Showing 183001 words to 186000 words out of 186291 words
Mk ya shawo kan Iyah ta yarda su tafi tare, dan kuwa da tace ya tafi da Faridan ita zata je daga baya.
Zuwa wannan lokacin cikinta wata bakwai, ta yi wani irin girma, fuskarta ta fara aunewa, haka baki da hanci tabbacin yadda cikin Jawad ya mayar da ita haka ma wannan zai yi mata.
Farida ta yi matu'kar mamakin yadda ta ga Sa'adah da tsohon ciki, tunda ba kasafai suke haduwa ba.
Wani irin kishi ya shaketa, amma sai ta yi ta addu'a tana namen tsari da yin jayayya a hukuncin Ubangiji.
Kai tsaye Sa'a bayan mota ta shiga, matu'kar zasu fita tare dukkansu, ta sallamawa Farida gaban mota, wanda hakan na matu'kar yiwa Mk da'di.
Duk yadda take boyen cikin sai da Hajiya ta gane Sa'a ta kusa sauka tabbacin da ciki ta tare, tunda basu cika wata hudu da tariyar ba.
Sun dawo gida, maimakon Farida tabi Mk zuwa side dinta, sai kawai ta bi Sa'adah akan ta baata dambun da ta yi, tunda ta ga ta kaiwa Hajiya.
Suka shiga, kamshin wurin yana matu'kar birge Farida amma ba zata iya tambayar wanne irin spices ne mai bada wannan kamshin mai kamawa ba, ga turaren wuta sai kamshin ya hadu ya ba da wani irin kamshi mai kwantar da zuciya.
Duk da cewa side din Farida shima kamshi na mussaman yake yi, amma kamshin wurin Sa'a yafi kwanta mata a rai ko dan kishi ne oho.
Sa'adah ta zauna tana haki, ta ce shiga ki dauko muku ya nan a cikin warmer.
Ta shiga kicin din tana kallon komai, kayan tsilla tsilla amma kuma unique.
Ta fito ta ce "Na gode sosai Gogel".
Takaici ya kama Sa'adah wato Farida ba zata daina yi mata izgili cikin dabara ba.
Ta tuna sunan garin su Farida Torondi, Amma bata ta'ba kiranta da hakan ba, ta tuna yadda yan set dinsu suke ce mata Taller saboda tsayinta, amma ita bata fa'da mata hakan ba.
Ta sake tuna yadda ko Farida bata fa'da a gaban Jawad sai dai Anti! Amma shine ita zata dinga ce mata Gogel, ta tuno har a asibiti ta yi mata kashedi, amma saboda tsokana sai ta sake fa'da.
Ta yi tsaki tana tunanin abin da zata yi mata idan ta sake.
Ai kuwa washagari zata fita wurin aiki ta leko ta kawo mata dish dinta.
Suka gaisa lafiya Lau ta kai kicin ta ajiye mata.
Zata fita ta kalli yadda Sa'a ta zama gari guda.
Ta ce "Gogel indai ba twins bane a cikinki, gaskiya kin kusa sauka, sai dai kuma na ga sai yanzu ne muke shirin four months a gidan nan".
Kafin ta rufe baki Sa'a ta yun'kura ta ce "Idan zaki iya tuna kwanakin da kika yi ba kya ganinsa da rana, ba ya cin abincin ki da rana, to sune kwanakin da aka samu cikin, shi ya yi abinsa bayan an shafa fatiha ba wai shege bane".
Nan da nan Farida ta muzanta ta ce "me ya kawo wannan maganar kuma Gogel?"
Ai kuwa Sa'a ta ce "Tsugudidinki da tsokanarki, ta nunata da yatsa ta ce "Taller ki fita a idona tun muna shaida juna".
Ga mamakin Farida sai ta ji Sunan da Sa'adah ta kirata da shi na Taller ya yi mata zafi ba ka'dan ba.
Idonta ya ciko da 'kwallah ta ce "Sa'adah daga wasa?"
Daidai lokacin Mk ya shigo!
Sa'adah ta ce "ke Kika san wannan, to bana son wasan indai irin wannan ne".
Ai kuwa Farida ta hau hawaye.
Sa'a tana kallonta bata yi mamakin hawayen data fara dan ta ga mijinta ba, da'din abin dai bata isa tasa ya daketa ba.
