Showing 153001 words to 156000 words out of 245004 words
Chapter 52 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
baki ruwan addu'a kiba wannan yarinyar tayi amfani dashi,"
Amsa mashi tayi da toh sir,sannan yaja da baya tare da juyawa ya koma wurin board,
Jiki asanyaye sehrish ta koma tare da zaunawa tana faman sauke ajiyar zuciya,aranta tana mamakin ruwan addu'ar mi zai bama amrish ta bata,gaskiya ni bazanyi amfani dashi ba,lafiya ta lou,koya ban zubarwa zanyi.......'
Sai faman sambatu takeyi ƙasa ƙasa sam takasa samun natsuwa har sai da Malamin yabar Class ɗin,tashi amrish tayi tare da binshi don ta amso mata ruwan addu'ar dayace zai bata.
bayan mai taxi ɗin ya sauke su,hannunshi ruke dana Amal suka shiga cikin gidan,gaba ɗaya duk tabi ta susuce tana kallon katafaren gidan duk a tunaninta kodai gidansu ne ya kawo ta? Lokacin da suka shiga katafaren palourn babu kowa acikin shi,tsayawa yayi tare da ita atsaye yana jiran ganin ko wani zai fito,ita kuwa Amal wuyanta kamar zai tsinke saboda kalle kalle muryar Ayaan ce ta katse ta da cewa"har yanzu ciwon na maki zafi?girgiza kai tayi tare da cewa"a'a babu zafi ina lafiya,"
"Okey,ki ɗan ƙara jira nasan matar gidan zata fito ne,bari na sake kiran layinta,"
Hannu yasa tare da ciro wayarsa yana ƙoƙarin danna ma Amani kira,kunnan shi suka jiyo mashi takun takalmanta kwas kwas,ɗagowa su kayi gaba ɗaya suna kallonta,hannunta na ɗauke da tray da alama kayan breakfast ɗinsu da suka ci na safen nan ta fito dashi daga bedroom ɗinta dake a upstairs,jallabiya ce fara ajikinta ta yafa mayafin akanta,
A hankali take saukowa down stairs sam bata lura da mutane ba,ƙura ido Amal tayi tana kallonta sam takasa gane wacece,juyawa ta danyi tare da kallon Ayaan tana neman ƙarin bayani,a lokacin shima idonshi na akanta yace"baki gane ta ba ko"?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,murmushi yayi tare da cewa"Bari ta matso kusa,"
Gyaran murya Ayaan yayi wanda hakan yasa Amani tayi firgit tana kallonsu,murmushi ta saki ganin Ayaan cikin sauri taƙarasa saukowa daga saman stairs ɗin ta tunkaresu,zuba mata ido Amal tayi tana kallonta tabbas taso ta shaidata amma abunda yayi confusing ɗinta shine,taya zata kasance wadda take tunani tunda saurayin ya kawota gidan tafi tunanin ko Auntynshi ce,
Tunkan Amani ta ƙarasa inda suke,hankalinta yakai ga Amal binta da kallo ta dinga yi cike da mamakin ina Ayaan ya samo wannan yarinyar haka,duk taji jiki kodai ya fara taimakon marayu ne,
tsayawa tayi kusa dasu idonta na akan Amal ita ma kallonta takeyi,ji tayi gabanta na faɗuwa rasss rassss,cikin sauri ta mayar da idonta akan Ayaan murya na rawa tace"who...who is she pls?
Murmushi ayaan yayi yace"i don't even know,ni dai ta bani numbar auntynta ne tace na kira mata ita,shine dana sa numbar Auntyn nata sai sunanki ya bayyana akai,that's why nayi deciding kawota wurinki,maybe adace.........'tunkan ya ƙarasa maganar a firgice Amani ta saki tray ɗin hannunta ya tarwatse ƙasa,zube wa tayi saman guiwowinta kusa da Amal ɗin ta ruƙo hannunta tana cewa"Amal kece dagaske nake gani,ko idona ne Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un,"!!!
