Showing 207001 words to 210000 words out of 245004 words
Chapter 70 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download
nasu iri daya,amma hali ba iri ɗaya ba,Ayaan ta 6angaren Abbansu yake,shi kuma jahan sak mommynsu ce,
daƙyar Ayaan ya samu jahan ya bisu suka shiga cikin falon,atare suka zauna saman 3 seater,ita kuma ta zauna saman 2 seater tana fuskantar su,yarda jahan ke ta faman yatsina fuska,ba karamin dariya yaso ya bata ba,ji yake kamar ya ɗosana ass ɗinshi asaman ƙayoyi haka yake ji,
Ayaan ne ya soma magana"Aunty amani kinji mu shiru ko?ba mu sake zuwa mun duba jikin Amal ba,ban ji daɗi ba wlh abubuwa ne sunyi mana yawa,amma tana aran mu,shiyasa ma muka yanke shawarar zuwa yau mu duba ta,'
taji daɗin kalaman ayaan sosai,fuskarta ɗauke da murmushi tace"Amal taji sauƙi sosai,kullum sai ta tambayeni ina twins ɗin nan suke,musamman kai Ayaan tafi tambayarka saboda kaine ka kawota wurina,yanzu bari naje na kawo maku abun ta6awa,kafin na kira maku Amal ɗin ku gaisa,"
Ta ƙarasa maganar tare da mikewa ta wuce cikin kitchen,
Tana barin wurin jahan ya buga tsoki tare da cewa"Wlh ayaan ka bani haushi!ka zauna ka gama tsara mata ƙaryar cewa mun zo duba jikin wannan ƙarmasasshiyar yarinyar ne,yarinyar da nama manta da zancen ta ni,mtswwww,'ya kawar da kanshi gefe yana hura hanci,
Ayaan yace"Am sorry bro,nasan ban kyauta ba,amma kayi hakuri kasan banason 6acin ranka,ni aganina bamu kyauta ba,tun ranar da nakawo yarinyar nan,ba mu ƙara zuwa mun dubata ba,kuma abunda ya dace ace munyi ne,"
ta6e baki jahan yayi tare da kallonshi yace"sannu ko?sarkin tausayi,"
Jin takun tafiyar Amani ne yasa su kayi shiru,ƙarasowa ciki tayi hannunta ɗauke da tray,cups ne guda biyu,sae lemu masu sanyi acikin roba tare da plate na snacks,asaman table ta ajiye masu sannan ta juya tana cewa"bari na kira Amal din ku gaisa,"
ɗaukar lemun ayaaan yayi tare da buɗe shi ya tsiyaya masu acikin cup,ya dauki ɗaya ya miƙa ma Jahan,ya kar6a sannan shi kuma ya ɗauki ɗayan,yana sha,
Saukowa amani tayi daga upstairs,ta dawo wurinsu ta zauna saman sofa din tana cewa"gata nan zuwa,"
Ayaan yace"Allah ya kawota lafiya,"
Gaba daya sun mayar da hankalinsu wurin shan Lemun dake hannunsu,su ka jiyo takon takalminta,kwas kwas,
Ayaan ne ya fara ɗago da ido yana hangen yarinyar dake saukowa daga saman benen,juyawa yayi ya kalli amani tare da yin ƙasa da murya yace"ita ce ko"?
