Showing 81001 words to 84000 words out of 245004 words

Chapter 28 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download

17 Mar 2025

25257

fawan ne kawai suka samu nasarar cutar dashi harya zauce ssae tun shekaran jiya suna asibiti ana duba su sai jiya ne muka dawo gida tare da su............'
  tunkan abban nasu ya ƙarasa maganar tashi tuni Junaid ya saki wayar dake hannun shi sakamakon faduwar da yayi nan take ya sume...................dama abunda abbansu ke gudu kenan

hankali atashe yake cewa "junaid!junaid !!! Kana jina kuwa !! Meya faru ne,
  yarda yake fidda sautin maganar yasa kowa dake a falon kallon shi, dama duk suna a falon sun hallara saboda sun fiddo da fawan yana kwance asaman 3 seater yana amsa ya jikin da mutane keyi masa,
gaba ɗaya hankalin kowa ya tashi,suka shiga tambayar shi meke faruwa ne,
zumbur ya miƙe yana cewa "wlh junaid ne daga faɗi mashi halin da fawan ke ciki shikenan ya yanke jiki ya fadi ina tunanin ya suma ne awaje,'
"Subhanallahi," mutanen wurin suka haɗa baki wurin cewa haka, fawan dake kwance kuwa tuni ya shiga kiran sunan junaid yana fadin "Abba akawo mun junaid inason ganin shi," ya faɗi akasalance,tun jiya dama yake so yasa shi a idonshi amma bai samu dama ba,
  atare abbansu da cg abbas suka fito domin ɗauko shi, tun kan su isa sai gashi ɗaya daga cikin soldiers din dake cikin gidan ya ɗauko shi sa6e a kafadarshi, cikin sauri Abbas ya kar6e shi tare da yima sojan godaiya, sannan su ka koma ciki dashi,

********************SGR hospital

tun safe su hossana da jahad suke ta faman jiran yaya Omar ɗinsu saboda yazo ya ɗauke su amma shiru babu alamarshi, suna kwance a gado ɗaya saboda since yesterday night hossana ta maƙale ma jahad aɗaki ɗaya suka kwana tana agefenta,hankalinsu kwance saboda kyakkyawar kulawar da suka samu a wurin nurse Camila,tun da sukayi breakfast wanda anan asibitin suke rabawa marasa lafiya abinci kyauta kuma lafiyayyen gaske,sunci sunyi hani'an suna jiran omar yazo, duk in Camila tashigo duba su sai sun tambayeta yaya Omar dinsu yazo? Sai tace musu a'a su ƙara jira kaɗan tun suna tambayarta har suka gaji suka daina,

Around 12 na rana, Motar Omar ta shigo cikin asibitin, bai samu damar zuwa ba saboda busy ɗin daya shiga hakanne yasa shi aiko major domin ya ɗauko su kamar yarda yayi musu alƙawarin cewa da safe zai sa asallame su, dalilin dayasa ya turo masu da major kenan amaimakon shi,
  Bayan major yayi parking ɗin motar sannan ya fito ya shiga ciki, kai tsaye ɗakin dasu su hossana ke ciki ya nufa,
  suna ganin shi suka fara murna don sunsan cewa yana tare da Ya omar,
    "Ya jikin naku"?
Cikin sauri suka amsa mashi da cewa "Alhmdllh jiki da sauƙi,"
Yace "masha Allah,kun ganni ni kaɗai ko?
Hossana tace "eh, ina ya omar din, shi bai zo ba tun ɗazu muke jiran shi,"
  Murmushi major yayi kafin yace "kuyi mashi Uziri yana busy sosai, amma ya aiko ne nazo don na duba ku,sannan nasa a sallame ku mu tafi gida,"
  ba ƙaramin daɗi suka ji ba, don aƙagare suke da su ga inda zasu zauna wurin da zasu fara sabuwar rayuwa,
  "bari naje naga dr, yanzu nan zan dawo," yayi maganar tare da fuce wa daga ɗakin,
  Cike da murna hossana tace "Shikenan mun rabu da wahala, yanzu zamu fara kyakkyawar rayuwa, saboda nasan yaya omar har makaranta zai samu,har na hango ni yarda zan koma nan da 1 month,"
Kallonta jahad tayi da yake sun tashi daga zaune tace "jibgegiya zaki koma kamar buhun fulawa,nikaina naƙosa naga yarda rayuwarmu zata canza,abu biyu nake tunawa da suke sani kwanciyar hankali na farko shine bani da wata sauran damuwa dama hossana ke nafi ji, damuwata aduk lokacin da muka shiga hadari kece ina tsoran kar na rasaki,abu na biyu kuma shine ƴar Uwarmu SEHRISH,duk da bansan a ina take ba amma inaji araina cewa TANA TARE DAMU, INA NUFIN TANA A KUSA DAMU SABODA INAJI A ZUCIYATA!! With confidence tayi maganar in serious matter,
  jinjina kai hossana tayi kafin tace "Jahad nima inaji araina cewa REESHI TANA A KUSA DAMU,komai ma zaizo mana cikin sauƙi yanzu tunda zamu samu kwanciyar hankalin nemanta,ga kuma YA OMAR,NASAN DAGA MUN FAƊA MASA CEWA ƳAR UWARMU TA 6ATA MUNA NEMANTA KUMA KAMANNIN MU ƊAYA SAK MU TRIPLET NE,SAI MU FAƊA MASHI SUNANTA NASAN ZAI TAIMAKA MANA WURIN GANO TA.................✍️💋

