Showing 45001 words to 48000 words out of 186291 words

Chapter 16 - Halin Yau By Surayyah Dee

18 Dec 2025

9722

ba ya ce zai iya ganin ta. Maimakon ya jira a turo masa ita sai ya ce bari ya je ya dawo.

Ashe sayayya ya tafi lodowa, bayan ya dawo bai jima ba, ya ba wa Sa'adah manyan leda har biyu shake da kayayyaki, yana fadin, "Na gode da mutuntuwa, Ubangiji Ya sanya alheri a tsakanin ki da wanda za ki aura" Ya yi mata sallama ya tafi yana jin ciwon rasa ta don so yake mata na fisabilillahi.

Sai a lokacin Sa'adah ta ji sanyin jiki tana jin tausayin sa na ratsa ta. Tana shiga gida, ta zauna kusa da Inna ta fara bude ledar da ya kawo mata. Ta shiga dubawa, manyan leshi masu tsadar gaske guda biyu, da shadda getzna, ita ma biyu, da kuma atamfa Super Wax ita ma biyu, kowanne kuma da mayafinsa sai turaruka. 'Dayar ledar kuma takalmi da jaka ne har set shida masu tsananin kyau da tsada, da envelope wanda da dukkan alamu kudi ne, za ta ya ga ke nan,
Inna ta ce, "Kar ki bude ki bari Baffan ku ya gani".

Inna tana daga kaya tana fadin, "Wannan ya gane cewa aka yi ya yi ha'kuri? irin wannan kayan sai ka ce mai hada lefe?"

Sa'adah dariya ta yi sannan ta ce, "Kai Inna duk da dai kayan masu daraja ne amma ai ko an sayar da su sai dai a hada lefe irin local din nan."

Zuba mata ido Innar ta yi, sai kuma ta yi kwafa sannan ta ce, "ko ma yaya ne ai an yi 'ko'kari wata ai ba ma za a mata lefen ba, bare ta ga ya yi ka'dan."

Cikin dariya sosai Sa'adah ta ce, "Yo kuwa Inna wacce ba za a mata lefe ba ai sai bazawarar da ta sarayar don tana bu'katar auren, da kuma budurwar da ba ta da daraja ake neman kai da ita."

"Dariya ita ma Innar ta yi tana cewa "Ashe yayarki ma ba ta da daraja! don kuwa babu lefe aka aurar da ita, ba kuma neman kai mu ka yi da ita ba."

"Auran Anty Sumayya ai irin na zamanin jiya aka mata, kar ki ba da misali da auranta"

Ta nisa ta ce, "Iyah ba ki ga kuma saboda mijin natan ya san mutunci ya zame mata irin mijin da ba a cika samun su a Yau ba! Ke da kanki kin san mijinta irin mijin JIYA ne ba na YAU ba, ki yi fatan dacewa kawai, duk auran da aka ƙaranta wahala da bidi'a ya fi karko ya fi albarka".

Cike da rashin gamsuwa ta ce, "A'a Inna gara dai a yi maka din, mijin ma ai sai ya raina ka, danginsa su isheka da gorin sadakar ka aka ba shi."

Shiru Inna ta yi ta kyale ta, tana tunanin ashe akwai kallo ranar da tasan irin auran da za'a mata.

Baffa da ya ga kayan da Alh Mamman ya kawo bai yi fada ba, kamar yadda yake yi a baya, ya farke envelope din sai ga rafar dari biyar wato dubu hamsin wanda ta zarce darajar dubu darin yanzu.

Ya ajiye kudin, kayan kuma ya ce su dauka ta yi amfani da su, tunda dai sai da aka fada masa gaskiya sannan ya ba ta. shikenan rabuwar su da Alhaji Mamman.

Tunda aka tsayar da maganar aure Sa'adah ba ta sake tsayawa da saurayi a fili ba, sai ta waya wanda suke cika mata waya da kudi, sai kuma Khalil da ta kasa rabuwa da shi duk da ba ta yarda ya zo gidansu sai dai idan ta je gidan su Halima ko kuma idan ta je gidan su Zainab Ma'aji sai ya zo.

Soyayyarta da MK a gurinta za ta ce ba laifi, idan ya kira ta a waya yana dan jimawa su yi hira, haka nan yanzu sau biyu ya ke zuwa zance a sati, wani zubin ma har sau uku.

Amma dai ita ba sosai ta gamsu da kulawarsa ba, kawai dai tana bin sa da yadda yake yi, da fatan Allah Ya sa ba soyayyar ne bai iya ba ta bakin Halima da Safina, da suke kushe shi duk da sai yanzu da aka tsayar da maganar aure, suka san da gaske soyayya suke yi.