.murmushi amani tayi tare da daga mashi kai alamar eh,
Satar kallon jahan yayi wanda hankalinshi ba a kansu yake ba,
A hankali Amal ta ƙarasa saukowa daga saman benen ta nufo inda suke,lokacin da ta ƙaraso wurinsu fuskarta ɗauke da murmushi tace"sannunku da zuwa,"
Kai tsaye muryarta ta daki dodon kunan Jahan,daɗin muryarta ne yasa Jahan juyowa cikin sauri don yaga wacece,ai yanayin arba da wannan kyakkyawar fuskar ta Amal nan take ya saki Cup ɗin dake hannunshi ƙasa,ya tarwatse lemun ciki ya zube,
A gigice ya miƙe tsaye yana kallonta yayin da zuciyarshi ke bugawa da ƙarfi da karfi,yarda kasan hurool aini awurin kyau haka yarinyar ta koma mashi,
fara ce tass,har ma tafi Amanin haske,fatar jikinta har wani ƙyalli takeyi saboda gyaran da tasha,tabarakallah masha Allah ta ko'ina amal ta haɗa,ga manyan idanun nan nata dara dara dasu,ga dogon hancin nan nata kamar zaiyi sujjada,la66anta kuwa sunyi red colour sosai tamkar ta shafa janbaki,idan tayi murmushi kamar gonar auduga saboda hasken haƙoranta,lallai ba ƙaramin gyara Amani tayi ma ƙanwarta ba,ta canza mata kamanni sosai,ta fito a balarabiyarta,sleeping dress ne ajikinta pink colour riga da wando,ta yafa gyale fari asaman kanta,
dare ɗaya Allah kanyi bature,acewar ayaan,
Ina labarin Jahan daya miƙe tsaye ya zuba mata ido yana kallonta ko ƙyaftawa baiyi,abun tamkar a mafarki yake kallonshi,gaba daya ya gama ruɗewa,muryarshi na rawa yace"ke!kece!'cike da mamaki yayi maganar,
Amal kuwa aɗan tsorace taja baya,tana faman zazzare mashi kyawawan idanunta,ganin yarda ya harzuƙo kamar zai rufe ta da bugu,
murmushi kawai Amani ke saki ita da ayaan suna kallonshi,dama wannan duk shirin Ayaan ne,
"Aunty amani!surgery akayi mata ne?if not taya akai tayi transforming haka"? A ruɗe jahan ke tambayarta,
miƙewa tsaye amani tayi tare da takawa zuwa inda suke ta ruƙo hannun Amal tana cewa"ikon Allah ne jahan,babu wani surgery da akayi mata,gyarane kawai tasha,dama can Amal kyakkyawa ce,wannan asalin kamannin fuskarta ne ya dawo,'
Jiki asanyaye Jahan ya koma tare da zaunawa saman sofa din,har lokacin bai janye idanunshi daga kallon fuskar Amal da yake yi ba,kamar ya haɗiyeta haka yake ji,ya jima yana mamakin wannan ikon Allahn,
Miƙewa Ayaan yayi tare da cewa"mu zamu wuce gida,ana can anata shirye-shiryen haɗa walimar murnar dawowar uncle abusufyan,ina fata zaki zo mana tare da Amal,'yayi maganar yana kallon Amani,
Tace"mai zai hana,ae muna nan zuwa anjima insha Allah,tare da mu za'a buɗe taron walimar,"
"Allah ya kawo ku lafiya,'yayi maganar tare da mayar da idanunshi kan JAHAN daya ƙurawa Amal ido kamar mazuru yace"bro,tashi mu tafi mana,kada time ya ƙure mana,"
jiki amace jahan ya miƙe tare da ruƙo hannun ayaan cikin nashi,su kayi mata sallama tare da kama hanyar fita daga falon,
Suna tafiya Jahan na waiwayon Amal kamar zaiyi tuntu6e,hakan ba ƙaramin dariya yaba shi ba,saida suka fito daga cikin falon,bayan sun shiga cikin motarsu,Ayaan ya ɗan kallo shi cikin zolaya yace"Jahan ya kaga ƙarmasasshiyar ne?ko nace kingin rami ko?ya ma kace mun ran nan a asibiti daka ganta"?
A tsiwace jahan yace"bansani ba!dallah ni ka tashi motar mu tafi gida,"
dariya sosae Ayaan yayi yayin da yake tashin motar,ya ja ta suka bar gidan,yana driving yana kumshe dariya abakinshi,jin yarda Jahan ke ta faman buga tsoki,duk yabi ya susuce tunda yayi arba da Amal acikin idanunshi,ya nemi natsuwarshi ya rasa,a haka har suka ƙaraso cikin gidan,
wuraren ƙarfe sha biyu,sgr ya fito daga cikin toilet jikinshi sanye da bathrobe,yayin da hannunshi ke ruƙe da guntun towel wanda yake goge Sumar kanshi dashi,agaban dressing mirror ya tsaya yana ƙarasa goge sumar kan nashi,koda ya ɗago da idanunshi da niyyar ya kalli fuskarshi acikin madubin,sae ya dinga ganin fuskar sehrish acikin mirror ɗin amaimakon tashi,lokaci guda ya shiga tariyo duk abunda ya faru jiya atsakaninsu,tun daga lokacin daya je taimakonta,har izuwa lokacin da yaje yi mata allura,tana faman cizon la66anta,hakanan yaji yana marmarin son ganinta acikin idanunshi,tambayoyi ya shiga yi aranshi yana cewa meyasa batazo ta kawo min breakfast ba?ko har yanzu jikin nata ne?
