Showing 147001 words to 150000 words out of 186291 words

Chapter 50 - Halin Yau By Surayyah Dee

18 Dec 2025

9708

ki gane ubangiji yana tare da ke".

Jikinta ya yi sanyi ta san kalamansa duka ba karya, illah wadda ya ce ta fi duniya, da hakane ai da sai ya bari kaddarar ta kasheta in yaso shima ya zauna jiran wa'adinsa babu aure har ya mutu, su hadu a aljannah su sake rayuwar da babu bacin rai, amma yanzu ya gama curarta ya bari wannan makirar da take boye ainihin kalarta, ta san komai nasa, ta mallake shi, shine zai zo ya mata da'din bakin wai ta zarce duniya? kai namiji Hankaka ne tabbas.

Ganin ta yi lakwas sai ya ce "kin gamsu kin yarda?"

Ai kuwa tamkar wadda ya mareta har huci take yi ta ce "Wallahi ko shiga kunnuwana wai kana sona fiye da duniya bata yi ba, na dai yarda Baffah da Jawad na zarce komai a gunsu".

Ya fesar da zazzafar ajiyar zuciya ya ce "shikenan ba sai kin yarda ba. Ko ba kya sona mu komawa aurenmu, son da nake Miki, da wadda Jawad yake miki ya isa yasa ki rayu cikin farin-ciki".

Ta goge kwalla ta ce "har abada ba zan yi farin ciki a hannun ka ba, ka rufe idonka ka ce mini ina ha'intarka, ka rufe ido ka ce mini ana maka sharing dina"

Muryarta ta fara rawa tabbacin tsumin bacin rai ya taso, ta nisa ta ce "ka rufe idonka ka barni ka dauki wadda kasan na tsaneta saboda munafuncinta, ta faki idon mutane ta tsokane ni, amma sai ta layance a kuma bata gaskiya. Allah ne ya rufawa al'umma asiri ba karatun lauyanci ta yi ba, dan anga kwarewa wurin bada kariya ga karya".

Da 'kyar ya ce na janye kalamina, wallahi tashin hankali ne da kishinki, Amma nasan ha'inta dai babbar ha'inta ba zaki yi ba, na san ni ka'dai ne na muaamalance ki, na tabbatar da hakan har zuciyata".

Wani abu mai nauyi da ya danne kirjin Sa'adah shekaru uku ya fa'da mata sai dan saura.

Ta ce "to shikenan na yafe maka. Amma ka sani gaskiya ban da buri ko sha'awar auren mai mata kishi kashe ni zai yi, kawai ka barni na auri wadda zan sami nutsuwa, ka bar ni nima na dandana wani namijin kamar yadda ka ke dandana Balarabiyar Yemen".

A sanyaye ya ce "Sa'a ina jiye miki tsoron kar ki zama ajalina, domin kuwa banda lafiya, duk sadda na ganki sai kin yi mini fami a akan jinyar da nake yi".

Kai tsaye ta ce" Tunda bakin cikin ka bai mayar da ni gawa ba, na tabbatar kaima ba zaka zama ba".

Cikin gajiyawa ya ce "Next week Jawad zasu yi hutu, gaba'daya zai yi hutunsa a gurinki".

Maimakon ta ji dadi saboda ta san dan ya faranta mata ne yasa ya yanke wannan hukuncin, sai ta yi nufin gwasale shi.

Ta ce "bana bu'katar ganinsa ma bare ya mini hutu, inace saboda kar ya zo na zuga shi yasa ka kai shi makarantar kwana? Saboda kana son sai ya so Farida sama da ni yasa ka hana ya kwana a gidan nan sai dai ya zo ya yini? To shima na barka maka shi ban bu'katarsa, Ni kuwa a duniya me zaka mini na huce, ka zalunce ni iyaka".

Kafin ya yi magana sai ganin Innah suka yi, a ladabce Mk ya sunkuya ya gaishe ta, ta amsa babu yabo babu fallasa, daga gaisuwar bata ko tambayi Hajiyarsa ba bare matarsa, ta juya tana cewa "kin dora girki kin barshi zai kone, daga cewa zaki karbo sako?".


