Showing 180001 words to 183000 words out of 245004 words
Chapter 61 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
hawaye ke cigaba da zuba a idanunta,
shiru Sgr ya ɗanyi na wani lokaci batare da ya motsa ba,hakan yasa ta fidda rai da cewar zai yafe mata,
Hannu tasa tana sharar hawayenta tana kallon bayanshi,cigaba da tafiya sgr yayi kai tsaye ya tunkari wurin dressing mirror ɗinshi,hannu yasa tare da janyo drawer chest din dake ajikinshi,sabon scissors ya ɗauko cikin ledarshi, ya fiddo dashi yana kallonshi,
lokacin daya juyo hannunshi ɗauke da almakashin nan,hankali atashe sehrish ta zaro ido tare da miƙewa tsaye daga kneel down ɗin da tayi tana ja da baya tana girgiza mashi kai,alamar karyayi mata haka,
Gadan gadan Sgr ya tunkare ta,hannunshi ɗauke da almakashin nan sai faman salƙi yake yi,hannu sehrish ta aza asaman kanta tana cewa"Nashiga uku!innalillahi wa'inna ilaihirraji'un..........dan Allah kada ka datse mun gashin kaina ......'tana magana tana ja da baya yayin da shi kuma yake tunkararta,abu kamar wasa haka suka shiga zagaye ɗakin yana binta tana ja da baya,a ƙarshe daya fusata a zafafe ya damƙo hijabin dake jikinta tare da tun6uke ta daga jikinta yayi wurgi da ita gefe guda,yarda ya fusge hijabin daga jikinta gaba ɗaya ta tafi zata faɗi kasa,yakai hannu tare da janyo ta ta faɗo saman wide chest ɗinshi,kuka take kamar ranta zai fita saboda ba ƙaramin so takeyi ma gashin kan nan nata ba,ta kwallafa rai akanshi shiyasa kullum take ƙokari wurin gyara shi,har tasamu tatara shi da yawa bayan yanke shin da akai da zata fara aiki gidan,gashi yau akan kuskuren da ba ita ta aikata ba,za'ayi mata aski tana ji tana gani ba yarda zata yi,
tunda sehrish ta faɗa jikinshi gaba ɗaya ya rasa duk wani kuzari na jikinshi,ƙamshin turaren jikinta ba ƙaramin kashe mashi jiki yayi ba,abunda bai ta6a yi ba arayuwarshi,a hankali yakai hannunshi tare da Cire ribbom ɗin da ta ɗaure gashin kanta dashi,ya warwaro shi duka tare da yin wurgi dashi gefe guda ya fadi kasa saman hijab ɗinta,
Nan take lallausar suman kan nata mai laushin gaske ya tarwatse abayanta yayi mata tamkar hijabi,
Ai ina baku labari tunda boss man ɗin nan ya zura hannunshi acikin sumar kanta nan fa yashiga murza gashin acikin hannunshi,laushin gashin kan nata ne yake fisgarshi har yayi hakan batare da saninshi ba,
A hankali ya russinar da kanshi tare da kai tsinin hancinshi saman sumar kanta yana shaƙar daddaɗan kamshin dake fitowa daga cikin sumar kan nata,wani irin bugu zuciyarshi tashiga yi da sauri sauri take harbawa,
ƙankame shi sosai sehrish tayi ta hanyar zagayo da hannayenta abayan waist ɗinshi ta ruƙo shi sosai kamar wani zai kwace mata shi,ba ƙaramin yanayi ta jefa Sgr ba ta kara sanya mashi kasala ajikinshi,kamar yarda itama ta shiga yanayin,tunda ta lafe mashi ajikinshi tayi lamo,wata irin natsuwa ta ji
da bata ta6a ji ba atattare da ita,shessheƙar kukan nan da takeyi gaba daya ta neme ta ta rasa,tsit tayi tana sauraron heart beat ɗinshi,
Suna cikin wannan yanayin na shauƙi sai ga Abbansu ya faɗo cikin part ɗin nasa yana neman shi,ganin baya acikin falon yasa ya wuce izuwa bedroom ɗin shi,tunkan ya ƙarasa ya hange su manne da juna kamar tip da tyre, adaidai ƙopar shiga bedroom din nashi,abban nasu ya tsaya cike da mamaki yana kallon wannan abun al'ajabin,ko motsi basa yi,bakomai yafi ɗaure mashi kai ba,face yarda sgr yake cakuɗa sumar kan yarinyar acikin hannunshi sai faman murzar gashin kan nata yake,ga kuma hancinshi daya cusa asaman kan nata yana shaƙar kamshin da sumar kan nata ke badawa mai daɗin gaske,
