Showing 165001 words to 168000 words out of 245004 words

Chapter 56 - Abban Sojoji Book 2 Complete Pdf Download

17 Mar 2025

25237

magana,da hanzarin gaske ya dakatar da ita ta hanyar yi mata nuni da hannunshi alamar ta tashi ta tafi,murmushi jahad tayi tare da miƙewa cikin sanɗa tabar saman sofa ɗin ta koma saman 1 seater ta zauna tana kallon dramar da ya Omar ɗinsu zai shirya,cikin sanɗa ya lalla6a tare da komawa wurin da jahad ta tashi ya zauna,sannan yakai hannunshi tare da ɗan janyo wutsiyar gashinta,
A fusace tace"dan Allah jahad ki rabu dani inji da abunda ke damuna,ki tashi kiban wuri,"
Murmushi Omar yayi tare da cewa"zan tafi amma ki fara faɗamun meyasa kika damu da yaya Omar ɗinki har haka"?
Sam hossana bata gane voice ɗinshi ba saboda ranta a6ace yake,
"Saboda inason shi sosai,jahad nasan ni kawai nake haukana,yana can wurin hayatyn shi,suna shan soyayya.....'
Katse ta Omar yayi da cewa"kina kishi ne"?
A faɗace tace"saboda me bazanyi kishi ba,nima ae zuciyata ce a ƙirjina ba dutse ba,"
Wannan maganar ta hossana ba ƙaramin dariya taba marshal Omar ba,hatta jahad sai da ta murmusa daga inda take,
Kwantar da kanshi ya ɗanyi abayanta yana cewa"am really sorry babyn Omar,nayi missing ɗinki sosai,nasan nayi laifi ayimun afwa bazan ƙara ba..."jin muryar Omar raɗau a kunnanta yasa tayi hanzarin ɗagowa tana kallonshi da idanunta da suka cicciko da kwalla,
Waro ido Omar yayi yana kallonta ba ƙaramin tsorata yayi ba da ganin makeup ɗin da ke a fuskarta,ta dambara Uwar foundation kamar wata aljana,Jan bakin da ta shafa ya 6ata fuskarta har wurin cheeks ɗinta saboda uban kukan da tasha,ga maskara ta zazzago mata a ƙasan idonta,
Hankali tashe Omar yace"subhanallahi,kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,Babyn Omar wannan kwalliyar fa?dama itace kwalliyar da ake cewa anyimun don inzo in gani,"cike da zolaya yayi maganar,amma tamkar ya tunzura hossana nan take ta 6are baki tare da fashewa da wani sabon kukan,
Dariya jahad ta dinga tiƙa kamar kamar me har tagaza dakatar da kanta,
Yama rasa ta inda zai fara shawo kanta don ya lallashe ta,hakan ya ƙara hasalata,kamar wata ƙaramar yarinya,ba ƙaramin tausayi ta bashi ba yasan duk don saboda rashin zuwan shi ne,hannu yasa tare da janyota jikinshi yayi hugging ɗinta sosai yana ɗan bubbuga bayanta,lokaci guda ta nemi kukan da takeyi ta rasa,sai gata tana faman sauke ajiyar zuciya,
a hankali ya furta"am really sorry hossana,bazan ƙara 6ata maki rai ba,kullum zan dinga zuwa idan ma bansamu halin zuwa ba zan kira ku awaya mu gaisa,"
Ya ƙarasa maganar tare da cewa"kin yafe mun"?
ƙasa ƙasa tace"na yafe maka,amma karka ƙara,"
murmushi yayi tare da ɗagota daga jikinshi yana kallon fuskarta,sai faman cin magani takeyi tana haɗe mashi fuska,
"Kin ci abinci kuwa"?
"A'a banci ba,"
"Why"? Ya tambaya yana kallon bakinta da take ta faman turowa irin na shagwa6a66u,
"Kai nake jira kazo ka bani abaki,"
"Really"? ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Juyawa ya ɗanyi tare da kallon jahad dake zaune tana kallonsu gwanin burgewa yace"dagaske hossana bata ci komai ba"?_
Amsa mashi tayi da eh,jinjina kai yayi sannan yace"ki kawo mata dinner ɗinta anan,sai na tabbatar da taci ta ƙoshi sannan zan tafi,"
Murmushi jahad tayi tare da miƙewa ta wuce downstairs don pta shiryo masu dinner din,"

