Showing 171001 words to 174000 words out of 245004 words

Chapter 58 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download

17 Mar 2025

25275

ɗagawa,babban abunda yake tsoro kada wani ya faɗo ya same su acikin wannan yanayin da suke,
   kiciniyar kwace kanshi ya shiga yi da iya ƙarfinshi na karshe amma hakan ya gagara,a ƙarshe daya rasa yadda zaiyi saiya daddage ya garza ma jahan cizo asaman ƙirjinshi,ko gizau baiyi ba,
   wani irin juyi Ayaan yayi anan ya samu nasarar hankaɗe jahan yayi gefe guda ƙasa,shi kuma ya tashi cikin sauri yana gyara short ɗin jikinshi,
      Har yasa ƙafa zai bar ɗakin,yaji gabanshi yayi wani irin mugun bugu,cikin sauri ya juya tare da kallon jahan da idanunshi ke kallon sama,kwata kwata baya motsi komai nashi ya tsaya cak da yin aiki,waro ido waje yayi da hanzarin gaske ya koma wurinshi tare da zubewa saman guiwar ƙafafunshi yana ambaton sunanshi hankali a matukar tashe!
  "Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!Jahan!jahan!don Allah kayi magana!ɗan uwana kada ka mutu ka barni!bana fata ace ni nayi silar barinka duniya!na cuce ka jahan nagaza cetonka!ka yafe mun ba laifina bane!"
   Kuka sosai Ayaan keyi yana jijjiga jikin Jahan,bai da wata mafita a halin yanzu,ji yake tamkar ya watsa aguje yaje ya sanar ma su Abbansu halin da ake ciki,amma fargabar kada ace jahan ba mutuwa yayi ba,in har hakan ta faru to tabbas zai iya farkawa agabansu ya cakume shi ya shiga ƙoƙarin biyan bukatar shi agabansu,tunda baya acikin hayyacinshi,
   Yasha kuka sosai kamar kamar me,a ƙarshe ya yanke shawarar zuwa ya ɗauko ruwa don ya yayyafa mashi ajikinshi ya ga ko zai farka,
  A hanzarce ya miƙe tare da kama hanya ya fuce daga cikin bedroom din,
  Sauri yake yi tamkar zai tashi sama aranshi sai addu'a yake yi Allah yasa jahan ba mutuwa yayi ba,

Fitar shi ke da wuya daga cikin bedroom din nasu,Haroon ya faɗo cikin ɗakin afusace don yayi masu magana akan Money bag ɗinsa da yake zargin su suka ɗauke shi,koda yayi arba da jahan kwance aƙasa baya motsi,abun ba ƙaramin ɗaure mashi kai yayi ba,ta6e baki yayi tare da shigewa ciki,ya zukunna adaidai inda jahan ɗin yake kwance,yakai hannu tare da shafa ƙirjinshi,da yake shu'umine,nan take ya gane awane hali jahan yake,
   sunnar da kanshi yayi tare da haɗe bakinshi wuri ɗaya dana jahan,zura tongue ɗinshi yayi acikin bakin jahan,aikuwa awani irin yanayi Jahan yayi motsi alamar yaji abunda yakeso,batare da 6ata lokaci ba Haroon ya shiga biya mashi buƙatar shi,
  
  Ayaan na ƙarasawa wurin fridge ɗin yasa hannu tare da buɗewa cikin sauri,hannu yakai cikin jerin bottles water ɗin dake a jere cikin frigde ɗin,har zai ɗauki robar ruwan swan idon shi ya sauka akan Robar ruwan addu'ar nan da junaid ya ajiye ta sehrish,bakomai ne yaja hankalin shi akan robar ba,face rubutun Larabcin dake rubuce ajikinta,tunda akeyi masu order na abunsha,ba'a ta6a kawo masu kalar robar ruwan nan ba,mai rubutun labarabci ajikinta,zubama robar ido yayi yana kallonta nan take abunda ya faru ɗazu ya faɗo mashi aranshi,wasiwasi Ayaan yashiga yi acikin ranshi yana cewa"wannan roban ruwan kamar itace na ɗauka ɗazu nasha!kuma tunda nasha ta komai nawa ya canza,tabbas ina tunanin cewa tana tattare da wani abu ajikinta,amma kuma waye ya ajiyeta indai haka ne?don ina da tabbacin cewa ba'a kawo mana kalar wannan bottle water ɗin acikin gidan mu!bari na jaraba kaima Jahan ya sha,tanan zan gane abunda ke tattare da robar ruwan nan!"