Ita kuma ta ƙankame mashi qugunshi da hannunta,ta kwantar da kanta asaman chest ɗinshi,
baki asake Abbansu ke kallon wannan tashin hankali,jinjina kai ya shiga yi cikin ranshi yana cewa"Oh ni hussein!tun yaushe wannan al'amarin ya soma faruwa acikin gidan nan batare da sani na ba!Hmmmm yanzu haka zare mata ido yakeyi yana tsoratar da ita don ya samu abunda yake so,nasan maganinka Rafayet,"ya faɗi hakan tare da kama hanya yabar part ɗin nashi fuskarshi ɗauke da murmushi,don shi wannan abun farin ciki ne awurinshi,ji yake kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha don tsabar farin cikin ganin rafayet tare da mace,baida burin daya wuce wannan arayuwarshi,shi dae yaga Sgr yafara kula mace da sunan soyayya,yau dae gashi Allah ya nuna mashi,
Janye hancinshi yayi daga cikin sumar kan nata,sannan ya tattaro gashin nata tare da sanya almakashin ya datse mata shi,sosai ya yanke gashin,yabar mata guntu wanda ko kafaɗarta bai sauko ba,'
hankali a matuƙar tashe sehrish ta raba jikinta da nashi, da sauri takai idonta akan hannunshi dake ruƙe da dogon gashin daya yanke mata,kamar a mafarki take kallon gashin nata daya yanke mata,
A hanzarce takai hannu tare da shafo kan nata don taji sauran daya rage mata,
Fashewa tayi da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita,dakyar takai hannu tare da ɗaukar hijab ɗinta, sannan ta juya tare da watsawa aguje tana kuka ta fuce daga cikin ɗakin nashi,
ajiyar zuciya ya sauke tare da takawa izuwa gaban dressing mirror ɗin nashi ya mayar da scissors ɗin aciki tare da gashin kan sehrish daya datse,duka ya tura shi aciki ya ajiye,sannan ya maida drawer chest ɗin ya rufe,
Komawa yayi tare da haye wa saman gadonshi ya kwanta,yanayin da bai ta6a ji ba atattare dashi ba yake ji,tsananin tausayinta ne ya kama shi,har ya dinga jin tamkar baiyi mata adalci ba daya datse mata gashin kanta,ya lura ba ƙaramin so takeyi ma gashin kan nata ba,lumshe idanunshi yayi a hankali yana tariyo abunda ya faru tsakaninta dashi,especially lokacin da ta watsa da gudu tana kuka,duk baiji daɗi ba saboda shi baiyi mata hakan da nufin ya 6ata mata rai ba.*
*💋Boss Bature💋*
Join this link to follow my tiktok acct👇
https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1
قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖
Saboda masu complain, nacewa nace zan tura da safe ban turo ba,Allah ne bai nufa zan tura da safen ba,
Ga half page nan,later zan tura sauran
komawa cikin bedroom ɗinta tayi tana ta faman sharar hawaye ranta na kuna,wuri ta samu ta zauna daga gefen gadonta tana ƙarashe kukan nata,babban takaicinta guntun gashin da Sgr ya bar mata da kyar in zaiyi parking da ribbom,koma yayin ba lalle ribbom din ya tsaya ba,ta jima tana azaune tana matsar kwallar bakin ciki,kafin daga bisani ta miƙe tare da nufar wurin dressing mirror ta tsaya tana kallon kanta acikin madubin,cikin shessheƙar kuka tace"Meyasa bai aske gashin duka ba yabarmun kwalkwali?me zanyi da guntun gashin nan daya barmun?ban son gashin!na tsani ganin shi,'ita kaɗae take ta faman sambatu rai atsananin 6ace,
Kwankwasa ƙopar ɗakin nata akai,a tsiwace tace"Wanene"!
