Showing 81001 words to 84000 words out of 186291 words
65-66.
Ta yi murmushi ta ce " mai zai hana na fada maka idan kana so?"
Ya bugi sitiyari ya ce "my sweet Sa'adah, sometimes you are so funny".
Ta yi shiru ta kyale shi, ya sake cewa " ke yanzu ko inkiya da Jawad baza kimin ba, naga yanzu daga mace ta haihu take karawa Mijin ta matsayi ta hanyar yi masa alkunya da sunan yaronsu".
Ta tabe Baki, ta yi shiru, sai kuma ta kasa hadiye maganar.
"Akan mai zan maka alkunya da Jawad alhalin wadda ta fini cusa kai ta riga ni? Inace Farida Abban Jawad take kiranka? Kasan Ni kuwa har abada bazan bi ra'ayin ta ba, banda azarbabi, ba sai ta bari idan ta haifar maka nata sai ta yi komai ba, amma dan son sai ta nuna ita gwanace akan kayan da ba nata ba yasa ta ke yi mini katsalandan, ai na so ta yi kataborar ce min Iyah Basiru, wallahi da jikinta ya fa'da mata domin kuwa ba abin da zai hana na mata 'kamshin mutuwa".
Ganin za ta tunzuro da yawa sai ya share maganar da cewa "Na zabi miji, amma Zauj za ki dinga fad'a maimakon miji".
Yana rufe baki ta ce " duhun fata ta kadai, ya isa ka gane ni ba balarabiya bace, dan haka nafi kishin yarena".
"Amma duk musulmi dole ya dau larabci yarensa ne, domin yaren kura'ani ne, duk sallar duniya kuma a larabce muke yinta".
"Wannan daban" ta bashi amsa a takaice, daidai lokacin kuma suka iso gida.
A gidan ma maganar ya yi ta ja, inda ita tace Malam ta zaba, dan haka Malam zata dinga fada.
"Na fada miki ban son wani Malam, duk sunayen zamani, da na soyayya ki rasa mai zaki ce mini sai Malam sai kace tsoho ko wani Malamin zaure, duk yadda muke da ke darajata a iya ta Malami take a gurin ki?"
Tana dariya tace "kololuwar daraja kenan, Malaminka ai tamkar mahaifi ne, ana canja Miji, amma ba a canja mahaifi da Malami, domin ko ka guje shi, ya dai koyar da kai abin da baka sani ba, sannan ya koya maka tarbiya, a wurina Malam is a jewel.
Shikenan mafarin cemasa Malam tun yana ki, har ya fara amsawa, a lokacin da Jawad ya fara iya magana shima ya bi bakin uwarsa wurin kiransa da Malam.
Juyin duniya ya yi da Jawad kar yace masa Malam, amma da ya fara cewa Daddy, idan yaji Sa'adah tace Malam shikenan shima zaice Malam.
Sai ya fara cemata Daliba, ko abune sai ya bawa Jawad yace humm kaiwa Daliba, a kokarinsa na itama Jawad ya dinga kiranta haka😂
Amma sunan bai bita ba, sabanin shi da Malam ya zauna a bakinsa radam, ita kuwa Mami yake kiranta.
Tun lokacin Mk yake yiwa Sa'adah mitar yasan Jawad yafi sonta da shi, itakuma dariya yake bata idan yana wannan rikicin nasa.wataran tayi dariya, wataran tace haba Malami na. Sai ya yi murmushi yace
"A da nake Malamin ki".
Tace "har yau Malami na ne, tunda har yanzu karatu nake yi a gabanka".
"Wanne karatun kike yi yanzu?"
Tace " da ka koyar da Ni, ilimi da tarbiya, yanzu kuma kana koya mini karatun kyankyansar jarirai".
Tana fadin hakan ta gudu ta barshi, ya bita yana dariyar maganar ta karshe, wai kyankyansar jarirai? ya zauna kusa da ita yana cewa "ai kuwa dai kin yi gaskiya, Ni yanzu ma so nake mu zama mu hudu, ya kamata kije ki cire abinnan, mu fara sabon karatun kyankyansar jariran".
Tana dariya tace "ka rufa min asiri kai da kace sai na fara karatu, na yi nisa, da ka sake yi min ciki?".