  Yana ƙarasa zancen zucin nashi batare da 6ata lokaci ba,ya sungumi robar ruwan a hannunshi,bayan ya rufe frigde ɗin,da saurin gaske ya wuce part ɗinsu,
  Yana gab da shiga bedroom ɗin nasu,ya dinga jin wani irin gurnani mara daɗin ji,a wani irin tsorace ya afka cikin ɗakin,waro idonshi waje yayi saboda tsabar 6acin rai baisan sa'adda yayi wurgi da Robar ruwan dake a hannunshi ba,nan take ta faɗi ƙasa tana gangarawa murfinta ya cire,ruwan cikinta ya kwarare ƙasa gaba ɗaya,
   A fusace ya ƙarasa tare da damƙar rigar haroon da iya ƙarfin shi na ƙarshe yayi wurgi dashi gefe guda,ɗagowa haroon yayi yana kallon Ayaan da idanunshi waɗanda suka canza launi izuwa jawur dasu,sai faman lashe bakinshi yake kamar wani tsohon maye,
   Rai a6ace ayaan yace"wai kai wani irin daƙiƙin mutum ne dabba!kuma jahili wanda baisan ciwon kanshi ba!mugu azzalumi kawai,banta6a ganin fasiƙin mutum irinka ba!wanda baya tsoran Allah!"ran Ayaan ba ƙaramin 6aci yayi ba,yana magana hawaye na gangarowa daga idanunshi masu zafin gaske,
   Duk a tunaninshi haroon zai ji haushin kalamanshi,amma abun mamaki fuskarshi ɗauke da wannan shu'umin murmushin nashi yace"Kwantar da hankalin ka mana!nifa ceton rai nike,duk irin son da kake ma Jahan ka gaza taimakon shi,kana ji kana gani zai mutu,ni kuma bazan so haka ba saboda inason ɗan uwana,shiyasa nayi hakan don na cetoshi daka halaka......'
  Tunkan ya ƙarasa maganar Ayaan ya daka mashi tsawa tare da cewa"Karka kuskura ka ƙara ambaton sunan jahan a matsayin ɗan uwanka!kai ba jinin mu bane,mutun mai halin dabbobi irinka bazai ta6a zama jinin mu ba,yanzu bana doubting akan haka,Haruna kai ba ɗan uwanmu bane!ka wulaƙanta rayuwarmu,Allah ba zai ta6a barin ka ba,ƙarshen ka bazai yi kyau ba haroon!tun wuri ina baka shawarar ka tattara kayanka kabar gidan nan tun kafin lokaci ya ƙure maka!!!!"
   fashewa da dariya haroon yayi,a yayin da yake miƙewa tsaye daga zaunen da yake a ƙasa,takawa yayi izuwa wurin da Ayaan yake sannan yace"naji duk bayananka akaina,kuma naji shawarar da ka bani,inaso ka sani cewa ko kaɗan banji tsoro akan kalaman da kayimun ba,ka ajiye wannan zamuyi magana akanshi,abun da ya kawoni ɗakinku shine Jakar kuɗin Da kuka kaimun ban ganta ba,an ɗauke ta daga ɗakina,kuma ba kowa nake zargi ba face ku,saboda ku kaɗae kukasan da zancen kuɗin,bayan ku babu wani da yasan da maganar!!ina jakar kuɗina take!!"