_💋Boss Bature💋_

Yau da wuri suka dawo cikin gidan wuraren karfe goma dai dai,wani irin tsoro da fargaba sehrish taji,musamman da azmee ta sanar da ita cewa ga dinner ɗin sgr can taje takai mashi,bakomai ya faɗo mata arai ba face abunda ya faru ɗazu tasan cewa dole ya tuhumeta saboda ita kaɗai ce macen da take shiga part ɗinsa,sai faman zarya takeyi acikin bedroom ɗinta,tana tunanin yarda zata tunkare shi ayau ɗinnan,

Hayaaam

Tafiya takeyi cikin sanɗa tana waige waigen ko akwai wani a main palour din cikin sa'a taga babu kowa,murmushin mugunta ta saki tare da nufar kitchen din,tana shiga tayi arba da tray na abincin da Azmee ta shirya ma Sgr,asaman dogon table na kitchen ɗin ta ajiye mata,jinjina kai hayaam tayi tare da cewa"hmmmmm yarinya kenan yau zaki fara sanin koni wacece wurin iya makirci,"
Tana faɗin hakan ta shiga ciki kai tsaye ta tsaya wurin tray din,hannu tasa tare da buɗe warmer ɗin dake ɗauke da chicken ppr soup,sai faman ƙamshi yake yi,murmushi hayaam tasaki tare da kai hannu cikin sumar kanta,ta cinko gashin kanta sannan ta jefa acikin chicken ɗin hadasa hannu ta motsashi aciki,sannan ta rufe murfin,duk hakan bai mata ba sai da tabi komai na abincin ta sanya gashi aciki,sannan cikin sanɗa tabar kitchen ɗin,tana faman sakin dariya don tasan cewa da zarar sgr yaga gashin nan yarda yake da tsaftar nan ba ƙaramin ƙyamatar yarinyar zaiyi ba,kuma tasan dole ya koreta daga yi mashi aiki,bama wannan ba dole ya hukuntata, tashin hankali da ba'a sama shi date,

💋💋💋

Fitowa sehrish tayi bayan ta gama zullumin nata,kitchen ɗin ta nufa batare da 6ata lokaci ba ta ɗauko tray ɗin a hannunta tare da wuce wa upstairs,hakanan tadinga jin gabanta na faɗuwa kamar wani mummunan abu zai faru da ita,tsayawa tayi abakin ƙopar shiga falon nashi,sai da ta dai²ta natsuwarta sannan ta zabga sallama,tana jiran jin amsawar shi,
Jin shiru yasa ta ƙara maimaita sallamar,har kusan sau uku ana huɗun ne tajiyo muryarshi yace"Come in,"