Muryar junaid taji daga waje yana cewa"It's me junaid,tun ɗazu fa nake jiranki,ki fito mu tafi na sauke ki,'a ƙagare yake maganar don ya gaji da jiranta,
Ita gaba ɗaya ma ta manta da batun zuwa makarantar,sai da junaid ya tunasar da ita,
hannu tasa tana share hawayenta tace"junaid ka jira ni,acikin mota yanzun nan zan fito,"
Amsa mata yayi da"Okey," sannan ya juya tare da barin kopar dakin nata,
Sai da tafara shiga toilet ta wanko fuskarta sannan ta fito tare da ɗaukar hijab ɗinta dake ajiye gefen gadon ta zura ajikinta
Cikin sauri ta fito ɗauke da school bag ɗinta,ta fice waje wurin harabar ajiye motocinsu,hannu tasa tare da buɗe motar junaid ta shiga daga ciki ta zauna,
ɗan kallon fuskarta yayi tare da cewa"Reesh,na jima ina jiranki,bansan me ya tsayar dake ba,gashi ma har kinyi late,ina fata dae lafiya?"
daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tare da cewa"lafiya lou ba wani abu,mu tafi kawai ina ƙara makara,"
ajiyar zuciya ya sauke tare da jan motar suka bar gidan.
Ita kuwa Hayaam dama tunda taga Sehrish ta nufi part din sgr da coffeen ta sulale ta shige dakinta don kar a gano abunda ta aikata.
*HOSSANA*
Zaune take saman gadonsu ta takure kanta sai faman shessheƙar kuka takeyi,ta sanya uniform ajikinta amma taƙi tashi ta zura hijabin,ta hana kanta duk wani jin daɗi,
Fitowa jahad tayi daga cikin toilet tana kallonta gwanin ban tausayi tace"Hossana,dan Allah kidaina wannan kukan,duk kinbi kin takure kanki,ni nasan cewa ƴa omar ba hakanan ya daina zuwa wurin mu. Ba,Abubuwane suka yi mashi yawa shi ya sanya bai samu halin zuwa ba,'
muryarta na rawa tace"jahad ba zaki gane bane,bazan ta6a samun kwanciyar hankali ba in har bansa ya omar a idona ba,Allah in har baizo ba yau,zanci shinkafar 6era ne na mutu kowa ya rasa,'
dariya jahad ta fashe da ita,hakan yasa hosana ɗaure fuskarta tana jifarta da harara tace"jahad dariya kike mun ko?
tsagaitawa tayi da dariyar tana girgiza kai tace"hosana dole nayi dariya,shinkafar 6era fa kika ce?
ɗaure fuska tayi tana murguɗa mata baki,
Murmushi kawai jahad tayi tare da komawa wurin closet ɗinsu,ta buɗe tare da ciro uniform ɗinta ta shiga zura su ajikinta,shaf shaf ta kammala shiryawa,ta ɗauko school bag ɗinta,sannan ta dawo wurin hosana tace"tashi mu tafi kada mu makara,"
Girgiza kai hosana tayi tace"Jahad ku tafi kawai,ni zan zauna a gida,saboda ko naje ba gane karatun zanyi ba,'
Zuƙunnawa jahad tayi agabanta tace"pls hosana ki daina sa damuwa aranki kinji?ni da kaina yau zan nemo maki ya Omar,'
jin abunda jahad tace yasa hosana sakin murmushi tace"dagaske Jahad"?
