Showing 129001 words to 132000 words out of 245004 words

Chapter 44 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download

17 Mar 2025

25242

makamancinshi duk da nasan cewa zaiyi wuya nasamu kamar shi," hannu takai tare da janyo drawing book ɗinta,ɗago da kanta tayi ta zuba ma zanen fuskar junaid ido tana kallon kyakkyawan murmushin nan nashi,
  Nan take taji wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta,hannu tasa tana shafa zanen,tana ci gaba da kallon shi,kamanceceniyar su da Marshal omar har taso tayi yawa,saboda junaid fuskar Abbansu ce sak,kuma marshal omar yana ɗaya daga cikin masu kama da abban nasu sosai,hakan yasa kamarsu ta fito sosai,
     (Tashin hankali,son maso wani,junaid nason sehrish,ita kuma Rafayet takeso,yayin da shi kuma rafayet har yanzu baisan menene So ba,ga kuma jahad tafara faɗawa tarkon junaid,Ya kenan?)
  A ƙarshe Ina taya Hossana murna,dama bai cancanta tasha wahalar soyayya ba,kasancewarta mai ta6in hankali,in har bata samu abunda takeso ba,to fa acan dawanaun kano zamu tsinto ta,amma duk da hakan kuna tunanin cewa Zasu samu Juna cikin sauƙi ita da marshal Omar!???????????

Tuni su Hayaam sun jima da barin maid suna kan hanyarsu ta zuwa Abj,kafin ta bar gida sai da Mamynsu ta haɗata da magungunan data amso mata a wurin bokansu,kala kala wanda zata yi amfani dasu na mallaka,akwai na shafawa ajiki,da wanda akeyin turarensa,da kuma na zubawa acikin abinci ko abunsha wanda za ta zuba ma Sgr,tsaf ta kammala shirya komai saura aikatawa kawai ya rage,
(Nace ba, Allah ya ba mai rabo sa'a)
jin shiru babu kowa acikin gidan ya ba Amal damar tashi daga saman katifar da take kwance tana jinya tun jiya,ba ƙaramin jiki taji ba baiwar Allah,tazama abun tausayi ga yunwa ga ciwo ga kuma rashin wanka,
dakyar ta iya fitowa daga cikin ɗakin adaddafe take tafiya,tsayawa tayi tana tunanin mai yakamata tayi,
Babu kowa a tsakar gidan,tun bayan da Sofwan yazo ya ɗauki Hayaam,Mammynsu da Abra suka fita rakiyarta daga can kuma suka wuce gidan makwabtansu,gidan da suka saba zuwa zaman kashe buje,daga kaga mata sun taru agidan toh fa tsegumi ne da gulma yakaisu,tun daga kan sunan matar gidan zakasan cewa ba ƙaramar guyababba bace,suna kiranta tsigai acan suke kai Amal wurinta in Amani tazo,su rufe ta aɗaki don karsu haɗu da ƴar uwarta,
Shiru Amal tayi tana tunanin abunda ya dace tayi tunda babu kowa agidan yanzu lokaci ne da yakamata ta yanke shawarar yarda zata haɗu da ƴar uwarta,
Cikin sauri ta nufi ɗakin Mammynsu abrah gabanta na faɗuwa tsoranta karsu shigo su tarar da ita,a hankali tasa ƙafa ta shiga cikin ɗakin nata,tsayawa tayi tana faman waige waigen inda zata samu koda waya ce,
Karaf idonta suka sauka akan kuɗaɗen dake baje saman gadon Mammynsu,sabbin ƴan dubu dubu,da alama mantasu tayi a wurin bata kwashe su ba,
nan da nan tunanin Amal ya kasu kashi biyu,
"Amal kina buƙatar kuɗin da zaki je wurin Auntynki!wannan dama ce agareki,yakamata kiyi hanzarin kwashe kuɗin nan kafin su dawo,ki tattara kibar masu gidan,Amal kada ki bari damar nan ta wuce ki!!!ki je ki ɗauka!ki ɗauka mana!Amal ki tafiiiii!!!!!!!"
zazzare ido tayi lokacin da taji abunda zuciyarta ke sanar da ita,
Wani tunanin kuma ya sake zuwa mata
"Amal kada ki ta6a kuɗin nan!wannan sata ce,in kika ɗauke su Allah zai kamaki!ki hanzarta barin ɗakin nan tunkafin kiyi danasanin zuwan shi!kiyi haƙuri kibarma Allah komai mai wuce wa ne,"
Runtse ido Amal tayi yayin da idanunta ke fitar da hawaye masu zafin gaske,
"Ni ba 6arauniya bace,bazan ɗauka ba,saboda bana son Allah ya kama ni da laifin sata," cikin shessheƙar kuka ta furta hakan abayyane,
Sannan jiki asanyaye ta kama hanyar fita daga ɗakin,har tasa ƙafa zata fita daga cikin ɗakin,kwatsam kwakwalwarta ta soma tariyo mata wani abu daya ta6a faruwa,a lokacin Mammy tayi ma Amani ƙaryar cewa za'a je nemo Amal,amma ana buƙatar kuɗi saboda za'a haɗa da manyan malamai domin suyi addu'ar neman dace wa,jiki na rawa Amani ta turo da kuɗi kusan dubu ɗari uku acikin acct ɗin Abra da niyyar akaima malam kuɗin don suyi addu'a akan lamarin,A ranar da abra ta ciro kuɗin a banki,tunkafin tadawo gida ta wuce kasuwa tayi masu siyayar kaya masu yawan gaske,
ƙiri-ƙiri suka hana Amal ko sisi acikin kuɗin nan,kuma ita mammy da kanta ta kira Amal tare da jan kunnanta ta janyota har cikin ɗaki ta nuna mata kuɗin da Amani ta turo da kuma kayan da suka siya saboda rashin imani, aranar Amal tasha kuka sosai,
Cike da ƙwarin guiwa Amal tace"Bazan bar kuɗin nan ba!haƙƙina ne su!nima sunci mun kuɗina,"
Cikin sauri ta juya tare da nufar cikin ɗakin,kai tsaye ta tunkari gadon Mammyn tasu,hannunta na kerma zufa na tsastsafo mata a fuskarta,haka tasanya hannu tare da tattara kuɗin gaba ɗaya ta haɗesu guri guda acikin hannunta,a ƙalla sunyi dubu hamsin,
kamar daga sama taji motsin wani ya faɗo acikin ɗakin,a wani irin firgice Amal ta watsar da kuɗin tare da juyawa tana kallon bakin ƙopar shigowar idonta azazzare~~~~~~~~~~

