Showing 96001 words to 99000 words out of 186291 words

Chapter 33 - Halin Yau By Surayyah Dee

18 Dec 2025

9697

zan kuma maka laifi ba, zaman lafiya zamu yi, fiye da yadda ka ke so".

Ya yi murmushi ya ce "na la'anci zaman lafiyar da ki ke so mu yi Sa'ade, zuciyarki bata da alheri, kwakwalwarki ba ta da tsinkaye, harshenki yafi na maciji dafi, ba sauran zaman lafiya tsakanin mu, idan har kika zauna lafiya da ni ban yafe miki ba".

"Zuwa Gombe, ko yanzu kina iya tafiya, sai dai idan ina da hakki akan ki, ba za ki ga alheri a yayin tafiyar da dawowar ba in sha Allah".

Ya ja dogon tsaki yana fadin shashar yarinya da bata san mutunci da kyautatawa ba".


Ya sake jan dogon tsaki ya fice, ya barta tana kukan ita yake yi wa baki da mugun fata?.









SURAYYA DAHIRU
✍️✍️
18/04


•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•



*SADAUKAWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.



75_77


Hannu ta 'dora aka ta dinga kuka,tana fadin "Hasbunallahi wa ni'imal wakil".

Har akayi azahar tana zaune inda take, ba abin da tasa a bakinta, duk da ga tiren abincin nan a gabanta, ba idonta kawai ba, hatta fuskar ta kumbura ta aune sosai saboda kuka, ta fada ta yi zuru zuru, ta dinga lissafin adadin rikicinsu, aduk fa'dan da zasu yi ita take janyowa, ta sake tuno adadin alherinsa hatta iyayenta bai huta da yi musu alheri ba, tun kafin ma ya aureta.

Ta sake tuna duk laifin da take ganin ya mata cikin biyu ne, ko dai kawai zuciyarta ta raya mata ya Mata kaza a matsayin musgunawa, sai wadda 'kawayenta zasu ce ya yi a makaranta, ko ya mayar da ita Bagidajiya, alhalin ita tasan yadda yake girmamata yake girmama dukkan ra'ayin ta, amma sai tunanin ta ya bace ta biye musu.

Ta tuna yadda yake tsananin son su zauna lafiya, su rayu cikin walwala da mutuntata juna, sai gashi yau da bakinsa yana la'antar zaman lafiya, yana fa'din bai yafe mata ba, idan ta zauna lafiya da shi.

Idan ta yi wadannan tunaninka sai ta rushe da kuka, tana yi tana cewa "wallahi da gaske na gane gaskiya".

'Kiran sallah ya sa ta tashi, ta yi alwallah ta yi sallah, ruwan Lipton kawai ta sha.

Tana zaune har dare! sallah ke tayar da ita, gefe kuma tana tunanin Jawad, da ya nan da ya debe mata kewa, yau kwanansa uku a gidan Samira, tunda suna hutu.

Akan idonta ya dawo, kusan a guje ta sha gabansa tana kuka, tana cewa "Dan Allah ka yi ha'kuri, ya girgiza da ganin yadda fuskarta ta koma a yini 'daya kacal, ta so bashi tausayi amma da ya tuna haka take idan tana son abu, da zarar ta samu muradinta kuma za ta sake kirkiro wata matsalar.

Ya dubeta ya ce "Ba ki fara kuka ba, sai burina na raba Safina da gararanba a titi ya cika"

Ta kalleshi a razane, bai damu ba ya ce "babban burina ta zame mini amarya, na tabbatar zan sami nutsuwa da ita, ki adana hawayenki zuwa wannan lokacin".

A gurin ta yi fa'duwar yan bori tana kuka tamkar yarinya har da tirza 'kafa irin yadda Jawad ya ke yi.
tsaki ya mata yana fadin "Ba kuka ba ko bubburwa za ki yi bai dame ni ba". Ya shige ya rufe kofarsa.

Washagari daga sallar asuba bai dawo gidan ba, hankalin ta ya tashi ba ka'dan ba, ta kalli agogo ta ga har karfe uku ta tabbatar yana shago tunda yau lahadi.