Ai kuwa Mk ya nemi jin ba'asin kukanta, ta ce Ba komai".
Ta juya ta fita, shima ya bi bayanta, bai yarda ta fita da damuwa ba, sai da yaga ta saki ranta, da kansa ya bude mata kofar mota ta shiga ta zauna, ya rankwafa ta windo yana cewa "drive with care please".
Yayin da zuciyar Sa'a tamkar ta fashe saboda duk tana hangensu ta windo.
Sai da Farida ta tafi sannan ya koma wurin Sa'a ya sameta, ya dinga yi mata sababi akan ta zo wurinta ne zata wulakantata har ta sakata kuka, har yana fa'din ke baki san halin Farida da son raha ba, ki dinga jin tausayinta mana".
Ba'kin cikinsa yana neman kassarata.
Ta hadiye kukan ta ce "Ai yanzu na gama ganeka, ita bata laifi, komai ta yi daidai ne, kome take so haka zaka yi mata, saboda ita din Babanta zai siya mata kowanne irin miji".
Ai kuwa ya hassalo yana fa'din "wulakanci ki ya tashi ba? Ni kika fa'dawa wannan maganar?"
Ta kasa magana saboda a yanzu shakkarsa take ji sosai, ba kamar da ba, hawaye ya balle mata.
"Ta ce ta zo har 'dakina ta tsokane ni, bayan ka san har fa'da maka na yi akan ka yi mata togaciya, amma ba bincike ba komai, ka bi bayanta, ka rarrasheta, ni kuma ka zo kana mini jidali".
"Jikinsa ya yi sanyi, fishinsa ya sauka, ya isa gareta da nufin rungumeta, ta goce ta ce "Tun bamu je ko ina ba kana son sai na gaza".
Ya sassauta murya ya ce "Tausayinta nake ji, bata da lafiya sosai, bata samu haihuwa ba, sannan na fi son wata akanta, fa'da mini dan Allah bata cancanci a ririta farin-cikinta ba?"
Ta zuba masa ido ta ce "Ban son wannan tausayin da ka tsananta akanta, ina jin fargabar abin da nake gani a idanuwanka akan lamarinta".
"Ni meyasa baka jin tausayi na irin haka?"
Ba ja in ja ya ce "Ina tsananin sonki Ubangiji ne shaida, kina da cikakkiyar lafiya, Ubangiji ya hore miki, kina haihuwa Ubangiji ya arzurtaki, Ubangiji ya arzurtaki da mahaifin da ba kowanne 'da ne yake samun irinsa ba.
Fa'da mini ta inda baki kereta ba".
Ya ru'ko ta, tana cigaba da kuka tana cewa "Allah ka bawa Farida haihuwa ko wannan tausayin da yake neman zame mini barazana ya yi sau'ki".
Haka ya lallabata.
Haka da Farida ta dawo, ya ja kunnanta da cewa "da bakin ki, kin ta'ba cemin kina fakar idon mutane kina tsokanarta, to ki bari tunda bata so, Nima bana so, ki kiyaye bana son muna samun sabani".
Ta tsiri fishi! Ya tattara ya watsa da ita, ya shareta, dake bame yawan fishin bace da kanta kuma ta dawo hanya.
Haka rayuwar take gudana yau fari gobe tsumma kowa ha'kuri yake yi da abin da rayuwa ta zaba masa.
A haka Allah ya sauki Sa'adah lafiya! Ta haifi danta lafiyayye mai kama da Jawad sak, kenan Mk shima ya biyo.
Kwananta'daya a asibiti aka sallamota bayan an tabbatar da lafiyarta da ta jariri.
Tana zaune a dakinta ta tsurawa jaririn ido tana ayyana abubuwa masu yawa, bai zo da wuri ba a lokacin da Mk ya matsu ta haihu, haka bai yarda ya fito a jikin Farida ba, bai kuma fito a jikin wani namijin ba, tabbas kudurar Ubangiji yawa ne da ita, duk tsawon shekarun nan sai da ya jira ya fito ta tsatsonsu a lokacin da ba a yi zato ba, Wannan ka'dai ya isa aya ga mai hankali.
Dai dai lokacin Mk da Farida suka shigo. Dukkansu suka isa gareta cike da kulawa suna yi mata sannu.