ɗaga mata kai tayi alamar eh tace"nayi maki alkwarin,duk inda yake indae yana acikin garin nan saina nemo maki shi,"
Wani irin farin ciki ne ya lullu6e hosana,jiki na rawa ta tashi ta ɗauko hijabinta bayan ta zura safarta da takalmanta suka fuce atare,
A waje suka samu motar osman na jiransu,bayan sun shiga ya tashi motar ya fuce dasu daga cikin gidan,hosana sai murna take jahad tace zata nemo mata Omar,batasan cewa ita da wasa ta faɗa mata ba don ta sanyata farin ciki ne kawai,
Wuraren ƙarfe 12 na rana,jirginsu hajiya azeema yayi landing daga lagos,kanal yousouf ne tare da su irfan suka je tarbosu,a lokacin hayaam suna a kitchen tare da azmee suna shirya lunch ɗin gidan da kuma na tarbar baki,daga kasa ƙafarka acikin main palour ɗin zaka ji daddaɗan ƙamshin abincin da suke girkawa ya gauraye ko'ina,
Cike da son jin gulma hayaam tace"Aunty azmee,wai Uncle ɗin nan nasu da zaizo daga ƙasar turkey,yana da aure ne"?
Azmee tace"a'a bai ta6a aure ba,ina tunanin ma ko budurwa bai ta6a ajiyewa ba,"
jinjina kai hayaam tayi tare da cewa"tabɗijancen amma da alama zaiyi ji da kai,"
murmushi azmee tayi tare da cewa"yarda kike tunani ba haka yake ba,Abusufyan wayayyan mutun ne,ta wani 6angaren ma bai ɗan jin magana amma dai nasan yanzu ya kimtsu tunda girma ya kama shi,amma lokacin baya da yake zuwa mana nan, yarda kikasan junaid haka ɗabi'unshi suke,da yake shi rainon goggonsu ne,'
murmushi hayaam tayi tana ɗan ta6e baki tace"Amma aunty azmee,ita wannan yarinyar sehrish,yakamata ace aikinta ya qare acikin gidan nan,tunda gani nazo kuma zan jima anan ne,ni a ganina bai kamata tana yawo acikin gidan nan ba,ita kaɗae ƴar matashiyya da ita,ya kamata ace tana gaban iyayenta yanzu,'ta ƙarasa maganar tana faman yatsina fuska,ta zuba ma azmee ido tana jiran jin me zatace,
shiru azmee tayi saboda bata da amsar da zata bata,
Cigaba da magana hayaam tayi"Yarinyar ta cika rawar kai sosai,yakamata ta tsaya a iya matsayinta na ƴar aiki mana,ni ina ganin akwai abunda take hari acikin gidan nan shiyasa ta liƙe har ta samu matsayi a wurin babban yaya,"
"Hayaam muyi sauri mu kammala aikin girkin nan,lokaci yana ƙure mana,"da gangan azmee tace mata haka,don ta dakatar da ita daga yi mata zancen Sehrish,don ita ta tsani gulma arayuwarta,
ta6e baki hayaam tayi,aranta kuma taji haushin yarda azmee ta katse mata hanzarinta batare da ta ƙarasa maganarta ba,daga bisani kuma ta saki shu'umin murmushin nan nata,tana tunanin ko ya Sehrish ta ƙare da sgr,don tasan cewa dole yaga gashin nan kuma zai hukuntata akan hakan,taso taje tayi masu la6e amma tsoro ya hanata gudun kar wani ya kamata asoma zarginta,