Abin duniya ya taru, ya mata yawa, idan ta tuna kalamunsa wai son Safina ya ke yi, sai taji tamkar ta shide, ta tuno yanayin halittar su daya, ko a makaranta ana yawan fadin dirin jikin su shigen iri daya ne, da gaske za ta iya daukan hankalinsa kenan?

Hawaye ya sake goce mata, karon farko da ta fara jin tsanar Safina a ranta, tana raya ba zata kuma ganin dariyarta ba, bare ta ga fuskar zama a gidanta

Maganar ta mata ciwo fiye da zaton mai zato.
Tana zaune ta ji wayarta ta hau kuwwa, da hanzari ta dauka, ganin Hajiyar Bichi ce, tun daga muryarta Hajiyar ta gane ba ta cikin sukuni.

"A kwance kike ne Sa'a? na ji muryarki ba walwala".

Duk yadda ta ke danne kukan sai da ya subuce mata, hankalin Hajiya ya tashi ta dinga tambayar ta dalili amma ta kasa yin magana, sai kukan kawai.

Dai dai lokacin kuma Mk na zaune dakin Hajiya yana cin alalan gwangwani da ya ji lafiyayyen manja da yaji.

Ta kashe wayarta ta zubawa Mk ido, tana jin takaicinsa na kamata, a kausashe tace "mai ya hada ka da Sa'a?"

A nutse ya ajiye cokalin hannunsa, ya kalleta yace "Me tace na yi mata?"

Ranta ya sake baci ta ce " Na tambaye ka, ka amsa mini da tambaya! Na lura da kai, ka mayar da ni shashar uwa, duk sadda ka sami matsala da matarka sai ka tattaro ka dawo da kwanon abincinka wurina saboda ka zubar mini da mutunci a idon yarinya, amma zan gyara".

Ya yi sukuri dan yasan gaskiya ta fada, yana yin hakan. A raunane yace "Hajiya ni fa ba abin da ya ha'damu, kinsan kuma yadda nake son 'dan'danon girkinki, dan na yi aure shikenan sai bazan ci ba?".

Ido kawai ta kafe shi da shi, tun yana murmushi har ya fara shafa 'keyarsa, yana jin kallon na shiga jikinsa, yana tuna lokutan baya na 'kuruciya, idan Hajiya ta musu irin wannan kallon take suke shiga hankalin su, saboda yadda ya 'kunshi abubuwa da yawa ba sai ta yi magana ba .

"Tashi ka kaini gidan, na ji ba'asin kukan da take ta faman yi, wa ya sani ma ko dukan ta ka yi".

"Haba Hajiya! Kinsan dai ban samu tarbiyar dukan mace ba, ita kukan banza ne da ita, duk sadda zuciyarta ta raya mata, kuka take yi, da dalili ko babu".

"Mahaukaciya ce ai".

Jin amsar Hajiya yasa shi yin shiru ya lura ranta a bace yake da shi, ya mi'ke ya dauki waya da mukallin motarsa da ke gefensa ya kalleta ya ce "Allah ya huci zuciyar ki Hajiya, ina jiran ki a mota".

Kozai kozai suka tarar da ita, cikin kwanaki uku kacal gaba'daya ta lalace, karon farko da Hajiya ta ganta kaca kaca, kullum fes zata tarar da ita, haka muhallinta.

Hajiya ta ka'du kwarai da yadda ta ganta, da sauri ta isa kusa da ita, ta ri'ke ta, ita kuma ganin ta sami mai rarrashinta yasa ta kwantar da kanta a jikin Hajiyan ta dinga rera kukan tamkar mai wa'ka.

Mamaki ya kama Mk! ya coge a bakin kofa yana kallon kukan shagwaba da iskanci a wurin Sa'adah, ta masa laifi, ta kai 'kararsa.

Ya na'de hannunsa a 'kirjinsa, yana sauraren 'korafin da ta ke rattabawa Hajiya! "kuskure na masa cikin rashin sani, na yarda na yi laifi, na bashi hakuri tamkar harsena zai tsinke ya ki ha'kura, yanzu kuma sai ya fara soyayya da kawata dan ya ci mini fuska ya kuma janyo mini raini"
Cikin kuka sosai take bayanin.

