Showing 75001 words to 78000 words out of 186291 words

Chapter 26 - Halin Yau By Surayyah Dee

18 Dec 2025

9714

ki yi irin haihuwa ta, ko irin ta uwar mijinki, kin ga dai shi ma su uku ne a dakinsu, da bakin ki kika ce mini sai da ya shekara goma aka haifi Ahmad kaninsa, ni kuwa tun a kanki aka rufe mini kofa, ki kwantar da hankalinki, idan Allah ya sauke ki lafiya, idan mijinki ya yarda zan daukar miki Jawad ke ki ji da jariri ko jaririya".


Sai Azahar ta tafi, har girki ta mata, sannan ta tafi ta bar Jawad na kukan zai bi ta ya gan ta da Hijabi.

Ba ta da'de da tafiya ba, Sa'adah ta dinga jin kwankwasa kofa, ta san ba Mk ba ne tunda da key a hannun sa budewa kawai yake yi shi yasa ba ta sa sakata.

Da Jawad a hannunta, ta fita ta bude kofar, ta yi turus ganin Halima da Safina a tsaye, cikin kwalliya ta burgewa sai kamshi suke yi.

Har suka shiga cikin gidan wani irin kallo suke mata, na uku saura kwata, suka zauna, ita kuma ta fice zuwa kicin ta zuba pure water mai sanyi, akan tray, ta kawo musu tana cewa "Sannun ku, daga ina kuke haka?"

Safina ce ta ce "Daga makaranta kin san sai yanzu aka fara daukar sababbin dalibai saboda dogon yajin aikin da ASUU ta yi".

Sa'adah ta ri'ke baki ta ce "Oh kuce da students nake tare, wane course kuke yi?"

Still Safina ce ta sake cewa dukkan mu Diploma in Public Administration muke yi, ba mu samu degree ba, saboda points din mu ba su kai ba, amma a satin nan zamu cike JAMB tunda an fara za mu sake trying".

"Ma Sha llah! Congrats, na muku murna, ni ma In sha Allah zan yi JAMB din, gara da na ji da wuri, amma ni Sociology ne zabina ko kuma English Language".

Sai lokacin Halima ta ajiye wayarta da take ta latsawa ta dube ta sannan ta ce "A ina za ki yi wannan karatun da kike fa'da?

Kai tsaye Sa'adah ta ce " B.U.K mana".

Dariya Halima ta yi irin ta iyashege sannan ta kalle ta, ta kalli cikin jikinta, ta sake mahar da kallon ta ga Jawad, ta ce, "Sai dai idan a gaban Uncle za ki yi karatun, tunda shi ma harshen Turanci ya karanta, yake kuma koyarwa".

"Ban gane ba?" Sa'adah ta tambaya da alamun karin bayani.

Ba kunya ba komai Halima ta kalli cikin idonta ta ce "Na ga ya mayar da ke akuya ne, ke kuma kin biye masa, don Allah dubi yadda kika zama just one year da aure".

Kalmar akuyar nan ta bugi Sa'adah, ta kasa hakuri ta ce, ni ce na zama akuya?"

"To mene ne banbancin ki da ita? Ki kalli kanki mana, 'da a hannu, 'da a ciki".

Idon Sa'adah ya cika da kwalla tabbas da gaskiyar Halima irin haihuwar akuya za ta yi.

Kafin ta yi magana, Safina ta tsoma baki ta ce "Ni fa tunda na zauna mamakin Gogel nake yi, ta saki jiki za ta mayar da kanta tamkar irin jakunan matan nan na kauye da ba su san komai ba sai dai su ci, su haihu duk shekara, duk iyashegen da namiji zai musu ba yadda za su yi saboda sun tara garke da shi, yo a wannan karnin wacce macen ce za ta yi irin wannan?"

Halima ta cafe da fa'din "Ba ki ga yadda ta susuce ba? tamkar ba Gogel fine girl din nan ba, duk ta tsofe, ta sakar masa jiki, shi ya tsotseta da daddare, dansa ya yini yana tsotsarta, duk kuma abin da zata ci sai anraba musu da unborn, in and out suke lasar ta, ba dole ta fita a hayyacinta ba".