Farida ta rungume yaron da tun jiya da ta 'dora ido akansa ta ji son yaron ya shigeta tamkar ta sace shi ta gudu.
Sosai ta rungume shi, karon farko das tausayinta ya kama Sa'adah!
Mk ya dinga tambayarta ko abin da take so ko bu'kata?
Ta ce "Ba komai so dai nake yi na je gida ko kwana goma ne! Ka ga Umman Fanshekara bata jin da'di ba iya zama mini zata yi ba".
Ya girgiza kai da sauri ya ce "ba zai yiwu ba, abar maganar".
Ta yi shiru tana cewa "An barta".
Mamamki ya kama Farida ada kallon mijin ta ce take yi masa indai akan Sa'adah ne, ashe ba ita ka'dai yake hana yin wasu abubuwa ba har da tauraruwar tasa.
Tsawon lokaci sannan Farida ta mike da nufin basu guri ta ce "Tamkar na tafi da shi, tamkar na dawma ina kallonsa".
"Tafi da shi mana Farida ai d'anki ne".
Sa'a ta fàdi hakan a tausashe sannan ta mike da kyar tana janyo akawatin kayan yaron, Mk ya ce karfa ki fa'di".
Ta dire a gaban Farida ta ce "Ki tafi da shi, ki dauwama kina kallonsa,ya dauma a 'danki, ina miki al'kawari ni dai a bakina wani mai rai ba zai ji ni na haife shi ba, ke din masaniyar magaganganuwa ce, kin san wadda zaki sha ya taimaka ruwan nono ya zo miki, na shayar miki da shi na kwana 'daya da yini, ubangiji ya taya ki tarbiya da juriyar raino, ina kuma yi miki fatan ki samar masa 'kanne ta tsastonko masu yawa".
Mk ya mike da sauri ya rungume Sa'a yana jin sonta yana sake tumbatsa.
Da rawar murya ya ce"Tunda kika yi sa'a Baffah na ya haife ki, na sani zaki yi abin da yafi haka na karamci! Na gode miki sosai Ina tabbatar miki har yau din nan ke ta dabance a cikin duniyata. Allah ya miki albarka! Idan har aljannarki tana 'damfare da yardata ne, wallahi daga yau na yarje miki, daga yau din nan Ubangiji ka shaida komai Sa'adatu zata mini na kuskure, har zuwa karshen zaman mu na yafe mata, na yarda da ita, Ubangiji ka yarda da ita".
Farida tana tsaye tana kallonsu tana Jin inama itace Sa'adah! Ta matsa kusa da ita ta kalleta cikin ido ta ce "Wallahi Sa'adah kin fini kirki, kin fini hakuri, na tabbatar a yanzu da nake jin 'kaunar yaron nan ba zaan iya yin kyauta da 'da ba, koda na haifi guda goma.
Ba abin da zance miki, sai fatan alheri, Ubangiji ya fini yabawa".
Ta saba 'danta ta fice da shi, sai lokacin Sa'a ta fashe da kuka, tana jin girman 'karfin halin da ta yi.
Ya dinga rarrashinta.
Ta ce "shikenan Farida ta haihu, ta sami 'da Kamar Jawad! Sai ka daina takura shi sai ya je wajenta ya kwana, sai ka daina wannan tausayinta da yake neman zame mini barazana".
Ya sake rungumeta tsantsan yana gasgata dinbin sonsa take yi, ya sani ba macen da take sonsa a doron 'kasa irin Sa'adah, idan aka cire Hajiya.
Ya sani saboda tausayin Farida da yake yawan yi ne, ya sanya ta bada abin da yasan ba kowacce mace ce zata iya yin hakan ba.
A fili ya dinga "cewa Madallah da ke Sa'adatu, a yau na sake ganewa ke din jarumace, mai kuma 'kaunata ce, zan sake maimata miki abin da na ce ba zan sake fa'da ba.
Wallahi ban taba son wani abu a duniyata kamar ke da 'Yay'anki ba, Wallahi kune farin-cikina, kune duniyata, har na daina numfashi kece jagorar zuciyata.
Ya rasa mai zai yi mata, sai ya ce ki shirya Gobe na kai ki gida, ki yi sati uku Inna ta sake gyara mini ke, kafin ba'di ina fatan ki haifo na ki wadda zaki ri'ke a hannun ki, a dakinki".
