Showing 42001 words to 45000 words out of 186291 words

Chapter 15 - Halin Yau By Surayyah Dee

18 Dec 2025

9741

mom!" Sannan ta juya ta tafi.

Ta isa da sallama yana tsaye yana amsa waya, ya yi kwalliya da yadin kufta kalar ruwan kasa (brown), ya dora hular da ta dace da kayan. Sosai ya yi kyau, musamman yadda sumarsa da hula ba ta rufe ta gaba'daya ba tana ta sheki alamun ta sha gyara na musamman.

Ya katse kiran yana zuba mata ido sosai sai kuma ya hau murza dukkan idanuwansa, ya sake kallon ta soasai, ya bude baki alamun mamaki tsawon sakanni goma sannan ya nisa ya ce, "Sa'adah ce kuwa, ko idona ne ya ke mini gizo?"

Ta tura baki tana dan murmushi tare da shagwabe fuska.

Hakan da ta yi sai ta sake burge shi ya ce, "Kin canja fa! Ba ki ga yadda kika yi kyau ba, ganin ki na yi tamkar 'yanmatan Ethiopia."

Da'di ya kamata musamman yadda bakinsa ya yi daidai da na Innar ta, ya lura da yadda take murmushi, ya fahimci tana son a ce ita mai kyau ce, ko ta yi kyau.

Ya ce "Ki fa daina wannan shagwabar ita ma tana sani a wancan yanayin!"

Ta rufe fuskarta da gefen Hijabinta, ba tare da ta iya cewa komai ba.

Ya sake cewa, "Idan ba so kike na zama agwagwa ba, to ki daina yin ta a yanzu. Ki tara mini ita zuwa lokacin da za mu tsinci kanmu a dakinmu!"

Ta sake rufe ido sosai tana ayyana wai shi ba ya jin kunya ne?

Ganin yadda ta rufe ido ta makale a bango sai ta ba shi dariya sosai.

Ya dan juya dan ganin ba wanda zai ji shi, ya yi kasa da murya ya ce, "Ba ki ji yadda na ji ba, ina ma ni kika makale ba wannan bangon ba! Kunyar nan ma burge ni take yi, komai na ki is special!"

Shiru ta yi ta kasa juyowa, bare ta tanka masa, tana ji a jikinta yadda idanuwansa ke yawo a kanta.

Da kyar ta bar jikin bangon ta shimfida tabarma tana cewa, "Bismillah!" Ya yi kicin-kicin da fuska tamkar ba shi ne mai walwala yanzun nan ba.

Ya ce, "Ba zan zauna ba!"

Ta dago ta kalle shi a kunyace ta ga yadda ya hade fuska, gabanta ya fadi, tana tunanin me ya 'bata masa rai kuma?

A hankali ta ce," Tafiya za ka yi?"

Ya girgiza kai sannan ya ce, "Zaman ne ba zan yi ba, ki dinga shimfida wa Honorable."

Ta yi shiru tana jin fargaba na taso mata!

Ta nisa ta ce, "Amma dai ai na ba ka ha'kuri, magana sai ta wuce."

Da sauri ya ce, "In dai sai na zauna a inda yake zama to kuwa magana ba za ta wuce ba!"

Ya juyar da kansa gefe guda, ganin yana Shirin dawo mata da yanayinsa da ba ta so na nuna ko in kula ta kalle shi ta ce "Bari na dauko maka wani abin zaman to."

Bai ce komai ba, ta nade tabarmar ta shiga da ita, ta dawo da kiret din lemon kwalba mai kwari, ta ajiye ta dora sallaya a kai, kamar ba zai zauna ba sai kuma ya zauna din.

Ita kuma ta zauna a kan wani dutse da ya ke zauren. Ta kalle shi ta ga bai ware ba, ta daure ta ce, "Ba don fishinka na gigita zaman lafiya ta ba, da haka zan so ganin ka kullum. yadda ba yanmatan da za su ga fuskar tunkarar ka, saboda kwarjini da tsare gida."

Dariya ta kwace masa, ya nisa ya ce, "Kina da son kai Sa'adah! Ba kya son na kula yanmata amma ke ba ki kiyaye kula wasu mazan ba."

Ganin ta yi kasa da kai sai ya canja maganar da cewa, "Mahmoud ya na gaishe ki"

A hankali ta ce "Na gode!"

Sun jima suna hira bayan ya sha ruwa, suka shiga ya gaida Inna, ya ajiye mata kudi, sannan su ka koma zauren, ba su dade da zama ba Baffa ya dawo, ya tarar da su, a kunyace, MK ya sauko daga inda yake zaune ya tsugunna ya gaishe shi. Baffa ya amsa cike da farinciki, har ya wuce sai ya dan tsaya ya ce, "Da ma kuwa ina son ganin ka, idan ka samu lokaci ka same ni."