Tuni hawaye sun cicciko acikin idonta,
Itama Amal ɗin tuni ta fara shararo hawaye saboda ta ganeta yanzu musamman data ambaci sunanta,
Cikin shessheƙar kuka tace"Ni...Ni ce aunty Amani,ashe dama zan sake ganinki arayuwata.........'kukane yaci ƙarfinta hakan ne yasa takasa ƙarasa maganar,atare suka fashe da kuka suna yi kamar kamar me,
Muryar Ayaan ce ta katse su da cewa"pls Aunty amani,ki lallasheta akwai wounds ajikinta idan tana kuka hakan zai ƙara mata raɗaɗin ciwon,"dakyar Amani ta tsagaita da kukan nata kallon fuskarta har izuwa jikinta,tayi matuƙar tsorata da ganin yarda yarinyar ta tsotse ta rame ta ƙanjame kamar kwarangwal,ƙashin wuyanta kamar zai ballo waje,komai na yarinyar da zai nuna cewa ita macece babu shi,sai dai ta hanyar shigarta ta mata da kuma muryarta,
Janyota tayi ajikinta tare da rungumeta sosai tana ci gaba da ambaton sunanta"Amal amal ɗita ce ta koma haka?meya faru dake Amal ya akai kika 6ata,ki ka tafi kika barni inata nemanki Amal,"
Ganin halin da suka shiga yasa Ayaan yanke shawarar tafiya yabarsu,juyawa yayi kawai tare da kama hanya ya fuce daga falon dama jahan sai doko mashi calling yake,
Anan ƙasa Amani da Amal suka zauna atare suna fuskantar juna,
"Amal kina jin yunwa"? Jin wannan tambayar yasa hawaye suka ƙara cika mata ido,yaushe rabon da wani ya tambayeta tana jin yunwa harta manta Allah sarki ɗan uwa mai ɗaɗi,musamman in ya kasance shaƙiƙin kane kuma kuna son junanku,
Murya asanyaye tace"bana jin yunwa naci abinci a asibiti,"
Jinjina kai Amani tayi tare da cewa"inason jin Ya akai kika 6ata Amal kika barni?mammy ta sanar dani cewa bakyajin magana wai kina zuwa yawo sun hanaki kin ƙiya shine kika 6ace aka neme ki aka rasa....'
Girgiza kai tashiga yi yayin da hawaye ke cigaba da sharara a idonta tace"Aunty amani wannan duk ƙaryace suke yi maki!nagode ma Allah da ya haɗani dake,a yau inaso zan sanar dake komai game da irin cin zalin dasu Mammy sukayimun na raba ni dake,
Hankali tashe Amani ke kallonta murya na kerma tace"faɗamun meya faru dake!wani irin cin zalin su kayi maki,"
Batare da 6ata lokaci ba,Amal ta zayyana mata duk irin ƙarairayin da sukeyi mata akan cewa ta 6ace,da kuma irin wahalar da takesha a hannunsu da kuma kaita da sukeyi gidan makwabtansu ana kulleta,babu abunda Amal ta 6oye mata kaf takwashe ta sanar da ita,
A kiɗime Amani ta miƙe tsaye cikin tsananin 6acin rai,jikinta har kerma yake yi,wasu irin zafafan hawaye ne suka shiga shararowa a idonta,
Sai faman cizon yatsa take yi tana danasani,kai aƙarshe data rasa abunyi sai ta sake fashewa da wani matsanancin kukan tana girgiza kai tana cewa"Wlh bazan ta6a raga masu ba!mugaye azzalumai kawai,banta6a ganin mutane masu zuciyar kafirai ba irin tasu,Sun cutar dake Amal kuma sun cutar dani sun yaudareni sunyi mun ƙarya suna samun kuɗi awurina na cewa za'a ba malamai suyi addu'ar neman sa'a akanki ashe duk ƙarya ne!!!!basu tsaya a iya kanmu ba sun cutar da mahaifiyarmu har saida tabar duniya ga mahaifinmu da suke ta gana ma azaba,nayi tunanin soyyaya suke nuna min ta ƴan uwantaka shiyasa na saki jiki dasu har nake ƙoƙarin taimaka musu wurin cimma wannan mummunan ƙudirin nasu,ashe cutata suke suna can suna gana ma ƙanwata azaba,na cuci kaina!tun yanzu Allah ya fara nunamin irin kuskuren da nake ƙoƙarin yi na taimakama waɗancan bijimayen.......'tsagaitawa tayi da maganar tana faman shessheƙar kuka,daga bisani ta ɗaura da cewa"wlh saina tarwatsa duk wani plan ɗinsu uban kowa ya rasa don bazan kyalesu ba,muddin ina numfashi hayaam ko abra ɗaya daga cikinsu bazai ta6a auran jinin salahuddeen hussein ba!!!!,