    takaici ne yasa Ayaan kasa yin magana tabbas da ace yana da halin kawar da haroon da tuni yakai shi inda ya dace,
   Cike da takaici Ayaan yace"maganar ɗauke jakar kuɗinka sam bata shafe mu ba,don haka tun wuri ka nemi wanda ya ɗauke maka kuɗinka!idan ma kanaso kayi amfani da wannan damar ne don kayi mana wayau ka ƙara samun wasu kuɗin awurinmu to inaso ka sani cewa ko sisi bazasu ƙara fitowa a wurin mu ba!bazamu baka ba!kaje kayi duk abunda kaga dama,'
  Wani irin huci haroon ya runƙa fitarwa yana kallonshi yace"Kadaina yi mun magana A gadarance!taƙamarka kun goge videon dake a wurina to inaso ka sani cewa akwai wani videon a wurina!ni ba shashasha bane kamar yarda kukayi tunani!dama sai da raina ya bani cewa akwai wata ƙullalliyar da kuka shiryamun,don haka muddin baku dawomun da jakar kuɗina ba saina fallasa ku Uban kowa yaga abunda kuke aikata........'bai ƙarasa maganar ba saboda Ayaan daya kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya,nan take kan haroon ya ɗaure yashiga mamakin dalilin dariyar ta Ayaan,
  Sosai Ayaan yake 6a66aka dariya kamar kamar me,hada dafe cikinshi,tashin hankalin da ba'a sama shi date,kwatsam yake zuwa,
  duk wannan surutan da suke yi Jahan yana kwance a ƙasa sai faman juyi yakeyi saboda raɗaɗin da cikinshi ke yi mashi,sam baya acikin hayyacinshi,saboda he isn't satisfied,
   "Me kake yi ma dariya"?haroon ya jefa mashi tambaya,
  tsagaitawa da yin dariyar yayi yana Girgiza kai yace"Haroon ka gama yawo!wlh ka mutu!kai baka da tunani ne,bazan baka satar amsa ba,amma kaje kayi tunanin waye ya ɗauki jakar kuɗin nan!taya akai wani yasan da zancen jakar kuɗin nan har ya bi ɗakinka ya ɗauke ta!junaid kaɗae ne ya shigo cikin bedroom ɗinka a lokacin da muke tattaunawa,kuma kasan cewa junaid baya acikin sense dinshi ya shigo,koda ace yana cikin hayyacinshi bazai iya ɗaukar maka jakar kuɗin nan ba!to waye ya ɗauki jakar kuɗin?mu dai bamu bane!"?
  shiru haroon yayi yana kallonshi gaba ɗaya ayaan ya burkita mashi tunaninshi,hakanan ya dinga jin gabanshi na faɗuwa,bai ƙara tanka ma Ayaan ba,cikin sauri ya kama hanya tare da fucewa daga ɗakin,
Ajiyar zuciya Ayaan ya sauke,jin hannun mutum a ƙafarshi yasa yayi hanzarin kai idanunshi ƙasa yana kallon Jahan dake ta faman fitar da numfashi sama sama,hankali tashe ya shiga neman robar ruwan daya shigo da ita acikin ɗakin,can ya hangota ta gangara wurin shoe rack ɗinsu,murfinta ya cire ga ruwan ciki ya malale ƙasa,dafe kansa yayi da hannunshi na hagu cike da takaicin ruwan daya zube,
   ƙokari jahan yake yayi mashi magana akan ya kira mashi Abbanshi karya mutu baisa shi a idanunshi ba,amma kwata kwata sounds ɗin bai fitowa abakinshi,ko idonshi bai iya budewa bare ya iya yin magana,gaba ɗaya Ayaan ya rasa yarda zaiyi,kanshi ya gama kwancewa,kamar yayi hauka haka yake ji,yana cikin wannan yanayin dubara tazo mashi,juyawa ya kuma yi yana kallon roban ruwan,Ruwan ya malale gaba ɗaya kasa ya tattaru a wuri guda,