Jin takun tafiyar mutun abayanshi yasa shi kai idanunshi wurin ta cikin madubin ya hange ta tsaye duk a tunaninsa yarinyar ce tazo,koda yayi arba da fuskar hayaam sai ya kawar da fuskarshi cike da mamakin wacece wannan?meya kawota bedroom ɗinshi,
ƙarasawa ciki hayaam tayi tana tafiya cike da kwarkwasa,wankan atampa ta ɗauka ajikinta,riga da skirt ne,kayan sun matse ta sosai,sun bayyana surar jikinta soaai,musamman saman rigarta boobs ɗinta sun fito waje kamar zasu ciro daga cikin rigar,akwai mayafi a jikinta lokacin da ta fito daga bedroom ɗinta,tana ƙarasowa ɗakin nashi ta cire mayafin tare da ruƙe shi a hannunta don taja hankalin shi,cike da ƙwarin guiwa tazo ɗakin nashi,saboda kwallin data shafa ma idanunta,wanda bokansu ya bata don tayi amfani dashi,ya tabbatar masu da cewa muddin sgr ya sanya idanunshi acikin nata,shikenan sun gama dashi,zai haukace akanta,ya rasa natsuwarshi,
Tsayawa tayi daga bayanshi,tare da kashe murya tace"ya kake ranka shi daɗe,ka tashi lafiya,"
Shiru Sgr yayi bai amsa mata ba,gaba daya lamarin ya gama ɗaure mashi kai,ƙarfin halinta ya bashi mamaki,
daƙyar ya iya buɗe baki yace"Ke!wacece ke!what are u doing in my room?yayi maganar batare daya sanya idanunshi acikin nata ba
zagayowa hayaam tayi ta gabanshi tamkar zata manna ƙirjinta asaman nasa,
Cike da rangwaɗa tace"Zuwa nayi don na gyara maka bedroom ɗinka,tunda ita yarinyar dake kula da part ɗin naka,bata jin ɗaɗi bazata iya yin aikin ba,idan ba damuwa inaso ka bani damar na ci gaba da kula dakai kanka,ina mai tabbatar maka da cewar zaka ji daɗin kasancewa tare dani,saboda ni ina da komai da komai,ba gyara ɗaki kaɗai ba,hatta ɗebe maka kewa zan dinga yi,nasan dole ka buƙaci mace akusa dakae especially da daddare haka.