Wannan shagulatin bangaro da Inna ta yi masa ya matu'kar dukan zuciyar sa, yana ganin rashin nasarar sa a fili, Bai ga laifinta ba ko kadan, domin ya fahimci tana kan fahimtar su Baba Isa da Hajiyar Bichi ne. Wato Baffah ne kawai hoope dinsa.

Akwai gumurzu kenan dan kuwa sai inda karfinsa ya kare, yanzu ne zai yi dambar jefa alkalamin sa cikin Tawada. Domin ya ga maneman nata dukkansu basu da makusa, shine ma mai tarin kalubalen rashin samun goyan baya a wurin iyaye da Sa'adatu sa'ar Mata.





Surayya Dee
✍️✍️.

🌺 *HALIN YAU*! 🌺

NA

*SURAYYA DAHIRU*.

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/



*_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai da satar Dukiya._*

_*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.



*GAISUWA GA*
*HAUWA BELLO GANDI*.
*MUM KHADY*.

98-99.


Har sati ya zagayo Mk bai da nutsuwa, Farida kanta bata da sukuni adalilin halin da take ganin Mk a ciki, duk yadda take jin kishin Sa'adah sai take yin jarumtar boyewa.
Take ta hadiye sauyin da take gani a tare da shi, gefe daya ma sai take hilatar sa da bashi labarin fa'dansu da Iyah a FGC, idan kuwa ta yi hakan sosai ta ke samun walwalarsa ya yi ta dariya, hirar kuma ta yi tsayi.


Ranar dauko Jawad da wurwuri Mk ya tashi yana ta saurin tafiya, wani irin zumudin dawowarsa yake yi domin shine tsani na biyu da zai taimaka wurin shawo kan Sa'adah. Ya tuna yadda Jawad ya matsa mata ta gaishe shi ranar visiting. Ya sake tuna rokon da ya mata akan ta yarda su taho Kano tare, dalilin da ya zama sanadin da ta doke shi.

Ya dinga murmushi yana jin kwarin guiwa na shigarsa.

Tun jiya kuma Farida take ta faman hada masa snacks din barka da zuwa.
Domin a harkar Baking ta yi zarrah, abinci wahalar sarrafawa yake yi mata amma idan ta yi za'a ci cikin dadin rai ba wai iyawa ne ko kadan bata yi ba. Amma harkar cake da su meatpie hadi da su samosa tafi karfi anan.

Wannan karon har wani cake ta yi masa na mussaman, tamkar na murnar zagayowar haihuwarsa saboda girmansa da kyaunsa.
An rubuta welcome to Home Dear Jawad!.

Lamarin da ya farantawa Mk rai ba ka'dan ba, ya dinga gode mata, tare da yabawa.

Yana futa ta zube kan kujera, tana son ta ga dame Mk ya rageta?

Ta gama tunaninta ta gamsu bai rageta da komai ba, ko a harkar auratayya kuwa, anan bangaren ma ta lura yana daga mata kafa soasai saboda lalurarta, amma bu'katar sa ta zarta yadda yake mu'amalantar ta saboda rauninta da yake gani.

Tsananin son Jawad da yake yi ne kawai yake dan mintsinin zuciyarta, domin ta gane son uwarsa ne ya shafe shi. Ta kuma amince ba laifi bane yin hakan, sai dai zuciya da bata da kashi, yasa take jin rashin da'din soyayyar, duk da kuma zata shaidi soyayyar Jawad bata rufewa Mk ido ya kasa tsawatar masa ba, yana iyakar kokarinsa wurin saita yaron, ko akan al'amarinta ma ba ya yi masa ta Da'di.

A bangare 'daya ne, take ganin raunin Mk akan 'dan nasa, matu'kar suka fita shopping, indai ya ga ta zabi kaya to kuwa sai ya daukarwa uwarsa irin kayan sai banbancin kala, Mk kuma baya iya hana shi, ko cewa ya yi ya rage, da zarar ya bata rai shikenan zai ce ya dauka.