Ƙasa ƙasa tayi da murya tare da cewa"Koda ace bai hukunta ta ba,nasan cewa zai fara tsanarta ne,kuma zai gane cewa ƙazama ce ita,zanci gaba da shirya mata makirci har nasamu na maye gurbinta a wurin sg......'bata ƙarasa maganar ba,saboda jin shigowar Hajiya Azeema tare dasu kanal yousouf da sauran da suka je ɗaukota,zuba ido hayaam tayi tana kallonta,ganin irin ruwan wankan gwala gwalan data ɗauka,
jikinta na sanye da material launin sararin samaniya,mai tsadar gaske sai faman ƙyalli yake yi,rigar takai mata har wurin guiwarta,sai zane data ɗaura,ta yafa gyale asaman kafaɗarta,yayin da ta kashe ɗaurin ɗan kwalin nan ture kaga tsiya,amma ita nata sunan shi ture kaga arziƙi,don akwai abun arziƙi,gaba daya earrings dinta da awarwaron hannunta da kuma sarƙar wuyanta duk gold ne,ta wanku iya wankuwa,Hajiya azeema kenan ɗaya daga cikin biloniyas din family nasu,idan aka cire shugaba kuma jagora wato Surgeon General Rafayet,
Sai faman sakin murmushi take yi,tsantsar farin cikine ya lullu6eta yau gata agidan ɗan uwanta hussein,anjima ba'a haɗu ba,harkar kasuwanci ta 6oye ta,saboda bata cika zama a nigeria ba,kunsan business woman bata nan bata can kullum cikin hawa jirgi take wurin zuwa harkar kasuwancinta,
Atare suka ƙarasa cikin main palour ɗin,Kanal yousouf na ruƙe da Trolley ɗin da tazo dashi,
Anatse take bin ko'ina na gidan da kallo komai ya canza mata,ba kowa take muradin gani ba,face Junaid don har mafarkin shi tayi,shiyasa ta ƙagara tazo don tagan shi,juyawa tayi tare da kallon irfan tace"wai ina yaya hussein ne?naga kamar ba kowa gidan ko"?
"Abban mu ya ɗan fita garden tare da babban yayan mu da kuma ya Omar,amma ina da tabbacin cewa nan bada jimawa ba zasu shigo ciki,"ya ƙarasa maganar tare da nuna mata wuri yace"Aunty ki zauna mana,bari nayi ma Aunty azmee magana ta haɗa maki farfesun nan nata,nasan baki manta ɗanɗanon shi ba,"
dariya tayi tare da dan bugun kafadarshi tace"wato kallon acici kakeyi mun ko?daga zuwana ko hutawa banyi ba zan fara neman farfesu,kamar wata mayya,ni duk bama wannan ba,nifa hankalina bazai kwanta ba in har bansa junaid acikin idona ba,'
Kanal yousouf yace"Aunty gaskiya nafara kishi da junaid,haba kowa junaid junaid,ko hutawa ba kiyi ba amma kin fara ambaton sunanshi kamar shi kaɗae ne ɗa acikin gidan nan,"cikin zolaya yayi maganar tashi,
Kafin Azeema ta kuma cewa wani abu,sai ga azmee ta fito daga cikin kitchen fuskar nan ɗauke da murmushi tana cewa"wata sabon gani, hajiya azeema,Sai yau zamu sake sanyaki acikin idanunmu"?tayi maganar a yayin da take ƙarasawa wurinta suka rungume juna,dama suna ɗasawa da ita,mutuniyarta ce kodan saboda iya girkin azmee yasa take shiri da ita sosai,don ita bata wasa da abinci,akwai son cin mai daɗi,kullum tazo Abuja wurinsu burinta tasha farfesun azmee,
Raba jikinsu sukayi dana juna,Azmee taci gaba da cewa"Hajiya azeema kece kika koma haka?