Da girmamawa MK ya amsa da Fadin, " Koyaushe ina da lokaci."

Baffa ya ce "To bayan La'asar gobe idan ranmu ya kai."

Sai da ya shige sannan ya koma gun zamansa, Sa'adah na masa dariyar yadda ya takure.

Ya kalle ta ya ce, "Idan akwai abin da ya fi haka na kunya zan ji tunda yarsa nake so ya ba ni, ya kuma san abin da zan yi da ita!" Shike nan ya rufe bakinta ruf.

Ya zuba mata ido ganin yadda ta turo baki gaba alamun fishi-fishi.

Ya waske kamar bai gani ba, ya nisa ya kira ta da alamun seriousness "Sa'adah!"

Ta yi shiru, sanin halinta na shariya da sanin ta ji shi ya zarce da fadin, "Magana za mu yi ta gaskiya, ki nutsu ki ban hankalin ki."

"A kan kunnenki Baffa ya ce za mu yi magana, ga zatona mafi karfi ina ganin zai yi maganar idan mun shirya kanmu na turo da magabatana."

Nan ma ba ta ce kala ba.

Ya nisa ya sake cewa, "Kina ji na kuwa?"

Kai ta daga masa alamun tana tare da shi.

Ya ce, "Tsakaninki da Allah ki fada mini gaskiya don na san yadda zan tunkare shi. Mun kai lokacin da ya kamata a ce mun fahimci juna, maganar aure idan manya suka shiga ta kare fa! Ba maganar canjawa idan dai ba mayar da iyaye abokan wasa za a yi ba.
So nake yi, ki fada mini da bakinki idan Baffa ya tambayi mun shirya kanmu, me zan ce masa?"

Ta yi kasa da kanta ta kasa cewa komai, tsawon minti guda sannan ya dora da cewa, "Kar ki ji nauyin fadar gaskiya na yi miki al'kawarin zan fahimce ki, zan kuma fahimtar da Baffah yadda ba zai ga laifinki ba."

Ta kasa bude baki ta yi magana ita kanta ba ta san me yasa harshenta ya yi mata nauyi ainun ba? Tsawon mintuna yana dakon ta magantu amma shiru.

"Ina ta magana kin yi mini shiru kuma kin san ba na son ina magana kina ji amma ki yi kunnen uwar shegu."

Ta sake yin kasa da kai, da kyar kuma a hankali ta ce, "Ni to me zan ce?"

Bai ji dadin yadda ta ce ba amma sai ya ce, "kinsan me za ki fada mini da zai nuna kin aminta da Ni ko akasin hakan".

Ta kasa fadar ko daya, ya gaji da sauraronta ya ce "Shirunki yana nufin na yi hakuri, na sha kaye a hanun abokan takara".

Yana gani ta bude wayar dake hannunta wacce ta Inna ce ta fito da ita.

Ba zato ya ji wayarsa ta yi kara kadan, alamun shigowar sako (message) bai duba ba ga zaton sa MTN ne.

Ganin ta share ta hau daddana waya sai ya sake jin rashin dadi sosai, a tunzure ya ce,
"Silent again?"

A kunyace ta ce, "Ka duba wayarka!"

Bai yi musu ba ya dauko wayar sa ya shiga ma'adanar sakwanni (inbox) ya ga text din da ya shigo ita ta turo shi. Da sauri ya bude, harrufa uku kawai ya gani.

"*YES*"

Kawai ta rubuta wani irin dadi ya mamaye zuciyarsa da sauri ya ce, "Kin amince mini na turo Sa'adah da gaske?"

Kai kawai ta daga masa don ta sake ba shi tabbaci.

"Alhamdulillah!" Yake ta fadi tare da cewa "Na gode!" Ya bude murya sosai ya kira ta, bai jira amsawarta ba ya zarce da cewa, "Idan fa kin zabe ni har na turo aka nema mini aurenki, hakan na nufin kin rabu da Honorable, da wannan tabbataccen yaron! Da ma kowa da kowa, sai ni kawai.

Kin ga saboda na san kina da damar ki zabi wanda ya miki shi yasa nake danne kishina, amma tsakani da Allah idan har maganar aure ta kullu tsakanin manya dole ki rabu da kowa kin amince?"

Ba wani dogon Turanci ta ce, "E!"

Farincikinsa ya karu ya hau fadin, "In Sha Allah ba za ki yi nadamar zabe na a matsayin mijin aurenki ba."

Shauki ya debe su ba su ankara ba har aka fara kiran sallah sannan ya tafi yana cewa, "Duk yadda muka yi da Baffa za ki ji."