Wannan kenan

Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku
Ina kuke mata hamshakai wayanda suka amsa sunan su wajen mazajen su ina mata masu son qamshi shin ko kunsan tsafta bata tafiya seda qamshi ina masu son turare mai riqon gida tareda qamshin shi mai sanyaya zukata mardie collection tazo muku da dadadan turarukanta masu lasting riqon gida harma da jiki ku tuntube mu da nmb kamar haka 08136666994 inda zaku samu kaya kamar haka
Wadrobe balls
Madarar kulleccham
Vaseline kulleccham
Kajiji
Halut
Couscous
Khumrah
Da dai sauransu harda abin wanke toilet yayi tas komi dafe warshi wato BETHALEX METAL ku garzayo kar ayi baku

It's not just good ...it's finger linking good faster than fast food, better fine dining.
Snack
Awarah
Farah
Zobo
Samosa
Cup cake etc
Contact me 09063302182or 09012179727.
Kada abaku labari

********************** ⬇ **************************
********** Ai Hausa Novels ****************
*************************⬆ **********************

DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog.

Visit > https://www.aihausanovels.com.ng

Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post.

Email > aihausabooks@gmail.com

******* FOLLOW US ******

Facebook: Ai Hausa Novels

Twitter: Ai Hausa Novels

Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels

WhatsApp Number: 08138873799


Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafin ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu.

********************** ⬇ **************************
*************** Ai Hausa Novels ****************
********************** ⬆ **************************