Shin mai zai faru idan Aunty babba tayi arba da fuskar Sehrish😳 yaya zata kasance tsakanin Haroon da twins? Baku tunanin cewa dole ALEXANDRA tazo nigeria domin duba jikin fawan😲? haka zalika AMMI ma muna hasashen zuwanta domin ganin fawan😲, ga kuma goggon katsina karfa ace itama zata zo domin ganin fawan shin ya zatayi a lokacin da tayi arba da fuskar sehrish wadda takasance kamanninta ɗaya da ƴa'ƴan abusufyan ɗinta?🤣, to kodai shima abusufyan dake zaune ƙasar turkey zaizo nigeria ne?😯, ni duk bama wannan ba🤨 abunda yafi damuna shine HAYAAM ƙanwar aunty babba wadda ke shirin dawowa gidan da zama 🥱 in har dagaske ne kenan sehrish itace a tsaka mai wuya tabɗijan can, ga haroon ga aunty babba ga wata wai hayaam🥴 wayyo har kaina yafara ciwo don tunanin yadda zatakasance, yakamata naje na kwanta fa, amma kafin nan akwai hasashe ɗaya daya rage mun shin ya zata kasance idan Hossana da jahad suka sanar da Omar game da ƴar uwarsu wadda takasance ita ɗin ƴar ukunsu ce kuma sunanta SEHRISH 🥺🥺🥺
 
 

Alhmdllh last page da nayi alƙawarin zan saki kafin na tafi hutu till 10 oct zamu cigaba insha Allah, nagode ssae da fahimtata da kukayi kuma insha Allah nima bazan baku kunya ba da zarar lokaci yayi zamu ɗaura daga inda muka tsaya in darai da lafiya,🥳
...Much Love to my novel readers am really proud of u guys😍😘🥰 Anatare insha Allah kuma Allah yabar zumunci atsakanin mu daga nan har gidan aljanna😍💃
  Ya Allah kasa mu cika da kyau da Imani🙏