Ae tunda taji Voice ɗinsa jikinta ya shiga yin kerma,addu'o'in neman tsari tashiga karantowa abakinta,ta jima atsaye tana faman zullumin abun da zaibiyo baya kafin daga bisani ta daure tare da shiga cikin falon nashi,ƙamshin turaren nan nasa ne ya wanko mata hancinta har saida ta lumshe idanunta,tunkan taƙarasa ta hango shi kwance ya miƙe kafafunshi asaman 3 seater,jikinshi na sanye da pyjamas yellow,ba ƙaramin kyau su kayi mashi ba,kunnanshi na kare da wayarshi alamar waya yake yi,
   Gabanta na faɗuwa haka ta nufe shi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table dinsa,saboda tsabar rashin gaskiya,tana ajiye tray ɗin ta juya cikin sauri zata bar parlourn nashi,kamar daga sama taji anyi ma mayafinta kwakkwaran ruƙo ta baya,nan take mayafin ya sulale daga jikinta,zazzare ido waje sehrish tayi jikinta na kerma,nan take tashiga haɗiyar yawu,tsayawa tayi tana jiran maizo biya baya,
   Jin alamun motsin shi abayanta ya tabbatar mata da cewa shine yaja mayafinta daga jikinta,tsayawa tayi tana ambaton sunan Allah abakinta,ganin kusan minti biyar bata ji ya ƙara motsawa ba yasa tayi hanzarin juyawa a wani irin firgice sam bata tsammaci yana tsaye abayanta ba sai dai kawai taji ta kai mashi karo,ja da baya ta ɗanyi tana faman zare ido,tunkan ya tambayeta ta shiga cewa"dan Allah kayi haƙuri,nasan na 6ata maka rai,wlh nima bada son raina hakan ya faru ba,nashiga na gyara maka bedroom ɗinka ne,bayan na kammala shine na ɗan cire mayafina na ajiye asaman gadonka don naji daɗin yin aikin,ashe kafin na fito daga cikin toilet ɗin ka dawo,shine na same ka akwance kana bacci saman mayafina,saboda ina tsoran ka farka ka ganshi yasa nayi ƙoƙarin janshi daga jikinka,shine...cikin bacci batare da saninka ba ka...........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda jin yatsun hannunshi da tayi asaman lips ɗinta,alamar tayi mashi shiru,sannan ya hankali ya ɗan ware eyes ɗin nashi akan fuskarta............



 
 💋BOSS BATURE💋

Follow this link to join my tiktok acct👇


https://www.tiktok.com/@boss_bature?_t=8WKx0lm4jaP&_r=1



قصة حب رومانسية بين سحريش والجراح العام رفايت💋💘❤🤍❤💕💖

Father of soldiers (takun ƙarshe)



A tsananin tsorace take kallon fuskarshi ganin ya ware idanunshi yana kallon fuskarta,a hankali ya zame finger ɗinshi daga saman tausasan la66anta dake ta faman kerma,sai faman haɗiyar yawu take yi tsoranta wane hukunci zaiyi mata,sau biyu yana ƙoƙarin buɗe mouth ɗinsa zaiyi magana amma ya kasa,saboda ya rasa me zaiyi ma yarinyar,tun da yake wata ƴa mace bata ta6a ƙetare iyakar da yarinyar ta ƙetare ba,a matsayinta na wadda ba muharramarsa ba kuma ƴar aikin gidansu,ƙara matsawa yayi kusa da ita,cikin sauri sehrish ta ƙara ja da baya,tana faman girgiza mashi kai Alamar yayi haƙuri karya hukunta ta,tuni ta soma fitar da ƴan matan hawaye a idonta,ba komai take kallo ba face damtsen hannunshi da kuma wannan faffaɗan ƙirjin nashi,uwa uba yarda ya tsaya agabanta tamkar wani zaki,