abun ba ƙaramin ƙona ma Amani rai yayi ba,ta fusata ainin zuciyarta har wani tafarfasa take yi saboda 6acin rai,
Hannu tasa tare da matse kwallarta sannan ta juya tare da takawa takai hannu ta ruƙo hannun Amal ta miƙar da ita tsaye,sannan ta wuce da ita cikin bedroom ɗinta gado ta nuna mata tare da cewa"Amal ki kwanta ki huta kin raunata sosai,amma karki samu damuwa tunda Allah ya haɗaki dani ƙarshen wahalar ki tazo insha Allah,zakiyi rayuwa tare da Auntynki zan baki kyakkyawar kulawa,kuma zan kira doctor domin ya ƙara dubamin lafiyarki da kyau har kiji sauƙi,
Ba ƙaramin daɗi Amal taji ba farin ciki har bakinta ya gaza rufuwa,sai da amani ta tabbatar cewa Amal ta kwanta sosae saman gadon sannan ta zauna daga gefen gadon tana kallonta har bacci yayi awon gaba da ita,amani bata bar wurin ba,kallonta take hawaye na zuba a idonta haƙiƙa su Mammy da Aunty babba ba ƙaramin cutarta su kayi ba,
Jinjina kai tayi tare da cewa"rama cuta ga macuci ibada ne,Aunty laila kin shiga uku dani,zanbi duk hanyar da zanbi don ganin na tarwatsa plan ɗinki,dama ke jani talau ce sai yarda akai dake sannan kike bi,zanyi amfani da wannan damar wurin lalata shirinki"
Haka Amani ta dinga tufka da warwara a ƙarshe ta shirya nata plan ɗin.
****************
Hayaam na zaune saman gadonta hannunta ruƙe da wayarta tana jiran shigowar kiran Sofwan,harta fidda rai da zai kawo mata trolley ɗin sai ga message ɗinshi ya shigo wayarta,cikin sauri ta buɗe tana karantawa,
_hi beb ya kike ya kwanan gidan surukai ina fata kina lfy,nafa zo gidan ki turo wani ya amsar maki trolley ɗin kayan,don bazasu bar ni nashigo ba_
Jin hakan yasa tayi saurin saukowa daga saman gadon tare da ɗaukar dogon hijabinta dake ajiye saman gadon,zurawa tayi ajikinta sannan tafito daga cikin bedroom ɗin,kama hanya tayi ta fito main palour ɗin tana wurga ido don tasamu wanda zai kar6ar mata kayanta,tana cikin wannan tunanin sai ga Fawan ya fito daga part ɗinsu,
kwala mashi kira tayi cike da kisisina tace"Fawan"!
ɗagowa yayi yana kallonta da wannan kallon nashi na rainin wayau,
cikin sauri hayaam ta nufe shi sai da tazo kusa dashi sannan tace"dan Allah taimako nakeso kayimun,wani brother ɗina ne ya kawo mun trolley ɗin kayana,an hanashi shigowa ciki shine nace ko zaka taimaka ka amso mun,"
Yatsina fuska fawan yayi tare da cewa"Am sorry ni bazan iya wannan wahalar ba,zan dai kira ɗaya daga cikin security guards ɗin na basu umarnin su barshi ya shigo abokina ne inyaso sai kije ki kar6o kayanki,"
washe baki hayaam tashiga yi tana cewa"thank u so much fawan,kana da mutunci sosai naji daɗin taimakonnan da kayimun,' ɗan ta6e baki fawan yayi tare da kai hannu ya ciro wayarshi a aljihun rigarshi,call ya buga tare da kara wayar a kunnanshi,ɗaga kiran akayi sannan ya sanar dasu cewa subarshi ya shigo abokinshi ne,amsa mashi sukayi sannan ya kashe kiran,
batare da ya kalleta ba yace"kije ki amso kayanki,"
da hanzari Hayaam ta juya tare da kama hanyar fucewa daga falon sai faman sauri take yi kamar zata tashi sama,
Ruƙe ƙugu fawan yayi tare da cewa"Ikon Allah,nifa bangane ma Yarinyar can ba,Naji tana cewa zata amshi trolley ɗin kayanta me hakan ke nufi"?ya jefa ma kanshi tambaya,cizon la66ansa yayi tare da cewa"zaki gane kuranki ne,"yana faɗin hakan ya kama gabansa