   Da saurin gaske ya ƙarasa wurin robar ruwan,tare da zubewa saman guiwowinshi,hannu yakai tare da ɗago da robar ruwan ya zaunar da ita ta tsaya tsaye,sannan cikin sauri ya sanya tafukan hannayenshi tare da kwalfo ruwan acikinsu,ya dinga zubasu acikin robar,yana ɗebowa wani na zubewa ahaka ya samu ya ɗan tara kaɗan wanda bai wuce ayi mashi kur6a uku ba ya ƙare,
   ɗaukar robar ruwan yayi da sauri ya koma wurin jahan tare da zuƙunnawa agabansa,sannan yasa hannunshi na dama asaman lips ɗin jahan yana ƙoƙarin buɗe bakinshi,ya rufe bakin gam,hakan yasa Ayaan ya gaza samun damar buɗe mouth din nasa,
  tsoranshi kar ace jahan ya mutu,saboda yayi delaying wurin kawo mashi taimakon gaggawa,
  "Jahan pls,ka buɗe nasamo maka ruwan ka sha!banaso na rasaka ɗan uwana,"muryar shi tamkar zaiyi kuka haka ya dinga rokon shi akan ya buɗe bakin nashi ya sanya mashi ruwan,amma ko motsi wannan baiyi ba,
  hannunshi har kerma yakeyi wurin ɗaga robar ruwan ya kaita saitin idanunshi yana duba rubutun dake ajikinta,larabci ne kuma shi baijin harshen larabci,balle ya gane me aka rubuta ajikinta,
  Ganin zai rasa ɗan uwansa yasa ya ajiye robar ruwan ƙasa,sannan ya daddage da iya ƙarfinshi na ƙarshe ya sanya dukkan hannayenshi biyu ya shiga ƙoƙarin buɗe bakin Jahan,cikin sa'a bakin ya ɗan saki,da sauri Ayaan ya ɗauko robar ruwan tare da kafata a bakin Jahan nan take ruwan ya dinga shiga acikin bakinshi daƙyar daƙyar,wani na shiga wani na fita,ahaka yasamu ya bashi,bayan ya kammala yayi wurgi da robar ruwan gefe guda,sannan ya zauna tare da zabga tagumi yana jiran ganin sakamakon da zai biyo baya,hawaye sai shararo mashi suke a idanunshi,aranshi yana cewa"idan na rasa jahan bansan ya zanyi da rayuwata ba,nima zan bishi ne kawai,"
   Yayi maganar tare da runtse idanunshi yana matse hawayen dake fita daga eyes ɗinshi,
  Kafin Ayaan ya ankare,wannan baƙin hayakin ya soma kurɗaɗowa ta cikin ƙofofin hancin jahan,yarda kasan an koro shi daga cikinsa,haka ya dinga fitowa kafin kiftawar ido,hayaƙin yayi disappearing gaba ɗaya,tamkar bai ta6a existing ba,
    Fitarsa ke da wuya,zufa ta soma tsastsafowa a jikin jahan,kamar an watsa mashi ruwa ajikinshi,haka zufar tashiga feso mashi,a hankali bakinsa ya buɗe ya shiga ambaton"La'ila ha'illallah!
   A wani irin firgice Ayaan ya ware idanunshi sai lokacin ya kalli jahan dake kwance zufa ta gama wanke mashi jikinshi,wani irin farin ciki ne ya cika Ayaan la66ansa har rawa suke yi wurin ambaton sunan shi"ja..jahan"
  Amsa mashi yayi da"Na'am,"
"Alhamdulillah!Alhamdulillah!Allah na gode maka!" Ayaan ne ke faɗin hakan yayin da yakai hannunshi yana tatta6a fuskar jahan dake ƙoƙarin buɗe idanunshi,
    Tunani yazo ma Ayaan aranshi yace tabbas Ruwan cikin robar can ba normal ruwa bane da suka saba sha,akwai wani abu atattare dashi,tun da gashi Yaba jahan yasha kuma ya tashi da irin yanayin daya tashi dashi ɗazu da rana daya sha ruwan,ya tashi yana zufa kuma shima Jahan gashi zufar ce ke fita,hakan na nufin cewa shima Jahan ya warke kenan,