Hannunshi yakai tare da ruƙe waist ɗinshi yana kallon yatsun hannunta dake ta faman kerma,
 A natse ya soma magana"I will punish you for the mistake you made in my bedroom on my bed,so that you know under whom you are working,cos u crossed your boundary,"
Gabanta ne taji yayi wani irin bugu jin abunda sgr yace,hankali tashe take kallonshi,muryarta har kerma take wurin cewa"bazan ƙara ba,"
   girgiza kanshi yayi alamar bai amince ba sannan yace"You are going to start frog jumping around the chairs without stopping, if you do that I will let you go, but if you dare stop,I will punish you badly," yana ƙarasa maganar tashi ya juya tare da komawa saman sofa ɗin yana kallonta yace"Am watching u,"yayi maganar tare da nuna mata blue eyes ɗinshi da 2 fingers ɗinshi,alamar idonshi na akanta, 
   Tamkar ta fashe da kuka haka taji,ga matuƙar tsoranshi da take ji,ga punishment ɗin daya bata na tsallan kwaɗi abunda ta tsana arayuwarta saboda tasan wahalarshi,ba abune mai sauƙi ba bazata ta6a mantawa da lokacin da fawan ya sanyata frog jump ba har jini ya 6alle mata,saboda tsabar wuyar da tasha har suma tayi lokacin,
   gyaran muryar da Sgr yayi mata ne yasa tayi saurin zuƙunnawa tare da kama kunnanta da hannayenta sannan a hankali ta soma yin tsallen kwaɗin,in da Allah yasota ma Wando ne ajikinta ba skirt ba da abun yafi muni,da sauri take yin tsallen har ta zagaya ta bayan sofas ɗin ta kuma dawowa ta gabansu duk yana kallonta,tun Sehrish tana yin tsallen kwaɗin cikin daɗin rai har ƙafafunta suka soma rurruƙewa,wani irin zogi suka shiga yi mata,nan take hawaye suka fara shararowa daga idanunta har da majina duka ta haɗa,
  Yana jin shessheƙar kukanta amma ko ajikin shi,a ƙarshe ma sai ya ɗauki lemu mai sanyi ya tsiyaya acikin cup ya shiga kur6arshi a bakinsa yana sha,tun yana shan lemun daga zaune har ya ɗan kishingiɗa kafaɗarshi saman sofa hand ɗin,
   A wani irin galabaice sehrish ke ɗaga kafafunta tana yin tsallen kwaɗin,a ƙalla ta zagaye kujerun kusan sau takwas amma sgr baice ta dakata ba,tun tana sa ran zai tsayar da ita harta fidda rai,saboda tsabar tsoro da firgicin da take ciki yasa ta gaza gane cewa sgr fa bacci ya kwashe shi asaman sofa ɗin,duk in ta zagayo ta wurinshi sai taga kamar idonshi biyu,batasan cewa tuni bacci yayi awon gaba dashi ba,har ya ajiye cup ɗin dayake shan lemun dashi,

Wani irin matsanancin ciwon kaine ya far mata,ga raɗaɗin da kafafunta keyi mata,lokacin da ta ƙara zagayo wa ta wurin shi,cikin shessheƙar kuka tace"...Am really sorry babban yaya,i ave realized my mistake,bazan ƙara ba nayi maka alƙwarin hakan," tabbas yajiyo muryarta acikin ears ɗinshi amma sam bazai iya buɗe idanunshi ba,saboda nauyin baccin da yayi,
  Ganin bai tanka mata ba,yasa sehrish cigaba da yin tsallen kwaɗayin da takeyi dakyar dakyar,tana cikin wannan yanayin wani irin stomach pain ya taso mata haikam,nan take ta yanke jiki ta faɗi saboda galabaitar da tayi,taji jiki sosai,

Sai faman zagaye hayam takeyi a tsakanin upstairs da kuma down,ba don komai ba sai don taga a wani yanayi Sehrish zata fito daga sashen sgr,har wani murmushin mugunta take saki don tasan cewa muddin Sgr yaga siraran gashi a cikin abincinsa dole ya kikkifa Mata mari,sannan ya kore ta daga yi mashi aiki,daganan  ita kuma zata samu shiga a wurin shi,gajiya ta fara yi da zagayen ganin cewa har ƙarfe sha biyu na dare tayi Sehrish bata fito daga part ɗinshi ba,hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,baƙin ciki kamar ya kashe ta,tsayawa tayi ruƙe da qugu tana cewa"Ko uban me yarinyar can takeyi a part ɗinsa har wannan lokacin bata fito ba!wlh na tsani yarinyar can,ko son ganinta bana yi,shisshiginta yayi yawa nasan yanzu haka tana can ta liƙe mashi tana kalle mun surar jikin mijina,Allah bazan ƙyaleta ba sai nayi maganinta mtssw,!"ta ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki sannan ta kama hanyar komawa bedroom ɗinta tana faman sambatu kamar wata zautacciya ,"