*Wattanni shida a gaba*
Zuwa lokacin Sa'a na dauke da wani cikin na wata biyar, yayin da yaron Farida mai sunan Mahaifinta Nasir(Amir) ta yi masa alkunya, yake wattanni shida.
Yaron ya yi wani irin girma gashi fari kwal saboda farin Mk ya yi, sannan yana shan nonon farar mace, sai ya sake zama tamkar dan larabawa, irin ku'din da Farida take narkawa akan yaron abin tamkar a littafi, albashinta akan yaron yake karewa, haka Mahaifanta duk fitar da zasu yi sai anyi masa akwati guda, hatta Sa'a dalleliyar mota mahaifin Farida ya aiko mata a matsayin tukuicin sanya farin-ciki a zuciyar diyarsa.
Shayarwa ba karamin karabar Farida ya yi ba, idan Sa'a tana ganin status din Farida da 'danta wani lokacin har kusan shidewa take yi tsabar kishin yadda suke daukar ido, domin komai designer take masa amfani da shi, yaron ya zama one in town.
Haka fita goma shiga goma zata ganshi a kafadar Mk.
Idan ya shigo da shi ta mika masa hannu sai ya ki, 'kiwa yake yi mata ba Yar kadan ba, tunda ko wurin aiki da shi Farida take tafiya da mai rainonsa.
A wannan lokacin Mk ya kalallame Sa'a ta ajiye aikinta, ta zama lauya mai zaman kanta, a lokacin kuma tafiya zuwa kasar Amurka ta taso masa inda zai yi kwas na wattanni shida.
Ya tisa Sa'adah ya tafi da ita.
A can ta haihu still dai boy, ta saka rai girl zata samu sai dai Ubangiji ba hakan ya so ba.
Sun more sosai a a zamansu na wattanni shida a U.S. Ta dawo da d'anta mai kama da ita wadda Baffah(Bashir) aka yiwa takwara Jawad ya ce *Jadid* za'a dinga ce masa.
*Shekaru biyu a gaba*.
Hankali kowa ya kwanta arziki da cigaba sai sauka yake yi a gidan Mk! Mussaman da ba'a yi masa tashin hankali, duk da kuma basa shiri.
Dan hatta Amir har yau bai wani sake da Sa'a ba, idan Mk ya zo da shi baya yarda ya ajiye shi, ya dinga kuka yana cewa "Malam dauke ni"
Ba zai yi shiru ba sai ya dauke shi, ko ya mayar da shi wurin uwarsa.
A lokacin Sa'a ta yaye Jadid ta haifi mai sunan Mahmoud, da suke 'Kira da Junior, ta Kuma je asibiti ta sanya loop da amincewar Mk, tana addu'ar ta yi auta kenan, duk da tana tsananin son Baby girl, mussaman da ta lura Mk ma ya matsu ta haifi yar budurwa, amma itakam ta gaji ta fahimci ita da Sumayya basu da rabon haihuwar girls har gara ma Sumayya ta samu Khairat itama kuma sai a karshe domin itace ta biyar kuma autarta.
A lokacin Ubangiji ya sua'kar da ayarsa Farida ta samu juna biyu, murnar da mk ya yi ba yar kadan bace, sosai yake tattalin ta har Ubangiji ya sa ta haihu lafiya duk da dai c.s aka yi mata, yarinyarta mace mai kama da su Jawad kwabo da kwabo mai tsananin gashi irin nata.
Bidirin da akayi ba kadan bane, tun akan Amir farida ta gane jama'a na sonta na tausayinta, haka a wannan ma aka sake nuna mata kauna.
Sosai Mk yake ji da yarinyar nan. Aka sanya mata sunan Hajiya Babba! Wato Aisha, Farida ta sanya mata Amira.
Mafi yawa Mk ya fi yawo da Amir da Amira tun Sa'a na jin wani iri har ta hakura ta gane ba dan komai bane illah ya samu Amir ne bayan ya dauki lokaci babu haihuwa, ita kuma Amira only girl ce.
Jawad ya kammala karatunsa na sakandire, ya wuce kasar Canada yana digiri dinsa akan engineering.
Haka rayuwar ta cigaba da gudana cikin nasarori da kuma kalubale kala-kala.
A yanzu haka Mk ya samu appointment ya zama minister ilimi na kasa, yayin da ya nada Mahmoud mai magana da yawunsa.