Alkalamin
*SURAYYA DAHIRU*
✍️✍️.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.


*TALLAH*!

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._








41-42



A Daren ranar Baffa ya sake zaunar da Sa'adah tare da mahaifiyarta, ya ce "Ina sane na bar ki kina sauraran wasu bayan Mutari.
Saboda na ba ki damar da shari'a ta ba ki, na kar na aurar da ke bisa dole, duk da shari'ar tace ni na fi cancanta na zaba miki mijin aure kasancewar ki budurwa.
Amma tunda muna wani irin zamani da 'ya'ya suke ganin sun fi iyayensu sanin abin da ya dace da su, ya sa na ba ki damarki, na sha fada miki aure zan miki, ba kuma zan miki auran dole ba, sai dai na dora ki akan shawara mai kyau. Alhamdulillah lokaci ya yi, don haka ki fada mini a cikin masu zuwa wajenki wa kika zaba? Ina son ya turo mini magabatansa a tsayar da magana guda daya."

Ta yi shiru kanta na kasa, Inna ce ta tanka , "Ai na ga alamar sun daidaita da Muutar din."

Hannu Baffa ya daga mata alamun ta yi shiru, ya bude murya ya ce, "Iyah tsakanin Alhaji Mamman da Mutari wa kike so?"

Ta sake yin shiru, ya nisa ya ce, "Dole fa ki yi mini magana saboda duk hukuncin da zan yanke, ya kasance da yardar ki, ba na so daga baya ki ba ni matsala, kwanakin baya da Alhaji Mamman ya same ni ban ba shi amanna ba, amma na ce ya nemi yardar ki, saboda shi ma mutumin kirki ne, ya samu yabo a wurin mutanen da suke kewaye da shi. Yanzu kuma lokaci ya yi da zan sallami daya a cikinsu."

Inna da ta ke sauraran su ta ji tamkar ta ce Alh Mamman zai sallama amma ta yi shiru saboda bai ba ta damar yin magana ba.

Ya sake kiran ta a karo na biyu, "Iyah!"

Ta amsa murya a dakushe. "Wa zan sallama a tsakaninsu? Ko kuma dukkansu ba ku shirya ba?"

Ta jima kafin ta bude baki ta ce, "Dazu Inna ta fada ai."

Da'di ya kama dukkansu, ya ce, "Kina nufi da Mutari ku ka shirya?"

Kai ta sake yin kasa da shi ba tare da ta amsa ba, Inna ce ta yi fit ta ce "Ka san ba za ta iya amsawa ba, amma na lura da Muutar ne za'binta."

"ALHAMDULILLAH!" Baffa ya furta a fili. Ya zarce da fadin, "Shike nan da kaina zan ba wa Alhaji Mamman hakuri, Allah Ya sanya alkhairi a tsakaninku, ki yi ko yi da uwarki wurin biyayya, Allah Ya tabbatar da alherin da muke zaton sa tsakaninki da yaron nan."

Da haka ya sallame ta wanda da kyar ta iya tashi.

Washegari kuwa bayan La'asar MK ya samu Baffa, zatonsa ya tabbata domin kuwa maganar turo magabatansa ya yi bayan ya tabbatar masa ya yi magana da Sa'adah ta ce shi ne zabinta. Godiya sosai MK ya yi tare da cewa, "Za su zo ba da jimawa ba."

Baffa ya nisa ya ce, "Ka yi shirinka a hankali sannan zan fada maka ni ba a kawo mini lefe sannan ni ma bana yin kayan daki, don haka ka shirya dakin da za ka ajiye ta da iya abin da za ka iya, ni ma zan hado ta da yan tarkacen da zan iya.
Daurin aure kawai za a yi sai kuma uwarta za ta dan yi taron mata a gida, zuwa yammaci da kaina zan kai ta dakinta, Ban yarda da wani taron maza da mata da sunan fati ko wani abu na daban ba! Idan kun tare kuna da ra'ayi, da damar yin walima wannan sunna ce sai ku yi. idan har wannan tsarin ya yi, akan hakan za ka turo mini magabatanka, Saboda idan sun zo, zan sanar da su."

Godiya sosai Mk ya sake yi tare da fadin, "In Sha Allah yadda duk ka ce haka zan yi Baffa, na gode sosai da karamci Allah ya saka da alheri."

Da haka suka rabu MK na jinjina halin wannan dattijon, ko irin su nawa ne suka yi saura a cikin al'ummar mu?

