Showing 126001 words to 129000 words out of 245004 words

Chapter 43 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download

17 Mar 2025

25286

yake damunka wlh,duk cikin abokanan mu da mukayi aiki dasu babu wanda yanzu bai ajiye jikoki ba,wani ma cikin jikokin sunyi aure,duk acikin mu babu wanda ya tara ƴa'ƴa maza kamarka,haba hussein ya kamata kayiwa kanka adalci ƴa'ƴa kusan goma sha wani abu ka tasa su gaba kana kallo,ni bansani ba ko shakkarsu kake ji ne shiyasa kaƙi aurar da su," ƙarasa maganar dattijon yayi yana faman ɗaure fuska,da alama abun ba ƙaramin ciwo yake mashi ba,
  Tunda ya soma maganar tashi Abban nasu bai katse shi ba sai da yakai aya sannan yace"Nima kaina bani da burin da ya wuce wannan,amma narasa yarda zanyi dasu ne,ba wai ƙarfina suka fi bane,bana so na takura masu ne ko nace zanyi masu auran dole,nafison in Allah yasa sun samu wadda ta dace da rayuwarsu suka ji suna so sai in aura masu.......'
  bai bari abban nasu Yakai ƙarshen maganar tashi ba yace"kaji matsalar!bakomai bane yajawo hakan ba face shegen son da kake ma yaran nan!shi ya hana kayi masu aure,kuma inaso ka sani wannan ba soyayya bace!tun da har zaka iya hana farin cikinka don ka faranta masu a matsayinsu na ƴa'ƴan daka haifa!har yaushe ne zaka zauna kana jiran su kawo maka matayen da suke so ka aura masu?kai da kanka fa kace ko soyayya ma basa yi!shin zaka zauna kana jiransu ne batare da ka cika burinka ba?yaushe kenan?bayan ka tsufa tukuf ko kuma bayan ka mutu kenan?
  Shiru Abba yayi yana sauraron shi,
"Ni dai ina baka shawara kaima ka jaraba yin irin nawa,Yaran nan fa kai kake da iko dasu kaine ubansu duk duniya basu da kamarka,kuma na lura yaran nan ba ƙaramin sonka suke yi ba,sau da kafa haka naga suna binka suna yi maka biyayya,"
  Sai lokacin Abban nasu yace"naji kace,na jaraba yin irin naka,amma baka yi mun bayani ba,"
  Murmushi tafeeda yayi tare kai hannu zai ɗauki lemu ya zuba acikin cup,cikin sauri Abba ya riga shi ɗaukar roban lemun ya buɗeta tare da tsiyaya mashi acikin cup sannan ya mika mashi,
  Hannu yasa ya kar6a tare da kaiwa bakinshi yana sha,bayan ya gama kur6e shi duka ya mayar da kofin ya ajiye,sannan ya mayar da idonshi kan Abban nasu yace"shekara bakwai da suka wuce,kasan nima yaran nawa kamar na wajenka suke,banbancin kawai ni na wurina basa jin magana sun fiye taurin kai,kullum ina yi masu maganar aure babu wanda ke kulani acikinsu tunda suka dawo daga karatu kowa aiki yasa agaba,basu da lokacin kula mata balle suyi tunanin yin aure,wannan abun ba ƙaramin ƙona mun rai yake yi ba,raina yana 6aci sosai,don haka nace badai nine ubanku ba,zanyi maku auran inga ta tsiya,a lokacin munje masallacin juma'a daya ke atare muke haduwa muje,bayan an kammala sallah nace akwai ɗaurin auren ƴa'ƴana da za'ayi amma basu da mata,duk wanda yasan yana da ƴa mace da ta isa yin aure kuma ya shirya yi mata auren,yayi magana ga ƴa'ƴana nan ashirye nake dana aurar dasu,hankalinsu ya tashi haikam jin abunda nake ƙoƙarin yi masu,ina baka labari mutumina,ba mu bar masallacin nan ba saida aka shafa fatihar kowanne daga cikinsu,yanzu labarin da nake baka tun suna nuna 6acin ransu yanzu takai ga tsakanina dasu godiya ce,nace masu da kuka ce baku so, ga abun arziƙinan hada yaransu gwanin burgewa,"