_💋Boss Bature💋_


Join this link to follow my tiktok acct👇

https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1



Lokaci guda Amal ta sauke nauyayyar ajiyar zuciya,ashe magen hayam ce ta faɗo ɗakin,sai faman kuka takeyi miyauu miyauu,da alama yunwa take ji ne,Batare da 6ata lokaci ba Amal ta zuƙunna ta shiga tattara kuɗin da sauri da sauri jikinta na kerma,don a matuƙar firgice take saboda magen nan data tsorata ta,
  Miƙewa tayi hannunta ɗauke da kuɗin cikin sauri ta fice daga ɗakin,komawa tayi cikin ɗakinsu hayamm,jiki na rawa ta buɗe wardrobe ɗin kayansu,doguwar riga ta ɗauko ta Abra tare da mayafinta,
A hanzarce ta shiga zura rigar ajikinta,ba ƙaramin yawa rigar tayi mata ba har ƙasa take ja,ga wuyar rigar da yayi mata yawa,yafa mayafin tayi,
  Sannan cikin sauri ta fito daga cikin ɗakin,a nan waje ƙopar ɗakin ta ɗauki slippers tare da zura wa aƙafarta,
   Jiki na kerma AMAL ta kama hanyar fucewa daga cikin gidan,sai da takai baƙin ƙopar fita sannan ta ɗan tsaya tare da juyawa tana kallon cikin gidan yayin da hawaye ke shararowa daga idonunta,bazata ta6a mantawa da irin uƙubar da tasha acikin gidan ba, ta dan jima a haka,daga bisani tasa kai cikin sauri tabar gidan,
   Kamar walk'iya haka Amal tabar santar gidan gaba ɗaya,duk da bata jin kwarin jikinta,haka ta jure ta kama hanyar sauri sauri gudu gudu,ita kanta batasan ina zata dosa ba,amma tana da tabbacin cewa tasha zata nema domin ta hau motar zuwa Abuja,
...(Finally Amal taci nasarar barin gidan,saura fatan sauka lafiya)

*****************
Sosai jahan ke ta faman sakin dariya cike da nishaɗi,bakomai yasa shi dariya ba face Ayaan dake zayyana mashi irin halin daya shiga na barazanar da haroon ke masu,hankalin su kwance basu da wani sauran damuwa,suna a kwance cikin hotel room ɗinsu,basu jima da fitowa daga wanka ba,kowannansu na sanye da white shorts ajikinshi,suna rungume da juna cikin lallausan bargo,
  "Wlh jahan naji jiki sosai,wai ashe haka abun yake?sai gani a sume,gaskiya haroon ba ƙaramin shaiɗani bane,nasha Wahala a ranar nan,"
     "dama kai rago ne Ayaaan,nafi ka juriya shiyasa abun yazo maka ahaka,ranar naji kishi da baƙin ciki sosai,har yanxu in na tuna abun ba ƙaramin ƙuna zuciyata ke yi mun ba,"acewar jahan,
   "Pls ni banaso muna tuna abunda ya wuce,hakan zai iya sanya mana damuwa acikin zuciyoyin mu,mubar maganar kawai,"
  Jahan yace"shikenan mu bar maganar amma inaso na tambayeka pls,yanzu kwatsam a lokacin nan da ace bamu ba haroon kuɗin nan ba,ya saki videon mu a social media har Abba da babban yayanmu suka gani,me kake tunanin zai biyo baya,"
  Da wasa jahan yayi maganar amma har sai da zuciyar Ayaan ta ɗan buga,
   "Abunda zai faru shine,zuciyar Abban mu zata buga anan take ya yanke jiki ya faɗi,babban yayan mu kuma zai yi mana bugun mutuwa,abunda ba'a fata kenan,"Ayaan ya ƙarasa maganar yana dariya,
    Shima jahan dariyar yayi yana cigaba da sauraron shi kafin daga bisani suka ɗaura daga inda suka tsaya,"
  
**************Sehrish

Tun bayan da tadawo cikin bedroom ɗinta,wanka tayi tare da ɗauro alwala,bayan ta kammala sallar,ta koma wurin wardrobe ɗinta,ta ciro kayan da zata sanya,dogon wando ne na roba,Army trouser tun lokacin da suka je siyayya,ta ɗauke shi saboda ba ƙaramin burgeta kayan sojoji suke yi ba,tare da farar shirt off shoulder ta zura ajikinta,ba ƙaramin kyau tayi ba,komawa tayi gaban dressing mirror ta ɗauki turarenta tabi ko'ina na jikinta ta feshe shi,wuri ta samu saman chair ɗin da ke a front ɗin madubin,ribbom ɗinta ta ɗauko tare da zura shi a hannunta,yau taci alwashin saita ɗaure gashin kanta,
da iya ƙarfinta na ƙarshe ta tattare gashin ta haɗo shi wuri guda,tare da zura ribbom ɗin ta ɗaure shi sosai,ya sauko a gadon bayanta,