Hajiya ta rasa mai za tace! ta fahimci Sa'a ba 'karamin kishi ne da ita ba, kishin nata kuma ya zarce ka'ida, amma da ta lura har da 'kuruciya a kanta, sannan dabi'a ce ta matan YAU sawa miji ido da kuma 'dorawa kai zazzafan kishi tamkar wadda aka musu busharar an janye ayar da ta bawa maza damar auren abin da ya musu da'di, daga mata biyu, uku ko hudu.

A hankali ta ce "akan yana da budurwa ki ka maida kanki haka, Ina ruwan ki? ki daina sa ido ko bibiyarsa, ba ruwan ki da abin da yake yi matu'kar bai tauye miki hakkin ki ba, idan kuma ya na 'ketare dokokin shari'a wannan kuma tsakaninsa da ubangijinsa ne".

Kan Sa'adah na 'kasa tana ta kuka, kukan kuma shi yake tayar da hankalin Hajiya.

"Wai wannan kukan na menene haka Sa'a? Kin ga kuwa yadda fuskar ki duk ta aune?"

Murya a dakushe ta amsa da cewa "ki ce ya daina mini fishi, sannan idan na dafa abincin ya dinga ci".

Kafin Hajiya ta yi magana, Mk ya yi fit yace "Ni yaro ne da za ki dinga control 'dina? Na 'ki na ci abincin na ki"

"Kin ji da kunnen ki ban isa da shi ba, dan haka ki share hawayen ki, komai da ki kasan hak'kinsa ne ki masa kar ki gaji, ubangiji ne yace ki masa biyayya, idan ya zalunce ki, ba zai barshi ba".

Ta mike tana gyara zaman Hijabin ta, ta sake cewa "Ki yi hakuri, kar ki biye masa, kinsan idan tururuwa ta so lalacewa fuffuka take yi, Allah ya miki albarka kin ji! Ki tashi ki yi wanka ki ji da'din jikin ki".

Ta juya ta fita ba tare da tabi ta kan Mk ba, da ya bita a baya yana cewa "Hajiya! ko kula shi bata yi ba ta yi ba, a waje juyin duniya akan ta shiga motarsa ya kaita, kamar yadda ya kawota, ta 'ki bude baki ta masa magana bare ta amince, haka ya dinga bin ta har titi, ta tari adaidaita sahu tana shiga, shima ya yi wuf ya fa'da, har suka isa Na'ibawa ba abin da ya ke yi sai tunanin mai zai yiwa Sa'adah ya huce.

Ba zai iya tuna lokacin da Hajiya ta masa irin wannan fishin ba.

Suna isa ta sau'ko ta wuce gida, ya tsaya ya biya kudin, sannan ya bita cikin gidan

Yana isa ya tarar da ita zaune a tsakar gidan, bata shiga dakinta ba tabbacin ba zata saurare shi ba.

Ya tsugunna, ya dinga bata ha'kuri, ya dade yana fama, kafin ta ce "Nunawa ka yi fa ban isa na zartar da abu a kanka ba, ganin na isa ne yasa ta ce na yi maka magana, kai kuma ka bata amsa da ta ke nufin ban isa ba, dan haka duk ranar da Sa'a ta fara ganina ba 'kima kar ka ga laifin ta".

Ya yi shiru yana ayyana wai su mata haka suke ne? manya da yaransu sun iya kacaccala magana, su juya ta, komin gaskiyar ka sai sun nuna su ka zalinta ko ka ketawa haddi?

Kan dole ya ce "Ki yi hakuri Hajiya Dan Allah! sannan ina tabbatar miki da ikon Allah ba macen da zan zauna da ita alhalin bata ganin girman ki".

"Fatana ki huce, ki yafe mini bacin ran da na sanya ki".

Fuska ba walwala ta ce "idan har kana so na huce, hankalina ya kwanta, to ka zauna lafiya da matarka, na lura itace bata da gaskiya, amma abin da zaka lura ko a lahira wani na cin albarkacin wani, ka manta komai ta yi maka, ka mata afuwa, ba hankalinku daya ba".


Ya nisa ya ce "Allah Hajiya ban so ki ka shigar mata ba, so nake kawai ta
banbance tsakanin zaman lafiya da kuma zaman tashin hankali, ta fitine ni wallahi".