Yana Abuja tare da Farida a dalilin itama ta samu transfer a wurin aikinta zuwa Abuja.
Sa'adah kuma tana kano tana cigaba da zurfafa iliminta, a yanzu haka digiri na uku take duk a fannin shari'a.
Duk week end din duniya sai ya biyo jirgi ya zo, sai dai idan baya ' kasar.
Ta da'de da tarewa a gidan Jawad, haka nan Mk yana kan yi musu gini da ya zarta wadda take ciki.
Ta dauko Hajiyar Bichi suna zaune tare cikin girmamawa.
A yanzu da shekarun hankali da girma ya zo mata sai ta gane ba abu mai Dadi a rayuwar mace irin samun miji na gari mai adalci, ita da kanta idan ta tuno ta'barar da ta yi a baya sai ta ji kunya ta kamata, ta kuma godewa Mk domin ba abin da bai mata ba, ta kuma gasgata shi da ya ce shi din tamkar Sumayya ne a wajenta ba wai miji kawai ba, ba abin da bai yi mata, yana kuma tsaye akan dukkan bu'katunta, sannan yana hakuri idan borinta ya tashi.
Haka nan ta gasgata shi da ya ce Baffanta Babansa ne ba nata ba, domin ba abin da bai yi musu ba, ya rushe gidansu ya zamanantar da shi, ya kai iyayenta sun sauke farali.
Itama ta je, ta koma Umrah, duk da bata aiki kuwa.
Ranar juma'ah ta yi ferfesun naman rago ta kaiwa Hajiyar Bichi dakinta, sannan ta ce "Hajiya zan je na gaida su Baffah".
Da murmushi Hajiya ta ce "Ki gaishe su Sa'a, Ubangiji ya yiwa kokarinki albarka, yasa kema naki 'Ya'yan suji 'kanki.
Ta isa gidansu ta tarar da iyayen nata zaune a falo sun yi shar da su tamkar tsufa bai cimma musu ba, ta zauna tana cewa "wayyo Baffahna".
Da wata irin 'Kauna ya ce"sarkin hakuri, giwar mata, mowar 'ya'ya".
Ta murmusa ta ajiye masa kwanon naman a gabansa.
Inna ta ce "Danma dai uwa mafi uba ko da uban sarki ne".
Cikin tsokana ta ce"Ai ni Baffah kam ya wuce ki Inna, sai dai ki yi 'hakuri kawai".
Ta mike ta shiga kicin din da yanzu yana cikin falon ta debe bowls ta zuba musu, suna ci, suna saka mata albarka.
Ta hada kan kayansu kananu ta wanke su tas.
Ta yiwa Innah ganeral sanitation duk kuwa da ta daukar mata Yar aikin da take zuwa ta yi mata shara da wanke wanke.
Amma duk da hakan duk karshen wata sai ta zo ta yi mata gyara na mussaman.
Baffah ya tsura mata ido yana godiya ga Ubangiji, da ya arzuta shi da samun 'Yaya mata, ya tarbiyaantar da su har ya aurar da su, yanzu gashi sun zame masa gata, sun janyo masa mazajensu suna ta hidima da shi, ya yi Imani ko yana da 'yaya maza ba lallai su yi masa abin da Mukhtar d Idris din Sumayya suke yi masa ba.
Gashi kuma ya'yan nasa sun haifa masa 'Ya'ya takwas maza, domin nassin al'kura'ani ya nuna jikanka danka ne.
Madallah da iyayen da basa zaben jinsin da suke son su Haifa, suke godiya ubangiji ta hanyar tarbiyaantar da ya'yansu mata cikin adalci da tausayi.
Sa'a ta koma gidanta, iyayenta suna saka mata albarka da nemawa zuri'arta tsari daga rudin *HALIN YAU*
Mk ya cigaba da kula da iyalinsa cikin adalci da tausayi.
'Ya'yansa biyar Sa'a na da uku
Jawad, Jadid da Junior.
Yayin da Farida take da biyu
Amir da Amira.
Wani week end ya zo Kano, suna zaune a falo ya kalleta ya ce "sai nake tuna shekarun baya da kike ce mini kin yi mafarki, kin zama big Madam, na zama Alaji, na 'kera mana mansion".
Itama ta ce "Na tuna