   Murmushi ta saki tana kallon kanta acikin mirror ɗin kafin daga bisani ta miƙe tare da wuce wa gaban gadonta,within 15 mins ta kammala gyara bedroom ɗinta,komawa tayi tare da hayewa saman gadon,takai hannu ta ɗauko wayarta dake ajiye saman side drawer,
   Wi-fi ta kunna nan take messages ɗin whatsapp dinta suka soma shigowa acikin wayarta,shiga whatsapp grp tayi na school ɗinsu,new student ne ke ta introducing ɗin kansu tare da pics ɗinsu,tunani ta soma yi bata da hoto ko ɗaya,gashi tana buƙatar pictures saboda ita ma tayi nata introduction din,
   tana cikin wannan tunanin kiran junaid ya shigo wayarta,cikin sauri tayi picking tare da karawa a kunnanta,
  Tun kafin tayi sallama yace"yunwa nake ji,"yana faɗin hakan ya katse kira,murmushi Sehrish tayi tare da cewa"shagwa6a66e kawai"
  Ajiye wayar tayi saman pillow sannan ta miƙe tare da saukowa daga saman gadon,sam ta manta bata yafa mayafi ba,saboda saurin da take yi nata kai mashi tadawo don tayi pictures din,takalmi kawai ta zura a ƙafarta,sannan ta buɗe ƙopar ta fita,
  A natse take tafiya hanyar kitchen ta nufa,wayam babu kowa a main palour ɗin da alama duk suna cikin bedroom ɗinsu wasu kuma sun fita,
   Batare da 6ata lokaci ba ta haɗo mashi cornflakes tare da snacks acikin tray,kai tsaye ta wuce upstairs bedroom ɗinshi,
  Tsayawa tayi tare da yin knocking ƙopar bedroom ɗin nashi,
  daga ciki tajiyo muryarshi yana cewa"a buɗe take fa,just come in,"
  a hankali ta tura door din tare da shiga cikin ɗakin nashi,
  yana tsaye agaban mirror waist ɗinshi na ɗaure da farin towel da alama fitowarshi kenan daga wanka,
   ƙarasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table din dake kusa da gadon shi,
   Juyowa junaid yayi daga gaban mirror ɗin da yake,zuba mata ido yayi yana kallon bayanta,wandon jikinta ba ƙaramin fidda mata shape ɗin jikinta yayi ba,
  takawa yayi a hankali ta bayanta ya tsaya sannan yakai hannunshi tare da ruƙo lallausan sumar kanta,a firgice Sehrish ta juya tana kallon shi,sakar mata wannan kyakkyawan murmushin nashi yayi,
  A hankali ta ambaci sunan shi"junaid"!
  bai amsa mata kiran sunan shi da tayi ba,sai cewa yayi"reesh ina mayafin ki yake ne"?
   Sai lokacin ta tuna cewa bata yafa komai ba ajikinta ta fito,
   "Mantawa nayi ban sanya ba,"ta bashi amsa tana kallon fuskarshi,
  "Kinyi kyau sosai,but pls kada ki ƙara fitowa haka batare da mayafinki atare da ke ba,"ya ƙarasa maganar cikin sanyin murya,
  Har lokacin bai saki wutsiyar gashinta ba daga hannun shi,sai faman murza gashin yake acikin hannun shi,
  Sakin gashin yayi tare da zagayawa da hannun shi ta bayanta,ya zame ribbom ɗin dake akanta,nan take sumar kan ta tarwatse abayanta,duk tana tsaye tana kallon shi batare da ta hana shi ba,
   tura hannunshi yayi acikin lallausan gashin kan nata,wasa ya shiga yi mata dashi,ganin abun nashi ba mai ƙarewa bane yasa tace"junaid wai menene haka?kamar wata ƴar baby ka kama mun sumar kai sai murzawa kake yi,"
   Murmushi yayi tare da cewa"kwarkwata nake son cire maki,don nasan baza a rasa su acikin kan nan naki ba,abunda baki sani ba su suke saki yawan mantuwa,"
  Buge hannun shi tayi tana dariya tace"wlh ka 6aci da ƙarya junaid,bansan waya koya maka ƙarya ba,"
  tayi maganar tare da wuce wa tana nufar hanyar fita daga ɗakin,cikin sauri yakai hannu tare da ruƙo nata acikin nashi yace"pls kada ki tafi,ki tsaya na kammala lunch ɗin mana,inyaso sai mu fita atare,
    Batare da musu ba tace"bazan tafi ba amma zan fita daga waje,idan ka kammala sanya kayan saina shigo,"
    ƙarasa maganar tayi tare da fucewa ta tsaya daga waje tana jiran shi,
Shaf shaf ya kammala shirya wa cikin jeans da t shirt,sannan ya samu wuri daga gefen gadon ya zauna tare da kwala mata kira,
   dawowa ciki tayi tare da takawa zuwa gefenshi ta zauna,

   "Sehrish inason magana dake,"

