Showing 159001 words to 162000 words out of 245004 words
Chapter 54 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
karsu shigo su same su a wannan yanayin ita da sgr,
Hayaniyar da suke yi ce,ta fara disturbing ɗin baccin nashi,hakan yasa ya fara motsi alamar zai farka,waro ido waje sehrish tayi cike da fargaba jin alamar zai farka,
Hannunshi ya janye daga ruƙon da yayi ma sehrish,hakan ne ya bata damar kufcewa daga jikinshi,kamar walƙiya haka ta mirgina tare da faɗawa ƙasan gadon,sam bata ji zafin buguwar da tayi ba,tana faɗowar nan ta yunkura tare da miƙewa tayi wuff ta faɗa bayan labulan ɗakin shi,
Shigarta ke da wuya,Abba da marshal suka shigo cikin ɗakin nashi atare bakunansu ɗauke da sallama,
A hankali sgr ya soma buɗe idanunshi dake cike da bacci ga wata irin kasala data mamaye shi don baccin bai ishe saba,daƙyar ya iya sa hannunshi tare da dafa mattress ɗin ya tashi daga zaune tare da jingina back ɗinsa asaman pillow yana kallon Abban nasu tare da Omar sai faman lumshe ido yake yi,
Zama Abban yayi daga gefen gadon nashi yana kallon fuskar kyakkywan yaron nashi yace"Rafayet bacci kuma a irin wannan lokacin?ko baka ga time bane?
Sai lokacin sgr yakai idonshi akan diamond clock ɗin dake manne a bangon ɗakinshi ƙarfe 6:30 na yamma,
lumshe idonshi yayi kafin ya waresu akan Abban nasu yace"Abba bansan time ɗin da baccin ya ɗauke ni ba"
jinjina kai abban nasu yayi
kafin yayi yunƙurin cewa wani abu karaf idonshi suka sauka akan jan bakin sehrish dake zane asaman breast ɗinshi,
waro ido waje abban nasu yayi tare da cewa"Kai me nake gani haka kodai idona ne"?yarda yayi maganar a ruɗe yasa marshal Omar ɗan matsowa daga tsayen da yake ya russina yana ƙare ma Ƙirjinshi kallo,cike da mamaki Omar yace"ba shakka Abba,ba idonka bane wannan alamar sumbata ce,ga zanen la66an mace nan raɗau asaman fatar kirjinshi,
Gaba daya sun gama confusing ɗin Sgr,sam bai gane inda zancen nasu ya dosa ba,"
Hankali atashe Abbansu yace"Rafayet tell me the truth!wa kayi feeding haka har ta goga maka jan baki asaman breast dinka!!!"
Saboda tsabar kiɗima tuni jikin sehrish ya soma tsastsafo da wata irin zufa,duk da sanyin ac dake gauraye da ko'ina,
Ganin yarda sgr ya dabarbarce kamar bai gane kan me suke magana ba,hakan yasa omar ƙarasawa gaban dressing mirror ɗinshi,yasa hannu tare da ɗauko ƙaramin madubin dake ajiye asaman shi,
Ƙarasowa yayi wurinshi tare da saita mashi madubin yarda zai gani da kyau,
Ware manyan idanunshi yayi yana kallon zanen la66an dake asaman chest ɗinshi cike da tsananin mamakin a ina ya same shi.......
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.*💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖
Ansamu long page🥱
________________________Zuba mashi ido su kayi suna jiran amsa,Omar yace"pls ka faɗa mana gaskiya kawai,wacece wani abu ya shiga tsakaninka da ita har akasha wannan Love haka?kaga dai daga ni sai Abba babu wanda zaiji abun da ya faru,"wani irin kallo sgr ya wurga yana mashi ƴar harara yace"Omar bana so, ka fara ko"?