"Sai ikon Allah, ke da karatu, sai ya gama tsofar da ke, kin daina burge shi, kiga ya dallo sabuwar yarinya, da ilimi ya gogar da ita, tunda kullum yana ganin yan mata sabbin 'kyan 'kyasa".

Hankali Sa'a ba karamin tashi ya yi ba, saboda yadda ta gasgata maganganunsu, mussaman da tasan kullum a cikin ganin tsala tsalan yan matan Jami'a ya ke.

A sanyaye tace "ya zanyi ne? ni kaina ban shirya haihuwa yanzu ba, sannan kuma shine yaki yarda! da nace sai dai a cire"

Dukkansu dariya suka sa mata, sai da suka tsagaita da dariyar! sannan suka ce, mai
yasa da kika yi arbain, ba ki je asibiti an dora ki akan maganin tsarin iyali ba?"

Kafin ta amsa, sun zarce da fadin " kar ki sake yin ganganci irin haka, idan kuma kin ki ji, ba Kya ki gani ba".

"Tuwo Inna ta yi mana zaku ci ko na dafa muku indomie?"

Shiru suka yi tamkar basu ji ba, sai can kuma Safina tace "Ni kam bana cin tuwo".

Halima bata dago ba, tace yi Indomie din kawai, amma plz kisa mana pepper sosai".

Haka ta dafa musu indomie da ta ji albasa da attaruhu, ta hada musu lemon Tang a jug ta fasa kankara ta jefa a ciki.

Sai da suka ci, suka gyatse, suka yi la'asar sannan suka tafi bayan sun jefa mata wasiwasi a zuciyar ta.

Daf da maghrib ya dawo gida, a gurguje yayi wanka ya tafi masallaci, sai da ya dawo, ya dauko musu abincin, suna ci, ya lura Sa'adah ba ta da walwala sosai, ya tambayi ko bata jin dadi ne! ta ce kalau take, ta isar da sakon gaisuwar Inna, da fara'a ya ce "Ina amsawa, ta biyo sawunki kenan? Ina fatan dai kin fa'da mata, bani da alhakin rashin ganin ki a gidansu?"

Kai tsaye ta ce "ko ban fada ba, ai tasan kaine, tunda ka mayar da Ni Akuya".

Maganar ta shige shi, amma sai ya ce ban gane na mayar da ke akuya ba?"

"Eh mana wata biyu da haihuwa ka sake dirka mini wani cikin, ai akuya ce mai hakan".

Ya kalleta soasai ya tabbatar wannan maganar ba daga zuciya da kwakwalwarta ta fito ba, ya kuma tabbatar ba a bakin mahaifiyarta ta ji ba.

Ya numfasa yace " Inna bata yi farincikin ganin ki da cikin ba kenan?"

"Hmm ita da take ta murna wai dama har addu'a take yi mana kar na gado rashin yawan haihuwar su ita da Hajiyar Bichi".

Ya sauke ajiyar zuciya, hankalinsa ya sake tashi, tabbas akwai wacce ta zo take kokarin birkita masa zaman lafiya a gidansa.

A zahiri sai ya murmusa ya ce " Ashe adduar Innace ta sauka akan mu, ba wai akuya na maida ki ba".

Ta tura baki gaba, tana jin ba zata sake yarda ta yi irin wannan gangancin ba a gaba.


A kicin ya ga tray din da aka ci indomie mai dauke da fork guda biyu.

duk yadda akayi wadannan bakin da ta yi ne, suka kitsa mata maganganu, tunda duk boren da ta masa a farko, ai tunanin ta bai bata irin wannan kalamin ba.


Bai sake shan mamaki ba, sai da suka kwanta, ya ji ta ce zasu yi magana, ya ce "Ina jinki".

"Uncle so nake yi nima na cike jamb foam".

Ya ji zuciyar sa ta buga, sai ya danne, cikin dabara dan ya fahimci inda ta dosa.

Ya ce " da kam ina da buri ki yi a wannan shekarar, kafin lokacin da komai zai kammala na samun admission kin yaye Jawad sai ki fara karatun ki, ba wata matsala".