_💋Boss Bature💋_




dawowa major yayi shida dr Emran,a cikin ɗakin da aka kwantar dasu hossana,fuskar major ɗauke da murmushi yace. "An yi discharge ɗinku,kwanan asibiti ya ƙare yanzu zamu wace gida,"
  Murmushi suka saki gaba ɗayansu,jiki na rawa hossana ta sauko daga saman gadon,itama jahad lalla6awa tayi a hankali ta sauko saboda ƙafarta,
  Kallonsu dr emran yayi tare da cewa"zamu yi missing ɗinku sosai gsky,amma tun da a wurin omar ku ke, zamu dinga zuwa muna ganinku,"
  Murmushi suka saki gaba ɗayansu,gaisawa major ya ƙara yi da dr emran sannan yayi mashi sallama,
  shiga gaba yayi su hossana suka bi bayanshi, daker jahad ke taka ƙafarta da taimakon hossana take tafiya saboda ta dafa kafaɗarta gudun karta fama ciwon ƙafarta,
   A haka har suka ƙaraso harabar asibitin wurin ajiye motocinsu, hannu major yasa tare da buɗe masu ƙopar back seat don su shiga su zauna,har jahad tasa kai zata shigo suka jiyo muryar nurse camila tana cewa "wait !! Wait !!,
  Dakatawa su kayi gaba dayansu suna kallonta dama kuma sun so su tambaye ta,ɗan zaman da su kayi da ita ba ƙaramin shiga ransu tayi ba, ƙarasowa tayi kusa dasu tana faman sauke ajiyar zuciya hannunta na ruƙe da jakar kaya, daga bisani ta ɗago fuskar nan ɗauke da murmushi tace"ba sallama twins?yanzu da banzo ba shikenan zaku tafi ko? Ku barni da kewarku,
  murmushi sukayi gaba ɗayansu jahad tace "a'a bamu ganki bane shiyasa,"
   kallon major tayi tare da cewa "tare dani zaku tafi, saboda already mun yi magana da marshal omar, ya dauke ni amatsayin wadda zata cigaba da kula da lafiyarsu,inaso naga gidan saboda in na tashi zuwa,
  wani irin farin ciki ne ya rufe su hossana da jahad saboda sun lura da irin mutuncin dake gare ta, ba ƙaramin kula zasu samu a wurinta ba,
  Murmushi major yayi tare da cewa "naji daɗin jin hakan sosai,saboda na lura da yadda kikeson yaran ina fata zaki kasance tare dasu,kuma zaki riƙe su amana,". 
  Jinjina kai Camila tayi tare da cewa "NA RIƘE AMANA,"
  daganan suka shiga cikin motar jahad da hossana suna a back seat,major na a mazaunin driver yayin da Camila ke Zaune a other seat ɗin,"
   a hankali yake driving dinsu harya fuce daga asibitin,ya miƙi shantalelen titi dasu, ajiyar zuciya kawai suke sauke wa ga wani farin ciki daya baibayesu, ba don komai ba sai don sanin cewa Ƙarshen wahalarsu yazo, yanzu lokacine da zasu huta ma rayuwarsu,suyi rayuwa ta ƴanci kamar kowane ɗan adam, batare da an ƙuntata masu ba ko an cutar 😇
  Lokacin da suka ƙaraso gidan Uncle Abusufyan nan fa hossana ta zaro ido tare da buɗe baki alamar mamaki yarda kasan ƴar babyn roba haka ta koma sam bakinta yaƙi rufuwa don murna, ita kanta jahad bakinta a buɗe don murna fararen hakoran nan nata kamar gonar auduga, adai dai bakin gate ɗin major ya tsayar da motar sannan ya danna horn da ƙarfin gaske,
  sai gashi an buɗe masu gate ɗin ta ciki, ba kowa bane face abokin Major ɗan leƙen asirin shi, acikin gidan ya kwana saboda omar ya dauke shi aiki, bayan alherin da yayi masa na kyautar mota sabuwa mai kyau da tsadar gaske, ga kuma uban salary daya yanka masa,😇
   A hankali major ya shigar da motar cikin gate ɗin ɗan dagatawa yayi da driving ya zuge glass ɗin motar ya kalli osman yace "Shege mutumina, ka ga yarda ka canza jiya izuwa yau har wani haske ka fara? Cike da zolaya yayi maganar,
  Dariya Osman yayi tare da cewa "ba dole kaga canji ba,an gaya ma yin karin kumallo da farfesun kaza wasa ne? mutun ya kwana a ac,sannan yayi wanka acikin kwami haba ae dole ma ne in canza,"
  gaba ɗaya suka fashe da dariya jin abunda yace,
   Major yace "nifa wasa nake maka malam, taya zaka canza kawai daga jiya zuwa yau don ka kwana a ac, kayi breakfast da farfesun kaza? Nace sannu ko uban son banza ae sai nan da irin one month haka,nan zamu ga canji,
  Murmushi osman yayi tare da cewa " ka shiga ciki ka sauke su,in ka dawo zamuyi magana dakai, akwai labari mai daɗi,"
   Major yace "okey bari nazo," yayi maganar tare da sauke glass din motar ya wuce dasu ciki, adai adai stairs ɗin da zai sadaka da main palour ɗin gidan ya sauke su,
   Buɗe motar Camila tayi ta fito, sannan suma su jahad suka fito daga ciki suna ƙarewa katafaren gidan kallo ya haɗu iya haɗuwa abun ba'a magana, Omar yasa an canza mashi komai nashi an ƙara ƙawata gidan sosai,
   gaba dayansu sun ƙame suna kallon haɗuwar gidan, ganin basu da niyyar shiga daga ciki yasa major cewa "let's go in pls,"
  Cikin rashin sani jahad ta take ƙafarta ba don komai ba sai don hankalinta daya tafi wurin ƙarewa gidan kallo,ƙara tasaki tana yarfa hannu tana faɗin "wash Allah na," jin haka yasa camila tayi saurin dawowa ta inda suke, ta taimaka mata wurin yin tafiya don su shiga ciki,