  dariya sosai abba yayi aranshi kuwa yana ayyana abunda zai faru idan har ya kuskura ya jaraba irin na abokin shi tafeeda,tabbas ba ƙaramin bomb zai haɗa ma kanshi ba,ba kowa ma ya fi jin fargabarsa ba irin RAFAYET,saboda wasu abubuwan nashi sak irin na mommynsu ne Alexandra,ita babu wanda ya isa yayi mata abunda ba tayi niyya ba,in kuwa hakan ta faru to fa za'aga tashin hankali,
  gaba ɗaya Abba yayi nisa acikin tunanin shi muryar Tafeeda ce ta katse shi da cewa"Naji kayi shiru mutumina na,ni nasan cewa kana jin shakkar ƴa'ƴanka ne shiyasa bazaka iya yi masu hakan ba,amma inaso ka sani yanzu lokaci yayi da yakamata ace kayi abunda ya dace a matsayinka na Uba!hussein kayi ƙoƙari sosai wurin tarbiyyantar da ƴa'ƴanka,kowa yana alfahari dasu,duk in da naje naji ana yabon ƴa'ƴanka sai inji wani irin farin ciki araina,har ma in dinga cewa ae ya'yan aminina ne,kuma da zarar nace haka sai kaga ana ta respecting ɗina,hussein abu ɗaya ya rage yanzu kayi masu shine aure,zasu yi alfahari da hakan sosai,kada kace na takura maka akan maganar ka aurar da ƴa'ƴanka,ina yin hakan ne saboda farin cikinka!saboda nasan cewa abun nayi maka ciwo sosai,hakan ne ma yasa kake yawan kirana a waya kana sanar dani damuwar da kake ciki,Hussein har yaushe ne zaka dinga la6ewa aɗaki kana matse hawaye akan yaran da ka haifa?
  Jiki asanyaye Abban nasu ya ɗago yana kallon abokin nashi,tabbas abunda tafeeda ya faɗa gaskiya ne,sau dayawa idan damuwar tayi mashi yawa yakan farka tsakar dare yayi alwala ya shiga jera nafilfili yana kai kukan shi wurin Allah duk akan rashin son auren ƴa'ƴan nashi,abun ba ƙaramin ciwo yake yi mashi ba,gashi bai da wani buri daya wuce wannan,shi kaɗae ne Last ambition ɗin da yake dashi kafin yabar duniya gashi babu alamar cewa burin nashi zai cika nan kusa,
   Sosai Tafeeda ya shiga tunxura abban nasu game da aurar dasu ya kuma ƙarfafa mashi guiwa sosai har yake jin cewa zai jaraba yin hakan,

  (Tabɗijancan)
    
Bayan sehrish tabar garden ɗin komawa tayi wurin su junaid ta tsaya daga gefen ragar tana kallon wasan nasu,tun da yaga sehrish yake ta faman ƙoƙarin yaga yaci kwallon amma abun yaci tura,saboda mugunta sojojin suke yi mashi,sai ya watsa da gudu zai tari kwallon sai asamu wani ya taɗiyo ƙafarsa ya faɗi ƙasa yaraf saman grass carpet ɗin dake a wurin,tuni ran sehrish yayi mugun 6aci saboda ta lura da yarda suke zaluntar shi,maimakon su tausaya mashi su bar shi yaci ko da sau ɗaya ne amma sai wurgi suke yi dashi,.