  Ƙarasa tunanin nashi yayi tare da kai goshinsa ƙasa yayi sujjada yana ma Allah godiya,🥰
   Bayan Jahan ya gama farfaɗowa,Ayaan ya taimaka mashi wurin kaishi toilet yayi wanka,nan take yaji wata irin natsuwa ajikin shi,basu 6ata lokaci ba wurin hayewa saman gadonsu,tare da lullu6ewa da bargo saboda baccin da kowannansu ke ji,yau gaba dayansu sunyi bacci cike da kwanciyar hankali,kuma Ayaan Yaci alwashin sai yayi investigation akan wannan robar ruwan da suka sha,

(Banji daɗi da ruwan addu'ar nan ya zube ba,wlh nima ina buƙatar shi don nasha)

Yanayi mara daɗi,a daren ranar Omar ya kwana yana kukan zuciya saboda abunda yayi ƙoƙarin aikata ma Hosana, ya kwana da tunanin wane hali suke aciki?sunyi bacci kuwa?baida amsar tambayoyin shi dole sai inya gansu,gashi baya jin zai iya takawa yaje dubasu saboda fargabar karsu gane cewa shine yayi masu wannan abun kunyar,matsananciyar damuwar daya sa ma ranshi ne da tunane-tunane ya haifar mashi da wani irin severe headache na 6arin kai,yaji jiki adaren nan har magani yasha amma bai sauka ba,a haka ya kwana yana juyi asaman gadonsa,
  Adaren ranar nan dai abubuwa dayawa sun faru masu daɗi da marasa daɗin ji,dama haka rayuwa take ba kullum ake jin daɗin ta ba,idan yau anyi farin ciki,gobe zai iya kasancewa baƙin cikine,idan yau anyi dariya gobe zai iya kasancewa kuka ne,haka rayuwar ke tafiya babu wani yanayi da yake kasancewa permanently,Allah yasa mu dace,yasa mu fi ƙarfin zuciyoyinmu,kuma ya kare mu daga aikata aikin danasani,wasu sun ɗauki rayuwar duniya wani abu,da har suka ɗauke ta da zafi suna aikata abunda suka ga dama,sun manta da cewa acikin seconds za'a iya zare ransu su bar duniyar gaba ɗaya suje su fuskanci abunda suka shuka,duka nawa ne jin daɗin duniyar?basa tuna donme aka halicce su,ta wace ƙopa suka faɗo duniyar nan,taya zasu koma ga mahaliccinsu?daga kai fa sai likkafaninka za'a binne ka cikin ƙabarinka,sai kuma halinka daka je dashi,na gari ne kona banza,😢Allah yasa mu cika da kyau da imani🙏

Wuraren sallar Asuba Sgr ya farka daga dogon baccin daya ɗauke shi,a hankali ya buɗe eyes ɗinshi,yayin da bakinsa ke ambaton addu'ar tashi daga bacci,a kasalance ya miƙe daga kwancen da yake saman doguwar kujerar,mamaki ne ya kama shi ganinshi kwance a palour ɗinsa yana bacci instead of saman gadon shi,ya jima yana mamakin yarda bacci yayi awon gaba da shi adaren jiyan nan,sauko da ƙafafunsa yayi ƙasa,idanunshi suka sauka akan tray ɗin da sehrish ta kawo mashi na dinner ɗinsa da baici ba jiya,tsayawa yayi yana ƙoƙarin tuna abunda ya faru adaren jiya,yunƙurawa yayi tare da tashi tsaye daga saman sofa din ya soma takawa walking slowly,jin sul6in wani abu a ƙasan tafin kafarshi yasa shi yin saurin kai idonshi wurin yana kallo,mamaki ne ya kama shi ganin Mayafin yarinyar nan yashe a kasa,yasan cewa shiya cire mata mayafin amma abunda ya ɗaure mashi kai zaman me gyalenta keyi acikin part ɗinsa?