Murmushi Abban nasu yayi kafin yace"abunda Omar ya faɗa gaskiya ne,Son bai kamata ka 6oye mana komai ba tunda Allah dai yasa yau asirikinka ya tonu munga komai,ashe kana kula mata har romance kake dasu asaman gado ko?faɗamun ƴarwa ka kwamushe acikin ɗakinka har akai abun arziƙin nan bansani ba,"cike da zolaya Abban nasu ke magana,
ɗaure fuska Sgr yayi tare da haɗe girarsa wuri guda ya tsuke small lips ɗinshi yana kallonsu,yarda suka tasa shi gaba suna tuhumarshi kamar wani ƙaramin yaro ba ƙaramin hasala shi yayi ba,gashi sam ya rasa amsar da zai basu tunda bai isa ya ƙaryata abunda suka gani ba asaman ƙirjinshi,don shi kanshi a ruɗe yake da lamarin abun ya ɗaure mashi kai,taya aka samu jan bakin mace raɗau haka asaman ƙirjinshi!?bai gama zancen zucin nashi ba muryar Omar ta katse mashi tunani,
"Abba zargi fa ya tabbata,kalli ka gani,"Omar ne yayi maganar yayin da yake ruƙo mayafin sehrish dake a ƙasan laps ɗin Sgr ya danne shi,
dafe kirji abban nasu yayi cike da razana yace"ƙalu innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Rafayet!wannan fa?ya akai yazo wurinka"?ya tambaya hankali tashe yana kallonshi,
Runtse ido sehrish tayi daga 6oyen da take bayan labulen ɗakin,hada ƴan matan hawayenta saboda tsoran hukuncin da zata kar6a,
Cikin sauri sgr ya aza eyes ɗinshi akan mayafin da Omar ya ruƙo a hannunshi just speechless,amace bakin shi ya mutu yama rasa bakin magana abun ya zarce tunaninshi,
Omar ne yace"Abba tunda kaga yayi tsit ya gaza magana,to ya aikata ɗinne kasan mara gaskiya,ni fatan da nakeyi ma Allah yasa iya mayafi ya cire mata bai........'kasa ƙarasa maganar yayi saboda saukar pillow daya ji a saman fuskarshi,hannu yakai zai ƙara rarumar wani pillow abban nasu ya dakatar dashi da cewa"Wannan fa alamar rashin gaskiya ce,tun ɗazu kaƙi buɗe baki ka ce uffan,sai faman ƴan kame kame kakeyi mana,kaji tsoran Allah ka faɗa mana gaskiya,Rafayet yin hakan kuskure ne bai kamata don kana ra'ayin mace ka runƙa kawota har bedroom ɗinka ba asaman gadonka don ka rage zafi da ita ba,in kaga yarinya kanaso Ni zakayi ma magana sai aje masallaci ashafa fatiha kaga shikenan sai a kawo maka ita ɗakinka babu mai jin kanku,taka ce halak malak.....'
Zare blue eyes ɗinshi yayi yana kallon Abban nashi,rai a6ace ya ciji la66ansa tare da ɗago pillown hannunshi ya ɗaga sama zai jefa ma Abban nasu a saman fuskarshi,sai kuma ya saki filon a saman katifar,
Ganin ya dakata yasa Abban nasu cewa"ae fa kai yanzu komai ma zaka iya,saurayin da zai iya kawo mace ɗakinshi har saman gadonshi acikin gidan ubansa meke bazai iya ba Omar? Ya ƙarasa maganar yana kallon Omar dake ƙumshe da dariya yace"of course Abba,ina goyon bayan maganar ka,yanzu sai dai mu bishi da addu'a don na lura yarinyar ba ƙaramin zautar dashi tayi ba tunda gashi har ya gaza buɗe bakinshi yayi mana magana,rashin gaskiya dai baiyi ba,"
gaba ɗaya sun gama hasala Sgr,yama rasa amsar da zai basu su dukansu,a ƙarshe ma daya rasa abunyi kawai sai ya fashe da dariya unexpected,tsananin mamaki ne ya kamasu ganin Sgr yana 6a66aka dariya yau shi da kanshi,yaushe rabon da suga sgr yayi dariya irin haka,white teeth ɗinsa sun fito rairasss,da wuya kaga yana dariya sai dai wannan murmushin nashi na gefen fuska shima kuma in kaga yayi wannan murmushin tofa zai bada horo ne,don ya iya murmushin mugunta,