Ta dinga jin sha'awar haihuwa na mamayarta, ta daga hannu ta ce "Na sani sarai baka manta da ni ba ya Allah! Idan ka tashi bani, ka bani mai lafiya, mai jin kai, mai kuma albarka. Ina neman tsari da wadda zai gigita zaman lafiyata da ta mutanan da suke kewaye da shi, Ina neman tsari da marar lafiyar da jinyar sa zata shagalar da ni yin ibada da yawan tuba da godiya bisa ni'imomin da ka mini marasa adadi".

Hawaye ya ziraro mata ta sa tissue ta goge idanuwanta, ta sake cewa"Allah kar ka bari na kunyata, kai ka halattawa maza yin mace sama da daya, albarkacin yarda da hakan da na yi Allah kar ka bari na wulakanta akan wata da muka yi tarayya a jinsi guda".

Kuka sosai ya kwace mata saboda kishin Sa'adah na neman hanata sukuni a zuciya.

Ta Dade kafin ta tashi ta yi wanka, ta doro alwallah ganin takwas har da rabi sai tada sallar walaha, tana ta rokon a sau'ka'ka mata kishi, a kuma karawa Mijinta sonta da tausayinta.

Ta rufe addu'ar da yiwa Mk fatan samun cikakkiyar lafiyar da zai gamsar da su, da kuma budin arziki, ta sake rokar masa ikon yin adalci, tana kuka take cewa Allah ka hana shi zaluntata, Allah ka bashi karfin zuciyar da zai yi adalci na gaskiya.

*Ko mata nawane masu irin wannan dabi'ar?*
*Shin kina sallar Duha kuwa?*
*Idan ba kya yi maza ki fara domin Allah ya yi rantsuwa da lokacin, sannan kin yiwa gabbanki sadaka a yinin gaba'daya*.

Sun iso Wudil, Mk ya ji bari ya ziyarci tsohon amininsa da suka yi F.C.E. Bichi tare.

Ya laluba ba lambar wayarsa, ya dai dinga shiga hanyar ya gano gidan.
Ai kuwa a kofar gidan ya tarar da shi yana alwalar sallah juma'ah.

Da wata irin murna ya kar'bi Mk! Ganin lokacin sallah ne kawai sai suma suka yi alwalar suka zarce masallaci.

Suna dawowa aminin nasa ya baibaye su da abinci tamkar dama yasan da zuwansu, Mk ya dinga tsokanar su da cewa wai har yanzu baka kara aure ba? Kullum uwargida na office?"

Dai dai lokacin matar gidan ta dawo sanye cikin uniform tabbacin Ma'aikaciyar lafiya ce. Mk ya tasa ta gaba yana fa'din " bazai yiwu kullum kina barin aminina shi ka'dai a gida ba, dole zamu lalubo wadda zata zauna ta kula da shi.

Tababa da ke mai kunyace ta fice ta bar Mk na yi musu sha'kiyancinsa da baya gajiya.

Za su tafi ta kawo turare ta bawa Jawad, da wata kullin leda mai dauke da man shafawa da na zafi ta ce na Hajiyar Bichi.

Mk ya tsaya cak yana fa'din" Tababa ta Malam ki ji tsoron ubangiji, ita kuma Farida ina nata sakon, gaba'daya kin saka son zuciya a lamuran ki, saboda ba kawar ki ba ce ita"

Da sauri ta koma daki ta dauko kyawawan mafitai guda biyu ta ce ga shi nan, ta yi maka fifita ni bana son sarhutunka".

Ya karba yana fa'din kin fanshi kanki, yayin da mijinta ya yi gaba yana fa'din ranar da za'a mata amarya ai ban san irin boren da zata yi ba, idan ka ga yadda ta yi kukan aurenka sai ka yi mamaki, ta taya Sa'adah kuka irin wannan ina kuma ace ita za'a yiwa?'

Mk ya murmusa ya ce ai kuwa dai Tababa kwantar da hankalin ki, daga yadda na ga kin iya karrama ba'ko , zaki dade kina jan zarenki, muma kaddara ce ta fado mana, Ina fatan idan kuma kaddarar ta fa'do muku ba zaki yi watsi da kyawawan dabi'unki ba".

