayi aljanna za'a sani,"ta ƙarasa maganar tare da jan guntun tsoki,
dariya suka sa gaba dayansu hakan ya ƙara tunzurata,
Jan motar Osman yayi tare da fucewa dasu daga cikin gate ɗin gidan,
Abu kamar wasa suna cacar baki da jahad,sai ga hossana ta dawo back seat wurinta,harara jahad ta watsa mata tare da cewa"shiyasa nace ke zararriya ce in ba haka ba,taya zaki dawo daga gaban mota zuwa inda nake salon jan faɗa ko,"
Jin wannan maganar yasa hossana ta cakumi wuyan hijabin jahad,nan fa suka shiga dambatawa acikin motar,duk yarda osman yaso ya dakatar dasu abun ya faskara,sun cika motar da tsiwa sai faman kokoyi sukeyi,
A haka ya samu ya ƙarasa dasu cikin makarantar,tsayar da motar yayi tare da fitowa ya bude masu ƙopa,kowacce daga cikinsu sai faman huci takeyi,rai a6ace hossana ta sungumi school bag ɗinta tare da wuce wa fuuuu tabarsu a motar,
cikin sanyin murya osman yace"ke ma meyasa kike biye mata?ina ganinki mai hankali bai kamata ace kina biye ma hossana ba,itafa yanzu tamkar kanwarki take saboda ta6in hankalin da ke gare ta,"
tuni idon jahad sun cicciko da kwalla saboda tsananin 6acin ran yarda Hossana ta cakumi hijabin jikinta duk tayi uban squeezing kamar batayi guga ba,jiki asanyaye takai hannu tare da ɗaukar school bag ɗinta sannan tasa ƙafa ta fito daga cikin motar tafiya ta soma yi tana matse kwallar idonta,
Sam osman baiji daɗin hakan ba,dama kusan kullum in zai kawosu school sai sunyi faɗa acikin motar kuma duk Hossana ce sila,sam batasan zaman lafiya kamar ƴar dambe haka take,
Shiga cikin motar yayi tare da janta yabar cikin makarantar,
"Madam kin yada ribbom ɗinki,"wata irin sanyayyiyar murya ce ta ratsa kunnanta,dakatawa jahad tayi da tafiyar sannan cikin sauri ta juyo don taga wanene,
Waro ido waje tayi tana kallonshi saboda tsabar mamaki abun kamar a mafarki take ganin shi,
zuƙunnawa junaid yayi tare da kai hannu ya ɗauki ribbom ɗin jahad dake yashe ƙasa,ɗagowa dashi yayi a hannunshi fuskar nan tashi ɗauke davwannan ƙayataccen murmushin nashi ya miƙa mata shi tare da cewa"basai kin gode mun ba,nayi ne don Allah,"har lokacin bai ɗago da idonshi ba ya kalleta,la66an jahad har kerma sukeyi wurin son ta buɗe baki tayi mashi magana amma sam tagaza,gaba daya ta sandare a tsaye tana kallon kyakkyawar fuskar junaid,
Ganin taƙi yin motsi bare ta kar6i ribbom ɗin nata,hakan yasa yakai hannunshi tare da ruƙo yatsun hannun jahad,bude tafin hannun yayi tare da sanya mata ribbom ɗin aciki,
Sannan cikin sauri ya juya tare da tunkarar motar shi ya buɗe ya shige ciki,sannan yayi mata key tare da janta ya karya kwana tare da fucewa daga babban gate din makarantar,
Sai lokacin jahad ta sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya,tunani tashiga yi anya ba gizau yayi mata ba kuwa?taya zata ga mutumin data zana a zahiri kuma a kusa da ita yanayi mata magana"?gaba daya tayi confusing ɗin kanta,daƙyar ta iya jan ƙafarta tare da nufar hanyar class ɗinsu,