"Kaine Babba hakuri za ka yi! sonka take yi, shiyasa ta ke kishin ka, tunda ka fahimci matsalolinta sai ka kiyaye abin da zai tunzura ta, har hankali ya shigeta, wata rana ko ance ta yi wani abin ba zata yi ba".

"Shikenan na ha'kura saboda ke, amma wallahi ki dinga mata fa'da Hajiya! tana sake yin mini yadda ta ga dama ne saboda kina bin bayanta, kwalbar ha'kuri na ta kusa fashewa akan lamarinta".

"Kai kuma haka za ka yi? mahaifinka mai ha'kuri ne akan sabgogin mata, kafin muga fishinsa mukan
'dade, duk yadda zan bata masa rai kuwa da zarar nace yi hakuri to maganar ta kare".

Shiru ya yi! A ransa kuma sai cewa yake yi ba za ki gane mai yarinyar nan take mini ba ne, inda a iya kishin ne ai da sauki.

A fili kuma ya ce "shikenan Hajiya ta ci albarkacin ki magana ta kwanta".

" So nake ta mutu murus, ba wai ta kwanta ba".

Ya yi dairya ya ce "ki mata fa'da, idan ta kwantar da hankalinta, magana ta wuce, amma idan tana tayar min da hankali ai dole laifin baya ya dinga tasowa, yana zama sabo".

"Zan ja kunnenta sosai, amma ka ri'ke a ranka na kashe wannan matsalar, kaima ka kashe ta a ranka, sannan kar ka kuma zuwa cin abinci gurina idan kun yi fa'da, bana so! bana so".

Ya amsa da "to sannan ya mata sallama ya tafi, yau har zaure ta taka shi tana cewa "ka zarce gida kai tsaye ka nuna mata na isa da kai."
Ya amsa da fadin "To In sha Allah".

Madallah da uwar miji irin Hajiyar Bichi, masu maida surukansu tamkar ya'yan su, suke musu adalci irin wadda ko wacce uwa take so ayiwa 'yarta.

Gidan kuwa ya zarce, ya sameta a inda suka barta har lokacin kuma kukan ta ke yi, sai dai alamun sun nuna ta yi wankan duk da ba kwalliya ta yi ba.

Ya tsaya a bakin 'kofar falon ya zuba mata ido yana jin takaicinta na kama shi sosai.

A kausashe ya ce "Rashin mutuncin ki kullum 'kara tunbatsa take yi, ki mini cin mutunci, ki raina arzikina ki nuna mini bariki ya fi aurena, sannan ki zame ki kai 'karata, saboda kin koyi munafunci?"

Ta kasa magana sai kukanta da ya 'karu.

Shi kuwa ya zarce da fadin "Tunda kin zama macijiya ki sare ni, ki koma ki baibaye uwata da kalolin alherinki na makirci da tuggu, to Ina tabbatar miki nima daga yanzu kome kika mini sai na fadawa Baffa, su dinga raba 'bacin ran tare da Hajiya".

Ya ja tsaki ya shige dakinsa.
Ta jima tana zaune cikin rashin sanin abin yi, sannan ta tashi ta bi bayansa, cikin sa'a bai rufe 'dakin ba, yana zaune a bakin gado iskar fanka na kada shi.

Akan gadon ta zauna kafadunsu na gogaiya da juna, ta ri'ko hannunsa tare da jingina kanta a kafadarsa murya ba amo tace"Am sorry Malam! Wallahi zuciyata ba za ta iya 'daukan fishinka irin haka ba, ka yafe mini' ka manta dan girman Allah".

Ta karasa cikin kuka na sosai.

"A hankali yace "Na ha'kura, amma mantawa sai a hankali, idan kin kiyaye, kin kuma rufe 'kofofin da zan dinga tunawa din! ki sani ba dan Hajiya ba, da ban san ranar da zan miki afuwa ba, saboda kin riga kin shayar da ni mamaki da ba'kin ciki mai yawa".

"Na yarda na yi ba dai dai ba, dan Allah kar ka yanke mini kauna, ka sake bani dama".