Kiri-kiri suka nuna mata me zai sa ta yi gangancin barin Alhaji Mamman inda za ta huta, ta bige da auran mai fama da alli da hidimar gidan su?

Ita dai Sa'adah sai dai ta ji su, ta yi shiru. Musamman da ta ta'ba ce musu ba son sa take yi ba Baffa ne ya mata dole, ai nan ma suka mata ca tare da cewa, "A wannan karnin na 21st century za a miki dole?"

Ta yi shiru tana jin yadda suke ta sakin maganganun rashin 'da'a tare da ingiza mai kantu, suna jaddada mata da dai ta auri mugun Malamin da ya gama tozarta ta a bainar nasi, gara ma ta auri Khalil Ibrahim sa'anta.

Shiru take yi, wani lokacin zuciyarta ta shiga wasiwasi akan MK Bichi, musamman yadda bai kai su Khalil nuna mata soyayya ba. Amma dai ta san ba ta isa ta koma ta ce wa Baffan ta ta fasa ba.




Alkalamin
*Surayya Dee*
✍🏼✍🏼.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.


*TALLAH*.

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._








43-44



A kwana a tashi ba wuya wurin Ubangiji. Watanni biyu suka zo suka shude tamkar walkiya, mai ya'ki da zuciyarsa kadai ke ribatar lokacin sa a cikin wannan zamanin da ababen shagala suka kewaye shi.

A wannan lokacin manhajar 2go ta bullo, matasanmu samari da yanmata suka yi tururuwar karban wannan sabuwar manhajar wanda hakan ya taimaka wurin sake ruguza tarbiya matasa da yawa, saboda yadda ake hira da musayen hotuna na rashin da'a ba tare da jin shakku ko nauyi ba.

Sa'adah na cikin jerin yan matan da suka yi tashen 2go da taimakon su Safina da Halima, yini take yi da waya a hannu har sai da Inna ta fahimci sabuwar rayuwar da ta shiga na yadda ta fi bawa waya muhimmanci fiye da komai.

Ada kafin Inna ta fito da safe Sa'adah ta kammala komai na gyaran gida, wani lokacin har abin karin kumallo za ta yi, musamman idan Baffa ba ya gari, amma a yanzu sai ta kai rana ba ta share gidan ba, ga wanke-wanke a gefe kudaje na bin su, ko karyawar ma sai Inna ta yi ta faman kiran ta sannan za ta fito, Nan ma tana cin abincin amma wayar na hannunta, tana ta latse-laste tana murmushi.

Wannan abin ya yi matu'kar damun Inna musamman yadda ta lura wanka ma Sa'adah sai ta kai la'asar ba ta yi ba, sabanin lokutan baya da sanyin safiya take wankanta da zarar ta kammala ayyukan gida, amma yanzu sai yamma likis ko ma dare.

Ranar wata Litinin aka tashi da rashin wuta a unguwar gabadaya, cikin rashin sa'a ta kwana da rashin caji a wayarta, don haka sai ta tashi sukuku da rashin karsashi. Tana kwance lamo a kan katifarta, ta kalli agogon bango dake jikin dakin, ta ga karfe 7 na safiya, sai ta ga lokacin ma baya gudu don haka sai ta yun'kura ta gyara dakinta, ta gangara tsakar gida. Kafin wani lokaci da ba shi da yawa ta gama komai har wanke-wanke, gefe kuma ta dora musu abin da za su ci.

Koda Inna ta fito ta gan ta, a tsakar gida sai mamaki ya kamata, musamman yadda ta gan ta ba waya a hannunta, ta gaishe ta ita ma ta amsa da walwala, sai da suka karya, ta yi wanka ta shirya ta yi fes da ita, ta fito tsakar gida ta sa tabarma ta zauna saboda lokacin zafi ne.

Sai lokacin Inna ta dube ta ta ce "Wannan ita ce Iyah da na rayu da ita, wannan ita ce Iyarmu, ta jiya da ragowar kwanakin da suka shude ba Iyar mu ba ce ma'abociyar aikin gida da kuma ado"!.

Kunya ta kama Sa'adah ta sa hannunwanta biyu ta rufe fuskarta, ita kanta ta san ta shagala, tana son ta tashi ta yi ayyukanta, amma sai ta kasa ajiye wayar tana ganin bari a dan jima, a haka har sai lokaci mai yawa ya tafi ba tare da ta an kara ba.