***********************
bayan sun kammala aiki acikin kitchen ɗin Hayaam ce ta shiga kai abincin tana jerawa asaman d table,bayan ta kammala jera musu ta koma cikin ɗakinta,bata jima da shiga ba sai ga kiran sofwan ya shigo acikin wayarta dake ajiye saman pillow ɗinta cikin sauri takai hannu tare da ɗaukar wayar takara a kunnanta ko sallama bata yi mashi ba kuma bata jira yayi mata ba tace"sofwan ina trolley ɗin kayana yake?jiya nabarshi acikin boot ɗin motarka,inaso ka kawomin shi yau ɗin nan ina jiranka,"tana faɗin hakan tayi rejecting kiran tare da mayar da wayar ta ajiyeta asaman pillown,
murmushi tashiga saki tunawa da abun harinta Sgr,cike da zumuɗi tashiga toilet donta gyara jikinta saboda takai mashi breakfast ɗinshi,
Sai da ta fito daga cikin toilet ɗin sannan ta tuna cewa babu fa kayan da zatayi gayu dasu hatta kayan kwalliyarta duk suna acikin trolley ɗin nan data baro a boot ɗin motar Sofwan,tsoki taja tunawa da wannan,tunani tashiga yi yanzu ya zatayi taje wurin shi,gashi wannan short gown ɗince ajikinta,murmushi ta saki tunawa da hijabin data zo dashi,don haka cikin sauri ta buɗe wardrobe ɗin dake a ɗakin don anan ta ajiyeta jiya,
ɗaukowa tayi tare da zura hijabin ajikinta sannan ta kama hanya ta fito daga cikin ɗakin tana tafiya anatse kamar wata kamila,
lokacin data fito daga cikin corridor ɗin anan tasamu mutanen gidan sun hallara a saman dining chairs sunayin breakfast,
Jin takun tafiyarta ne yasa suka ɗago gaba ɗayansu suna kallonta,hakan yasa hayaam duk tabi ta dabarbace tashiga ƴan kame kame,
"Azmee wacece wannan ko bakuwa mu kayi ne"? Abbansu ne yayi wannan tambayar saboda bai gane fuskarta ba,
Fawan yace"kamar ƙanwar Amani naga suna ɗan yanayi ,"
Kowa da hasashen shi akanta,amma basu ganeta ba kai tsaye,
Murmushi azmee tayi tare da cewa"wannan Hayaam ke nan,kanwar su Amani,jiya tazo gidan nan alokacin duk bakunan kun fita,"
fuska a sake Abbansu yace"Masha Allah,shine tayi mana zuwan bazata batare da ta sanar damu ba"?jin yarda abbansu yayi maganar fuskarshi ɗauke da farin ciki hakan yasa hayaam ta ƙarasa wurinsu tana faman sakin murmushi,gaishe da abbansu ta shiga yi,
ɗan ɗaure fuska yayi cike da zolaya yace"gaskiya fushi muke dake,saboda bakyason zumunci,gashi nan har mun fara mantawa da kamannin fuskarki,meyasa baki leƙo mu"?
Sunnar dakai tashiga yi tana cewa"ayimun afuwa Abba,abubuwane sunyi mun yawa shiyasa bansamu lokaci nazo ba,Amman kuna araina shiyasa nazo wannan karon don na goge laifina,"
Kallon juna Ayaan da jahan su kayi bakinsu kumshe da dariya,dama su ba'ayi masu gwaninta,su dai su jabeer basu ce komai ba,binta kawai sukeyi da kallo,kanal yousouf kuwa hankalinshi na akan abincin da yake ci,amma yana sauraronsu,
Murmushi Abba yayi tare da cewa"koke fa,yanzu naji magana,ina fata dae azmee tayi maki tarba mai kyau ko"?