Ya damkawa yarinyarta karama kudi, Yana ta godiya da karamacinsu, ya tafi ya barta da sanyin jiki tana addu'ar kasancewa ita ka'dai.

Har la'asar Mk na Wudil domin tare da aminisa suka je ainihin gidan su Baba Isa ya ziyarce su, suka dinga sa masa aalbarka ya ajiye musu buhun shinkafa da katon din taliya, har da ku'di a kanin Baba Isa Wanda shine babba a gidan yanzu.


Sai da suka fito ya ajiye Aminin nasa a kwanar gidansa, suka yi sallamah.

Sun tsallake gadar Wudil ya samu wuri ya tsaya. Ya ce "Jawad dawo gaba kusa da ni, kana mini hira".

Hakanan kuwa aka yi, sun zo dai dai Yar gaya, Jawad ya ce "Allah sarki Muhsin Yargaya! ko yana ina yanzu?" Ya dinga bashi labarin Muhsin da irin halin da yake ciki da matar Babansa.

Nan Mk ya fahimci inda Jawad ya samu dalilin juyawa Farida baya, ya dinga jin tausayin yaran da suke fuskantar kalubalen rashin rayuwa tare da uwarsu.

Cikin hikima ya ce "Ashe Muhsin ya fa'da maka u have to be careful with Aunty saboda kar ta raba mu?"

"Eh mana Malam! Saboda na san kai baka san hakan zai iya faruwa ba".

Mk ya yi murmushi ya ce "Jawad kowa da halinsa! Da zata raba mu da tuni ta yi hakan, fa'da mini ta ta'ba dukan ka lokacin da muke Uk?"

Ya girgiza kai alamun a a, Mk ya zarce da fadin "abinci ne bata baka ko?"

Da sauri Jawad ya ce "Ah Malam tana ba ni, every day sai ta cika mini lunch box dina, abincina ya fi na kowa yawa, kullum sai na dawo da shi".

"Ka ga kenan ba halin su daya da Waccan da abokinka yake baka labarinta ba".

"Amma Malam ai ita kake so ba Mami ba".

Jikin Mk ya yi mugun sanyi a shekaru sha uku Jawad ya yi wannan maganar? Al'amarin yaran yau idan kana daukar maganar su tabbas zasu raba tsakanin ka da jama'a ne, ka yi ta ganin tamkar kitsa musu magana ake yi. Ko kuma ana koya musu iyashege ne alhalin kuma abin a jikinsu yake, sai dai ayi ta nuna musu kyakkawar turba cikin azanci da nasiha.

Mk ya nisa ya ce "wa ya fa'da maka bana son Mami? Ita ce fa ta haifa mini kai! Kasan kuma u are my only son, dole kuwa ta zamo very precious to me".

Da'di ya kama Jawad ya ce " To yaushe zata dawo gidan mu, tunda we are Muslims, polygamy is allowed, above all ma ka mini al'kawarin zan dawo hutu na ganta a gidanmu ba a gidan Baffah ba".

"Eh na yi maka ban kuma manta ba. Amma matsalar itace bata mini magana, bata gaishe ni, har Baffa yana mata fa'da amma still bata ji ba".

"Ni zan fa'da mata ta daina yin haka tunda kullum sai ta ce mini arogance ba kyau, ba dabi'ar mutanan kwarai bane".

" Yauwa sannan ka fa'da mata, kana son ganinta a gidanmu, if not jirgin nan da zaka siya mata zai zama nawa".

Dariya Jawad ya dinga yi yana cewa" Malam ka damu da jirgin nan, amma ai yanzu na ce har da kai zaka shiga. Ni ban san me yasa ta daina son dawowa ba, bana manta sadda take kukan so take ka zo ka dauke ta mu koma gidanmu"

Jikin Mk ya yi sanyi ya ce "tafiyar da muka yi, muka barta ne, amma idan zan sake komawa da ita zan tafi, kai kuma ka zauna tare da Anti a anan".