Tashin hankalin da ba'a sa mashi date,yau hayaam tazo yi ma Sgr kwartanci acikin ɗakinshi,ita ga kwararriyar ƴar bariki,tana magana tana ƙara kusanta jikinta da nashi,
Just speechless gaba daya ta gama rufe mashi bakinsa,ya rasa abun cewa,shiru kawai yayi yana jira yaga me take ƙokarin yi mashi,daga nan zai san wane irin hukunci ya dace da ita,don ya lura cewa giya tasha,tana bukatar adawo da ita cikin hayyacinta,kuma har lokacin bai kalli cikin idanunta ba,
Wannan shurun da yayi ne yasa hayaam ta fara tunanin cewa kodae ya amince mata ne?shu'umin murmushin nan nata ta shiga saki tana bin surar jikinshi da kallo sae faman haɗiyar yawu takeyi kamar zata lashe shi,aranta tana cewa"dama nasani,muddin yayi arba da sura ta,dole ya kwaɗaitu,yanzun nan zan canza mashi alƙibla,zanja hankalin shi sosai,har nasamu abunda nakeso,
Kafin Sgr yayi wani yunƙuri gaba daya hayaam ta afka mashi tai hugging nashi sosae,tashin hankali saboda tsabar mamakin daya shiga ne yasa bai janyeta Ba,kanshi ya gama ɗaure wa,domin kuwa tunda ya ke arayuwarshi wata ƴa' mace bata ta6a kuskuren ta6a wani sashe na jikinshi ba koda gigin wasa,sae wannan mai rabon shan dukan,
ita kuwa hayaam jin bai yi yunkurin yi mata wani abu ba yasa ta fara kokarin tura hannunta cikin Bathrobe din dake a jikinshi don tasan takan yadda zata ida kashe mashi jikinshi,aikuwa a zafafe ya finciko ta,ya ware faffaɗan tafin hannunshi da ƙarfin gaske ya kifa mata mari zazzafan gaske gami da hankadata ta daki dressing mirrorn,agigice hayamm ta fasa wata irin razananniyar ƙara,wani irin jiri ne ya ɗebe ta,nan take ta yanke jiki ta faɗi ƙasa tana birgima,taji ƙamshin mutuwa wlh,ihu ta shiga saki tana fadin Wayyo Allanta,
Adai dai lokacin Sehrish ta shigo part dinshi hannunta ɗauke da tray,na breakfast dinshi data kawo mashi,ganin bashi a parlourn yasa ta nufi bedroom din bakinta dauke da sallama, tana sanya ƙafarta acikin bedroom ɗin,ta jiyo sautin wannan ƙarar da hayaam ta saki,a firgice ta saki tray ɗin hannunta ya faɗi ƙasa kayan abincin suka tarwatse ƙasa,hankali a matuƙar tashe take kallonsu,sautin faɗuwar tray ɗin hannunta ne yasa sgr juyowa karaf idanunshi suka shiga cikin na sehrish,zuba mashi ido tayi tana kallonshi yayin da shima yake kallonta sae faman huci yake yi yarda kasan mayunwacin zaki,da ace sehrish bata faɗo ɗakin nan ba,da ba ƙaramin illata Hayaam zaiyi ba,so yayi ya nakasata,yarda bazata ƙara yin gigin takowa tazo bedroom ɗinshi balle har tayi yunƙuri ta6a wani sashe na jikinshi ba,
atsorace sehrish ta mayar da idanunta kan Hayaam dake a baje ƙasa,magashiyyan sae faman Birgima takeyi har lokacin bata dawo cikin hayyacinta ba,wato taji tafin hannun maza,dama zafin hannu gare shi,shiyasa bai cika son yakai bugu ba,saboda za'a iya samun matsala,da mari kaɗae zai iya sumar da mutun,
A zafafe Sgr ya juya ya tunkari hayaam dake baje kasa,da alama yau fa hayaam sai dai
buzun ta,ganin hakan yasa hayaam da kyar ta rinka jan jiki tana ja baya gami da yi masa magiyar yayi hkr kar ya kasheta hannunta guda dafe da kuncin,gaba daya sautin jin kunanta ya ɗauke ɗuff ta 6arin da daya mare ta,cikin husky voice yace"who the hell are u? da sauri cikin shesshekar kuka la66anta na kerma tace"ni...ni..ƙanwarku ce....au ƙanwar matar yayyen kuce ishaq da abbas" tsayawa Sgr yayi lokaci guda ya gane itace yarinyar da tazo rannan har aka faɗa masa"to waye ya shigo da ita gidan? Ya jefa ma kansa tambaya,
Ganin abunda ke faruwa yasa Sehrish ja da baya zata watsa aguje saboda tsoran kar itama laifin da hayaam ta aikata ya shafe ta,
da wata irin murya taji yace"ke!zonan,"
Jiki na rawa sehrish ta shigo cikin ɗakin nashi,sae faman kerma take yi kamar yace zai buge ta,
ƙarasawa kusa dashi tayi tana faman zazzare idanu hankali atashe take kallonshi,tana jiran jin me zaice mata,
daidaita natsuwarshi yayi tare da sassauto da muryarshi calmly yace"ya jikin naki!'?