Aikuwa suna cikin wannan yanayin sai ga Motarsu Sgr ta shigo cikin gidan,adai dai football field din Amstrong yayi parking ɗin motar,sannan ya fito tare da zagayawa ya buɗe mashi mota,a hankali ya zura ƙafarshi tare da fitowa daga cikin motar,tsayawa yayi tare da goya hannayenshi asaman wide chest dinshi yana kallon wasan ball ɗin nasu,gaba daya duk basu lura dashi ba,lokaci guda ya gane cewa mugunta suke ma Junaid ɗinshi,
   juyawa yayi ya kalli Amstrong dake tsaye agefenshi,cikin harshen turanci yace mashi"kana ganin abunda nake gani kuwa"?
  murmushi Amstrong yayi kafin yace"Sir,yakamata kaje kaima ayi wasan dakai,suna buƙatar lecture,"
   jinjina kai Sgr yayi tare da wuce wa kai tsaye ya shiga cikin filin wasan,
  lokacin da sukayi arba dashi nan take suka ji gabansu ya faɗi rasss,junaid kuwa da gudun gaske ya tunkare shi tare da faɗawa jikinshi yana kuka,
  Hakan ba ƙaramin fusata Sgr yayi ba,hannu yasa tare da ɗago fuskarshi yana kallon hancin shi da jini ke ɗiga alamar wurin ya bugu da kwallo,
   cikin sanyin murya Sgr yace"kana so na rama maka"?
  ɗaga kai junaid yayi alamar eh,
"Okey ka koma daga waje,kasha kallo kawai,"
   Wani irin farin ciki ne ya rufe junaid cikin sauri ya fuce tare da komawa wurin sehrish dake tsaye,sam bata ji zuwanshi ba saboda idonta na akan Sgr dake acikin filin wasan,
  Hannu yasa tare da ɗan bubbuga kafaɗarta,a firgice ta juyo tana kallon fuskarshi,
  "Ko tausayina ma ba kiji ba,kina tsaye kina kallon yarda suke ta wahalar dani,maimakon ki shigo ciki ki ramamun,".
  dariya sehrish tayi tare da cewa"junaid nifa nasan ciwon kaina,taya zaka shige cikin waɗancan garadan masu fuskar shanu kace wai zaka buga ball dasu,ae sunfi ƙarfinka,gayanan duk sun wahalar dakai abanza,
   ɗaure mata fuska yayi yana murguɗa mata baki,
   girgiza kai kawai tayi tana dariya kafin daga bisani suka mayar da hankalinsu kan filin wasan,

    Tashin hankali,ƙananun namun dawa sunyi arba da zaki,
Sai faman mazurai suke yi suna kalon shi,kusan su shida ne acikin ragar,in aka haɗa da sgr sun zama su Takwas kenan,gaba ɗaya duk sun sha jinin jikinsu saboda sun san mai zai biyo ba,dama tun alokacin baya idan yazo nigeria da zarar yaji hannunshi nayi mashi ƙaiƙayi,sai ya tara duka acikin ragar suyi Boxing,ba ƙaramin bugu yake yi masu ba,duk yawansu haka zai tarwatsa su,
  Hannu yasa tare da cire rigar jikin shi nan take ƙirar nan mai tsoratarwa ta bayyana,wurga ma junaid rigar tashi yayi cikin sauri yasa hannu ya cafke ta,
   "Junaid bani na ruƙe mashi rigar,"acewar sehrish,
  Miƙa mata rigar junaid yayi hankalin shi na a field din,hannu tasa ta kar6i rigar tare da kaita saitin hancinta tana shinshina ƙamshin turaren jikinta,rungume rigar tayi sosai ajikinta,sannan ta mayar da idanunta akan wasan nasu,
  Tunda suka ga Sgr yakai hannu tare da ɗaukar kwallon yana bubbugata ƙasa tana dawowa cikin tafin hannunshi,yayin da kyawawan idananuwan nan nashi ke binsu ɗaya bayan ɗaya yana kallonsu,hakan ba ƙaramin tsoratasu yayi ba,
   Wani daga cikinsu ne yace"Wlh kwara kowa yayi ta kansa da alama watan cin ubanmu ne ya tsaya,"