"A a Malam gaskiya ba a yin haka, da ni za'a tafi"
" To na yarda da kai zamu tafi, yanzu idan ka je gurinta sai ka yi ta bata hakuri ta dawo ta zauna da mu".

Murna tamkar Jawad ya zuba ruwa a kasa ya sha, wani irin farin-ciki ya bayyana a dukkan jikinsa

Sun iso kano Mk ya kalli Jawad cikin uniform dinsa sai ya dinga tuno shima lokacin da yake makarantar su ta 'Karaye. Haka yake tamkar Jawad, sai dai da alamu Jawad yana iya zarta shi tsayi domin a yanzu ma ya kusa kamo shi. Tsayin Jawad da saurin da karatunsa ya yi sai ake ganin tamkar ya zarce shekarunsa.

Da tarin kauna ya ce " A ina kake son yin hutunka?"

Kai Jawad ya sunkuyar ya ce "gidan Hajiya".

Mk ya ce "Antinka fa tana can ta shirya maka something special".

"Zan je amma ni gidan Hajiya zan zauna".

"Me yasa to ba zaka je unguwa uku ba?"

Ya marairaice tare da cewa "
Na san idan na ce can zani ba zaka yarda ba".

Da sauri Mk ya ce na yarda Jawad! Ka yi hutunka duka acan idan kana so".

Jawad ya kalle shi da mamaki! ya ga seriousness a fuskar Baban nasa ya kasa gasggatawa ya ce " please Malam are you serious, are u sure?"


Da sauri Mk ya kada kai ya ce very sure Babana! Yanzu zamu je gida kaa ci abin da Anti ta shirya maka, daga nan sai mu zo ka gaida Hajiya, sai mu koma ka kwana tare da mu, tomorrow morning da kaina zan kaika gidan Baffah ko gidan Anty Sumayya ko ina kake so nan zaka je".

Ya dinga murmushi irin murmushin Sa'adah, wurshiryar da ya samu daga gareta ya sake kawata murmushin nasa".

Da farin ciki sosai Mk ya ce "kyaun ka na bayyana idan kana smiling my boy".

Jawad ya sa hannunsa ya rufe fuskarsa wai shi kunya.


Da murna sosai Farida ta karbi Jawad ta dinga ina ka saka da shi, karshe ya shige dakinsa da komai na ciki blue ne, irin kayan alatun da aka shirya masa duk dan a hilace shi ya daina gudun gidan basu yi tasiri ba.

Wanka ya yi, ya shirya ya fito ya tarar da kayayyakin da aka tanada dan shi kala kala.
Farida ta dinga rawar jikin kyautata masa adalilin taga sassauci a tare da shi fiye da wattannin baya da ko kallon inda take ba kaunar ya yi. Ta ji farin-cikin sauyin da ta gani a tare da yaron.

Sai yamma lis suka fice da Babansa.

Basu dawo gidan ba sai dare sosai domin har sai da Jawad ya yi barci a dakin Hajiya.
Da ya zo yana tashinsa Hajiya ta ce
"Barshi mana tunda ya yi barci".

Da sauri ya ce " A a Hajiya bari kawai mu tafi lalla'ba shi nake yi ya daina gudun Farida, ta dora hankalinta akansa, amma yana gudunta tamkar kunama, yau dai na ga ya fara saukowa, gobe zan kai shi wurin uwarsa dan hankalinsa ya kwanta".

Hajiya ta ce "dan hankalinsa ya kwanta, ko dan ka samu dalilin ganin uwarsa babu hijabi?"

Mk ya ce "haba Hajiya"
"Haba Hajiya ko dai haba gaskiya?"

Washagari kuwa ya kai shi gidan da tarin tsaraba Niki niki tamkar wadda zai shekara, har da cake dinsa na murnar dawowar sa gida, bai ci ba, Mk ya ce ya taho da abinsa. har cikin gidan Mk ya shiga ya tarar da Innah na yin wainar shinkafa irin ta garin su Shafa'atun Bauchi ko da yake itama Innar ai daga Gamawa take kenan Inna Yar Bauchi ce. Sa'a na kicin na hada miyar cin masar.

Ya dinga tuno yadda Sa'adah take yi masa waina da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login