ɗaga kai tayi alamar eh tace"Aunty azmee ta karramani sosai,"ta ƙarasa maganar tare da kallon fawan tace"Ya jikin naka fawan?naji abunda ya faru dakai fawan nashiga damuwa sosai lokacin naso nazo na dubaka,amma bansamu halin zuwa ba,shiyasa nayi wannan zuwan na musamman saboda kai,"
baki asake fawan ke kallonta irin kallon rainin wayon nan,can kuma sai ya ɗan waske tare da sakin murmushi yace"nagode sosai da wannan kulawar taki,kuma jiki Alhamdulillah naji sauƙi sosai,"
Jahan yace"ae fawan ya riga daya warke,da kinsani kinyi zaman ki agida,ko waya kin bugo kiyi mashi ya jiki,basai kinsha wahalar takowa kinzo ba,"
"Wannan haka yake Jahan,"acewar Ayaan,
Nan da nan jikin hayaam yayi sanyi tashiga zazzare ido tana mazurai don bataji daɗin abunda suka ce ba,
Abbansu kuwa ba ƙaramin daɗi yaji ba,jin yarda ta nuna damuwarta akan jinin shi,kuma har ta tako tazo donta duba shi,
Yace"Gaskiya naji daɗin jin maganar nan taki sosai,fawan yaji sauƙi sosai,ga alama nan ma kin gani,"yayi maganar yana nuna Fawan dake tura wainar kwai abakinshi,
Murmushi suka saki atare ita da Azmee,
"Amma dae ina fata zaki zauna mana ko?don banason wannan zuwan naku shaf shaf azo atafi kamar ana korar mutum,"
ƴar dariya hayaam tayi tare da cewa"a'a abba insha Allah wannan karon har sai kun gaji dani,"
Jin wannan maganar ta hayaam,yasa su twins sakin cokulan dake a hannunsu atare cikin plate suka bada wani sauti wanda yaja hankalin kowa kansu,kumshe dariya su irfan su kayi saboda sun gane dalilin dayasa su twins suka saki cokulan hannunsu,
Tuni hayaam taji ta muzanta duk tabi ta turniƙe fuska tana ɗan tsuke baki,
Sai lokacin kanal yousouf yace"muna maki barka da zuwa baƙuwarmu,koda yake ke fa ba baƙuwa bace ƴar gida ce,"ya ƙarasa maganar da murmushi a fuskarshi,
Ba ƙaramin sanyi hayaam taji ba jin abunda yousouf yace mata,nan tashiga sakin murmushi tana cewa"ngde sosai yaya yousouf da tarbar dana samu a wurinka,"
ta jima tana gaisawa dasu kafin daga bisani ta wuce kitchen don ta shiryama sgr breakfast ɗinshi,
Bayan tafiyarta marshal omar ya sauko downstairs ɗin ya shirya tsaf acikin jean da t -shirt,ƙarasawa yayi wurinsu tare da samun wuri ya zauna shima,gaishe da abbansu yayi, da fara'a a fuskarshi ya amsa mashi,sannan su kuma su Yousouf suka shiga gaishe dashi,amsa masu ya shiga yi kafin daga bisani yace"Ya muka ji da abunda ya faru da suba"?
murmushi su kayi gaba ɗayansu kanal yousouf yace"gaskiya ba ƙaramin tashin hankali muka shiga ba,especially Abbanmu don nasan ƙiris ya rage zuciyarshi ta buga,saboda babynshi,"
Dariya suka kuma yi,girgiza kai Abbansu yayi tare da cewa"oh nazama abun tsokana ko?ae bani kaɗae naji jiki ba,kowa acikin ku sai da hankalinshi ya tashi akan halin da junaid ya shiga,'
Fawan yace"wai ina ma junaid ɗin yake ne"? Ya tambaya yana kallon abban nasu,
gaban azmee ne ya faɗi rass saboda tasan cewa duk basu son cewa shi ke kai sehrish school ba,
Kafin tace wani abu muryar abbansu ta katseta da cewa"tunda asuba yabar bedroom ɗina,ina tunanin ko yaje kai sister ɗinshi school ne,don naji ran nan yana cewa zai kaita school ne a motarshi,
Tunkan ya ƙarasa maganar tashi fawan yace"What!!junaid shike kaita school?for what reason?basu da school bus ne"?ya tambaya yana kallon abban nasu,gaba daya abun ya ɗaure masu kai,
Kanal yousouf ne yace"its enough pls,ku bari muyi breakfast cikin kwanciyar hankali,inyaso daga baya munyi magana akai,"
Jinjina kai kawai sukayi tare da mayar da hankalinsu akan abincin da suke ci,shi dai Marshal Omar baice komai ba hankalinshi na akan farfesun da azmee