Tsananin mamaki ne ya kama sehrish,jin abunda yace mata,kuma da irin muryar da yayi mata maganar,hakan yasa taji hankalinta ya kwanta,
muryarta na rawa tace"naji sauƙi sosai,yanzu bana jin ciwo atare dani,"
Jinjina kanshi yayi kafin ya kuma cewa"Okey,Allah ya ƙara lfy,'
"Ameen,"ta amsa mashi,
shiru suka ɗanyi na wani lokaci,kafin ya mayar da idonshi kan hayaam dake ta faman yi mashi tsuwa acikin dakinshi duk ta cika masu kunnuwansu,
A fusace yace"get out from my bedroom!'
Jiki na rawa hayaam ta miƙe da gudu zata fuce a tsawace sgr ya tsaidata ta hanyar cewa" hey! juyowa tayi har lokacin hannunta na akan kumatunta ya cigaba da cewa "make sure u pack all ur shit and leave this house! A kausashe yayi maganar, idasa fucewa daga cikin ɗakin tayi tana cigaba da shar6ar kukan nata,
Lumshe idanunshi yayi tare da buɗesu akan fuskar sehrish da tai tsuru² jin ance hayaam ta tattara kayanta ta bar gidan, yace"yanzu ya za'ae da breakfast ɗina da kika zubar mun a ƙasa?
cikin sauri tace"bari naje na haɗo maka wani" juyawa tayi da niyyar ta tafi,kwatsam taji ya ruƙo hannunta acikin nashi,a ɗan tsorace ta juyo tana kallonshi,gabanta ne taji yana faɗuwa ganin yarda Sgr yake kallonta,nan fa ta shiga taitayinta,
"Meyasa jiya,baki dawo gida ba?ko saboda na datse maki gashin kanki ne"?
Girgiza kai sehrish tashiga yi tana cewa"a'a ba haka bane,bani da lafiya ne,bacci ya ɗauke ni a school bansamu wanda ya tashe ni ba lokacin da aka tashi har junaid yazo dauka na bai ganni ba,shiyasa bansamu nadawo gida ba,'
Kallon bakinta dake bayanin kawae yake har ta gama,a hankali ya furta Okey,sannan ya saki hannunta daga ruƙon da yayi mashi,
juyawa tayi da sauri ta ƙarasa bakin kopar dakin nashi,zukunnawa tayi ta kwashe kayan abincin data zubar mashi aƙasa,duka ta tattara su acikin tray din,sannan ta fuce daga ɗakin nashi,
Gaba daya ta rasa natsuwarta,wani irin yanayi ta dinga ji atare da ita,kallon nan da yake yi mata ba ƙaramin kashe mata jiki yakeyi ba,kamar wadda aka cire ma lakar jikinta haka ta dinga jin kasala,
A kitchen ta samu azmee tana wanke kayan abincin da sukayi amfani dashi na breakfast,
Ganin ta ɗauke da tray a hannunta yasa azmee cewa"Har ya kammala yin breakfast ɗinne"?
girgiza kai tayi alamar a'a tace"matsala aka samu,ni ce na 6arar da kayan abincin,shine yace na sake kawo mashi wani,'
Azmee tace"wasa wasa sehrish kema kin iya shiririta wlh,kina sake da baki har kika zubar mashi da kayan abincin ko?
"Ae bada sanina,hakan ya faru ba,"ta yi maganar yayin da take ƙarasawa cikin kitchen ɗin,
"Shikenan bari na sake haɗa maki wani breakfast din ki kai mashi,Amma kada ki jima a part din nashi fa,da zarar na kammala gyara kitchen din,zanyi maki ƙunshin,ko baki so ne'?