Major ne yayi masu jagora su kuma suna abayan shi, har suka shiga cikin haɗaɗɗen jigunannan falon,nan fa suka baza ido suna kallon haduwarshi, wasu irin matsiyatan royal sofa set ne acikin sa masu numfashi ɗunɗuma ɗunɗuma a jere launin su brown colour,ga wasu set na Cushions Jere asamansu difference colour,duk gasu nan ba ƙaramin ƙawata kujerun su kayi ba, daga tsakiya wani ƙayataccen table ne legs dinshi brown ne, while daga saman glass ne, an ajiye flower asaman shi, ga fruits basket mai dauke da kayan mar mari, ba komai yafi tafiya da hankalin hossana ba face tanƙameman kwan filitar dake bama ɗakin haske tamkar zai faɗo ma mutun akai haka yake, sai kuma tv stand din dakin faskekiyar plasma ma ce mai dauke da speakers na jin sauti, ga wani telephone table dage a gefe, bari dae in taƙaice maku zance komai wannan da kuka sani a palour an zuba masu shi,
  Sai faman yarfa hannu hossana take yi, yarinya fa takusa zauce wa ganin irin gidan da yaya Omar dinsu ya gwangwaje su dashi, wani abun ma sai mun shiga bedroom,
   Jahad kuwa murmushi kawai take saki tana bin ko'ina da kallo,ita kanta Camila gidan ba ƙaramin burgeta yayi ba komai tsaf a natse ba tarkacen hauka,
   Can dae hossana tace "Allah yasa ba mafarki nake yi ba,dan Allah koma mafarki nake yi jahad kada ku tashe ni," ta fadi tana faman hadiyar yawu,
Dariya su kayi gaba ɗayansu, Major yace "wannan zahiran ne ba mafarki ba ne, kaɗan daga cikin irin son da ya'ya omar dinku yake yi maku kenan,zai iya yin komai akanku more than u think, ni dae fatana agare ku shine ku kasance masu yi mashi biyayya, ku bishi sau da ƙafa kada kuyi amfani da son da yake yi maku wurin karya mashi zuciya,ko ku ce zaku canza halayyarku saboda wata dama da kuka samu, yanzu lokaci ne da zaku more rayuwarku bayan duk wahalar da kuka sha,"
  Sosai major yashiga yi masu nasiha, duk sun kasa kunne suna sauraronshi,sannan kuma suna amsa mashi da insha Allah,
  Bayan ya kammala daga ƙarshe yace "ku samu wuri ku zauna mana,nasan kuna jin yunwa yanzu zan sa ayi maku oder na abincin da zaku ci, sannan ga bedroom nan zaku iya shiga ciki ku huta,"
  A natse suka ƙarasa tare da samun wuri suka zauna fuskar nan fa awashe,
  Mayar da idonshi yayi kan Camila yace "zamu tafi tare ne? Na sauke ki a asibitin ko kuwa,"
  cikin sauri tace "no i will stay here wit them,cos i ave done my work bani da sauran duty till tomorrow,"
  Murmushi kawai major yayi sannan yace "okey," sannan yasa kai ya fuce,
A jiyar zuciya ta sauke tare da samun wuri itama ta zauna, bayan ta ajiye jakan kayan data zo da ita,
  kallon juna suka shiga yi suna murmushi,yanayin iskar falon badae daɗi ba yadda sanyin ac ke ratsa sassan jikin mutun,
   Ganin sun zauna shiru yasa Camila cewa "ba ku buƙatar shiga daga ciki ne? ta tambaya tana kallonsu
  Jahad ce tafara cewa "inason nayi wanka, hossana ma tace "nima,"
  tashi camila tayi tare da cewa "mu shiga daga cikin ɗakin to, nima inason nayi wankan," tayi maganar tare da ɗaukar jakar kayanta,
  gaba tayi suka bi bayanta ɗaya daga cikin bedrooms ɗin suka tunkara, ƙoparsa a rufe take amma bada key aka datse ta ba, hannu tasa ta tura nan take ƙopar ta buɗe, shiga ciki su kayi atare,
haɗaɗden bedroom mai ɗauke da tafkeken gado fankacece, yaji lumbutsetsiyar katifa lallausar gaske ga wasu matassan kai masu laushi asama an jera su, irin gadon da kana hawa saman shi ko bakayi niyyar yin bacci ba nan take zai ɗauke ke saboda daɗinsa 🥱 an gyare komai an shimfiɗe shi da bedsheet,side by side na gadon akwai side drawers, masu ɗauke da lamps,
daga can ɗayan bangaren ɗakin kuwa wurin Closet dinsu ne, ga wani haɗaɗɗen Dressing mirror an cika masu front dinshi da kayan make up da tsadaddun mayuka na jiki, komai an sanya masu, jerin wurin takalmansu,hand bags da sauran abubuwa da dama ba abun da omar yabari komai ansa masu,
   jahad ce tafara shiga toilet ɗin don a ƙagare take da tayi wanka,lokacin da ta shiga cikin toilet nan fa taga zallar haɗuwa ta jima tana bin ko'ina da kallo kafin daga bisa ni tayi wankar daker tare da yin alwala saboda in an kira sallah tayi, fitowa tayi a hankali waist dinta daure da towel mai ɗan tsayi wanda ta samu acikin toilet ɗin, hannunta na ruƙe da doguwar rigarta da ta cire, samun su tayi zazzaune daga gefen gadon suna fira da hossana da Camila,
  Ganin ta fito yasa camila tashi ta shiga toilet ɗin,
a cikin laundry basket ta turo rigar, sannan ta ɗan juya ta kalli hossana dake ta faman lumshe ido alamar bacci tace "karfa kiyi bacci don na son halinki, ki bari kiyi wanka ke ma,"
  Murmushi tayi kafin tace"ae bazan iya bacci ba jahad, saboda gani nake kamar in na kwanta zan farka na ganni a gidan wannan matar da ta azabtar damu,nakasa yarda cewa wai mune acikin wannan katafaren gidan nan mu kaɗai abun mu,gsky yaya omar ba ƙaramin ƙaunarmu yake yi ba,"
   Jahad tace"nikaina ina mamakin hakan hossana,ashe akwai wata rana da zato mana irin wannan,mun samu yaya mai son mu tamkar ƙannensa duk don saboda mu ya Omar yabar komai nasa don ya ceci rayuwarmu,har yanzu ina mamamkin hakan hossana, yaya omar ya sanar dani cewa ɗan uwanshi yana kwance rai hannun Allah babu tabbacin cewa zai rayu,amma a hakan ya tsallake shi yazo wurin mu wannan wane irin mutun ne?samun mai iri Kyakkyawar zuciyarshi zaiyi wuya a faɗin duniya,