_💋Boss Bature💋_

Kwance yake asaman gadon Abbansu hannunshi rungume da pillow,yayin da idanunshi ke arufe tamkar mai bacci,
Yana jin lokacin da abbansu ya fito daga cikin toilet jikin shi sanye da Jallabiya,ƙarasowa yayi wurin gadon tare da samun wuri daga ɗan gefe ya zauna,sannan ya ɗan juya tare da kallon fuskar junaid da yayi likimo kamar mai bacci,hannu yasa tare da shafa sumar kanshi yace"sarkin rigima yayi bacci,"ya faɗi da murmushi a fuskarshi,janye hannunshi yayi daga saman sumar kan junaid,sannan ya miƙa hannu tare da ɗaukar wayarshi dake ajiye a saman bedside drawer,contact ɗinshi ya shiga ya lalubo numbar mommynsu junaid ya danna mata kira,nan take kiran ya shiga,cikin sa'a ta ɗaga kiran nashi,murmushi yayi tare da kara wayar a kunnanshi yace"Noorul ƙalbina"
  On the other hand alexandra tace"yau kuma soyayyarce ta motsa?ni zaka yaudara da kalamanka saboda kaji cewa zanzo nigeria ko?to ae ba saboda kai zanzo ba,zanzo ne don naga Yarona kuma da zarar nazo zan ɗauke abuna na dawo Australlia dashi,don bazan barshi a hannunku ba don ban yarda da irin rainon da kake mashi ba,"
   girgiza kai abbansu yayi tare da cewa"Yaushe zaki canza ne?ke ko tausayina bakya ji ne?baki damu da halin da nake ciki ba,na rashinki a kusa dani,ina fa sonki har yanzu kuma ban rabu dake ba,kece kika rabu dani kika kama hanya kika bar ƙasar nan batare da sani na ba,yanzu kinyi mun adalci"? Cikin sanyin murya ya ƙarasa maganar yana sauraron Amsarta
Junaid daya kasa kunne yana sauraransu sai faman murmushi yake yi idonshi a rufe,
   Shiru Alexandra tayi yayin da idanunta ke kallon sararin samaniya ta cikin windown katafaren bedroom ɗinta,kunnanta na kare da wayarta tana sauraron shi,muryarshi ta kuma ji yana cewa"kinyi shiru baki ce komai ba"?
  Ajiyar zuciya ta sauke tare da ɗan jinjina kai tace"me kake so yanzu"?
    Runtse ido abbansu yayi saboda ya rasa yarda zai fahimtar da ita,wata irin bauɗaɗɗiyar mace ce,ko don tayi aikin soja ne yasa ta kasance haka,saboda a tsaye take ba irin raunin zuciyar nan na mata,
   "Hossein in baka da abun cewa,Ni zan aje waya ne,"
  Muryarta ce ta kuma katse shi,a lokacin ranshi ya gama 6aci a faɗace yace"Fatima na gaji da irin wulaƙancin da kikeyi mun,nayi danasanin haɗuwata dake tun farko,kuma nayi danasanin haɗa zuri'a dake,saboda kin cutar da rayuwata,sam baki respecting ɗina a matsayina na mijinki,kuma uban ya'yanki,idan kinsan zaki tafi kibarni meyasa tunfarko kika sanyamun soyayyarki acikin zuciyata?
   Muryarshi araunace yayi maganar yanayin sautin kamar zai fashe mata da kuka,
   Jin tayi shiru bata ce mashi uffan ba yasa shi cewa"banaso ki dawo ƙasar nan!ki cigaba da zama acan,saboda zuwan naki baida amfani awurina,kuma babu ruwanki da ƴa'ƴana  dama can baki damu dasu ba,tun da har zaki iya tafiya kibarsu,batare da tunanin yaya rayuwarsu zata kasance ba"!
  Jin wannan maganar ta Abban nasu yasa hawaye suka soma gangarowa a idanun junaid,sam baiji daɗin yarda mommynsu ke 6ata ma Abbanshi rai ba,
   Bai jira Alexandra ta bashi amsa ba ya katse kiran nata tare da yin wurgi da wayar gefe guda,jiki amace ya kifa kanshi asaman gadon,idanunshi sunyi jawur sun cicciko da kwalla,