Hannu sehrish tasa a hankali ta ɗan yaye labulen tana leƙensu,ba ƙaramin bugun zuciya taji ba,kasa janye idonta tayi daga kallon kyakkyawar fuskar sgr da yake ta faman dariya kamar zautacce,gaba ɗaya dimples ɗin fuskarshi sun lotsa sosai abun ba'a magana sai wanda ya gani,suman tsaye sehrish tayi amace ta mace wurin kallon fuskarshi,aranta tana maimaita kalmar nan"tabarakallahu ahsanun khaliqin,"
Har wani duƙar da kanshi yake yi ƙasa yana dariyar hakan yasa sumar kanshi ta ɗan yarfo ta gaban fuskarshi,
Atare Omar da Abbansu suka haɗa baki wurin cewa"ikon Allah,abun mamaki abun al'ajabi,"
Tsagaitawa yayi da dariyar lokaci guda ya ɗaure fuskarshi tamkar dariya bata ta6a wanzuwa a fuskarshi ba,takaici ne dama ya ishe shi shiyasa ya fashe da dariyar,
Cikin sanyin murya yace"joking aside pls,abba nikaina bansan ya akai nasamu zanen lips ɗin nan asaman chest ɗina ba,sannan bansan ya akai mayafin nan yazo bedroom ɗina ba,na rasa ta yarda zansa kuyi understanding ɗina,gaba ɗaya kunyi confusing ɗina,kun tsareni da tambaya kamar wasu lauyoyi,that's why nayi shiru bance komai ba,"ya ƙarasa maganar a kasalance,
Murmushi Abban su ya saki yana kallon face ɗinshi,bakomai ya faɗo mashi araiba face Mommynsu,komai na fuskarshi irin na mahaifiyarshi ne,yafi kama da ita amma akwai wasu abubuwan daya ɗauko na Abbansu,
"Zan shiga toilet,"ya faɗi tare da saukowa daga saman gadon ya kama hanyar shiga toilet ɗin,
Bin bayanshi su kayi da kallo har ya shige cikin toilet ɗin,
Sannan Suka janye idanunsu,cikin sauri Omar ya samu wuri tare da zaunawa yana fuskantar abbansu ya ruƙo hannunshi tare da cewa"Abba,dan Allah ka aurar damu tare, nida Rafayet,kayi mun wannan alfarmar"
Murmushi Abbansu ya ɗanyi kafin yace"Omar bangane me kake nufi ba,har yanzu ɗan uwanka bai janye ra'ayin shi akan mace ba,ni kuma banson na takura mashi,duk da banda burin daya wuce wannan nima,inaso naga auran kowanne daga cikinku,musamman auran shi saboda ina tunanin cewa in soyayya ta shiga zuciyarshi zai rage wannan zafin kan nashi,zai sassauto ya zama tamkar kowa,idan har rafayet baiyi aure ba ya tsaya akan bakanshi,tabbas za'ayi asarar namiji har namiji Omar,bansan ya zanyi dashi ba,"yanayin da abban nasu yayi maganar zai tabbatar maka da cewa abun ba ƙaramin ciwo yake masa ba,
"Abba kadaina cewa bakasan yarda zaka yi dashi ba,shifa ɗanka ne halak malak Allah ya mallaka maka,kuma kana da iko Akanshi,idan yau kaso Abba gaba ɗayanmu zaka iya yi mana aure batare da son ranmu ba ko batare da saninmu ba kuma dole muyi maka biyayya,"
zuba mashi ido Abban yayi yana sauraran bayanin shi,
Ƙasa ƙasa da murya Omar yayi gudun kada Sgr yafito daga cikin toilet ɗin yaji abunda suke tattaunawa,
Yasa shi yin hakan sannan yaci gaba da cewa"Abba,namiji irin rafayet,aure akeyi masu batare da saninsu ba,sai dai kawai suji an ɗaura auran... "
Katse shi abban nasu yayi da cewa"baka tunanin cewa zai iya sakin matar anan take,kasan shifa ba'ayi mashi dole,"?
Murmushi Omar yayi tare da cewa"Abba ka fahimta mana,kaifa kake iko dashi,ka sama mashi mace ta gari wadda kasan cewa bazaiyi dana sanin zama da ita ba,ko kuma ni kaban za6i zan sama mashi macen data dace da rayuwarshi,ka aura mashi ita batare da sanin shi ba,sai bayan an ɗaura auran ka ware rana ɗaya ka sanar dashi cewa Umarnine ka bashi amatsayinka na mahaifinshi,in ya kuskure kuma yasan sauran,"
dariya sosai Abbansu yayi yana sauraron omar dakyar ya tsagaita da dariyar yace"Omar ka iya zolaya Allah kamar mahaifiyarku,yanzu rafayet kakeso nayima auren dole?so kake ya tashi bomb acikin gidan nan"?