(shiyasa Hafsat bature take kamu) 🙄
   ta yi maganar ne a lokacin datakai wurin closet tana neman ta inda zata buɗe shi,tana aza hannunta a jikin closet din nan take doors din dake jiki suka zuge da kansu, har sai da jahad ta ɗan tsorata tayi baya,
  tasowa hossana tayi itama tana kallon wurin kayan nasu, yadda suke tagwaye haka omar yasa aka jera masu komai kala biyu, jerin wurin pyjamas ɗinsu daban, jerin wurin dogayen riguna daban,jerin wurin jeans da t shirt daban, ga jerin under wears shima daban, komai nasawa ajiki an zuba masu shi,har sun wuce iyaka,
  "jahad har naji inason nayi wanka wlh,saboda in canza kayan jikina," acewar hossana dake ta faman yarfa hannu tana kallon kayan,
  Hannu jahad tasa tare da curo wasu pakistan masu kyan gaske,tana shafa jikinsu tunkan tasa har ta gano kyan da zasu mata,
     a gefen gado ta ajiye su, sannan ta koma gaban mirror tana shafe jikinta da ɗaya daga cikin mayukan da tagani ajare, bayan ta kammala ta kuma feshe jikinta da turare mai ƙamshin gaske,
   Sannan ta dawo ta tsaya a gefen gadon tana zura kayan ajikinta, duk hossana na can tsaye wurin closet ɗin tana ƴan ta6e ta6e,ji take tamkar tabi kowannansu ta gwada ajikinta,
  Bayan jahad ta gama kimtsawa cikin pakistan din komawa tayi gaban mirror tana kallon jikinta,riga ce mai dogon hannu har guiwar ƙafarta sai wandon burgujeje irin nasu,ta yafa mayafin asaman kafaɗarta, sumar kanta kuma ta zubo a bayanta, murmushi kawai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login