Yana dariya yace "da bakin ki Kika fadi wannan maganar?"
Ta rufe ido tana Jin kunya na kamata.
Ya zauna kusa da ita yace "kisan dai kin yi jamb, kyau ne bata yi ba, nace ki cike F.C. E. Kin kasa fahimta ta, da yanzu za ki fara N.C.E, kinga yanzu dole ki sake zaman jiran wata shekarar, maimakon haka gara mu sami Baby, ai akwai masu karatun da goyo".
Shiru ta yi, itama tana son haihuwar yanzu, mussaman idan ta tuno fuskar baby girl dinta da ta rasu mai kama da ita, sai ta ji ta zaku da ta sake haihuwa, tasan da ta rayu, da ta nan tana tafiyarta ko ina.
" Ance mini idan Ina haihuwa rututu ba barina zaka yi na yi karatu ba?"
"Ni kuma nace za ki yi, har sai kince ya ishe ki, shin maganar wa za ki dauka, tawa ko ta su?".
"Shikenan zan cire, amma yanzu ka manta Jami'an lafiya na yajin aiki?"
" Na manta, idan su koma bakin aiki sai muje a cire ko?"
Ya fada cike da kulawa da rarrashi.
Su Halima na zuwa ta fada musu, Malam yace ko da goyo zata yi makaranta, karatu har sai ya isheta.
Safina ta kaikaice tace "wato ya ga kin yi kyau, kin bar Sa'ade kin dawo Sa'adah, shine zai sake dirka miki wani cikin? ke kuma har kin yarda da maganar sa?"
Suka kwashe da dariya, Halima tace "na rantse miki da Allah karya yake miki, barinki ne ba zai yi ba, kar ki sake ki cire abin nan sai kin tabbatar kin fara makaranta, tunda shi son haihuwar yake, sai ki yi amfani da hakan ki cimma burin ki".
Sa'adah ta yi shiru amma bata fahimci bitar Halima ba.
Tace "kamar ya ya na cimma burina?"
"Eh tunda so yake ki cika masa gida da Yara, sai ki kafe, ba za ki haihu ba, sai ya nemo miki admission, idan har da gaske zai barki, maki uku ne kacal ya hana points dinki su kai, da ya so, da tuni ya samo miki admission, lakcara ne fa, Yana da alfarma wallahi".
Safina tace "Ai ni bansan wadda ya iya rainin wayo irin Man din nan ba, mugun macijin sari ka noke ne, idan kika ga yadda yanmata suke sintiri a gurinsa, sai mamaki ya kamaki, farar fatarsa da tsayinsa ke rudar su".
Halima ta cafe da cewa "itama Gogel din ai abin da ya rudeta kenan, banda haka Ina da kamar Alh Mamman da bazan yi kukan rasa komai ba, Ina zan tsaya kula wannan mutumin, kinsan Allah Safina!
da Alh Mamman ta aura Ni kaina da tuni na jike da arziki, mu ture ta Alh Mamman, zata iya cewa ya mata tsufa, matashin saurayin nan da kasuwa ta daukaka ke shi chairman din Buji ventures, shima ya sota fa".
Safina tace "Ina ruwanta da tsufansa? Lokacin da Dadin mu ya auri mom Dina, ai kamar ita da Alh Mamman ne, gashi nan har yau suna tare, ta yi lub tana cin arziki, har muma muna cikinsa,kawai rashin rabo ne irin na Gogel, ga kuma rabon Jawad da kanwarsa a jikin Uncle"
"Ai kuwa rashin rabo ne na yarda da ke, Allah ya rabamu da rabon wahala".
Halima ta fada tana Jin takaicin rashin auran Alh Mamman.
Duk zuwansu basu da aikin komai sai kushe Mk, alhalin a gidan suke zuwa suci abinci mai rai da motsi, suna ci suna kushensa, barin ranar da babu wuta ko nama a abinci, sun dinga fadin mutum kamar Mk ya kasa kunnawa matarsa da dansa 'daya janareto su ji dadi, dole sai dare, daren ma sai ya fara nisa, Allah muna rokon ka tsari daga auren matsolon namiji.