  Yana ƙarasa maganar tashi ya nufi hanyar fita daga cikin ragar da gudu zai tsere,sai dae ina kafin ya ƙarasa fita,Sgr yasa ƙafarshi tare da buga ball ɗin da ƙarfin gaske kai tsaye ta sauka a tsakiyar goshin shi,wani irin jiri ne ya ɗebe shi sai gashi ƙasa a baje yana faɗin"la'haula wala ƙuwata illa billah ,'
  .gaba ɗaya Sehrish da junaid suka shiga 6a66aka mashi dariyar mugunta hada dafe ciki,
   Ganin haka yasa sauran suka yi hanzarin ɗaukar ball ɗin don ayi wasan dagaske,gaba ɗaya suka kacame suna ƙoƙarin ganin sunci nasara akanshi,ba ƙaramar wahala sukaci a hannun Sgr ba,domin kuwa da mugunta ya dinga buga masu kallon da wasa da wasa sai da yayi masu jina jina a hancinansu,dama ba wasan yakai shi cikin ragar ba,ganin yarda suke nuna ƙarfi wurin junaid yasa shima ya shiga don ya nuna masu cewa gaba da gabanta fa,
a nan yabarsu baje ƙasa saman grass carpet ɗin sai faman wash wash suke yi,gaba ɗaya sai da ya tabbatar da cewa ya gama raunata ga66an jikinsu sannan ya fito daga cikin ragar,
   da gudu junaid ya ƙarasa wurin shi tare da rungumo shi ta baya fuskarshi ɗauke da dariya yake faɗin"My hero man,u did a good job,naji daɗi da ka ramamun nasan daga yanzu bazasu sake gigin ta6ani ba,"
  Hannu Sgr yasa tare da janyo junaid ya dawo ta gabanshi suna fuskantar juna sannan yace"junaid,u ave to be ur own hero,wannan ne burina,banason kana abu tamkar ba namiji ba,kai fa jini na ne!"
   murmushi junaid yayi tare da ɗan sunnar dakai cikin jin kunya yace"insha Allah babban yaya zan zama kamar yarda kakeso,"
   "Yawwa,haka nakeson ji,ina rigata ne"? Ya tambaya yana kallon shi,
   juyawa juanid yayi yana kallon Sehrish dake rumgume da rigar sgr a hannunta,
  Murmushi yayi tare da cewa"Tana a wurin sehrish,ita tace na bata ta ruƙe maka bari na kar6a maka,"
  Juyawa yayi zai tafi,cikin sauri Sgr ya ruƙo rigar jikinshi tare da cewa"zan amsa dakaina,wuce ka shiga cikin gida banason ganinka haka,kayi wanka sannan ka huta sosai,'
  Amsa mashi yayi da toh sannan ya kama hanyar zuwa cikin gidan da dan gudu² kamar yarda ya umarta,
   A natse ya soma tafiya har ya isa inda sehrish take atsaye ƙanƙame da rigarshi a hannunta,sam batasan meke wakana ba,ta manna rigar a hancinta idonta a rufe tana shaƙar kamshin turarenshi,da alama ba ƙaramin yanayi ta shiga ba,
    koda ya ƙarasa inda take tsaye,idonshi na akan rigar shi dake rungume ahannunta,hannu yakai tare da ruƙo rigar zai janyeta daga hannun sehrish,ae kuwa cikin rashin sani sehrish ta ƙara ƙanƙame rigar alamar bazata saki ba,duk a tunaninta junaid ne zai kar6i rigar,batasan cewa mai rigar bane yazo dakan shi,
   a karo na biyu ya ƙara kai hannu zai ruƙo rigar,cikin sauri sehrish ta cafke hannun shi tare da yin wurgi dashi gefe guda,fuskarta tamkar zatayi kuka tace"dan Allah junaid menene haka,bana ce kabarmin rigarba,zan kai mashi ita dakaina,"
   Sai da takai ƙarshen maganar,sannan taso ma tunanin wai hannun wanene ma ta ruƙo!tabbas wannan ba hannun junaid bane akwai bambanci sosai ko ta wajen girman hannun,
A hanzarce ta Buɗe idanunta tare da sauke su akan ƙafar Sgr dake tsaye agabanta,wata irin zufa ce ta soma kartomata a fuskarta,nan take ta soma haɗiyar yawu,sai faman mazurai takeyi tana zazzare idanu,
  Ja da baya ta ɗanyi murya na rawa a hankali ta shiga ambaton"nashiga ukuna!ashe shine da kanshi,wayyo Allah na wlh nayi tunanin junaid ne........'