*💋Boss Bature💋*
Wuraren ƙarfe 1:30 junaid ya ɗauko sehrish daga school,tun acikin mota ya lura da yanayinta duk a yamutse babu natsuwa a tattare da ita,har tambayarta yayi ko bata jin daɗine,sai ta sanar dashi cewa bacci ne kawai take ji,jin haka yasa ya ƙara gudun motar har suka ƙaraso cikin gidan,
Fitowa tayi daga cikin motar tare da komawa ta buɗe back seat ɗin ta curo school bag ɗinta sannan ta wuce cikin gidan da sauri,
Abun ya ɗaure ma junaid kai,ganin ta tafi batare da ta jirashi ba kamar yarda suka saba shiga cikin gidan hannunsu ruƙe dana juna,
hannu yakai tare da buɗe motar ya fito bayan ya rufeta,ya kama hanyar shiga interior ɗin gidan,koda ya shiga main palour ɗin kai tsaye ya wuce upstairs bedroom ɗinshi don shima a gajiye yake,
wani irin zazza6ine ya rufar mata,dama tun lokacin da suka haɗa ido da wannan malamin taji gaba ɗaya yanayinta ya sauya,tana shiga bedroom ɗinta tayi wurgi da school bag ɗin ƙasa,sannan ta faɗa saman gadonta tare da kwantawa tana faman juyi asaman shi,
A wannan yanayin bacci yayi awon gaba da ita,
Turo ƙopar bedroom ɗin nata junaid yayi anan ya same ta tana ta faman sharar bacci ajiyar zuciya ya sauke tare da juyawa zai fuce daga ɗakin karaf idonshi suka sauka akan Bottle water ɗin da malamin nan yaba Amrish takai mata,ashe lokacin da ta shigo ɗakin tayi wurgi da jakar nan take robar ruwan ta gangaro daga cikin jakar,saboda ta manta bata rufe zeep ɗin wurin data sanyata ba,
Murmushi junaid yayi yace"Oh ni reeshi kamar wata ƙaramar yarinya,wai yawo da robar ruwa acikin school bag hmmm,"yayi maganar tare da ƙarasawa yakai hannu ya sungumi robar ruwan,
Jin salaf babu sanyi ajikin robar ruwan yasa shi cewa"bari naje na sanya mata shi a fridge,zai fi daɗin sha,"
Yana ƙarasa maganar ya juya tare da fucewa daga ɗakin nata,kai tsaye ya wuce wurin fridge ɗinsu,hannu yakai tare da buɗewa ya sanya robar ruwan aciki,sannan ya mayar ya rufe ya kama hanya yabar wurin,
After some minutes sai ga su twins sun faɗo cikin main palour ɗin dawowarsu kenan daga masallaci,raba hanya su kayi Jahan ya wuce bedroom ɗinsu,shi kuma Ayaan ya wuce wurin fridge saboda wani irin ƙishin ruwa da ta zo mashi,hannu yasa tare da buɗe fridge ɗin,ya ɗauko bottle water ɗin da Junaid ya ajiye,
Buɗe murfin yayi tare da kafawa abakinshi ya shiga ɗaɗɗakar ruwan,sai da yayi rabin robar ruwan sannan ya mayar da ita cikin fridge ɗin ya ajiye,
Shafa ƙirjinshi yayi tare da cewa"Alhamdulillalh yanzu naji wani sanyi ya ratsa maƙoshi na,"
Yana faɗin hakan ya nufi bedroom ɗinsu,lokacin daya shiga samun Jahan yayi kwance yana jiranshi ya ƙaraso,
ɗaga kafar da zaiyi kenan yaji gaba ɗaya jikinshi ya shiga jijjiga ta ko'ina,ganin hakan yasa jahan tashi daga zaune yana cewa"lafiya Ayaan meke faruwa ne!!
A wani irin galabaice Ayaan ya zube saman guiwowinshi yana ambaton sunan Allah abakinshi,kafin Jahan yayi wani yunƙurin durowa daga saman gadon tuni ayaan ya yanke jiki ya faɗi kasa abaje idonshi na kallon ceilling yayin da launin idanunshi suka 6ace 6aat sai farar kwayar idon,
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un," jahan ne ya ambaci hakan a lokacin da ya ƙarasa durowa daga saman gadon ya ƙaraso a hanzarce inda Ayaan yake,
ya zube saman guiwowinsa agabanshi,hankali atashe yake ambaton sunan shi
"Ayyaaan!!!Ayaan dan Allah ka tashi!meke faruwa dakai ne rabin raina!!.,....'