Haka har lokaci ya sake ja, basu fasa zuwa ba, yanzu kuma sun dauki sarar shanye mata kayan tea ta hanyar yin Yar gullisuwa, ko sai sunci abinci, suce za su sha tea, ko cornflakes.
Suka sake cusa mata karya a ranta, bada komai take amfani ba, sai kaya masu tsadar gaske, yadda take tafiyar da tsarin rayuwar ta tamkar matar attajiri ba wai 'karamin lakcara ba.
Gayun ta ya 'karu, komai nata daukan ido ya ke, saboda sai zababbe, a lokacin Mk ba abin da yake so irin farin cikin ta, shi da kansa har mamakin yadda yake tsoron fishin ta yake yi, komai take so haka yake mata, kusan albashinsa da kyar yake rike su, saboda hidimnar Sa'adah, kowanne wata da Abin da zata ce, tana so, haka zai yi mata jikinsa na rawa, mantawa yake yi da hidimar kansa, daga ya sallami Hajiya shikenan zai sa Sa'adah da Jawad a gabansa.
Amma duk da hakan Sa'adah bata fahimci matsanancin sonta da take yi bane, da kuma sa'a da tayi mai son kyautatawa iyali ne, sai ta fara wuce makadi da rawa, bata cika nazari kafin ta aiwatar da komai ba.
Suna cikin haka Jami'ar Bayero ta fara yanka fili manya tana rabawa Malaman makarantar, a hankali za'a dinga cira a albashinsu.
Mahmoud da sai a wannan shekarar ya yi aure, kai tsaye biyu ya karba, da nufin idan ya tashi ginawa ya yi gini mai yalwa.
Mk kuwa fargaban karban 'daya ma ya shiga, saboda a halin yanzu, badan shagon askin sa ba da sai ya hada da bashi a wata.
Mahmoud ya yi ya karbi biyu, Mk na bude bakinsa sai cewa ya yi daya zan iya karba, shima sai na yi shawara da Sa'adah, kar nazo ta 'kuntata.
Mahmoud ya yi galala yana kallonsa ya kasa hakuri yace " idan nace ka bari tafi karfinka kace ba haka ba, idan nace tsoron ta kake ji ka karyata Ni".
Murumushi Mk ya yi tare da caewa "kowanne namiji da yadda yake zaune da matarsa, kowacce mace da irin alherinta, da irin kuskuren ta, Ni sonta nake da dukkan alherin ta, da kuma kuskuren ta, bana jin tsoron ta, amma Ina jin tsoron fushin ta, dan haka duk abin da zan yi ,dan na samu zaman lafiya da ita zan yi".
Mahmoud ya tsinci bakinsa da fadin "Hakane".
Mussaman da ya tuno, yadda ta iya girki, da kwalliya, gidanta kullum a gyare, hatta Jawad kullum fes za ka ganshi, sannan tana da kyakkawar mu'amala da jama'a, dan kuwa hatta amaryarsa yabon kirkinta da gayunta take yi! iya abin da ya sani na zahiri a kanta kenan, Ina kuma ga mu'amala ta sirri tsakanin ta da Mk, sai ya tsinci kansa da rashin ganin aibun yadda abokinsa ya yi deep a soyayyar ta, ya lalace a kanta, da yadda zai siya mata suturu na makudan kudade, shi ya siyi masu sau'kin kudi ya saka.
Bai karbi filin nan ba sai da ya shawarceta, tace "ka karbi biyun mana Malam".
"Idan na karbi biyu fa, hakan na nufin sai mun rage wasu abubuwan, tunda za a dinga yanke mini kudi ne".
"Tunda dai wataran gini zaka mini mai kyau, gashi kace idan filin biyun ne har garden zaka mini, ai sai a ha'kura da wasu abubuwan har Allah ya sa ka kammala biyansu"
Ya ji Dadi har ransa, da yadda ta fahimce shi,ya karbi filaye, Mahmoud na ta masa tsiyar Madam ta bashi go ahead kenan.