   a hankali hawayen suka soma gangarowa,kamar daga sama yaji tafin hannu a fuskarshi,cikin sauri yakai idonshi akan junaid dake share mashi hawayen fuskarshi,
  Cikin shessheƙar kuka yace"Abba don Allah kadaina zubar da hawayenka akan mommynmu,ba dole sai da ita zaka samu farin ciki ba Abba,Ni na isheka duk wani farin cikin duniyar nan,Abba ka ta6a faɗamun cewa ko kallona kayi kanajin sanyi aranka,why zaka Sanya ma kanka damuwa akan mommynmu?ka rabu da ita kawai Abba,akwai mata da yawa agari waɗanda suka fi ta hankali.........'
   Murmushi Abban nasu yayi jin abunda junaid yace,
   Miƙewa yayi daga zaune suna fuskantar juna yace"junaid bazaka gane ba!mommynku ba kamar sauran mata take ba,idon har tana raye ni bazan iya kula wata ƴa' mace ba,"
   ɗaure fuska junaid yayi tare da zum6ura baki yace"Saboda me Abba?me tafi sauran matan?duk yarda take 6ata maka rai?
    "Junaid she's special saboda ta bani babbar kyautar da har yau in na kalleta nake jin farin ciki araina,"
   Cike da mamaki junaid yace"Wata irin babbar kyautace wannan? Ya tambaya yana kallon Abban nasu,
   Murmushi Abbanshi yayi tare da nuna shi da yatsanshi yace"Am talking about u junaid!Matar da ta haifamun lu'u lu'u kamarka taya zan iya rabuwa da ita junaid?ta bani farin cikin da har na bar duniyar nan bazan ta6a samun makamancinshi ba,kyakkyawan yaron da kowa ke alfahari dashi,kowa yake so kuma yake ƙauna,Junaid bani da burin da ya wuce in farka in ganka akusa dani da ranka da lafiyarka...........'
  Tsagaitawa yayi da maganar yana kallon junaid da bakinsa yaƙi rufuwa saboda tsabar farin ciki kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha,sai faman washe baki yake yi,kamar wanda akayima albishir da gidan Aljanna,ya ma rasa mai zaiyi don tsabar farin ciki,a ƙarshe ya faɗa jikin Abban nasu tare da rungumeshi ya ƙankame shi sosai ajikinshi yana faman dariya,
    Zagayo da hannunshi yayi yana ɗan bubbuga Bayan junaid yaci gaba da cewa"I love u so much my baby boy,Allah ya nuna mun ranar auranka kafin nabar duniya,koda ace shine abu na ƙarshe da zan gani kafin na koma ga mahalicci na,Ina rokon Allah ya nuna min wannan ranar,da shagwa6a66an yarona zaiyi aure,zanso naga yaron da matarka zata haifa mana,wanda zamu dinga kira da Babyn baby,"
  Fashewa sukayi da dariya, suka dinga yi atare,har lokacin basu raba jikinsu ba,
   Ƙarar shigowar message a wayar Abban nasu ce,yasa junaid janye jikinshi daga na abban nasu sannan ya rarrafa tare da kai hannu ya ɗauko mashi wayar,ya miƙa mashi,
  Kar6a Abba yayi tare da duba message ɗin da aka turo mashi yana karantawa kamar haka
   "Forgive  me my love.......nasan na 6ata maka rai sosae,kayi haƙuri ka yafe mun kuma inaso kasan cewa nima ina sonka sosai har yanzu ba abunda ya sauya na sonka acikin zuciyata,zan dawo nigeria ne saboda na gyara alaƙata da uban ƴa'ƴana,da kuma ƴa'ƴan nawa,ka shirya tarbar amaryarka Alexandra...........'
  gaba ɗaya ya rikice saboda tsabar farin cikin saƙon da ya shigo mashi,saboda ruɗu har hannu yasa yana goge idanunshi wai ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login