Cikin hikima Inna ta sake fadin, "Ko a mafarki idan aka nuna mini wai zai ki zama yadda kika zama Iyah zan karyata na kuma yi gaggawar neman miki tsari da wannan karko irin na kifi.
Ta ya ya za a ce kin rayu kina tafiyar da komai na aikin gida da tsaftar jikinki akan lokaci da kuma kuzari, amma sai da aurenki ya zo gaf kuma sai lalacewa ta zo miki? Wayar nan mai tsada ta zamani hatsarin dake cikinta ya fi alherin da ke tare da shi. Ki rabu da wannan shiriritar tun ba ki fada tarkon da za ki kasa fitowa ba!"

Jikin Sa'adah ya yi sanyi sosai tana gaskata mahaifiyarta, yau kadai da wayar take kashe ta samu rarar lokaci har sallar walaha ta yi. Ta kuma samu sukunin tattaunawa da uwarta, ta yi abin da ya dace na ayyukan yau da kullum.

Inna ta sake nisawa ta ce, "Ba namijin da za ki je kina masa wannan ba'kin dabi'un da kika fito da su, ku samu zaman lafiya da shi, duk son da yake miki kuwa. Ban hana ki amfani da waya ba, amma ki dinga ajiye ta sai kin kammala komai na aki, nauyi ne zai sake kama ki, shi namiji idan yana da mata komawa yake yi tamkar jariri komai sai an yi masa, ta ya ya za ki iya kula da miji da hidimar gida da wannan danne-dannen wayar da tun ana ganin na 'dokin wayar ne har kuma ya koma na kauyanci da asaranci ya zarce hankali da ka'ida."

A hankali Sa'adah ta ce, "Zan gyara Inna."

"Na ji za ki gyara, sai mai za ki ce mini kuma"? Inna ta fadi haka tare da zuba mata ido.

Cikin kunya "Sa'adah ta ce kai Inna don Allah, to ki yi hakuri."

Kai tsaye ta ce, "Tafiya za ki yi ki fara rayuwa da wani mutumin da ba ki saba da shi ba, ba shi kadai zaman zai kasance ba har da dukkan ahalinsa don haka ki koyi ba da hakuri idan kin yi laifi, ki kuma zama mai karbar gyara yayin da aka gyara miki laifinki, wannan shi ne mafi dadin zama a cikin mutane, na lura da ke ba da hakuri na miki nauyi, sai tura ta kai bango kike tuba wanda alamu ne na girman kai. idan mijinki ya gane kina da girman kai kuwa, wahalar ki zai yi don shi ma girman kan zai miki indai ya san ciwon kansa, sai dai idan solobiyo ne."

***

Bangaren MK yana ta Shirinsa musamman na gyran gidan da zai zauna, saukin da ya samu gidan mallkinsa ne da ya fado a gadonsa, tun lokacin yan haya suke ciki sai yanzu aka tashe su yake gyara, a unguwar Gadon Kaya gidan yake, ba wani babba ba ne amma tsarin gidan ya yi kyau, falo ne matsakaici mai dauke da manyan dakuna biyu da bandaki a cikin daki daya. Sai tsakar gida mai matsakaicin girma, daga gefe wani dakin ne shi ma da bandakinsa, sai daya gefen kuma kicin ne da wani bandakin karami, daga harabar gate kuma akwai karamin filin da zai dauki mota guda daya, ya shuka flowers sun fara fitowa wanda nan gaba za su 'kawata gurin.

Gini ne mai aminci amma ba tayals ba ne siminti ne a dakunan.
Shi kuwa a kokarinsa na son dadawa amarya Sa'adah yake son sanya mata tayals a falo da bandaki duk da a lokacin an fi saka carpet irin dan yankan nan.

Aka fara aikin gida sai lashe kudi yake yi sosai, wanda hakan ya sake mayar da MK ya zama very busy kullum aka tashi a makaranta yana gidan gurin masu aiki, ko wurin neman ku'dinsa ba shi da lokacin kansa wanda hakan ya sake karfafa
zaton Sa'adah na bai iya soyayya ba.

Shi yasa take kula Khalil har yanzu! take kuma shan soyayyar 2go, idan MK ya zo shike nan idan bai zo ba, huta roro ba ta kewarsa.

Sakamakonsu ya fito wanda WAEC din Sa'adah ta kasance ba yabo ba fallasa, amma NECO ta yi kyau sosai, a lokacin suka shirya bikin kammala makaranta da murnar sakamakonsu, ba laifi a shekarar an ci NECO sosai.

A *HANG OUT* suka shirya yin bikin, a lokacin gun ne yake tashe a wurin samari da 'yan-mata, da kyar Inna ta bar Sa'adah ta halarci taron.