"Yanzu kuma shikenan sai ba zan yi ba?"
Ta fa'da da gatsali.

"Ya sake dannar zuciyarsa ya ce " za ki yi mana, amma dai sai next year".

Ta tunzuro sosai ta ce "kenan sai nan da shekaru biyu kake nufi zan fara?"

Ba ja in ja ya ce " eh".

Jin haka ta fara sakin magaganu "Ni wallahi bazan yarda ba, kafin nan da shekaru biyu only God knows mai zaka mayar da Ni".

Ya yi shiru yana ta neman tsarin Allah ya kare zuciyar sa daga sharrin shaidan da fishi.

Jin ya mata shiru ba'kin cikin ta ya karu,ta fashe masa da kuka mai sauti, tana fadin son kansa ya yi yawa, duk 'kawayenta kowa na karatu sai ita kadaice mai zaman banza da kashe wando.

Rukota yayi zuwa jikinsa tana fizgewa, kan dole ya kwantar da ita, yasa hannun sa ya zagayeta.

Ya ce "Duk kawayen na ki fa'da mini me kamar Jawad? fa'da mini mai miji irin naki da yake tsananin son ki".

Ta yi shiru tana jan hanci, sai kuma ta ce "su ai ba'a tauye su ba, ba a rufe su a gida ana shirin tsofar da su ba".

Ya yi shiru, yana nazarin maganganunta, da ya tabbatar kitsa mata aka yi.

Ya sake fadin yanzu zaman aure ne ya zama abin kashe wando da tauyewa a gurinki? duk yadda Allah ya miki ni'ima, kin raina?"

" Kawai ni son kanka ne ya dame ni"

Mai na yi miki na son kai a zamantakewar mu?"

"Gasu nan kala kala, ka sani haihuwa dole, sannan ka rufe ni a gida, kai kuma kullum kana ganin yanmata, wataran sai inji zaka w amarce da mai degree".

"Su Halima sun zo too nan ko?"
Ya fada ba tare da yasan a fili ya fada ba.

"Ba su zo ba".

"Hmmmm! kawai ya fa'da ya fara lalubarta a kokarinsa na son ya kawar da bacin ran dake neman taso masa.
Ai kuwa ta buge hannun sa tana cewa " Dan Allah ka bari, kullum aikin kenan, ka fitine ni da daddare, danka ya tsotse ni da rana, ga kuma wadda yake cikima bai barni ba, so haba da wanne zan ji".

Ai kuwa hakurinsa ya 'kwace ya ce "Duk ma wadda suka zo suka miki famfo, ke kuma kika yarda ina tabbatar miki kidahuma suka mayar da ke, sannan maganar karatun da kike ganin sun tsere miki da shi, su a gidajen iyayen su aka basu damar su yi".

Maganar ta mata ciwo ainun a harzuke ta ce "wato ni iyayena basu bani dama ba kenan?"

"Eh" kawai yace ya tsuke bakin sa, ai kuwa ta kara 'karfin kukanta, tana ta yunkurin tashi amma ya danneta ya'ki bata dama.

Sosai suka yi rikici, saboda ya ki amincewa da ra'ayin ta, na ta yi jamb a wannan shekarar.

Sai dai kan dole ya ajiye nasa fishin, Yana fadin ta yarda da shi, bazai taba juya mata baya ba, ita kanta yake so ba wani abu na kyan surarta ko zurfin ilimi ba.
indai zata biyewa maganganun wasu, ba abin da zata ci ribarsa a rayuwar ta, ko karatun take yi, wasu sai sunce ta 'ki aure da sauran maganganun marasa Da'di.

Sannan ba abin da yake ruguza Jin dadin zamantakewar aure irin ka bawa wasu dama su shigo cikin matsalar gidanka.

Tun a daren suka shirya, ya saukar da ita, daga famfon su Halima.

Haka rayuwar ta cigaba da gungurawa da su,har Allah ya sauki Sa'adah lafiya, ta haifi kyakkawar yarinya mai kama da ita kwabo da kwabo, sai dai yarinyar da lalura ta zo, ko kuka bata yi ba.