ganin bai da wata mafita yasa ya miƙe da gudun gaske ya fuce daga ɗakin nasu don yaje ya sanar ma wani,
Fitar Jahan ke da wuya,wani siririn hayaƙi baƙi wulik ya dinga fitowa daga ƙofofin hancinshi da kuma bakin shi,da yawan gaske hayaƙin ke kurɗaɗowa ya mamaye ko ina,kafin wani lokaci ya disashe tare da 6ace wa 😳😳😳
*SANARWA SANARWA*💃💃💃💃
*ME TAKEN NA AMARYA HUTAA$$*
*MUNA FARIN CIKIN SANAR DAKU CEWA MUNA BADA HAYAR KAYAN AMARYA(WEDDING GOWN), KAYAN BRIDAL SHOWER, KAYAN BIRTHDAY PARTY, KAYAN FITAR SUNA, SANNAN MUNA BADA HEAD AND SHOULDER, MUNA DA POSS, MUNA ALKYABBAR KAI AMARYA KO TARON WALIMAR SAUKA, MUNA DA KAYAN FULANI FARARE NA YARA DANA MANYA MUNA DA NA AMARYA BLUE BLACK, SANNAN MUNA GYARAN JIKIN AMARYA DA UWARGIDA CIKIN KWANA UKU CAKAL ZAKIGA KIN KOMA TAURARUWA MAI WALWALI. MUNAYIN TURARUKAN WUTA DA HUMRA DA KOLACCAR, KOWANNE KALA KIKE BUKATA AKWAI CIKIN FARASHI MAI SAUKI.*
*LOCATION KANO*
08062073990
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727._💋Boss Bature💋_
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖
Am really sorry 4 the late post👌
Wata irin zufa ce ta soma tsastsafo mashi a jikinshi kamar wanda aka tsamo daga cikin ruwa,lokaci guda yashiga Sakin atishawa yafi talatin a jere suke fitowa daga bakinshi,daga bisani kuma a hankali launin kwayar idonshi ya bayyana,komai nashi ya dawo yarda yake,ganin shi kwance a ƙasa yasa shi yin hanzarin miƙewa tsaye yana tunanin wai menene yakai shi ƙasa kwance?me ya faru dashi ne?hannu yasa yana shafo zufar dake a gefen fuskarshi har lokacin bata daina zuba ba,hakan yasa ya nufi toilet tare da shigewa ciki don yayi wanka,
Bai jima da shiga ba sai ga Jahan ya faɗo ɗakin yana atare da kanal yousouf,tsayawa su kayi abakin ƙopar ɗakin,Jahan na mamakin Ina ayyan daya bari cikin wani hali yashe a ƙasa
Kallon shi kanal yousouf yayi tare da cewa"Kace mun Ayaan ya faɗi ƙasa jikinshi na kerma,gashi kuma ni banga Ayaan ba,"
Fuskarshi aruɗe yace"Ya yousouf nikaina abun ya ɗaure mun kai,nan fa nabarshi kwance cikin wani yanayi yanzu kuma babu shi a wurin," jin hakan yasa hankalinsu tashi su duka biyun,
tsayawa su kayi kowa da abunda ranshi ke bashi,suna cikin tsayuwar nan sai ga Ayaan ya buɗe ƙopar toilet tare da fitowa jikinshi ɗaure da towel,ga danshin ruwan dake ajikinshi alamar wanka yayi,abun ba ƙaramin ɗaurewa jahan kai yayi ba hatta kanal yousof ɗin,shi kuwa hankalinshi kwance har zai gifta ya hangesu tsaye ta wutsiyar idonshi,hakan yasa ya ɗan ja da baya tare da juyawo yana kallon su,cike da mamaki yace"Ya yousouf!Jahan!meya faru naganku a tsaitsaye kunyi curko curko?ko lafiya,"?
ajiyar zuciya jahan ya sauke tare da tunkarar shi kai tsaye ya rungumo shi ajikinshi yana ɗan bubbuga bayanshi yace"babu komai ayaan,nashiga damuwa ne ɗazu dana ga ka yanke jiki ka faɗi nayi tunanin kowani mummunan abune zai faru dakai that's why nayi deciding kiran ya yousouf don yazo ya duba min kai," ya ƙarasa maganar tare da raba jikinshi daga na Ayaan,
"Nifa lafiyata lou,babu abunda ya faru dani,kawai jiri ne ya ɗan ɗebe ni but now Alhamdulillah har wani ƙarfi nake ji ajiki na,ko in gwada maka ka gani," yarda yayi maganar tare da ɗaga masu damtsen hannunshi ba ƙaramin dariya ya basu ba,girgiza kai kawai kanal yousouf yayi tare da juyawa ya fuce daga ɗakin,
wucewa Ayaan yayi ya nufi mirror,cikin sauri Jahan ya bishi tare da hugging ɗinshi