Shi ma sai da ta yi karyar yayar Zainab ce ta haihu za su je, nan kuwa iya su 4stars ne, sai samarinsu na aji Irin su Khalil da kuma saurayin Halima Sagir.

Haka suka yi wannan bidirin. Sa'adah a takure saboda wannan ne karon farko da ta ta'ba zuwa wani guri da sunan party, kuma a cakude da maza sai abin ya zame mata bako, ga dai kayan kwalama cike da teburinta hatta ice ream da ta ke jarabar so bata iya 'dan'danawa a bakinta ba, Khalil sai kaffa-kaffa yake yi da ita don ta sake, ita kuma sai raya ina ma kulawa da iya soyayyar Khalil, MK ne ya iya su.

Tana cikin wannan tunanin wayarta, ta shiga ruri, tana dubawa taga MK ne, ta 'ki amsawa, tana tunanin idan ya ji wannan kidan sai ya ishe ta da tuhumar inda take.
Bai daina kiran ba har sai da ta yi shahadar amsawa, jin hayaniya da kade kade yasa shi tambayar inda take, ta karkace baki ta shirya karyar ta raka Zainab gidan suna, yayarta ce ta haihu, ya yi shiru ba don ya gamsu ba, saboda ki'dan music yake jiyowa ba dan ka'dan ba.
Ya nisa ya ce, "Son ganin ki nake yi, ya za a yi ke nan?"

A ki'dime ta ce, "Ai anjima za mu dawo na san dai zuwa magariba mun iso."

Da sauri ya ce, "Har Magariba za ki kai a waje? yanzu karfe 4, ki tabbatar biyar da rabi ta miki a gida, ina jiran ki."

Ya kashe wayarsa ba tare da ya jira mai za ta ce masa ba, saboda bai gamsu a gidan suna suke ba.

Ta yi shiru da waya a hannunta, tana tunanin yadda MK ya mata magana a gadarance tamkar ya zama mijinta, wani sashe na zuciyarta kuma so yake ta isa gida kafin lokacin da ya ce din.

Duk kokarin Sa'adah na son ta bar wurin da wuri ya ci tura, su Safina sun hana ta, kan dole ta kashe wayarta don kada MK ya sake samun ta.

Sai bayan Maghrib suka kawo ta gida, ita ce a gaban motar su Halima na baya, duk yadda ta so su ajiye ta a hanya Khalil kin yarda ya yi, don so yake mugun malaminsu ya ganta a motarsa tunda a unguwar yake sana'ar sa ta wanzanci, ya san kuma saboda shi take son su ajiye ta daga nesa.

Su Halima na sake zuga shi ta hanyar cewa, "Idan ka ajiye ta a hanya wallahi soyayyarka ba ta kai ba!"

Dai-dai lokacin MK yana kofar shagon kusa da jikin gidansu ana masa gyaran tayar mashin dinsa da ta yi faci, daf da shi Khalil ya tsaya, tsaleliyar mota(Continue Discussion) a wancan lokacin ita ce motar da take tashe ko'ina ka shiga maganar motar ake yi wanda shi ma ta mahaifiyarsa ce ya dauko, gaban Sa'adah ya sake tsananta bugawa musamman yadda hankalin mutanen wajen ya juyo kan motar, ga ta ita ce a gefen hannunsu, ma'ana tana bude kofa dole kowa ya gan ta.

A tsarin mahaifinta ba ma MK kawai ba, bai kamata mutanen gurin su gan ta ta fito a motar saurayi a irin wannan lokacin ba.

Ta rasa yadda za ta yi ta fita, musamman yadda kayan jikinta suka kamata sosai duk da mayafin babba ne. Sai dai shara-shara ne, hijabi ta saka da za ta fito, saboda Inna ba za ta barta ta fita da wannan dinkin ba wanda anko ne telan Safina ya dinka musu, da ma nufinta tana isa zaure ta maka Hijabinta baki alaikum.

Kunya da tozarci iri-iri suka dinga bin ilahirin jikinta, ganin yadda ta kasa fita a motar ya sanya Khalil fita ya zaga, ido biyu su ka yi da MK ya hura hanci ya dauke kai, ya bude gaban motar yana fadin fito, da kyar ta fito fuskarta a kasa ta kuma ja mayafin har kanta aka bita da ido, mazan da suke gun dukkansu a ransu yaba surarta suke yi har daya a cikin su wanda dan kwaya ne ya kasa hakuri, a fili ya furta "Kai waccan baby

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login