Aka ri'ke su a asibiti, ko numfashi sai da oxygen take zuka, kwanata biyu tace ga garinku nan.

fadin irin tashin hankalin da Sa'adah ta shiga ma, bata lokaci ne, domin tunda ta dora ido akan yarinyar nan, sonta ya shigeta fiye da na Jawad.
Ashe mai gajeran kwana ce.

Kan dole ta ha'kura, ba kunya ta karbi Jawad a hannun Inna ta cigaba da shayar da shi ba tare da an ro'ke ta ba.

Mk ya dinga tarairayarta da lallashi, da nuna soyayya har ta warware ta cigaba da jegonta cikin salama.

Da yardarsa da amincewarsa suka je asibiti aka aunata, aka dora ta kan maganin tsarin iyali da ya dace da jininta, duk dan ta samu ta huta ta gyagije, shima ya samu hutawa da ita, da sau'kin gorin da ta ke masa na ya maida ta akuya😃.







*SURAYYA DAHIRU*.
✍🏼✍🏼
25/03.


🌺 *HALIN YAU*! 🌺




•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```

```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________

https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•





*_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._*


*A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*.


*SADAUKARWA GA*
*SADIK ABUBAKAR*.







63/64.




*Shekara daya a gaba*.


Zuwa lokacin shekarun su uku da aure, a shekarar Allah ya yiwa Hajiya Babba rasuwa, a dalilin ciwon siga da ya kamata, ba'a gane da wuri ba, har ya taba kodarta, kwananta uku a asibiti ta rasu! mutuwar da ta gigita dukkan yan gidan su Mk dama wadda yasan Hajiya, barin Hajiyar Bichi da akayi zaman makoki ita tana gadon asibiti.

Kwarai suka shiga alhinin rashinta, sai dai ita mutuwa duk yadda zaka yi, ba zata dawo da mutumin data dauka ba, dole aka ha'kura aka bita da addu'a.

Mafarin dawowar Hajiyar Bichi Kano gaba'daya kenan, kullum ta Allah sai ta yi kukan rashin Hajiya, ko na ido, ko na zuci, karshe sai ta musu addu'a tare da mijinsu, tana fatan itama ta riske su cikin aminci.

Mutuwar Hajiya Babba yasa Hajiyar Bichi ta gane abubuwan da Hajiyar ta kare , mussaman na rashin tasowar fitina a tsakanin yaran, tunda ta kwanta dama, yaran gidan kansu ya fara rabuwa mussaman manyan yaransu mata na 'dakin Hajiya Babba, da suke ganin dama kamar mallake musu uwa Hajiyar Bichi ta yi, kawai Samira a cikinsu bata biye musu to kuma itace karamar su.

Haka Hajiyar Bichi take ta ha'kuri da su tunda dai uwarsu ba abin da bata mata na alheri ba, duk yadda suke 'da'darewa da ita, yi take yi kamar bata gane manufar su ba, Abbas da Akil ne basa bata matsala, ko dan su maza ne?

Su Halima sun sami nasarar samun admission, dan haka ba sosai suke zuwa gidan Sa'adah ba, saboda sun koma new side.
Amma duk ranar da suka sami sararin zuwa gidanta sai Mk ya gane saboda yadda take daukan sabbin dabi'u.


Ranar wata litinin Safina da Halima sunje students affairs na cikin Jami'ar, gun a cike da dalibai kowa na yin abin da yake gabansa.

Suna daga can baya, kamar ance da Safina 'daga kai, sai ta hango Farida Torondi, da Uncle Mk na Sa'adah, da wata da bata ganeta ba.
A hanzarce ta zunguri Halima da hankalinta ke kan waya ta mata nuni da abin da ta gani.

"Munafiki dama ai nasan cin amanar Gogel yake yi, marar mutunci, ba dama aje gidansa ya dinga 'dacin rai da muzurai kenan, banda rashin gaskiya, menene na zargin mutane suna zuga maka matarka, ai dan yasan yana rashin gaskiya a waje ne".

Kafin su kammala, har su Farida sun gama sun fice tare da Mk.