Dariya azeema tayi tace"kinji ki da wata magana,kamarya na koma?nasan halinki fa azmee yanzu kince na ƙara ƙiba,'
Azmee tace"kin tsargu kenan,tunda gashi nan kin rigani faɗin abunda zance,'
Ta ƙarasa maganar tare da ruƙo hannunta tace"nasan kin kwaso gajiya sosai,shiyasa na gyara maki shinfiɗa inda zakije ki yada gajiyar da kika kwaso,sannan akwai special suya da kuma wannan farfesun da kika fiso na shirya maki shi,da zarar kin kammala hutawa zan shiryo maki shi,kici ki ƙoshi,nasan mutuniyar tawa bata wasa da cikinta,akwai bama ciki haƙƙinsa,"
Sai faman murmushi hajiya azeema ke saki,da alama taji daɗin karramawar da azmee tayi mata sosai,atare suka wuce ciki izuwa bedroom din da zata sauka,dama already azmee ta gyara mata ɗakin sai ƙamshi yake,
bayan sun shiga bedroom din,Sai da suka ƙara gaisawa sosai,kafin daga bisani Azmee tabar cikin ɗakin ta koma kitchen,
Ajiyar zuciya hajiya azeema ta sauke tare da cire mayafin cikinta ta ajiye shi saman gadon,sannan ta wuce cikin toilet,
Bayan shigarta kanal yousouf ya shigo cikin bedroom din hannunshi ruƙe da trolley dinta,jingine mata shi yayi ajikin wardrobe,sannan ya juya ya fuce,
fitowa azeema tayi daga cikin toilet din har lokacin fuskarta ɗauke da murmushi a fili tace"oh ni,koya junaid ya koma yanzu?nasan cewa ya ƙara girma sosai,gaskiya nayi missing shagwa6ar shi,nasan cewa da zarar yaji cewa na ƙaraso,zaizo ya ishe da rigima yana cewa Ina tsarabar shi,'ta ƙarasa maganar tare da hayewa saman gadon ta ɗan kishingiɗa donta runtsa,
Bata jima da kwanciya ba,Abbansu ya shigo cikin gidan tare da sgr da marshal atare suka ɗunguma zuwa masaukin nata,a hankali abba ya tura ƙopar ɗakin suka shiga da sallama,
Jin muryar ɗan uwanta,yasa ta yunkura tare da miƙewa daga zaune tana kallonsu fuskarta ɗauke da murmushi,
Ƙarasawa ciki su kayi,sgr da omar suka samu wuri saman doguwar sofa din dake dakin suka zauna suna fuskantarta,yayin da Abbansu kuma ya samu wuri gefen gadon kusa da ita ya zauna fuskar nan awashe sai faman farin ciki yake yi na ganin ƴar uwarsa daya jima basu haɗu ba,
gaisawa suka shiga yi da junansu,don ba ƙaramin kewar juna sukayi ba,
Abba yace"ina fata dae da shirin zama kika zo mana,dan wannan karan bazan bari ki koma ba,nagaji da kewarku da nake ta faman yi,'
"Yaya hussein,nasan ban kyauta ba,na rashin zuwana wurinku,abubuwane sunyi mun yawa shiyasanya na jima banzo ba,amma Insha Allah wannan karan har sai kun gaji dani,zan zauna ne har sai an ɗaura auren junaid,'
Fashewa sukayi da dariya gaba dayansu,banda Sgr wanda tun shigowarsu,ya jingina bayanshi ajikin sofa din tare da lumshe idanunshi,sarai azeema ta lura dashi dama sai da ranta ya bata cewar bazai tanka mata ba,
Omar yace"ae ni fushi nake da Auntyn tawa,haba aunty azeema yau kusan wata nawa kenan?yaushe rabon da mu sanyaki a idanunmu,baku son zuwa ganin ƴa'ƴanku,kuma babu damar mutum yace zaizo ganinku saboda kullum baku a ƙasar,'ya ƙarasa maganar tare da ɗaure fuskarshi,
dariya azeema tayi tana cewa"kwantar da hankalinka mutumina,ae wannan zuwan daka ga nayi,bazan koma ba har sai naga an shafa fatihar auranku,kai da wannan namijin zakin,'
tayi maganar cikin zolaya tana kallon Rafayet,aikuwa ya ƙara ɗaure fuskarshi alamar baiso,
Murmushi Abbansu yayi tare da cewa"kada ki samu damuwa,ae kuna anan ma zamusha biki,Abusufyan kawai nake jira ya ƙaraso,don nafison ya shaida wannan ɗaurin auren,ayi komai tare dashi don shine waliyyi"
Jin wannan maganar ta Abban nasu yasa shi buɗe idanunshi tare da miƙewa daga