"Abba baka fahimce ni ba,tunda muka taso tare da ɗan uwana,komai namu iri ɗaya muke yinshi tamkar twins haka muke,duk abunda nayi rafayet sai yayi shi,haka shima duk abunda yayi nima saina yi shi,yanzu abba aure ne zai banbanta ni da ɗan uwana"?
In serious matter Omar ke magana,wannan yasa Abban nasu ya gane cewa ba zolaya bace yake mashi,har cikin ranshi yake maganar kuma ba ƙaramin jin abun yake ba acikin zuciyarshi,bai gama zancen zucin nashi ba omar yaci gaba da cewa"Abba tuntuni ban ta6a sanar dakai ba,amma yau zan sanar dakai komai,najima inason na cika maka burinka na ganin cewa munyi aure, ba don komai ba sai don saboda farin cikinka,bakomai ne yasa nayi jinkirin yin aure ba face Rafayet!inason aure bawai banaso ba,rafayet shine dalilin dayasa naƙi yin aure,saboda ina ganin cewa kamar banyi mashi adalci ba,inna riga shi yin aure,saboda mun saba komai atare duk wani cigaban da zamu samu atare muke samun shi abba,taya zanso na samu wannan babban cigaban batare da ɗan uwana ba"? Ya ƙarasa maganar muryarshi asanyaye yana kallon Abban nasu,
Gaba ɗaya Omar ya gama kashe ma Abban nasu jiki,ba ƙaramin tausaya mashi yayi ba,lalle ba ƙaramar shaƙuwa bace a tsakanin shi da ɗan uwanshi ba,tun da har zai iya hana kanshi wani jin daɗi na rayuwarshi saboda ganin cewa tamkar baiyi mashi adalci bane,
"Abba,na jima ina jiran ganin cewa ɗan uwana ya fara soyayya koya fara maganar aure,amma har yanzu ba wani sauyi abun ba ƙaramin ta6amin zuciyata yake ba,bana faɗi ne kawai saboda nasan faɗin bashi da amfani zan 6ata bakina ne kawae,sau da yawa ina janshi da fira akan mace don na bugi cikinshi naji koya fara ra'ayin yin aure amma kullum babu wani cigaba game da haka,Abba rafayet shine yasa Omar ɗinka ƙin yin soyayya tun da jimawa kuma shine ya hana nayi aure,wanda bani da burin daya wuce wannan arayuwata....,.......'
Kasa ƙarasa maganar yayi saboda siririn hawayen daya zubo mashi a idonshi na hannun dama,
Cikin sauri abban nasu ya sanya hannunshi tare da yin saurin goge masu shi yace"Omar ban ta6a tunanin haka ba,meyasa tuntuni baka sanar dani wannan maganar ba?meyasa nagaza fahimtarku amatsayina na mahaifinku?ashe shaƙuwar dake tsakaninku har takai haka?nagode ma Allah sosai da kuka kasance masu son junanku,ina matuƙar alfahari daku ƴa'ƴana," magana yakeyi yayin da idanunshi suke cike tab da kwalla,
Sehrish kuwa dake la6e bayan labule sai faman shessheƙar kuka takeyi ta rufe bakinta da tafukan dukkan hannuwanta,tsananin tausayinsu ne ya kamata,tunda take a rayuwarta bata ta6a ganin ƴan uwa masu matuƙar ƙaunar junansu ba irin ahalin salahuddeen hussein,akwai soyayya da shaƙuwa tsakaninsu,zumuncin dake tsakaninsu mai ƙarfi ne sosai,da ace kowane ahali zasu kasance haka da ba ƙaramin cigaba za'asamu ba,amma yanzu zamanin da muke ciki,babu wannan soyayyar atsakanin shaƙiƙai ma,sai kaga na waje ma wani can yafika kusanci da ɗan uwanka shaƙiƙinka,idan kuwa akazo kan shiga matsala ko damuwa tofa zaka ga mutum indai bashi ta shafa ba,babu ruwanshi da damuwa akan halin da ɗan uwanshi yake ciki,sai ma ya kasance ɗan uwanka yana cikin ƙunci da matsanancin damuwa,amma kai