Halima so take su wuce gidan Sa'adah, yayin da Safina tace ita ba zata iya zuwa ko'ina ba tare da taci abinci ba, dan haka suka zarce capteria.

Anan ma suka sake yin tozali da Mk da su Farida suna cin abinci suna hirar su cikin nisha'di.

Suka kewaye su, suka tafi can baya suka zauna, ta inda su Farida baza su gansu ba, yayin da sukuma idonsu na kan duk motsin su, suna daukarwa Sa'adah rahoto.

Halima fadi take "wannan mutumin mugune, ya rufe yar mutane ya hanata fahimtar komai. ashe shi yana nan yana sheke ayarsa"

Safina ta furzar da hucin takaici tace saboda Allah kiga ya hanata karatu, shima daf yake da ya kammala Masters dinsa, (Jami'ar ce ta dauki nauyin karatun nasa). Sannan yana tarayya da mai yin degree a fannin hada magunguna (pharmacy), above all daga rich family ta fito, oh Allah sarki! na tausayawa poor Sa'adah".

"Ka'dan kenan a sharrin namiji" inji Halima da take jin tamkar taje ta rufe su da duka.

Suna zaune suka ga su Mk sun mike, sun fita, a motarsa ya 'debi su, kuma Farida ce ta shiga gaban motar.

Ba'kin ciki ya kamasu da gaske suka ji, suna taya kawarsu kishi, Safina tace "takaici na daya, da bamu samu damar yiwa Gogel bidiyon su ba".

Halima ta amsa da cewa "wlh kuwa basirar yin hakan ba ta zo mana ba"

Daga capteria, basu zame ko ina ba, sai gidan Sa'adah, suka kwashe komai suka fa'da mata, a kokarinsu na tserar da ita daga cin amanar namiji, ita kuma bata gane duk mai zuwa ya fa'da maka abin da zai ruguza farin cikin ka, ba masoyi na hakika bane, mai sonka idan yaga abin da zai tayar maka da hankali! 'Boye maka yake yi mussaman a fannin auratayya tunda dai kowa yasan namiji is entitled to 4 wives, dan angan shi da budurwa matu'kar ba ba'dala suke yi ba Ina ruwan ki?

Kuka ta dinga yi, tana fa'da musu kwanaki biyun nan wulakanci ya ke tata mata, ya tsiri ya yi wanka da magariba ya she'ka kwalliya ya ce mata ya tafi shago, ba zai dawo ba sai after 11.

Suka hada baki wurin cewa "karya yake miki ba wani shago, wurin Farida yake zuwa, yau munga zahiri".

Safina da ta fi Halima kishi tace duk ranar da ya wuce goma na dare bai shigo ba, ki rufe gidanki, ya koma can su kwana tare, ai dan ya ganki sanyi kalau ne ya samu damar yin wani abin"

"Wallahi kisan me kike ciki akan makaranta, baya son ki dinga ganin mai yake yi, shiyasa yake ta miki yawo da hankali akan karatunki, oh mai za'a yi da irin su Mk".

Ita dai banda kuka ba abin da take yi, tana jin wani irin kullutu ya tokare mata wuya da zuciyar ta, ya sababa mata nauyin kirji, da kyar take zuko numfashi.

Haka suka tafi suka barta da kunan rai, suna jaddada mata tasan matakin dauka akan mijinta🤔

Wawiyar kuma ta cika fam! tana jin yau ko yafi gyatumarsa kokari, ba zai yaudare ta da kalamansa na yaudara ba, ya maida ta wata nympho, da sun fara rigima sai yasan yadda ya yi suka kusanci juna shikenan sai ya kashe fa'dan, da zarar ya hau samanta bata sake tuna komai na bacin rai a tsakaninsu.

Ta ci kukanta ta 'koshi bayan tafiyar su, sai ta yi dabarar fara karatun kura'ani dan ta sami sau'kin 'kullutun dake neman fasa mata zuciya da makoshi.

A haka ya dawo ya tarar da ita, ta sami sau'kin bacin ran da ta ke ji.

Kusa da ita ya zauna yana sauraron kira'arta mai dadi, sai da ta kai Aya. sannan ta ajiye kura'anin ta mike tace "sannu da dawowa".

Ya amsa da "yauwa! Na gaji yau dinan sosai, na sha zirga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login