Ita da kanta ta yi dalilin da sai da suka hadu a lokacin, tun Mk na basarwa, har ya kasa cigaba da jarumtar ya ru'ko ta suka sami nutsuwa, haka nan sai da haduwar ta yi awon gaba da kaso hamsin na bacin ran da ke zuciyarsa.

Tun a wannan rikicin Sa'adah ta fahimci ta rasa damammaki a gurin Mk, ya matu'kar rage rawar jiki akanta, ya daina tattauna halin da yake ciki da ita, haka nan baya zama ya shiririce mata da hirarrki kamar da, za su yi hirar amma a gajarce, sannan mafi yawan hirar sai dai ita ta kawo.

Haka suke wannan zama har Jawad ya dawo daga gidan Samira, so take ya barta ta je Gombe amma tsoron tambayar ta ke yi, har mamakin kanta take yi, yadda take tsoron su yi rikici yanzu.

Washagari alhamis da safe ta tura Jawad ya tambayo musu za su je su gaida Maman Gombe da ganin Baby boy, tunda sai satin sama hutun su zai 'kare.

Jawad bai jima da zuwa ba, ta ji Mk na 'kwalla mata 'kira, gabanta ya fadi sosai da hanzari ta shiga dakin tana cewa" Na'am".

Kallonta kawai ya yi, ta gane ba zai barta ba, ta tsugunna tana sauraronsa.
Sa'a an 'kara kwas na respect 😁

"Kin aiko Jawad za ku Gombe, inace dama ban hana ki ba tun farko?"

Ta yi sukuri tana jin fargaba na kamata, da 'kyar ta bude baki ta ce " ai kace ba zan ga alheri ba".

"To yanzu na ce ki ga alherin! Aje lafiya, adawo lafiya shikenan?"

Ta kalle shi ta ga yana daddana waya hankali kwance.

"To kwana nawa zamu yi?"

"Sai kin gaji da zama sannan ki dawo".

Ya fada hankalinsa na kan wayarsa.
Hawaye ya cika idonta tana jin tamkar ta sume.

Murya na rawa ta ce "Malam yanzu fa ban yi maka komai ba, Allah shine shaidata, na yadda na ke gudun na 'bata maka, amma kai kwata kwata ka yanke mini kauna, ka ki ka yafe mini, kana zaune da ni akan tilas.."

Kuka ya kwace mata sosai, cikin ko in kula ya ce "kin so yin kuka ne, kince za ki je Gombe, nace adawo lafiya, har da abin arzikin ki yi iya adadin kwanakin da kike so, shikenan kuma sai ki bare mini baki, to fada mini me kike so na ce miki?".

Ta dago da manyan idanuwanta da suka yi ja ta zuba masa akan fuskar sa, tsawon lokaci idanuwansu a sarke, chemistry na aiki akansu, a sanyaye Mk ya janye fuskar sa gefe daya, yana kokawa da abin da ya taso masa.

A hankali ta furta "so nake ka ce kwana kaza za ku yi".

"To sati hudu ya yi miki?"

Da mamaki ta kalle shi ta ce"ai zuwa wannan lokacin su Jawad sun '
dade da komawa school".

Kai tsaye ya ce "Ba da shi za ki tafi ba ai, ke 'kadai za ki yi tafiyar ki, ki je ki yi abin da ki ka ga dama".

Jikinta ya yi sanyi ta tabbatar ba barinta zai yi ba, sai kawai ta mike ta ce "Na gode".
Ta fita zuwa kicin, ta hau aikin abincin rana, ta na yi tana kuka, bata ta'ba sanin Mk na da ri'ko ba sai a wannan karon.

Haka tana ji tana gani har Inna ta dawo ba ta je ta gano su ba.

Ko zuwa ta yiwa gidansu dan ta yiwa Inna barka da dawowa, da 'kyar ya barta, shima sai da la'asr lis da zai tafi shago ya tafi da ita, kafin su Isa magariba ta yi, amma dan son ya musguna mata bata fi awa daya ba ya mata waya shi zai tafi, idan kuma bata gama ba, ta taho idan ta kammala, alhalin yana kaiwa fiye da goman dare.

Haka ta fito ta bishi yana ta cin magani, har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login