   russunawa yayi tare da kai hannunshi ya ruƙo gyalen tare da ɗagowa dashi yana kallon shi,sai lokacin ya tuna abunda ya faru jiya tsakanin shi da ita,na commanding ɗinta da yayi akan tayi tsallen kwaɗi,to ina yarinyar take,tambayar daya jefa ma kanshi kenan,
   Cikin sauri ya zagayo ta bayan sofas ɗin tunkan ya ƙarasa ya hangi yarinyar kwance magashiyyan a sume bata motsi,tasha wahala sosai sam baiyi tunanin cewa zata cigaba da yin frog jump ɗin ba,yasan ba komai ne yaja hakan ba face tsananin tsoronshi da take ji,shiyasa bata yi tunanin ta tafi ba,tunda taga bacci yayi awon gaba da shi,
     A hankali ya ƙarasa takawa inda take sannan yaɗan zuƙunna agabanta yana kallon sumar kanta data rufe mata fuskarta,hannu yasa tare da ruƙo gashin kan nata,ya janye mata shi daga saman fuskarta ixuwa gefe guda,
   Zuba ma kyakkyawar fuskarta ido yayi yana kallon yarda tayi jaga jaga da hawaye duk ta yamutse saboda kukan da tasha,idonta sun kumbura,haka la66anta ma sunyi suntum dasu,tsananin tausayinta ne ya kama shi,baiji daɗin baccin daya ɗauke shi ba,da baibari tasha wahalar nan ba,ba da nufin ya cutar da ita yayi hakan ba,kawai yaso ya ɗan hukuntata ne donta kiyaye shi sosai,
    miƙewa yayi tare da nufar wurin fridge ɗinshi,ya buɗe ya ɗaukko bottle water daga ciki mai sanyi,sannan ya dawo inda sehrish take ya cire murfin tare da ɗebo ruwan a hannunshi ya yayyafa mata shi a fuskarta,ruwan na sauka asaman fuskarta,taja dogon numfashi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya,a hankali tashiga mutsu mutsu zata buɗe idanunta,
   "Get up" yace,jin muryarshi yasa sehrish ware idanunta akan sgr dake zuƙunne agabanta,jikinta har kerma yake yi wurin yunƙurawa tare da tashi daga kwancen da take ta zauna,tun kafin taji me zaice ta shiga bashi haƙuri tana cewa"dan Allah ka yafe mun babban yaya,bazan ƙara maimaita kuskuran da nayi....,.'
   Kasa ƙarasa maganar tayi,a firgice ta shiga girgiza mashi kai ganin yadda ya ɗago da hannunshi,duk a tunaninta marinta zaiyi amma sai taga akasin hakan,a hankali ya aza tafin hannunshi a saman lallausar fatar gefen fuskarta,ɗan zaro ido sehrish tayi tana kallon fuskarshi,yayin da shi kuma yake kallon brownish lips ɗinta dake ta faman kerma,
   Almost 5 mins sannan yace"Tashi ki tafi,"ya ambaci hakan tare da zame hannunshi daga gefen fuskarta sannan ya miƙe tsaye hannunshi ruƙe da bottle water ɗin yana maida murfin robar,daddagewa sehrish tayi tare da yunƙurawa daƙyar ta miƙe,aikuwa nan take ƙafafunta suka bada wani irin sauti ƙasss!,a gigice ta saki wata irin razananniyar ƙara nan take ƙafafun suka gaza ɗaukarta,gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa,sai dai ina kafin takaiga ƙasan tuni hannun sgr ya damƙi qugunta kwakkwaran ruƙo yayi mata da hannu ɗaya,gabanta ne taji yayi wani irin bugu daga bisani kuma ta shiga sauke ajiyar zuciya ba ƙaramin tsorata tayi ba,har lokacin hawaye ne ke zubowa daga cikin idanunta,janyota Sgr yayi ta faɗo saman jikin shi gaba ɗaya,sannan ya ɗan russinar da kanshi tare da ɗago da ita,ya sanyata a saman kafaɗarshi,yadda kasan ya ɗauki wannan ɗiyar robar ƴar tsana,haka ya sa6i sehrish asaman shoulder ɗinshi,tafiya ya soma yi ɗauke da ita,ya ƙarasa wurin fridge ɗinshi tare da ajiye roban ruwan dake hannunshi,sannan ya juyo tare da kama hanya ya fito daga part dinshi kai tsaye ya nufi downstairs,ajiyar zuciya sehrish ke ta faman saukewa tayi lamo abunta,yadda take jin daɗin kafaɗar tashi tamkar ta hau Jirgin sama,
   A natse yake taka matattakalar benen ɗauke da ita har ya ƙarasa saukowa da ita cikin Main palour ɗin nasu,bin ko'ina yayi da kallo babu kowa da alama basu kammala shirin zuwa yin sallar asubahin ba,duk da dama lokaci bai ƙarasa yi ba,a lokacin ake ta haramar fara kiran sallan,
Tunani ya shiga yi a ina zai sauke yarinyar,don shi bai ta6a sanin ma a ina yarinyar take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login