Shikenan sai suka canja daga rayuwar luxury zuwa tsaka tsaki, sai dai ba a dauki lokaci mai tsayi ba, abubuwa suka fara canjawa saboda yadda su Halima suke mata shaguben yadda Mk ya canja mata, suka dinga fadin ba wani fili da ya karba, yanmatan banza yake kashewa kudin, Raina ki ya yi, shiyasa ya shirya miki wannan karyar, itakuma tana gaskata su, ta kasa gane gadar zare suke yi mata.
Sannu a hankali sai suka fara kushe talabijin din falonta, alokacin plasma bata yawaita ba, sai irin ta falon wato LG slim tv.
Kullum Suka zo sai sunce wannan tv kamar ba gidan ma'aikacin gwamnati ba, kusan shekaru hudu amma ya kasa canja miki komai, tunda muke zuwa kullum abu daya muke gani.
Idan ta kawo musu pure water, sai sunce ruwan warin nama ko karnin kifi yake yi, suna fadin freezer da zai siya ta nama da kayan miyane yake ganin asara, gara yaje ya rabawa yanmata a waje.
Tun bata yarda, har maganganun suka shigeta, mussaman da ta ga falon amaryar Mahmoud, sai ta sake rikicewa, ba tare da ta yi nazarin kayan da suke rainawa, ita ba'a Mata kamar su ba.
Ta fara rikice masa, ya kasa gane kanta, ya zauna yana rarrashin ta, har ya samu tace ita tibin bango take so ya siya mata.
Ya rikota cikin kwantar da murya yace "ki yi hakuri zan siya, amma ba yanzu ba, kinsan dai yanzu ba cikakken kudi nake samu ba, amma da zarar naci karfin biyansu, zan siyo miki, ba sai na kammala biya gaba'daya ba, ya kara da fadin wacce kamfanin kike so?"
"Sumsung"
"To ki daina bata ranki akan maganar tv, mecece talabijin kuma?"
Ya lallaba ta da maganar tv. sai kuma wayar Black berry ta shigo, kullum su Halima hirar BB chart, Safina kam tuni ansiya mata, yayin da Halima take fatan saurayin ta ya siyo mata.
A ranar da saurayin Halima ya kawo mata wayar, suka je gidan Sa'adah suka nuna mata, Halima na fadin " kina ganin saurayi ma, da bana daga masa kafafuwa, ya fidda kudi ya siyo mini, bare ke da kullum yake hakar ki".
BB chart din nan ya matu'kar gigita Sa'adah mussaman da aka tabbatar mata, sai masu irin wayar ne suke yi.
Kullum mitar ya siya mata waya take, rannan da ya gaji, ya zaunar da ita yace "kinsan za ki dame ni mai yasa za ki sani karban filaye biyu? bani da kudin siya miki wayar da kike magana akanta, Ni kaina ban ri'ke ta ba".
Ai kuwa zamansu ya dawo wani iri, saboda ta kudire a ranta da gaske yanmatan banzan yake yiwa hidima, ita ya barta ko oho, mussaman da ya ki yarda ya kaita ta ga filayen nasa.
Ranar wata juma'ah sai ga shi da sabuwar plasma TV 32 inch, ga mamakinsa ba ta yi wani murna ba, lamarin da ya bata ransa sosai.
Haka ya daure, ya kira mai gyara ya hada mata har da satellite.
Kallonta kawai yake yi, a zatonsa siyan tv zaisa zamansu ya dawo normal, amma sai ya ga sabanin haka, saboda ta riga ta yi nisa a son Black berry, ta samu shedanun kawaye na mata famfo.
Haka suke ta gungurawa, yau fari gobe tsumma, mussaman da ya tsaya akan ra'ayinsa na ba zai siyi waya ta makudan kudade ba. haka jarrabawar jamb ta fito, a lokacin da F.C.E. ta fidda jerin daliban da suka sami gurbin karatu har da ita, inda zata karanta primary care education jiran lokacin fara daukan darasi take yi nan da yan wattanni. Hakan bai sa ta sauko ba, saboda ita B.U.K. take so, Safina sai cewa take "mijinki is very smart
Ya rantse ba zai kai ki makarantar da yake ba, dan kar agane yana da mata".
Yau da gobe akace ta fi karfin wasa, ya gaji da zaman rashin walwalarsu, ya kukuta ya siyo musu Android shi da ita, a lokacin bata jima da fitowa ba, dan haka itama mai tsada ce, ga mamakinsa ko Na gode ta gagareta fa'da wadda ko kadan ba halayyar ta bace, ko abu bai yi mata ba zata yi godiya ko a gajarce ne.