Yanayin yarda junaid yayi mata maganar da wata irin kasalalliyar murya yasa ta jin faɗuwar gaba batare da sanin dalilin hakan ba,
     Cikin sauri ta juyar da fuskarta tana kallon cikin idanunshi tace"menene junaid"
  ƙara matsawa yayi kusa da ita,fuskarsu ta kasance a kusa data juna,numfashinsu har harhaɗewa yake dana juna don ƙiris ya rage tsinin hancin shi ya ta6a nata,hakan ba ƙaramin tsorata sehrish yayi ba,tun da take arayuwarta bata ta6a ganin fuskar junaid da irin wannan yanayin ba batare da Murmushi ba,sam babu murmushin nan a fuskarshi,
  Cikin en ina sehrish tace"..junaid wai menene haka?me yake faruwa ne"?
  Lumshe kyawawan idanuwanshi yayi tare da sake buɗesu a hankali ya furta"I LOVE U REESH,I wanna be with u,for the rest of my life," in serious matter junaid yayi maganar,amma sai Sehrish ta fashe.da dariya kamar kamar me,
   Mamakine ya kamashi ganin tana yi mashi dariya,
  Miƙewa tayi daga saman gadon nashi tana ci gaba da yin dariyar,dakyar ta tsagaita tare da kallon shi tace"gaskiya junaid ka iya wasan kwaikwayo,wlh ni har gabana ya faɗi duk atunanina wani abun kirki ne ashe zolayar taka ce ta motsa,"
  Hankali atashe junaid ya miƙe tsaye yana kallonta yace"reesh nifa ba wasa nake maki ba,inason bayyana maki irin tsananin son da nake maki ne,"
   Muryarta ƙumshe da dariya tace"wlh junaid da ace kai actor ne acikin film ba ƙaramin ƙayatarwa zaka yi ba,saboda ka iya tsara wasan kwaikwayo,"
   Tana kai ƙarshen maganarta,ta kama hanya da sauri ta fuce daga cikin ɗakin nashi tana ƙarashe dariyarta,
  Jiki a mace junaid ya koma tare da zaunawa saman gadon,
   jinjina kai yayi tare da cewa"tashin hankali!ashe irin kallon da sehrish keyi mun kenan!yanzu taya za'ae na bayyana mata irin yarda nake ji a game da ita?
  Ya jima yana wannan tunnanin aranshi kafin daga bisani ya mayar da idanunshi akan cornflakes ɗin da ta haɗo mashi,. 
  A sanyaye yakai hannu tare da ɗaukar spoon ɗin dake acikin cup din,ya fara ɗebowa yana kaiwa bakin shi,

adai dai lokacin da Sehrish ke gabda shiga Corridorn da ɗakinta yake Sgr ya fito waya kare a kunnan shi,da alama waya yake yi,karaf idonshi ya sauka akan bayanta wanda lallausar gashin kanta ke baje har wurin ƙugunta,don bata maida ribbom din da junaid ya cire mata ba dama dakyar ta ɗaure shi ɗaxu,ƙarasa fitowa yayi slowly ya dafa handrail da hannunsa guda har lokacin yana amsa wayan da yake yi, yayin da blue eyes dinsa ke bin bayanta da kallo, ba komae ne ya ja hankalin shi ba face Army trouser din dake jikinta don ba ƙaramin kyau yayi mata ba dama kuma favorite color dinsa ne......

_💋Boss Bature💋_

Wuraren biyu na rana hossana tafarka daga dogon baccin daya ɗauketa,miƙewa tayi daga kwancen da take asaman sofa,sai faman hamma takeyi tana murza idanunta, a hankali ta ware idanunta tana neman Omar da bacci yayi awon gaba dasu,wayam tagani babu shi alamar ya tafi bataso hakan ba, dakyar ta iya tashi daga saman sofa din,tana tafiya a hankali saboda jirin da take ji,ga wata irin Yunwa dake cin ta,

Bedroom ɗinsu ta shiga,a nan ta samu jahad zaune saman darduma ta jima da kammala sallar Azhar,amma bata bar saman sallayar ba,tana zaune zugum tana tunanin duniya,
Jin alamar tafiyar mutum yasa ta juyowa tana kallon hossana dake tunkarato,
Ƙarasawa tayi wurin jahad tare da zuƙunnawa kusa da ita tace"jahad ashe ya omar ya tafi bai tashe ni ba,ko sallama ba muyi ba,"murya a kasalance ta ƙarasa maganar,
murmushi jahad tayi tana kallon fuskarta tace"kada ki damu,in dae ya Omar ne zaki iya ganin shi da anjima ko da daddare ma,"
Ta ƙarasa maganar tare da cewa"ko kina jin yunwa ne?naga kina ta hamma"
"E inaji sosai,'ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login