  Bai bari ta ƙarasa maganar ba,yasa hannu tare da kar6e rigarshi,sannan ya wuce izuwa cikin gidan batare da ya zura rigar ajikin shi ba,
  ajiyar zuciya sehrish tashiga saukewa hannunta na dafe da saitin zuciyarta,a haka ta nufi cikin gidan tana zullumin karsu haɗu dashi,bakomai tafi ji ba fa ce yarda tayi wurgi da hannunshi cikin rashin sani,tabbas a lokacin da bai kai zuciya nesa ba,Mari zata sha zazzafan gaske,amma sanin cewa ba da gangan tayi bane yasa baiyi mata komai ba,

_💋Boss Bature💋_

Ba ƙaramin bacci hossana da Omar suka sha ba ahaka,har lokacin jahad na a cikin bedroom ɗinsu kwance saman gadon bacci yayi awon gaba da ita,hannunta na rungume da zanen fuskar junaid da tayi,ta ƙanƙame shi a ƙirjinta kamar wani yace zai ƙwace mata shi,
   wuraren ƙarfe ɗaya,Omar ya farka a hankali ya buɗe eyes ɗinshi yana faman sauke ajiyar zuciya,mayar da idanunshi yayi akan hossana dake ƙanƙame dashi,gaba daya ta zura hannayenta tare da ruƙo waist ɗinshi,kanta kuma na akwance saman kafaɗarshi sai sharar bacci takeyi abunta,gashin kanta ya zuba harya rufe side face ɗinta,
  A hankali yasa hannunshi tare da ruƙo curly hairs din nata,yayi gefe dashi izuwa saman bayanta,hakan ya bashi damar kallon fuskarta da kyau,ba ƙaramin kyau tayi mashi ba,musamman yarda lips ɗinta ke motsi,dama jazamun ne hossana bata iya bacci batare da la66anta na motsi ba,haka zalika yatsun hannunta kullum cikin kerma suke saboda sabo da 6arna,
   Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarta,kafin ya mayar da fingers ɗinshi a saman brownish lips dinta,a hankali yake shafa tausasan la66an nata da hannun shi,dan tunani yayi hakan yasa ya fara ƙoƙarin janye  yatsan nashi yaji ta cafke shi da bakinta,sucking ɗinshi ta shiga yi batare da saninta ba,
  Murmushi Omar yayi yana kallon yarda ta ƙankame mashi yatsanshi acikin bakinta,tana tsotsa kamar wata jinjira,
   Da farko ya ɗauki abun wasa,amma daga bisani sai ya dinga jin wata irin kasala na rufe shi,lokaci guda ya soma shiga yanayi na son kasancewa da ita,hakan yasa cikin sauri ya zame yatsanshi daga mouth ɗinta gudun karya jefa kanshi cikin matsala,
   Lalla6awa yayi tare sanya hannunshi ya janyeta daga saman kafaɗarshi ya kwantar da ita saman sofa ɗin,sannan ya miƙe tare da ruƙo ƙafafunta ya haura dasu saman kujerar,
   Sannan ya dawo tare da zuƙunnawa adai² saitin fuskar hossana yana kallonta,
  A hankali yace"Me zan buƙata bayan wannan arayuwata?na mallaki komai da nake buƙata a duniyar nan,nagode ma Allah daya haɗani da ƙaddarata cikin sauƙi batare da nasha wahala ba,tana sona sosai,kuma insha Allah bazan karya mata zuciya ba,a shirye nake dana mallaka maki kaina....duk da takasance mai ta6in hankali,a haka nake ƙaunarta,shi so babu ruwan shi da wannan,burina nasamu wacce take sona tsakani da Allah badan wani abu dana mallaka ba,gashi kuma nasamu,ita wannan bata da cikakken hankalin da zata iya sona don wani abu,burinta kawai Ya omar ɗinta ya kasance atare da ita ko da yaushe....zanje kawai na sanar ma Abbana cewa,Nifa na isa aure,kuma na samu wadda ta dace da rayuwata,yarinyar ta kwanta mun araina sosai tun ranar dana fara ganinta,ashafa fatiha kawai Abba akaimun ita ɗakina,me ya fi wannan?