"Inaso mana,"tayi maganar fuskarta ɗauke da murmushi,
Batare da 6ata lokaci ba,Azmee ta kammala shirya mata wani kayan abincin acikin tray,ta bata takai mashi,sae da ta ja mata kunne akan karta kuskura ta ƙara zubarwa,'
fitowa daga cikin kitchen din sehrish tayi,fuskar nan ɗauke da annuri,wani irin daɗi takeji aranta,kamar anyi mata albishir da gidan aljana,
A hankali take taka stairs din,yayin da Zuciyarta ke tariyo mata abunda ya faru aɗakin sgr,batasan meya faru tsakaninshi da hayaam ba,da har ya kwashe ta da mari,amma koma meye dae tana da tabbacin cewa wani abu tayi mashi ba dae dae ba,
Ta6e baki tayi tana cewa"to ni ina ruwana?meye damuwata da ita?koma meye ita taja ma kanta,nasan cewa babban yaya bazai ta6a ɗaga hannu ya mari mace ba hakanan batare da wani dalilin ba,na yarda dashi sosai,kuma baiyi mun kama da irin mazan dake dukan mace ba,Yau dae hayaam take kowa ma,tasha mari wlh ko a ha6ar zani na,ba ƙaramin daɗi naji ba wlh,babban yaya ya burgeni sosai daya kwashe ta da mari,gobe ma in halinta ne ta ƙara yi mun shisshigi a aikina,angaya mata cewa sauƙi ne kula da babban yaya?nikaina kullum cikin fargabar kada nayi mashi kuskure nake,shiyasa nake lalla6ashi kamar kwai acikin cokali,Allah sarki yau hajia hayaam taji tafin hannun babban yaya koya raɗaɗin yake?tabb dole ma akwae mugun radadi tunda ta kasa cire hannu daga kan kuncinta, gwara ni Almakashi yasa ya datse mun gashin kaina,nan da wani lokaci gashin zai fito,ita kuwa marinta fa yayi? nasan har abada bazata manta da wannan ranar ba,
ashema hakanan take ma mutane kankanba ko sanin wacece ita bai yi ba"
Dariya sosai sehrish takeyi kamar wata zautacciya,sae faman sambatu takeyi,da alama taji daɗin Marin da Sgr yayi ma Hayaam,abun ko ajikinta,
Lokacin da ta shiga part ɗin Sgr,a kishingiɗe ta same shi saman doguwar kujera,ya miƙe kafafunshi,bai kaiga shiryawa ba,Vest ce kawai ajikinshi sae shorts farare,
Karasawa ciki tayi tare da ajiye mashi tray din asaman table,sannan tace"ga wani breakfast ɗin na kawo maka,"
sauko da ƙafafunshi yayi ƙasa ya miƙe daga zaune,ya jingina bayanshi a jikin sofan yana jira tayi serving ɗinshi,
Sehrish ta jima awurin sgr tana mashi ɗawainiya har sai da ya kammala yin break fast din nashi,sannan ta koma ta gyara bedroom ɗinshi,bayan ta gama ta dawo ta gyara falon sannan ta ɗauko kayan abincin da yayi amfani dasu,ta wuce dasu kitchen,sae da ta wanke komai ta mayar dashi a ma'ajiyar shi,sannan ta wuce ɗakin azmee don suyi maganar zanen lallen da zatayi mata,
Wuraren ƙarfe biyu na rana,Junaid ya kar6o mata kayanta,akwati guda ne na atampha da lace,da kuma shadda,hada materials,duk an ɗinka mata su,
acikin bedroom ɗinta ya ajiye mata akwatin kayan,
sae da suka kammala sallar azhar,tukunna suka zauna zaman yin ƙunshi,anan corridor din ɗakunan nasu azmee tayi masu shimfiɗa suka zauna sama,tunda suka fara ƙunshin junaid keta zarya awurin sae faman santin kunshin sehrish yake yi,tun kafin a wanke mata ƙunshin ma,cikin nishaɗi suke yin firar su,tana yi mata ƙunshin suna fira tare da junaid,don ya kasa ya tsare sae anyi tare dashi,
A6angaren Hayaam kuwa tunda ta faɗa cikin bedroom ɗinta saman gado,take ta faman shessheƙar kuka,fuskarta tayi jawur saboda kukan da tasha,gefen fuskarta dauke da sahun yatsun sgr ruɗu ruɗu sun fito wurin ya kumbura sosai gashi kunnanta daya dumm take jin shi,tunda take arayuwarta wani ɗa namiji bai ta6a gigin ta6a lafiyar jikinta ba,sae