Amma wannan ajiyewa ta yi a inda ya bata ba tare da ta duba ba, ransa ya baci da ita, irin wadda bai taba ji ba.
Ganin idan ya cigaba da zama kusa da ita, komai na iya faruwa a tsakaninsu na rashin jin dadi, yasa ya mike ya fita zuwa shagon sa, bai dawo ba, sai shadaya da ashirin da bakwai 11:27pm.
Ya sake tarar da wani 'bacin rai fiye da na farko, wato rufe masa gida, bugu ka'dan ya yi, ya hakura dan kar makwabta su fahimci abin da ke faruwa, ya dinga kiran wayarta ba kakkautawa, tana shiga amma taki dauka, karshe ma sai ta kashe wayar gaba'daya.
Haka ya kwana a gate a cikin mota, ya yi kwanan zafi, da sauro, barcin kansa rabi rabi ne, wannan daren yana cikin jerin dare masu tsayi da ya fuskanta a rayuwar sa.
Duk juyin da zai yi, tunanin irin hukuncin da zai mata yake yi, ya gaji da wannan bala'in, zai nuna mata, neman zaman lafiya ba shine lasisin da zata dinga wulakanta shi ba.
Koda asuba kin bude masa ta yi, dan iskanci kuma ta kunna wayar amma taki 'dagawa. Ya Mata text yafi sau goma, har kurarin zai fadawa Baffa ya yi, amma ko gezau.
Har taran safiya, yana harabar gidan. Takaicin sa daya, ba ya ajiye kaya a mota. Mahmoud ya kira ya fada masa halin da yake ciki.
Da kyar Mahmoud ya shawo kanta ta bude masa, domin kuwa cewa ta yi, ya koma ya dauwama a gurin Farida.
Yana jin lokacin da ta zare sakata, amma ba'kin ciki ya hana shi tashi, ya jima yana addu'ar samun sau'kin zuciya kafin ya samu sassauci. ya shiga gidan kai tsaye dakinsa ya shiga, ya yi wanka, ya fito ya shiga kicin, ya hadawa kansa Abu mai sauki, ya koma dakinsa ya rufe, yini guda bai fita ba, domin ramuwar barcin da bai samu ya yi ba.
Itakuma tana zaune cikin shirin ko ta kwana, har sun yi waya da Halima ta fada mata abin da ta yi masa jiya, tace mata da kyau, gobe idan ya sake har gate din za ki rufe.
Sai azahar ya tashi, ya fito da shirin fita masallaci, Jawad ya biyo shi, ya ri'ke hannun sa, suka tafi bayan ya masa alwala, suna dawowa, Jawad ya dinga Jan hannunsa, Yana cewa" Mami falo". Ya daka masa tsawa ya shige dakinsa ya daga murya yace "je ka wurinta kai, domin ita da babu duk daya ne a gurina" Jawad ya fashe da kuka saboda tsawar da bai saba da ita ba.
Abin ya yiwa Sa'adah ciwo, a fili tace "Allah yasa yau ka sake yin dare, zaka san Ni da babu daya muke".
Tsawon kwanaki biyu, zaman nasu ya sake yin tsami, domin shima fishi ya dauka sosai, ya dauke sabuwar wayar da ta bar masa a gurin, sannan ya karbe wadda take amfani da ita.
Lamarin da yasa rikicin ya sake ta'azzara a tsakanin su.
Ta dayan bangaren kuma sai shirin tafiya Abuja yake yi, saboda za su yi wata jarrabawar scholarship da gwamnatin tarayya zata tura malaman jami'oi karo ilimi a kasashen Birtaniya, Canada da kuma Rasha.
Bai fada mata zai yi tafiya ba, har sai da ya kammala shirinsa, da zai tafi, ya tsaya daga bakin kofar falon yace " Zan yi tafiya, sai Allah ya dawo da Ni, ya bawa Jawad dubu uku yace "kai mata".
Mamaki yasa ta kasa bude baki ta yi magana, ya juya ya tafi, Jawad