   ya ƙarasa maganar cike da zolaya yayin da fuskarshi ke ɗauke da ƙayataccen murmushi,
   yunkurawa yayi tare da miƙewa sannan ya juya cikin sauri ya fuce daga palourn saboda kiran salla da ake ta faman yi,
  sam ƙafafunta sun gaza ɗaukarta,jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,ashe tun lokacin da Omar yake zukunne agaban hossana yana furta waɗannan daddaɗan kalaman nashi take a tsaye tan sauraron shi,
Bata jima da farkawa daga bacci ba,fitowarta kenan tayi arba da wannan tashin hankalin,
  Allah sarki jahad,sosai tayi kuka daga tsayen da take,tama rasa kukan me take yi,shin na farin cikin cewa Omar yana son ɗaya daga cikinsu ne,ko kuma na baƙin cikin cewa Hossana yake so ba ita ba?
  Jiki asanyaye ta ƙarasa cikin falon,adai dai inda Omar ya zukunna saitin fuskar hossana dake kwance saman 3 seater ɗin, itama adai dai nan taje ta zuƙunna tana kallonta,sai faman sharar bacci takeyi,
  Cikin shessheƙar kuka jahad ta soma magana da wannan sanyayyiyar muryartata,
   "Ho..hos...sanah....ni bazanyi baƙin ciki dake ba,sam banji kishi ba da Ya omar ya bayyana soyayyarshi agare ki ba,duk da naso ace ni na mallake shi ba don komai ba sai don burin da nake dashi na ganin cewa na saka mashi da irin kyautatawar da yake yi mana,wannan ita kaɗae ce hanyar da zamu iya faranta mashi,idan har ya auri ɗaya daga cikin mu ni ina da tabbacin cewa bazai ta6a danasani ba,kawai abunda nake tunani shine,banda tabbacin cewa Hossana zata iya kyautata mashi sosai amatsayinta na wadda take da ta6in hankali,bansani ba ko hossana zata iya faranta mashi ba,idan har ya aureta taya zata iya ɗaukar dukkan wata buƙata tashi,taya zata iya?that's the reason why naso ya aure ni kenan saboda ni ina da cikakken hankalin da zan iya yi mashi komi yakeso,zanyi mashi biyayya sosai,zan bishi sau da ƙafa,amma sai dae kash ni ban samu wannan damar ba,hossana ke kika samu wannan damar,hossana you're among the most lucky women in the world,ina tayaki farin ciki sosai,ki tashi kiyi godiya ga ubangijinmu Allah subhanahu wata'ala daya mallaka maki kyakkyawar zuciya irinta ƴa' Omar,that's the most greatest gift hossana,"
   jiki asanyaye jahad ta ƙarasa maganarta,sannan ta miƙe a kasalance tana ja da baya da baya,yayin da idanunta ke ci gaba da zubar da hawaye,
   "Shi kaɗaine namijin da nake da burin na aura aduniyar nan,akan shi ne nafara jin so,na kuma son ya raɗaɗinsa yake,a duk lokacin da mutun ya rasa abunda yake so,"
   juyawa tayi da gudun gaske ta koma cikin bedroom ɗinsu tare da faɗawa saman gadon nasu,tana ci gaba da kukan da takeyi,
  Cikin kuka take faɗin"na rasa first love ɗina,Ya Allah ka bani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login