kuma hankalinka kwance sai ma ajika kana ta faman tiƙar dariya,mai makon arunƙa jajantawa juna,shiyasa dayawa zaka ga na waje ma wani yafika kusanci dashi saboda yafi damuwa da ɗan uwan naka,wanda dayawa hakan ke jefa rayuwar ɗan uwan cikin hatsari,ba'a janshi ajiki cikin gida tun daga iyayen har ƴan uwan,bakamar salahuddeen hussein ba, ya ɗauki ƴa'ƴanshi tamkar abokanan shi,ƙaramin ɗanshi ma tamkar amininshi ya mayar dashi,kuma hakan yasa basa jin shakkar sanar da mahaifinsu abu in ya same su,ko neman shawara awurinshi,wanda a yanzu zaka ga cewa wani a gidansu tsoro ma yake ji ya sanar cewa wani na cutar dashi awaje,saboda wasu iyaye basa tsayawa su fahimci ƴa'ƴansu daga sun ji abu sai afara hantarar mutum in ƙarami ne kaga an haɗa mashi da bugu ma,babu wannan shaƙuwar ta iyaye,da ƴan uwantaka da har mutum zai iya faɗin damuwarshi acikin gidansu,sai dae ya nemi abokinshi ya sanar dashi halin da yake ciki instead of wani nashi nakusa dashi,daga nan kuma awajen in Allah yasa abokin ba nagari bane shine zaka ga anzo ana danasani, don mafi akasarin mutane na fadawa mugun hali ne ta sanadiyyar abokai,ku yi koyi da wannan ahalin wurin nuna ma junanku soyayya,ku zama naku ku kaɗai babu mai jin kanku👌👍
Sehrish bata bar bedroom ɗin sgr ba,har sai da aka kira sallar magrib suka fita tare da abbansu domin zuwa yin sallar magrib sannan ta samu cikin sauri ta ɗage curtains ɗin,da hanzarin gaske ta sungumi mayafinta sannan da sauri hadda gudu ta haɗa wurin barin part ɗinsa,
Saukowa downstairs tayi a lokacin duk sun tafi salla masallaci,kai tsaye kitchen ta nufa tunkan ta ƙarasa ta hangi Azmee da hayaam suna ta haramar kammala dinner ɗin ranar,duk sai taji babu daɗi taso ace tare da ita suka fara,jiki asanyaye ta shiga kitchen ɗin da sallama a bakinta,
Juyowa sukayi suna kallonta atare,da alama ma sun kammala aikin nasu,Azmee ce ke haɗawa Hayaam warmers acikin tray tana kaiwa dining,
"Kin kammala gyara mashi part ɗin nasa ne?azmee ce ta jefa mata tambaya,
"Eh,nagama,"
"Ya akai kika daɗe acan ne"?
Sunnar da kai tayi tana wasa da yatsun hannunta saboda ta rasa amsar da zata bata,
Hayaam kuwa sai faman wurga mata harara take yi kamar kwayar idonta zata faɗo ƙasa,
Murmushi azmee tayi tare da cewa"ki wuce kije kiyi sallah,kada ki samu damuwa,nasan cewa wani abunne ya tsayar dake,"
Ajiyar zuciya sehrish ta sauke kafin ta juya tasa kai tabar cikin kitchen ɗin,bedroom ɗinta ta nufa domin tayi sallah,
A 6angaren su hossana kuwa,tun bayan da suka dawo daga school suke ta faman saran zuwan Omar amma baizo ba,burin jahad ta sanar dashi cewa taga ƙaninshi a school ɗinsu,gaba ɗaya yinin ranar sunyi shi ne cike da kewar Ya omar ɗinsu musamman hossana ko lunch bata ci ba tunda suka dawo gashi ko'a school ma bataci komai ba,saboda tayi alƙawarin cewa tare da ya omar zasu ci abinci zai bata abaki,hakan yasa taƙi cin komai,duk yarda jahad taso ta fahimtar da hossana akan ta zauna taci abinci sam taƙi,har dai tagaji ta ƙyaleta,
sai faman zagaye takeyi acikin bedroom ɗinsu,fuskar nan ɗauke da murmushi ae tunda tayi arba da Romeo sam tagaza samun natsuwa wani irin tsantsar son shi da