Gefe guda kuma tunanin yadda Sa'adah za ta karbi lamarin yake yi, ko ya ya za ta ji idan aka ce ba za a yi mata lefe ba? Sannan ya za ta yi idan ta gane cewa ita ma haka za a kai ta ba kayan daki, ba biki irin na zamani?😁

Da kansa ya ji dariya ta kufce masa haka ya samu gefe ya yi dariyarsa mai yawa, sai da ya gama a fili ya ce, "Sa'adah big girl ba lefe!" 😁

MK shiru ya yi bai fada wa Sa'adah tsarin Baffa ba, bai san mai yasa yake jin tsoron fada mata ba, ya ja bakinsa ya tsuke, ta ji maganar a bakin wanda ya tsara lamarin.


Takanas 'yan uwan mahaifin MK, Baba Umaru, da Baba Idi, suka taho Kano suka hadu da Alhaji Isa, suka rankaya gidan su Sa'adatu nema wa MK auranta. Kai tsaye ya ce ya ba su sannan sadaki kawai za su kawo masa. Bai boye musu tsarinsa na rashin yin hidima ba.

Dukkansu, sun yi farinciki, sun kuma yi amanna da tsarinsa, suna fadin ai mu ma da ga yau za mu yi koyi da kai don mu sami sauki a cikin zamantakewarmu, sannan darajar aure za ta karu za a daina fargaban yin sa, saboda an kewaye shi da hidimomi masu wahalarwa.

Baffa ya sake cewa "Na baku wuka da nama duk lokacin yaron ya kammala shirinsa kusa ranar aure da kan ku, sai ku sanar da ni, ina kuma rokon ku fada masa iya abin da zai iya shi zai yi, fatana dai Ubangiji ya albarkaci auren."

Godiya sosai suka yi
suna yaba halin kwarai irin na mahaifin Sa'adah, suka jaddada masa ba da jimawa ba kuwa zai ji ranar da suke ganin ta dace da shirin MK, suka sake yi masa godiyar wannan girman da ya ba su. suka rabu cike da farinciki, a hanyar su ma tattauna karamcin da suka gani suke ta yi.

Alh Isa ya ce, "Ai ni tun zuwan da na yi a farko na gane Mukhtar ya nemo aure a gidan mutunci, sai dai mu yi fatan Allah ya zaunar da su lafiya."

Dukkan su, suka hada baki wurin fadin, "Ameen."

Baba Umaru ya nisa ya ce, "Saboda karamcin wannan Mutumin, bayan sadakin da zan biya wa Mutari har kudin da zai shirya wa yarinyar daki zan ba shi ya kara saboda iyayenta su san muma mun iya karamci."

Su Alh Isa su ma suka hau fadin, "Ai kuwa mu ma za mu sake sabon shiri."

Sai da suka je gidan su MK suka yi wa Hajiya Babba bayanin halin da ake ciki, sannan suka tafi.

Dukkan dangin MK sun karbi tsarin mahaifin Sa'adah, na ba zai yi kayan daki ba, musamman da bai nemi a ba shi wani kudi ba, illa ma lefen da ya ce su ma kar su yi.

Da daddare suna falon gidan gaba'dayansu har Hajiyar Bichi, kasancewar duk sun zo gidan saboda haihuwa da Sameera ta yi, yau kuma aka yi suna, shi ne suka zarto gidan su. Hafsatu ce kawai ba ta nan, saboda a Lagos take aure, Hajiya Babba ta sanar musu.

Ta kare maganar da cewa "Kayan da na fara tarawa na lefe kuwa tabbas zan ba ta, don da sunanta na ke sayan su."

Hayaniya ta cika falon na yadda suka ji dadin tsarin suka hau fadin, "Ai kuwa dai za mu dage mu yi kayan daki masu kyau."

Abbas ya dubi MK ya ce, "Amaryar taka tana da 'kanwa ne?"

Falo ya sake daukar hayaniya Akil ya ce, "Saboda ka ji ba lefe ba bidi'oi?"

Shi dai MK bai sa musu baki ba, suka yi shewarsu, suka gama. Haka ma Hajiyar Bichi uffan ba ta ce ba! Haj Babba ce da ragowan yaran suke ta dabdalarsu.

Kwanaki uku tsakanin zuwan iyayen MK, Alhaji Isa ya sake yin tattaki da kansa ya sanar da Baffa suna son a yi auren bayan karamar sallah watanni biyar masu zuwa. Bai musa ba ya ce, "Allah ya sa ranmu zai kai"

Baffa bai yi kasa a guiwa ba ya hakurkurtar da Alhaji Mamman, da ke ba yaro ba ne rabuwa aka yi irin ta salin alin, duk da bai so hakan ba, amma ya hakura, ya kuma roki Baffa ya ba shi damar ganinta, a karo na karshe. Baffah bai ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login